Showing 162001 words to 165000 words out of 175038 words

Chapter 55 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6861

ya gyara Bedroom din sannan ya hau Saman Bed din tare da cewa kwanta Sweetlove ya sata cikin jikinsa suka kwanta ya fara kokarin cire mata yar rigarta,da sauri ta bude idonta cike da muryar kuka tace shike nan tunda kashe ni kake son yi sai ka dauki raina,Murmushi yayi tare da cewa ba abinda zan miki nafi so kawai najiki a jikina ba kaya kiyi hakuri My Meenat,Kai kawai ta daga mishi yana lashe mata hawaye da harshensa,tana shesheka tace ka..ka..kira min Ammah na gaisheta dasu Sisters kwana biyu bamuyi waya ba,Jiya fa ne kawai bakuyi magana ba Babyna amma bari na kira Sis Mufee,Yana Dialing Number din Mufee Aayan ne ya dauka yace tana schl sai anjima zan dakko ta ya akayi? Ameer yace kai ya Aayan wayar ma Tata idan tana schl tana hannunka kamar wani P.A,idan ta dawo kace ta kira Meenat back,ok cewar Aayan ya datse kiran,Ameer kuma ya Kira Ma'eesha wacce yanzu ta dan saba da harkar Yarima da sukeyi tana jin dadi kadan,Suna murza juna Kiran Ameer ya shigo Amma Yarima yace baza a daga yanzu ba sai sun gama tukun zasu kira back,Ammah kadai aka samu a waya sukayi Hira ba tare da ta gane komai ba,suna gamawa Meenat ta makale a jikin Ameer tana masa magana kasa kasa Allah ka bani wahala Honey jiya ko tausayina baka jiba,Am so sorry My love Bazan kara ba kinji yana lallashinta tana shagwaba .

Alhmdllh Daddy ya yaje Dangin Ammah Sati daya aka daura auren Ammah da Daddy ko su Aayan basu sani ba Hajja kawai ya fadawa tana asibiti har yau ba a sallameta ba, ina fitowa daga class an tashi naga Ma'eesha tana daga min hannu ita ta tafi Yarima yazo daukanta,ina daga mata hannu kawai naji an daga ni sama nasan Aayan ne ina jin kamshinsa,ana kallonmu fa zaka Sa ace bani da kunya,thts y nake so ai mu koma Abuja dagani sai ke babu me Sa mana Ido jira nakeyi ku gama zana last Exam ta Neco,Murmushin dake kara min kyai nayi tare da rike Hannunsa nace Muje Mijina,Office dina zamuje ki jirani na gama sai mu wuce gida ko,amma fa kasan bani da wata lfy kasala,ga saurin jin yunwa kuma ina tashin zuciya kaga kuwa akwai Matsala kar nayi maka Amai a Office,ba damuwa muje haka gobe baku da schl asibiti zamu je kar Babyna ya girma ba a fara dura masa kwayoyi ba,biyu da Safe biyu da dare,dariya na farayi shima haka nace kamar kasan yaran yanzu duk yan kwaya ake haifowa,sabo da tun a ciki ake dura musu kwayoyi.
Muna ta hirarmu har ya bude min mota na shiga shima ya shige Driver tare da escort suka ja sai Office katafaren building.

Tun a hanya nace a tsaya a siya min Doya da kwai haka yasa aka siya min,ya kwanto dani jikinsa yana tambayata sai me kike so Babyna?Nace Coconut da Alkubus,Ina zan samo Wani Alkubus ni kiyi hakuri na fadawa Ammah tayi miki idan zamu tafi gida sai mu biya mu karbo,banyi musu ba nace masa to Allah ya kaimu yace Ameen Sweetyna, ina jikinsa muka karasa Office yana signing da Sauran ayyuka ni kuma ina saman Cinyarsa a zaune kamar yarinya karama motsi kadan idan nayi sai yace min ya akayi ina ta ciye ciye na hankali Kwance,Duk abinda nace ina son ci da Sauri yake Bada Umarni lallai a kawo min naci rashin kunyar da yake zubawa kuwa na caring sai dai idan baza ka kallemu ba ka tafi.

Yau kwana Uku da Angwancewar Ameer jinya yakeyi har yau Meenat taki ta daina lango kullum tace bata warke ba ta wani narke zatayi kuka,amma a fagen Romancing itace kan gaba, 9pm Meenat taci uwar kwalliya sanye take cikin English Gown iya rabin cinya light blue and White sai kamshi takeyi gashinta yasha gyaran gaske kamshi ke tashi kawai ta ko ina,palon Angonta Ameer ta nufa tana Tafiya cikin nutsuwa tare da jan Hankali yana Palonsa sai chat yakeyi a waya yana Jin kamshin ta da Sauri ya fita daga WhatsApp din ashe Meenat ta gane me yayi,cikin takunta na kasaita ta karaso inda yake zaune Saman 3seater kafin ta zauna ya jawota jikinsa saman cinyarsa ta zauna yana shafa mata wuyanta da kafadunta ta baya,cikin muryar da ba a san Meenat da ita ba tace Ashe da ka shirya nan ka dawo? Yeah Princess ya furta yana Jan zip din rigarta kasa baya har yayi Zipping dinsa, Bra ya balle mata tare da janye rigar ya jata kasa ta koma kasan cikinta,Dukiyar Fulaninta masu matukar kyau da sheki suka bayyana juyowa tayi gaba daya a jikinsa ta kwanta Saman kirjinsa tare da rungumeshi tana rufe ido wai Kunya,Na shanunta ya shiga wasa dasu tana masa shagwaba,a shagwabe tace Husband ya amsa da Naam cikin dishewar murya,nuna min Chat dinka na WhatsApp na gani,Murmushi yayi tare da cewa gaskiya sai dai kiyi hakuri bazan iya nuna miki ko Contact dina ba, Ni Din?tana kallonsa kamar zatayi kuka,yace to me zaki gani in ba neman rigima ba,ni...Ni...Allah sai ka nuna min,am sorry to say gaskiya bazan iya ba,Fushi tayi a fusace ta kwace jikinta tare da maida Bra da rigarta tana niyyar tashi ga Kwalla na shirin kwararo mata,Ba shiri ya fisgota ta fado jikinsa me laushi da kamshi nan take ya mika mata wayar gashi kalla kuma nima sai naga naki murmushi tayi kyawunta ya kara bayyana ta karba tana me dauke da murmushi a fuskarta ta fara duba Contact,tana tambayarsa kowa taga Number din mace,haka WhatsApp nasa ma sai da ta bincika tas taga babu mace da suke chat,farin ciki ta shiga yi mijinta baya kula wata,Shi kuwa ko duba nata baiyi ba don baya zargin Meenat da komai.da kanta ta ja Hannunsa zuwa Bedroom dinsa sabo da tasan tayi masa laifi wajen danne masa hakki yayi hakuri da ita har ta fara Jin kunyar Ameer din nata,Rigarsa armless ta zare masa a hankali itama sannan ta kashe Light duf duhu ya gauraye dakin sai karar ac da kamshi kawai ke tashi,Bai ma san ta cire kayan ta gaba daya ba sai jinta yayi a jikinsa ta rungumeshi sosai Albarkatun kirjinta suka sashi ya saki ajiyar zuciyar ba tare da ya shirya ba ya dauki Meenat zuwa saman Bed,a nutse cike da wayewa suke gudanar da harkarsu har ya samu abinda yake so ba tare da tasha wahala ba,Gaskiya Ameer karshe ne hakan Meenat ke ayyanawa a ranta tana Jin dadi,bangaren Ameer ma hakan yake ji a ransa tana manne cikin jikinsa suna hira Sama sama har sukayi bacci abinsu.

Kwanci tashi yau Sati Uku kenan da auren Su Ma'eesha Sameera Yar daba taji sauki Sosai ta warke inda ta fitar da Alhajinta me kudi zatayi aure itama ta saduda da al'amarin duniya,an sallami Hajja daga Hospital Ta samu Lfy amma matan su Abbi basu canja ba,su Khaleel ne ma watarana suke dan tarewa Hajja sabo da su Abbi sun koma abin tausayi sun koma rakumi da Akala,Kullum Hajja kuka take sharba musamman idan taga danta Abbi Mustapha yana wanke wanke da shara yayi duhu ya rame,yau kamar kullum matar Abbi Sani ta sashi wankin kayanta sai zufa yake hadawa,Hajja ta fita tana dingisa kafarta da bata gama warkewa ba,tana fada kan ya daina wankin haka ya isa,suna haka sai ga matar ta fito babu bata lokaci ta shiga Zagin Hajja Munafuka,Karuwa sannan ta ture Hajja ta fadi rim again akan kafar data karye nan take kafa ta kara samun matsala dama bata gama warkewa ba aiki ya lalace ya dawo baya,Hajja yau tayi kukan da bata taba yi ba,ba shiri ta fara Allah na tuba ka yafeni,Na jawowa kaina,na cuci kaina da yarana na ruguza farin cikina na tarwatsa kan yarana,Hajja tana ta tuba tana tona asirinta,Khaleel da Mujaheed ne suka hango me ke faruwa da Sauri suka karasa kan Hajja suka sata a mota sai asibiti tare da sanarwa Daddy,Aayan da Ameer abinda ke faruwa,Ameer bakin ciki ya kamashi Key din mota ya dauka kawai Meenat lokacin tana kitchen ya leka da Sauri yace na fita ana kira na Babyna yanzu zan dawo har ya tafi ya dawo da Sauri ya rungume Meenat tare da kissing dinta a lips yace take care of ur self for me Wifedina,same too u Darling banda tukin ganganci kaji mijina,ya fita yana daga mata hannu ta kwalla da karfi am gonna Miss u Sweetheart kar ka bari a kalle min kai,shima da dan karfi yace Already started Missing u SweetMeenat ya fice dauke da murmushi ya manta ma da fushin da yakeyi Meenat ma murmushi take bazawa kawai.

Bai zarce ko ina ba sai gida wajen Su Abbi,yana zuwa a fusace Ameer bai kula kowa ba ya fara shigewa Bedroom din Abbi Mustapha Baban Ameer kenan ya fara watso kayan matar anci sa'a Abbi yana bayi yana wanka,kasan Bed din ya dage katifar sai ga Wata yar tukunya dauke da tarkacen tsafi a ciki tare da ruwan rubutu,Ameer bai jira ba ya fito ya jefota ta saman Bene tukunyar tsafi ta ragargaje,haka ya fita ya shige dakin Matar Abbi tana cikin gyara kaya taga Ameer ya fado da zureriyar Sandarsa tunaninta dukanta zaiyi ko Ya haukace sai ta fita da gudun tsiya,Abbi na ganin haka ya rufa mata baya dama sai abinda tace Kan tace ne kafin tace ya aikata,nan Ameer ya kulle dakin da key ya shiga bincike a dakin ya dinga samo guru,laya,ruwan rubutu,ya duba kasan bed din ba komai cikin pillow ya duba tare da Sa wuka ya tsarge pillow din ta ko ina ya fito da soson da suke ciki sai ga layu iri iri a Cikin pillow an hada dashi an dinke pillow tsab baza ka taba ganewa ba,yanzu mata abinda sukeyi kenan za a kai Amarya kafin a kaita sai an yanka pillow da razor a tura kulunboto sannan a mayar a dinke yanda ba Uban wanda zai gani sai kaga pillow normal ashe da tarkacen tsafi a ciki,miji yana ta kwanciya a kai,wasu har katifa ake yankawa asa sai a Sa zare da allura a dinke ba me ganewa Allah ka shirya mu.

Ameer yana fitowa ya fada dakin Abbin Yara Duk ya fita a hayyacinsa matar ta sashi sai ya goyata ya dinga zaga Bedroom da ita,gata wata me kiba katuwar gaske suna ganin Ameer da shegiyar wuka suka saki ihu ta fisgi Hannun mijinta suka gudu nan ma haka ya dinga kwakwulo kayan tsafi,sabo da Ameer duk irin wannan harkar ta malamai ya santa tunda suna zuwa da Hajja kafin Allah ya shiryeshi sannan Hajja tana sasu suna yin irin wannan abun wajen iyayensu mata,haka ma da Matar Daddy da kuma Matan Aayan duk irin wannan yasan su shi yasa yake da saurin gane irin wannan harkar,a leda ya kwaso komai ya fito dasu yabi ta baya duk ya warware layun sannan ya yayyaga komai da almakashi into pieces ya konesu tas,Sai ga su Abbi nan take sun dawo hayyacinsu,Hajja kawai suke nema da yaransu,Matar Abbi Mustapha kuwa taci duka hannun Abbi kamar jaka wai ta rabashi da Uwarsa,a wajen duk suka rubuta musu saki dai dai na musulunci Ameer da kansa yasa Securities sukayi waje dasu suna kuka tare da nadamar halayensu.

Da su Abbi tare da Sauran Yara suka dunguma zuwa asibiti wurin Hajja da take fadawa su Khaleel ku taimakawa iyayenku da addua su dawo cikin hankalinsu su dawo da iyayenku mata yan albarka masu biyayya,ni na jawo da nace sai sun sake aure,banyi adalci ba ko a baro sai an turani naje har gida na basu hakuri da kaina zanyi bikonsu ko da kafar katako ce,Mufeeda tare da kannenta suma zan nemi gafararsu,Daddy ne ya shigo a birkice nan Hajja ta damki hannunsa tana bashi hakuri tana kuka ka yafe min ni na jawo nice....Hajja na yafe tuntuni ni dama ban rikeki ba kuma aike Mahaifiya ta ce ba komai ya wuce ki bari kiji sauki ko na fitar dake kasar waje?Hajja tana goge Hawaye tana Allah ya maka albarka Ka yafe min dana,na maka abubuwa suna haka sai ga Aayan da Mufee duk ta kara wani fari tayi kiba da kyau Sabo da cikin dake jikinta,Hajja ta shiga bawa Aayan Hakuri da Mufee,Aayan yace shi ya hakura ta ma daina bata bakinta,Su Abbi su Ukun tare da Ameer suka shugo suma nanfa Hajja bata boye ba tace da kanta ta lalata zumuncin yaranta,To Allah yasa su Abbi sunyi Nadama nan suka shiga Yiwa Hajja fada da nasiha sannan sukace duk itace ta cucesu Amma tun da Allah ya ganar dasu sun yafe suma a yafe musu,a asibitin aka shiga yafewa juna anyi wa'azi tare da Nasiha wa juna an tunatar sosai dama wasu Iyayen da kansu suke bata zumuncin yaransu suna raba kan yaransu,a karshe Hajja tace da kanta zata je bikon iyayen su Ameer babu wanda ya kai su Abbi Murna za a dawo musu da matayensu yan kirki

Su Abbi sai gafarar Daddy suke ta faman roka sai lokacin ya fada musu ya auri Ammah kuma a satin nan zata tare a sabon gidansa daya tsantsara na fitar hankali,sun tayashi murna sosai har Abbi Mustapha na tsokanarsa an samu dangin kyau,Hajja kuwa Allura akayi mata anci sa'a ashe bata kara karyewa ba ta dan bugu dai a wajen Amma Dorin bai lalace ba,Aayan sai murna yakeyi shi da Mufee ashe Daddy ya auri Ammah basu sani ba,nan Mufeeda ta fita waje ta kira Meenat da Ma'eesha ta sanar musu Ammah ta auri Daddy ta labarta musu yanda Daddy ya basu labarin har yanda aka daura aure,Sunyi farin ciki Ammah ta samu me kula da ita,Meenat tace Sis kicewa Darling yataho gida haka na gaji da jiransa,Dariya Mufeeda tayi tace idan yazo me zai miki sarkin jaraba Bazan fada masa ba,dan Allah Mufeen Ammah ki fadawa Ameer dina na kira wayarsa a kashe,tana cikin haka sai ga Ameer ya fito, na mika masa waya nace ga Meenat tana magana,da Sauri ya karbi wayar yana murmushi yace Hello...tuba nake ranki ya dade kaina bisa wuya gani nan yanzu ki bani 15mnt Insha'allah ,Meenat sai Kukan shagwaba take masa ita yayi Sauri ya barta ita kadai.

Yarima da Ma'eesha saura 1wk zasu wuce Us sannan suje saudiya za a kwashi Amarci,dama anan ma Yarima baya daga mata kafa ko kadan,itama ta zama irinsa mayyarsa ce bata zuwa ko ina kullum tana gidanta kusa da Mijinta Office ma kusan kullum da ita suke zuwa,yauma 1pm yana Office ya kasa aikata komai kawai matarsa yake so yaji kusa dashi suna ta faman waya Amma bata gamsar dashi gaba daya,sai kawai yasa Driver ya dakko masa abarsa,ta gama shirya abincin da ake kai masa Office kenan tayi wanka tana shiri ya kirata a waya lallai tabi Driver suzo tare,zatayi Musu Yace dama ai ba sona kike ba yana narkewa kamar mace dole ta hakura ta shirya a mutunce tabi Driver tare da basket din Abincinta,tana zuwa yasa key a Office dinsa yace ya tashi daga aiki yau ko uban waye ya dawo gobe ko knocking kar ayi Masa suka shiga Soyewa da abar kaunarsa Ma'eesha itama ta gama gogewa da rashin kunya biye masa takeyi shi yasa yake kara sonta.

Kwanan Hajja Hudu aka sallameta tana dan digishinta haka tasa Driver ya kaita gidajen matayen su Abbi na farko tare da Daddy suka Bada hakuri da kyar suka amince aka sake daura aure tare da tarewa gaba daya,Daddy ya Mayar da Su Abbi kan aikinsu na da,tare da siya musu motoci na alfarma, Su Ameer da Sauran Yara sai murna iyayensu sun dawo Alhmdllh,lokacin kuma bikin Khaleel da Mujaheed,Sajeeda da Haneefa ya matso tunda ansa rana tuni,Saura Meenal,Sabeer da Aliyu nan gaba,gidan yanzu ya Zama gidan masu tarbiya da hankali kowa ya nutsu yasan mene rayuwa ba wulakanta dan Adam ba komai,mutanen unguwar ma yabonsu sukeyi yanzu sosai ana zaman lfy da mutunci da makwafta ba irin da ba,Su Haneefa gayu ya dawo yaci uban na da Amma yanzu na mutunci akeyin shigar mota sai wacce suka ga dama.
Yau Sati guda cif Sunday yaune kuma Ammah ta tattara nata kaf dama an shirya komai kamar wata budurwa,da wasu dattijai yan matasan iyaye kawayenta su Uku tun na tsohuwar unguwarsu tare da yan uwanta guda biyu sune suka kai Ammah dakin mijinta Daddy cikin lafiyayyun motoci guda kusan biyar,Ammah ba a ganeta sam Sabo da Su Mufeeda sun takura an kaita gidan kwalliya anyi mata,ga gyaran jiki ko ina kamshi fata na sheki gashi etc tasha tsumi iri iri abin ba a magana gata dama Ammah matashiyar Uwa me ji da kuruciya dai dai gwargwado tasha kyau an kaita duk an maida kowa gida lfy sai ita kadai a katafaren gidan sai yan aiki masu kaiwa da kawowa ko ina kamshi na tashi.
8pm Daddy ya shigo Bedroom din Ammah tana gefen Bed suna waya da Inna,tana ganinsa tace zan kiraki gobe Insha'allah ta kashe wayar, ta kalli Daddy dauke da lafiyayyen Murmushi yasha farar Shadda sai yau ta hango tsan tsan kuruciyarsa shima hakan dan sai yau ya tabbatar Ammah ta hadu ta ko ina,Gefenta ya zauna da ita suna shakar kamshin juna jikinsa na gugar nata,kunya ta lullube Ammah ta sunkuyar da kai kasa,Daddy irin Aayan ne sai zumudi yakeyi Da kyar ma ya Umarceta sukayi Sallar nafeela suka ci kayan makulashe Ammah da kyar ta karba Daddy yana bata a baki,Suna gamawa suka sake brush tare da wanka kowannensu yayi shirin Bacci suka haura Saman Bed,Ammah kunya take ji ta kasa sakin jiki,yana janta da Hira Amma da kyar take bashi amsa,Daddy cike da kulawa tare da tausasa murya yace Kin san nifa Bature ne kin sani asalin Bature ne mu ba haka muke rayuwarmu ba,ban saba da hakan ba,Mun zama daya ai ke matatace mene ne abin jin kunyata matsalar Hausawa kunya gaban me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login