Showing 21001 words to 24000 words out of 175038 words

Chapter 8 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6891

da dalili,ki nutsu Rayuwar gidanmu da zaki shiga daban take,da kanki zaki gane me yasa na aureki idan kin shiga gidan,bazan cuceki ba karki sa rai ina sonki, ko zan faranta miki,ko zaki ji dadi no Kasuwanci ne deal ne,zan biya ki kudin da zaki kula da yan uwanki kuji dadin duniya tare da Ummanki zan biya mata kudin hospital da komai,ko mene kike so a duniya zan baki,ni kuma zaki aureni ki zauna cikin kunci dan baza ki so Zama dani ba baza kiji dadi ko da minti daya ba,sannan ga matsalar family na sai kinbi a sannu zaki gane matsalarsu ko kiyi Nasara a Kansu ko suyi a taki wannan ya rage naki,ko da ace ina Sonki na aureki to fa ni bana haihuwa, kuma an auna lafiya nake amma nayi aure har sau Uku ban taba yiwa wata ciki ba,ba asibitin da banje ba,sannan zaki ji ance ina da Hawan jini ina da Diabetes wannan karya ne lafiya kalau Alhmdllh kawai fada nayi dan na samu sauki wajen family ta wani ban garen,bance ki dagawa kowa kafa ba a dangina sabo da ni kike aure ba su ba,amma banda rashin kunya karki soma raina min yan Uwa thts all,idan kin kiyaye zaki samu kudi da jin dadi,sauran yaki ya rage naki,ni dai ina da manufata da burina na aurenki wanda a yau zaki fara ganin daya.lets go,bana bukatar kiyi wani abu dan ki faranta min rai sabo da na tsani mata kaf banda uwata yayi gaba abinsa.

Ni ko a raina ban dauka serious ba tunda bani da wayo yarinya ce ni ga karancin ilmi,ai sai nace tunda zan samu kudin kula dasu Meenat da lafiyar Ammah kawai a daura banyi tunanin komai ba,duk na rude har na matsu a daura domin a mayar da Ammah a dinketa ta samu Lfy burina kenan,abinda ban sani ba tuni ma har anyi aikin an gama komai Ashe wayo suka yi mini dan ba yarda da wuri.
Gidan make up ya kaini da kansa yace na shiga ina shiga naga ana ta karramani Ashe sun San da zuwana,nan fa aka gyara min gashi da kwalliya yar sama sama,na fito shi kanshi saida ya kalleni ya kara kallona,amma sai ya tabe baki na shiga yaja muka tafi sai gidansu dake GRA,a cikin motar yace karki tunanin auren zan sakeki da wuri tunda kema dan kudi kikayi ni aurena ba saki sai da dalili,ni kuwa kudi nake nema dama kawai nace karka damu ni ma dan kudi nayi ai kasuwanci ne kawai nima idan kudin sun isheni zan nemi saki sabo da na auri wanda nake so ni insha'allah kamar yanda nake yar sunna sai nayi auren so da kauna na sunna.

Baki ya tabe ba tare da yace komai ba har muka shiga cikin gidan kafin na fito yace kiyi kamar muna son juna a gaban iya Family na,kudi da Ammah kawai nake hangowa nace to an gama, fitowa yayi nima na fito muka jera kamar masoyann gaske abin birgewa muna tafiya can wani part sai ga yan matan nan da samari birjiki muna hangosu kowa da abinda yakeyi na nishadi,a hankali yace action nan take na tuno kudi da Ammah ta kawai na kakalo murmushi lafiyayye na saki ina masa wani kallo da kowa zai ce Masoyina ne mun shaku da juna.
A hankali yace Good job Ashe lallai Yarima bincikensa yayi gaskiya kina son kudi,murmushi nayi nace na gaske ma kuwa ai na shaku da kudi a duniya bani da burin da ya wuce kudi,Muna tafiya muna magana tunanin mutane ai duk soyayya ce da kallo kawai ake binmu, muryarsa naji yace karki gaisar da kowa nasan ke village girl ce,nace an gama in dai da kudi baza ka samu matsala dani ba,wani kallo ya min yana yatsina fuska muna tafiya,yan matan nan suna ta mamaki yar iska nan Ya Aayan zai aura tab ai kuwa zata ci duka,nan take kishi ya turnike su zai auri wata ba su ba ga mata kyawawa a gidansu yan Uwa,nan take suka ci Alwashin ganin bayana,dan haka daya a ciki ta taso cike da kishi tace ya Aayan badai kazamar nan zaka aura ba,dama itace kace zaka kawota bayan gamu a gidan ka Zaba mana,kallo ma bata ishe mu ba harda ni ,aiko ta fusata tare da jawo gyalena ke yar matsiyata,na rigada na gama rainasu nan take na fisge mayafina tare da cewa kinci sa'a ina da muhimmin Uzuri banda lokacinku amma da kin San yau kin rike gyale me daraja nayi gaba abina,dan ta kara Jin haushi ma kawai nayi ta maza na rike hannun Aayan a karo na farko,yayi matukar mamaki nan take ya canja fuska,nace Business ne ka bari a gama lfy na fika Sanin dokokinsa muje kawai nima ina da dalilina na yin hakan a sannu zaka gane. mamaki
Ya cika shi a fili yace lallai Yarima yayi bincike me kyau,nace ba karya indai akan kudine shirka da kisa ne kawai bazanyi ba.
Muna wuce wajen yan matan na saki hannunsa ya juyo tare da gasa min harara karki kuma taba min jiki,nace an gama sai da dalili duk cikin kudinka,har muka shiga part din tsohuwar nan wato Hajja,tana takama da isa na durkusa har kasa na gaisa ta tsabar tsufa bata gane nice nazo polio ba,cike da wulakanci ta amshe ni,sai ga wasu dattijawa yan gayu su Hudu mata sun shigo nan ma kaina kasa cike da ladabi har kasa na gaisar dasu suma dai a wulakancen suka amsa,sai ga maza manya su Uku sun shigo ciki har da Abbi duk suna kama da Alama brothers ne,suma haka na gaisa su Abbi ya gane ni murmushin mugunta ya saki ya kalli Aayan tare da cewa karuwar taka zaka aura kenan,lallai bariki tayi dadi,dayan cikin su yace ke bafa ya haihuwa ba lafiyayye bane amma kin bamu mamaki da zaki aureshi to mudai baza mu rufe miki cutarsa ba idan kudi kike nema ma ki shafawa kanki ruwa idan kuma tuna ninki aure na gaskiya to kece a wahale,mamaki ya kamani amma na tuno Ammah kawai nace ina sonsa haka sabo da Allah zan aureshi,Abbi yace a ina danginki suke? dangina na uba suna Maiduguri,na kalli Aayan cike da fara'a nace ai munje da kai rannan kasan ko ina ka basu address suje,ido na kifta masa,mamaki ya kamasu karfa da gaske soyayya muke da Aayan gashi ma yasan dangina.

Yace muje na saukeki a gida ko,Abbi yace no Ku tsaya dole da ita za a tafi gaban iyayenta muka sani ko karya take,nace ba damuwa,muna zaune aka shirya tafiya maiduguri a jirgi abinka da Naira,Manyan mata su biyu su Abbi su Uku sai Aayan da ni kuma,ina kusa dashi babu wanda ke kula kowa,wai abinka da masu kudi sai gani a jirgi ina tsoro dai haka na maze,mintina kadan sai gamu a Maiduguri Allah yasa muna zuwa watarana,nasan ko ina,motoci aka kawo musu yan gaske nayi jagora har gidan su Abbanmu,nanfa yan uwansa Allah sarki suka dinga murna cewar Ammah dani mun girmamasu mun basu hakkinsu za ayi min aure amma su aka barwa komai a matsayin su na dangin uba,haba shi Kanshi Aayan yayi mamakin irin mutunci da karramawa da aka musu duk da cewa ba masu kudi bane amma an mutunta su matuka,matan ne kadai suke ta yatsina fuska suna tabe baki kun san dama mata sunfi maza kasa danne abu.

Nan take abin mamaki sukace a daura Aure domin su Abbi su gama shirya mugunta a kaina.
Dangin Abbana sai da suka tabbatar ina so da yarda ta sannan kawai suka tara mutane a masallaci shi kanshi Aayan baiyi tunanin Abbi zai ce yanzu za a daura ba,shi Sam bai ma kawo nan kusa za a daura auren ba,nan take dana sani da nadama suka lullubeshi.

Nima haka har kuka a boye yar yarinya dani yanzu na shiga 17yrs ace za ayi min aure,tunowa nayi Ammah na can rai a hannun Allah,ina zaune naji ana guda kamar wasa wai an daura Sadaki Dubu Dari Uku,ina jin yanda nayi tsada a sadaki na sai gashi ina murna naji kudi domin ni in dai kudi ne an gama kawai,har wani yanga na fara yi daga jin sadakina Dubu Dari uku,Aayan kamar ance an masa mutuwa ya kasa boye fushinsa,nan na karbi Numbers na dangin mu na basu tawa muka musu Sallama zamu dawo Kano,har kudi na dan basu kadan cikin na sadakina da kyar ma suka karba domin Aayan ya basu kudi masu yawa.

Bamu zarce ko ina ba sai kano a jirgi,muna sauka sai kauyen Rimin Gado dangin Ammah mun samu kadan daga ciki na nuna musu kaf dangina an karbemu a mutunce sai dai nace Ammah tace a gaishesu bata da lafiya ne,kamar yanda na fadawa Dangin Abba, sunji ba dadi har wasu sunce zasu zo dubata.
Sharp sharp muka gama komai suma sunsha kudi wajen Aayan amma kowa yasan wannan Ango bashi da fara'a kamar ba auren so ba haka muke dashi sosai yake fushi a fili.

Su Abbi sai kus kus sukeyi ana shirya mugunta.
A ranar muka dawo cikin garin Kano bani da burin da ya wuce naje naga Ammah ta samu sauki,daga ni sai Aayan a mota,yana Driving, cike da zumudi nace kayi waya naji an gama aikin tunda na yarda an daura auren,kallo na yayi a matukar hasale yace an dade da Gama mata aiki tuni anyi komai je ki gani,a hospital din ya saukeni ya figi motarsa ya barni tsaye baki bude da jakata a rataye,nace oho dai ni tunda zan samu kudi shike nan,ya kaga Ammah ta samu Lfy?gashi nayi auren da take buri nayi,na cikawa Ammah burinta gashi nayi auren da takeso,da sauri na shiga dakin da su Ma'eesha ke ciki special room aka bamu sabo da Naira.

Ina shiga gabana yaba da dum ganin su Meenat suna Rusa uban kuka,ga mutum nan a lullube da alama gawa ce,lokacin dare yayi jakata na jefar a kasa a tsorace na karasa tare da bude gawar Innalillahi na maimaita domin Ammah ce tabbas ta rasu.
Zubewa nayi kasa sumammiyya,nan likita suka shigo aka mai Dani gadon tare da rufuwa a kaina da kyar na farfado ina uban gunjin kuka,sai hakuri ake bamu su Meenat suna rungume a jikina,kwana mukayi kuka ni tunanina laifin Aayan ne mugu su suka kashe min Ammah ta gashi ya zalunceni na yarda an daura min Aure dashi amma sunyi ganganci da Rayuwar Ammah ta rasu wayyo Allah,yau ina Algus da nakeyi sabo da maganin Ammah duk sabo da kar ta mutu tasha wahala nake tsoro,kullum yawon neman Kudi na tsallake risk da dama don kawai na samo kudin magani.

Ba tare da Sanin uwata ba naje nayi auren kasuwanci don sabo da kar ta mutu ayi mata magani ta warke,nayi duk abinda zanyi amma kash baiyi amfani ba,sai ma gani nake ina zargin kaina cewar da hannuna na kashe Ammah domin nice na damu sai an mata aiki duk da cewa an fada mana cewar aiki biyu za ayi mata da na kafafu sai kuma wani a cikin Mahaifarta shine me matsalar ba lallai ta tashi ba,amma na dage sai anyi gani nake zata warke,dana sani da nadama nake ta faman yi,Ammah na zaune lfy na damu gashi ashe ta hanyar aikin da kudin da komai amma sai lokacin ta rasu,burina bai cika ba domin bani da burin da ya wuce nayi kudi Ammah taji dadin duniya tare da kannena sannan nayi aure Ammah taga mijina da jikokinta amma kash babu ko daya da ta gani domin wannan auren ma na Kasuwanci ne.
Iya karfina na kwalla kara da ihu,kowa sai ya tausaya mana,kuka muke ba ji ba gani tare da tumami harda birgima tare da shure shure abin sai wanda ya gani,sai da muka kwana cir muna abu daya,gari ya waye ma muka daura. lokacin akace Muzo mu nemo yan uwanmu maza a dauki gawa.
Nan take nayi waya dangin Ammah kaf da Dangin Abbah da sauran makwafta da abokan arziki tuni zancen ya watsu Ammah ta rasu,Allah ya taimakeni dangin uba na ne suka daura min Aure,haka dangin uwata da saninsu.h ar mamakin auren nakeyi sabo da kudi wai nan a rana daya anyi an gama komai gaskiya kudi sunyi a rayuwa.









AsmaBaffa
[1/3, 11:17 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA






21-25






Official






By
AsmaBaffa







CHOICE ths page is for u...=?
?d'

ASYCOOL ina kika boye ne?



Fans masu sharhi ta ko ina ina matukar Godiya da kulawa ina jin dadi yanda kuke kokarin yin Sharhi abin ba a cewa komai sai godiya Masoya ta ko ina,Allah ya bar zumunci ya biya muku bukatunku na alkhairi,tsakanina daku sai godiya,insha'Allah kowacce da page dinta masu sharhi,shine farin cikina da zan baku na yanda kuke sharhi.loves u all.=?
?=??=?
?=??d'd'









Gaskiya duk Wanda ya San Ammah mutuniyar kirki ya girgiza da mutuwar nan,nan take asibitin ya samu halartar dangin Ammah maza da mata da yake mutuwa ce har sunzo mana.da taimakonsu aka bamu gawar muka tafi da ita dan gidanmu na talauci,nan fa dangin Abba ma na Maiduguri sun samu Damar zuwa da yawa,ga yan unguwa harda kawata Nawwara,su Shehu me waya sune kan gaba,Adamu Kansila ma yazo haka aka hada gawa tare da sallatarta aka kaita gidanta na gaskiya,Kuka mukeyi sosai musamman ni da Meenat,Maeesha ba hankali sosai Sam bata ma damu ba sosai har ta daina kukan,mu kuwa sai nasiha ake mana da Wa'azi ana bamu hakuri, washe gari kuwa da safe ana ta kawo mana abinci daga makwafta,ga wani dangin Ammah sun dafa,

Ma'eesha tasha baccinta ta tashi ba hankali ta fara bude abincin iri iri sai ta rufe ta dawo gefe na tare da nuna min da yatsanta tana Sis ni wancan nake so cike da shagwaba tace ni me tiririn can nake so,saida ta bawa mutane dariya,da rana kuwa tana cin tuwon shinkafa tace Sis wai kamar ana biki? Muci tuwon mu musha Kokonmu Ammah ta tafi Rimin Gado kafin ta dawo. haka muke ta amsar gaisuwa,har akayi sadakar uku dangin nesa duk wasu sun tafi sai iya na Ammah mata da wasu mazan su uku wanda suke uba daya da Ammah,makwafta suna kawo mana abinci iri iri kullum,da kudin sadakina nake yin komai na kashe kudi sosai domin mutuwa yanzu kamar biki haka take,Meenat sunji ana ta ce min Amarya Allah sarki jiya aka daura mata aure sabo da har yan unguwar mu sun San anyi auren domin munzo da Aayan tare dasu Abbi sunga gidanmu na asali da muke rayuwa,haka kuma na hada su da wasu manyan dake makwaftan mu tunda mu bamu da yan Uwa a cikin kano sai abokan arziki,gashi Ammah na asibiti kuma Bai dace ace anyi aure ba wasu shedu ba babu Sanin mutane ai babu dadi a ganina bai dace ba,shi yasa nace dole Muzo sharp sharp su gani su San inda muke da zama duk da cewa dangin Aayan sun min kallon wulakanci ganin inda muke da zama har dariya suka yi masa dama sun San ai sai talaka ce zata iya aurensa.

Ni dai ko a jikina tunda kudi zan samu gani nake kudi sune maganin komai,sai gashi tun ba aje ko ina ba an saukar min da Aya,Meenat ce ta jani gefe tace Sis ya naji ana ce miki Amarya?ki Bari baki su tafi zan sanar daku komai,da gaske kinyi aure? No ki Bari idan mun nutsu zaki ji.Bayan anyi sadakar Bakwai muna zaune Dangin Ammah suka samu a tsakiya cewar zasu dauki Meenat da Ma'eesha su tafi dasu kauye ni kuma tunda nayi aure na zauna dakin mijina duk da cewa abin ya daure musu kai rashin ganin angon nawa a wajen janaizar Ammah,amma sai nace dasu baya kasar yayi tafiya kasar waje,cikin ladabi nace Ni bance karku tafi dasu ba dama Ku ya dace Ku rike mu,amma sabo da karatunsu kuma kauye ba schl baya ga haka basu saba da rayuwa acan ba,kuma nima zan shiga damuwa na rashinsu ga rashin Ammah me zai hana a bar min su mijina zai rike su ba matsala zai musu komai sai mu zauna tare,Dangin Ammah dama kadan suke jira nan suka fara masifa to ai gaki gasu in dai rikon dadi gareshi,sannu yan Birni Ku yan boko ko to dama dan mu fita hakkinku mukace zamu tafi daku amma tunda haka kuka Zaba shike nan, a cikin matan ma daya tace a'a haba a bisu a hankali ai yara ne ga rashin Uwa sunyi amma har ita Mufeeda kanta nawa take kuruciya ce kawai,nayi mamaki a birni guda amma kamar Mufeeda wai Fatima ta yarda tayi aure tana yar Sha bakwai a shekaru,duba fa yan Birni da sai su kai shekara talatin yarinya na yawo a titi wai karatu take.
Daya cikin maza kanin Ammah yace to Alhmdllh ai mijinta me kudi ne da alama zai iya rikesu da Amana na tabbata amma ya dace ace munje munga gidan mijin naki,gumi ne ya keto min nan take na rude.

Karya na kakalo nace ai ba yanzu zan tare ba,dazu munyi waya dashi jibi zai dawo daga turai sannan zasu sa ranar da zan tare sai na fada muku a waya ko nazo har gida na kawo kati sai kuzo ayi komai da Ku,ganin mijin nawa me kudi ne tunda sun ganshi tare da danginsa ba karya gashi sunsha kyautar kudi kawai sai suka washe baki tare da cewa to Allah ya kaimu ki tabbatar kin yo mana waya,da sauri nace Insha'allah,to yanzu abinci fa da sauransu wa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login