Showing 30001 words to 33000 words out of 175038 words

Chapter 11 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6890

samu kudi.

Washe gari 5pm Driver da katuwar mota ya Parker yace mu fito inji Oga,muka zuba kayanmu a boot Uwaliya munyi Sallama tuni ta tafi wajen aiki,munsha kyau domin duk jaraba sai da na dinka mana Atamfa me kyau ko wacce kalar tata daban,tasha dinki me masifar kyau riga da skert,da mayafi me kyau tare da takalmi me dan tudu me kyau,muka je saloon,sannan akayi mana lalle me arnen kyau har su Ma'eesha akayi komai.
Bayan munyi wanka Meenat ta tsantsara kwalliya tare da dauri me kyau dama ta iya watarana Amare marasa kudi suna kiranta tayi musu kwalliya da daurin gogoro sabo da tana da basira a nan sai ka rantse make up kaje aka yi ma,Haka tayiwa Ma'eesha ma kamar ka sacesu haka suka koma.
Amarya kizo na miki kwalliya kar mijinki ya raina ki yana kallonki a bagidajiya,da kyar na yarda Meenat ta zauna ta fara sheka min kwalliya tare da dauri me masifar kyau,ni kaina ji nayi kamar na lashe kaina sabo da tsananin kyan da nayi,kowa ya kalleni sai ya kara,sai kuwa ga Driver yace mu fito,Maeesha ce ta dinga kai kayanmu Driver ya zuba a boot dama ba wasu masu yawa bane,muka yafa gyalenmu kamar yan mata zamu party,Hips dina kamar zai fado tsabar tudu da fadinsa a skert, muna fitowa Driver sai wani girmamani yake,muka shiga mota nace Baba zaka kaimu makwafta muyi musu sallama,samun waje ga baki ga hanci amma haka nace Driver ya dinga kaimu gida gidan da muke mutunci sosai harda Nawwara mukayi musu Sallama cewar zamu dawo sai mu basu address na gidan mijina.sai kallo da gulma anga uwar motar da muke ciki makwafta ma sai an kaimu a mota,wasu suka ce Allah ne yasan manufar Jaki shi yasa bai Yoshi da kaho ba.
Bayan mun gama nace wa Driver muje ya kaimu gidan mun gama,ya fige mu muna dan kamshinmu har gidan Aayan dama na rigada na San gidan,Driver na parking muka ga wasu sunzo sun dauki kayanmu tare da shigar mana dashi ciki suka fito tare da cewa Oga yana ciki Ku shiga yace.

A raina nace ai ko bai ce ba zamu shiga kunji fa,muna zuwa kofa na danna Door bell ya bude muka shiga sanyi da kamshi ya ratsamu,yana jikin kofar ya bimu da kallon mamaki yanda yaga munsha kyau kamar yayan Larabawa zasu je Party musamman ni ba a magana,a ransa yace ashe dai suna da kyau,sai kuma a fili ya tabe baki yace kuje ciki mana kun zura min Ido,a hankali muka shiga tare da Zama a saman kujera,yana zuwa yace ba a Zama min a kujera,ya kalli Ma'eesha yace wannan ce kadai zata dinga Zama a kujera amma Ku banda Ku,shuru mukayi muka ji ya kuma cewa Bedroom guda daya gashi nan shi zaku dinga Zama bana so ana fitowa Palo ana takura min,bana son Surutu a gidana,akwai komai a kitchen na girki,dan ma bana so a bata min gida da hayaki ne amma da itace zan siyo muku yanda kuka saba kuyi girki dashi a Compound amma kunci Sa'a zaku iya amfani da Gas,wani dadi da murna ya kamani zan dinga dafa mana kayan dadi dama nasan gidan nan akwai harkar dadi.

Je ki duba kitchen abinda babu ki dawo ki fada min,da sauri na Mike ko kunya irin zan ga harkar dadi,ina shiga na tsaya turus ganin buhun dawa,gero,masara,wake,shinkafa yar hausa harda ta tuwo fara, sai maggi kala biyu Rak fari ajino motor da star,harda kanwa,Flower,kukar miya etc duk dai wani abu na cimar talaka futuk shine cikin kitchen,haka kayan cin abinci ma komai ya siyo na roba kar mu taba masa nasa na glass,komai irin cimar mu ta talaka ya kawo,haka fridge ba komai a ciki ko ruwan roba wai musha na pampo alhalin ko a gida pure water muke Sha duk talaucinmi.

Jiki a sanyaye na fito cike da jin haushinsa,nace Meenat kuje Bedroom,ba tare da nace komai ba na zauna a kasa tunda yace kar wacce ta hau masa Kujera,ko kallo na baiyi ba yana ta kallon News abinsa,nima ina kallo ne kawai don bana jin me suke cewa sai dai dai nake tsinta,sai satar kallonsa nake yana ta Shan juice lafiyayye da gani zaiyi dadi,yasha rabin kwalin sai naga ya ajiye glass cup din ya Mike tare da haurawa samansa,sai da na tabbatar ya shiga sannan na daga kwalin na kafa a baki na tare da shanyewa du na lashe bakina sai na fada kitchen na ebo ruwa a tap nazo na dura a cikin kwalin dai dai yanda ya bar lemonsa na maida cup din tare da dawowa kamar da na zauna na wani langabe kai irin Allah sarki din nan.

Kamar jira yake sai gashi ya fito sanye da shadda yar gaske yana sheka kamshi da alama fita?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? zaiyi,yana zuwa sai aka yi sa'a ya bude kwalin lemon da niyyar ya tsiyaya yasha Sam bai zata nice zan yi haka ba,yaga maimakon yaga lemo sai yaga ruwa na tsiyayowa da sauri ya jefar da kwalin tare da yin gefe ya firgita ko Aljanune,tunani ya shiga sai ko ya kalli bakin kwalin ya hango jambaki na a jikin abun,nan take ya gano nice na shanye na zuba masa ruwa,ni kuwa tuni na Mike tsaye cikina ya Duri ruwa jikina ya fara bari,yasan guduwa zanyi don yaga har na tattare skert sai naga kawai yayi hanyar fita waje,nan na sauke ajiyar zuciya,ashe Duk bedrooms da kitchen tare da sauran kofofi ya kulle ta yanda bazan iya guduwa ba, tuni Idona ya kawo Ruwa nasan yau sai dai gawata,saman 3 seater ya koma ya zauna tare da nutsewa a ciki yayi dai dai cike da isa yace zo,nace ni?yace no ni,da sauri na karasa tare da durkusawa a gabansa yace bude bakinki na gani,ba shiri na bude ya kuwa ganshi wani fes dashi,ruwan dana dura a kwalin ya dauko ya fara dure min shi a baki ina kwat kwat har ya kare ,jefar da kwalin yayi tare da barin gidan gaba daya.

Yana fita nace su Meenat su fito mu shiga kitchen,kayan abincinmu na talakawa muka shirya a store sannan na ebo dawa muka gyara ta na wanke na shanya ta a kwandon ta bushe,haka masara ma,na ebi gero cup 4 na jika shi zan kai markade sabo da kokon safe,waken da zan soya mana kosai ma haka na ebo komai dai muka gyara komai abinmu,Na fito wajen masu gadi nace dan Allah a ina za a kai min nika da Markade? Wani cikinsu yace Hajiya unguwar masu kudi irin wannan sai ansha tafiya me nisa,nace ni dai a gwada min,ai ko ya gwada min,nasa Meenat ta dauki Dawa a cikin Leda Viva,nima na dauki masara duk sun kai kwano uku uku,sai geron dana jika na Koko a cikin dan botiki dan kadan Ma'eesha ta dauka,muka fito tare da tafiya me uban nisa muna tambaya har sai da muka bar layin sannan muka samu gidan wata mata me Markade wani namiji kuma da injinan nika,na bada kudi nan take akayi mana komai da komai muka dawo gidan tare da tankade garin muka adana abinmu,Nasa hijab na kara fita yan su Curry da sauran abubuwan girki na bada kudi na siyo mana harda su kayan kamshi,kayan hada lemo,da zobo da sauransu,ina dawowa a gate na bawa gate man kudin pure water nace ya siyo mana manyan Leda biyar mu dinga Shan abinmu, na dawo su Kubewa bushashiya na bawa su Meenat dama akwai turmi dan karami a kitchen din suka daka mana muka tankade da yawa duk sai da muka shirya kayan abincinmu komai na marasa karfi na shirya kitchen tsaf muka gyara shi tas,pure water kuma na shirya wasu a fridge wasu kuma a can gefe na ajiye idan mun shanye sai mu dinga zubawa ciki,a hakan ma sai murna mukeyi abinci available zamu ci mu koshi a kan lokaci ba sauran wahala da babu kaza babu kaza,shi abinci ko garau garau ne kake ci in dai ba yankewa kuma akan lokaci to Shar za a ganka.
Bare har da su shinkafa ga ta tuwo ma,mangyada manja ai shike nan mu,shi yasa dana fita ma sabo da yau jira nake Allah ya kawo Aayan da dare na nuna masa cewar ina da zuciya.
Shi ko Aayan jira yake yazo gidanmu da wuri yaga wanne girki zamu kwaba tunda yasan ko kayan miya bai ce asiyo mana ba,ba nama bare kifi bai San na siyo mana kayan miya harda naman rago na Dari uku tare da danyar Kubewa zamu zabga girki.

Meenat tace sis mu wlh ai indai zamu dinga samun wannan ai Alhmdllh a gida ina muke samun haka kullum sai dai fa muyi girki tazarce,Nace Ku canja kaya kuzo muyi sauri mu kara gyara gidan nan sabo da idan yaga dirty daya to jaraba zai mana,nan take muka kara gyara gidan ya dau kamshi,ni kuwa ina kitchen sai girki nakeyi kamshi na tashi,Magrib nayi mukayi Sallah lokacin na gama miya tuwon danyar shinkafar nake karasawa,ina gamawa mukayi wanka da Sallar Isha tare da canja kaya marasa nauyi, Ma'eesha tasha 3qtr dinta dan me kyau da nake siya musu tare da yar vest na sa mata, Meenat kuma riga da skert tasa suma English wears na gwanjo amma masu kyau kalar yan gayu, ni kuwa doguwar rigar material nasa fitted nayi kyau amma ba kwalliya a fuskata.

A katon wani tire na roba na zubo mana miyar Kubewa danya da naman mu kowa yanka uku,Sai tuwon a leda har guda hudu manya,ga pure water shima na zubo a wata roba kalar ta Almajirai duk cikin kayan da Aayan yace a ciki zamu dinga cin abinci ne.
Na dakko mana komai muka zauna tsakiyar center Carpet na tattare rigata zuwa wajen hips gaba daya cinyata a waje take fara sal da Ita mul mul da su,Meenat ta fara dariya wai Sis ke baza ki taba cin abinci a hankali ba kuma sai rufe dankwali kin wani kwaye cinya jiba ana hango short wandonki,to mu da waye a cikin gidan daga ni sai ku,zamu fara ci kenan muka ji karar bude kofa kamshinsa ne yasa muka san shine ya shigo,Sallama yayi muka amsa na fara basu abinci a baki,tsabar sa ido shine yazo ya wani baje saman 3seater yana kallonmu a nutse,yanda yaga na kwaye cinya dankwali yayi kasa duk sabo da abinci,Maeesha tace Sis ki san masa abincin mana nayi banza da ita muna cin abinmu,ni na manta ma yana wajen Sam ina ci har cinyata nake dana da duka sabo da dadin girkin,idan na ci Loma daya sai na sosa kunne sai soshe soshe nakeyi kamar me kwarkwata ko cutar karzuwa sabo da ni idan da abinci a gabana mantawa nake da uban kowa,Meenat su Kansu dariya sukeyi tace sis ya dai wai abincin nan ko yafi Nama dadi ne,Ina lashe hannu tare da tsotse yatsu na ina tande baki nace ke Wannan gonar da aka shuka kubewar nan daban ce maybe kasar kalarta daban kinji har zaki zaki haka,wajen mutumin nan zan dinga siyowa,suka sheke da dariya shi dai Na'im yana kallo ina ta side plate din,Maeesha tace Sis ki kyale kwanon haka mana nace baki San ba kyau cin abinci ba tare da an side kwano ba ai sai Abar albarkar abincin a kwanon.

Aayan yana kwance yana ta faman kallon ikon Allah cike da alajabin abin nawa,muna gama nace muje a wanke hannu Muzo asha karatu,yana zaune yaga na Mike ina uban nishi tare da jansu muka je muka wanke hannu da baki sai ko muka kwaso jakan makarantarsu muka dawo palon kusa da shi yana kwance kai ka rantse nice shugaban masu ilmin boko na duniya yanda na faffake ina bude littatafai,Aayan yana jira yaji yanda zan fara koyawa kannena karatu.

Ga mamakinsa sai yaji Meenat ta bude wani English book tace fada min words din jiya naji,Bai san sanda ya bude baki ba wanda bamu San ma yana yi ba,Na fara cewa Singular and plural,Abu me guda daya da abu me biyu,Examples like Mango-Mangoes,Orange-Oranges,Bag-Bags,Lady-Ladies ina fada ina rubutawa a littafi har na gama,Maimakon nasa Ladies sai nasa Ladys nan take Ma'eesha yar karama taci gyarana tare da kwace biro tace sau nawa za ace miki haka ake rubutawa ladies wai yau kusan wata daya kenan kullum sai kin manta,Meenat tace to Saura mu fara present tense and past tense amma yanzu a koma baya muji,mene Noun? Nace Noun? Noun... to ....Noun.. dai shi sai na fada tunani tare da kallon sama kamar a nan zan samo amsa,nace to shi dai Noun... shine dai,nan take Aayan bai San sanda ya kwashe da dariya ba sai da muka kalle shi yanda dariya ke masa mugun kyau,Meenat tace Sis what is a Noun? Shine dai me? Na kara kallon sama tare da zura biro a bakina nace shi dai Noun is a name of....of.....yawwa shi dai Noun is a Name of Yawwa uhmmm....yes Animal dabbobi irin su Damusa, Kunkuru,zaki,kuma dai shi dai Noun is a Name of place like harda yanga irin na gano gaskiya harda daga yatsa kamar malama na kwalla da karfi nace like capital city of Nageria Abuja,na kara karfin muryata nace also kasar Masar,na daga kai sama nace yes Habasha,idan muka dawo gida Nigeria zan iya ce muku Rimin Gado,Kura,Kasuwar Rimi,yan Kura and also kofar wambai market,Aayan Dariya ta mugun kamashi duk uban labarin nan wai a Noun akeyinsa.

Meenat tace yes muna jinki sis,Nace kuma dai shi Noun is a Name of person na saki murmushi irin shegiyar nan nace like ni Mufeeda,Ammah Allah yaji kanta duk da ta riga mu gidan gaskiya amma zan sa da sunanta Fatima,Abba wanda ya arce,Maeesha kema kina cikin Noun,Meenat ma ta shiga ciki,Aayan ma gashi nan a kwance,Maeesha suka sheke da dariya, nace ah to dana fadi wasu banza na waje ai gwara na gida.

Na kara daga murya kamar me koyar wa a class nace Kai Noun shege ne wato shi ya hada komai harda Things kinga Bag,pencil,biro,spoon duk suna karkashin Noun.Meenat suka dinga dariya sosai suka ce kinyi dai dai amma labarin ai yayi yawa,nace wai me yasa Noun bai hado da abinci masu dadi a ciki ba aikin banza,ai kamata yayi ace akwai su Hen,su Ram,kabewar miya,Danwake,Taliya,Apple.
Aayan yana ta boye dariyarsa,Ma'eesha tace Saura Verb, nace Verb gaskiya ita bata dadi is an action word or a doing work, ni Verb bata birgeni sam,kamar yanzu munyi aiki yawwa Cooking,jumping,running,washing,kuji wani iskanci wai harda kallo watching ace yana cikin aiki,eating ma ai ba aiki bane amma a ce harda shi ciki,haka dai suka dinga tambayata ina bada amsa amma sai nayi dogon bayani da Hausa na cinye lokaci.
Ma'eesha tace daga yau an daina hausa sis duk bayanin da zakiyi sai dai kiyi mana da turanci kaf,na zaro Ido tare da cewa dan Allah kuyi hakuri ni dai me zance,Meenat tace wlh ba hausa gobe ki shirya naga Alama indai ba haka ba baza ki iya ba.

Sabon karatu sukayi min present tense an past tense,sannan sukayi nasu na manyan kwari tare da assignment ina kallonsu,sai kuma muka koma Islamiyya,anan kuwa nasan komai Qur'ani suke kara min da wasu littafan amma duk na iya tunda na iya karanta larabci da rubutu kuma ni nafi kokari a fannin Arabic sosai ko Aayan ya sheda daga jin yanda nake karatu ina cin gyaran su Meenat.har muka gama abinmu sannan Ma'eesha ta mayar da komai Bedroom ta dawo still Aayan yana kwance abinsa yana danna waya, nace su tashi muje su kwanta bai kula mu ba muma haka,amma yayi mamakin ganin yanda muka yi girki lafiyayye haka gamu yara kuma yasan fita nayi na siyo wasu abun amma abincin ya birgeshi sabo da shi yafi son abincin zallan hausawa fiye dana turawa.

Sai da ya dade sannan muka ji karar mota tare da bude gate wato mu kadai zamu dinga kwana a gidan,munyi addua na kara yi na tofa mana baki daya muka haye saman lafiyayyen bed din da bamu taba ganin irinsa ba muka fara bacci sosai,can cikin dare wurin 12:30 naji motoci sun shigowa gidan na farka tare da mikewa na daga labile na leka ta window Aayan na hango da ledojin take away dinsa a hannu ya dawo.A zuciyata nace dama yana kwana a nan? Na tabe baki tare da komawa na kwanta,shi kuwa yana shigowa sama ya haura yaci kayan dadinsa ya fesa wanka tare da shirin bacci yayi addua ya kwanta sai bacci.

Washe gari na tashe su mukayi sallar asubah tare da azkhar sannan nayi wanka suma suka yi tare da shirin makaranta ni kuma nasa kaya Atamfa riga da skert me kyau harda shafa powder tare da lipgloss,wake na gyara da sauri na fice tun gari baiyi wani haske ba na taka har inda ake markade sabo da Blender bata yin laushi yanda ake so,dan markade kadan nayi na dawo da sauri na daura ruwan dama Koko,sai na fara soya kosai yasha kayan miya kamshi ka rantse wani nama ake soyawa,Aayan yana jin motsinmu tare da kamshi yana tunanin wai ina muke samun abun girki me kamshin dadi haka, ruwa na tafasa na dama Koko me dadi da lfy,na ebi nawa a cup ina cin kosai ina kora Koko Malam,Meenat ma suka shigo sanye da uniform dinsu na zuba musu suka ebi kosai a plate da sugar suka fito Palo suna Shan abinsu,sai ga Aayan ya fito sanye da Jallabiya fara,suka ce ina kwana ya amsa ba yabo ba fallasa da lfy Alhmdllh,Ya kalli abinda suke ta ci bilhakki da gaskiya ganin yana kallonsu Ma'eesha tace Yaya gashi in zaka ci,baki ya tabe tare da cewa ban iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login