Showing 129001 words to 132000 words out of 175038 words

Chapter 44 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6880

tace a kawo miki kunun gyada ne,Godiya nayi na karba tare da kaiwa kitchen,Meenat ta kalli Ameer bari na gano Dakinmu Allah sarki nayi missing dinsa,kyaji dashi cewar Ameer, abincinka fa Ameer tun safe baka nema ba,a gidan su Meenat nayi Breakfast fa Anty,nace lallai Ameer dakai ma za a hada baki a gujeni ka kyauta,dariya mukayi gaba daya, nace ban baka labari ba My Man fa ya min kayan lefe baka gansu ba sun hadu,Ameer yace ai Meenat ta bani labarinsu,munafuka har ta fesa maka? Dariya yake yace haba Anty Ba munafunci tayi ba.

Magana nayi ba alamar wasa nace Ameer wai Aayan ya maka mata? Ameer yace ni din? Ban San zancen bama,nace to na rigashi ko yace ya baka mata kace na rigada nayi maka mata ni, Ameer dariya yayi yana tunanin wasa nake,nace wlh ba wasa nake ba,Anty wacece takin da kika Zaba to? Nace Meenat,ido ya zaro tare da cewa a'a gaskiya ai masifa zata ta yi min bakya ganin ta rainani gwara dai naji idan ta Ya Aayan tafi sai na karbeta Amma Meenat kina ganin yanda take iyayi tana ji da kanta,dariya nayi nace to ai kafi Meenat iyayi kai,i dan kuma bata sona fa? Nace a'a kai dai kace kawai Zabin Aayan kake so shine dan uwanka,Ameer yace haba dai ai wlh nafi son zabinki Anty,to ko Meenat dince baka so? Ni na Isa yanda take me kyau haka da tarbiya ai ta fiki kyau ma Anty sai yanzu na gane duk Meenat tafiku kyau,Dariya nayi nace karya kake kuma wannan a wajenka dai zaka ce amma a wajen Aayan nice gaba,haka Yarima kuma Ma'eesha ce,muna Hira sama sama sai ga Meenat ta fito tare da daukan uban wanka,da mamaki na kalleta nace dama kuna da kaya a gidan nan ne? Ina kuma kika samu gown haka? aro nayi cikin na lefenki,nace aiko baki isa ba koma ki cire tun ma kafin Mijina ya dawo ya ganta a jikinki ban masa kwalliya da ita ba,Dariya tayi tace to wasa nake da abata nazo a jaka ko Ya Ameer?yace kwarai yana daga kai da sauri kamar uwarsace na magana.

Gefen Ameer ta zauna tare da masa magana kasa kasa ba a jin me suke cewa sai gani nayi sun Mike wai zamuje mu dawo,nace ina? Ammah ta sani fa gidan kawata, dama ba wajena kuka zo ba ashe,yanzu fa zamu dawo am serious,sai kun dawo to,suna fita sai ga kiran Aayan ya shigo wayata.
Dagawa nayi fuskata dauke da murmushi na rangada Sallama cikin muryar da nasan ina zuke masa numfashi,zaki sa na dawo Sweet Heart,wannan murya me zaki haka ,Ya Office to,Yace alhmdllh,good kace da wuri zaka dawo amma shuru am missing u,Wani sanyi yaji a ransa yace 2pm zan gama just wait for me I wl be thr,Fari nayi da Ido kamar yana kallona nace Allah ya kaimu,me zaka ci? Kin san me nake so just make something delicious for me Baby,alright Insha'allah zanyi,kiss ya sakar min ta waya nima na aika masa,ina kukan shagwabata can kasa kasa nace kaga su meenat sunzo sunyi tafiyarsu yawonsu gidan kawaye dama ba wajena suka zo ba kuma tsoro nake ji Daddy yayi nisa da part dinmu da sai naje wajensa muyi hira. Laifin Ameer ne bari na kirashi sannan ya kashe kamar kar mu rabu,nan take ya kira Ameer yana ta Masifa Lallai su dawo su tayani Zama kafin ya dawo,ko Minti 10 Meenat batayi a gidan kawarta ba ta fito Ameer ya dawo dasu yana bata labarin masifar da Aayan ke yi, suna dawowa na dinga musu dariya, kitchen na shiga na fara shiryawa Mijina abincin da nasan yafi so fiye da ko wanne.

12am cikin dare Hajja ce ta fito direct dakin Mazan gidan ta shiga sabo da wai dole sai ta kama Aliyu da Sabeer,Suna ta bacci gasu nan birjik wasu a shimfida kasa wasu saman katifa,Sabeer yana bacci sai duka yaji a gadon bayansa,yana bude ido yaga Hajja ce sai ya kara shigewa bargo,Hajja ta girgiza shi amma yaki tashi sai ma maganganu da yake wai na mafarki,kan Aliyu ta koma ta fara tashinsa,Aliyu dama ba a tashinsa a bacci magagi ne dashi idan ya farka sai ya rufe mutum da duka kuma a bacci, yana farkawa ya rufe Hajja da duka gashi Namiji hannunsa Zafi ba shiri Hajja ta kwace da kyar ta bar dakin da dan gudunta,Abbi kwana uku kenan yana fita duk inda yasan zai ga Ameer da mutanen da zai tambaya amma babu labarinsa,yauma gwiwa ba kwari ya dawo gida ana Palo a zaune kowa da abinda yakeyi Abbi ya wuce a fusace ta palon ana masa sannu da zuwa ba wanda ya saurara ya kara gaba cikin Bedroom.

Mujaheed ya bude sabuwar Rezarsa yana yanke farcensa tun kafin ya yanke yatsa daya sai ga Meenal tace idan ka gama dan Allah ka bani na yanke wani farce da ya taso min yaki cirewa, Aliyu yace idan kin gama ki bani nima na yanke nawa,Wata uwar Harara Mujaheed ya zabga musu tare da cewa jarabar gida ko Kashi ka taba sai wani yace ka San masa zai taba shima ba tunanin ma cuta ta shige ku ko ina da ita ku kawai a baku.
Yana gama yankewa Sajeeda ta karbe ta gama ta mikawa Aliyu,Aliyu ma ya gama ya bawa Meenal,ta gama ta dan ajiyeta a gefen kujera sai ko yar karama Juwairiya ma ta dauke harda zuwa ta kyasta Ashana ta konata wai ta kashe cutar jiki duk kan rezar ya disashe ba kaifi amma haka ta yanke da kyar.
Khaleel kuwa wanka yakeyi ana ta jiran botiki ya fito ya bayar amma yaki fitowa yan matan duk da daura kirji suna jiran botiki, yana fitowa ya kallesu wai sabulunsa ake jira haka da botiki,sabulun ma duk ya gama narkewa Saura kadan,Ba tambaya ba komai Haneefa ta fisge tare da lakeshi a jikin sosonta,Sabeer ya faki idonta ya fisge har soson nata dama sabulun yana manne jiki bazai fita ba,haka ya shige wankansa yayi da sosonta,Khaleel baki bude yake kallonsu yace wai Ku ina sabulun da aka siya ne shekaran jiya?kowa an bashi nasa fa,sukace to ga wanka ga wankin su Inner wears ya zamuyi duk karewa sukeyi sabo da wanki kasan dai mata ba irin maza bane,kuma wlh gidan nan satar sabulu akeyi da nawa dana Meenal sacewa akayi,Aliyu yana daga Toilet yace nima wlh ina ajiye nawa jiya kafin na je Palo na dawo an dauke kuma Dan masifa ka rasa waye,Abbi ne ya fito tare da cewa wa dauki toothpaste sabo wani karami MyMy a saman gado na? Kowa yace ba shi bane,yace wlh duk Wanda bai fito dashi ba sai na kai sunansa wajen Malami ya mutu kafin safiya,Ko cikinsa ya kumbura dam cikin dare yayi ta tsaga ihu sai ya fito dashi,yan iska barayi,to wlh ban haifi barawo ba,da mu zauna da barawo gwara ya mutu,na gaji da sace sace da akeyi a gidan nan,dan Bala'i ko Guba ce a gidan nan ka ajiye sai an sata,to ko a fito dashi ko gobe wanda ya dauka ya mutu,Dama Juwairiya ce Ashe ta sace bata fi 14yrs ba bata da wayo jin ance mutum zai mutu ko cikinsa ya kumbura sai ta faki Ido ta dakko tace bari na tayaka dubawa Abbi tana shiga dakin ta daga Haukarsa ta sa a ciki,Abbi ya yarda da yarinyar ai yara baza su dauka ba manya ne,tace Abbi ka ganshi kasan hularka idonka ne tsufa ya kamashi,Abbi yace to jeki lallai hankali shi ke gani yarinya,Allah ya taimakesu da yau wani sai ya mutu a gidan nan,yarinya tace Abbi ko yayanka ne?yace kwarai kuwa.

Haka suka dinga layin wanka jikin mudubin dakin matan kowa ke shiga sabo da Vaseline din Meenal duk sun jere a wajen kowa na shafawa mata da maza,Dan Allah Khaleel ka matsa haka duk ka tare wajen sai wani taje suma kakeyi kazama da ita,Khaleel yace da Namu gashin da naku mata waye nasa yafi tsafta mu kullum sai kanmu yaga ruwa,ku fa mata wata ma sai tayi 3wk gashinta bai ga ruwa ba,kazamai shi yasa Bana son mace ta matso min da kanta kusa dani,Kazamai ba cewar Haneefa amma ba irinmu ba,dariya Khaleel yayi sabulu iri daya dai muke wanka hakan ma ni nake baku na wanki,shi dama Khaleel sabo da sabulu ya dade baya siyen na wanka na wanki yake siya yanzu ga araha gashi kato a dade ana wanka.
Da su Sabeer zasu siyo sabulu cikin kudin da suka damfari Hajja Khaleel yace kar a siyo masa sabulun wanka na wanki yake so gaba daya,ai kuwa kowa sabulun wanka daya dana wanki daya amma Khaleel nasa Sabulan wanki har guda Hudu da kudinsa shi yasa yake shanawa da abinsa duk an takura masa da aro.

Washe gari ma sabo na wanki ya fito dashi yayi wankansa,Abbi Sani da Abbin yara duk karbewa sukayi dashi sukayi wanka,dama Khaleel da yaji kira yasan sabulunsa za a karba,shi yasa ma ana cewa Khaleel sai ya dauki Sabulun ya tafi wajen kiran.
Yauma suna zaune a Palo Abbi Mustapha ya kwala masa kira da sauri ya koma daki ya dauko sabulun Sodarsa na wanki yana kumbura baki yaje tare da cewa gashi ai kuwa Abbi yace yawwa dama kiran kenan jeka, Khaleel ya juyo yana masifa dama nasan kiran kenan,Me ake mana a gidan ba asan a bamu hakkin mu ba,muna bukatar kayan sawa,takalma,kudin kashewa,bare azo kan su mota gida da aure duk banyi wannan yanzu ba sai yaushe zanyi kenan gashi kullum tsufa kamamu yakeyi ace na wuce 30yrs sai yaushe zanyi kudin bare aure gaba daya ma basa ta mu ta Kansu sukeyi

Mujaheed yace ai ko su Sabeer sun isa aure to bamu da aikin yi bare mu tallafa musu suma ina ma muka iya da kanmu sabulu yana gagararmu,na buga lissafin yaki bullewa, gashi jarabar dangin duk talakawa bare su tallafa cewar Khaleel,Khaleel yace da ace muna da yan Uwa a lagos da wlh tafiya zanyi na makale a wajen wani ko zan samu abin yi,Sabeer yace ina duk suna kauye Wlh babu wani jinin birni ko ace a kudu suke bare muje neman agaji,Aikin ma yanzu sai da hanya zaka samu siyan Offer akeyi,Aliyu yace Ku Allah ma ya taimakeku kunji dadi kun gama Degree gashi har wasu kasar kunje ko b?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 a komai kunci,mu fa?yanzu mukeyi mota ma lokacin Abbi hanawa yayi Aayan ya bamu wai zamu lalace,kai rabu dashi shi bamu San me yakeyi ba a wayarsa duk hotunan yan mata ne yan dagwas dagwas dasu yake chat,wata rannan duk talaucin nan a waya naji sunayi da Abbi wai zai aika mata da kudi za a bata kasonta, ita kuma tana Darling ayi sauri unguwa zanje fa=?
?=?
?,Allah Khaleel? Meenal ta tambaya yace tab ai kune mata kuna gida baku san me su Abbi sukeyi ba,mu mun San komai ke ai duk manyan nan dai dai ne na gari,musamman Abbi Sani kina ganinsa haka yan matan da yake kulawa bamu isa mu masu jini a jika muje ba,ai Duniyancinsu kawai sukeyi shuru mukeyi dan kar su Umma suji gwara a zauna lfy.
Haneefa tace karuwai ne?to mene in ba Karuwan ba cewar Sabeer,rannan zaki ga wasu sanda muna wancan gidan sunzo muke cewa yan maula?ai ciki harda budurwar Abbi Musty,hhhh suka sheke da dariya wato Musty ma? Khaleel ne ya kalli skin dinsa dai dai lokacin Hajja ta fito da kwano a hannu,Khaleel yace rayuwa sai Imani tsohuwa kalli fatata yanda take komawa,yaushe zan ji dadi ne?ga duniya gudu takeyi,maza matasa mutuwa sukeyi tsoro nakeyi kar kwana na ya kare Hajja banyi aure naji me akeji ba,ke kinji dakinki da dan mijinki har kin haifi su Abbi ko? Mujaheed yace kai Hajja ance a zamaninta yar soyayya ce baka ga duk jahilcin mutanen da sai da Hajja ta auri Bature Baban Daddy,Sajeeda tace Allah dai ya biya Hajja anci duniya,s una ta dariya Mujaheed yace ai da munyi rako duniya kuwa idan bamuyi aure ba munji me ake ji muma,Hajja tsaki taja tace yan iskan banza tayi gaba, Mujaheed yace kai yanzu Men cuta ta kama wani a cikin halin da muke ciki ai shike nan kuma sai mutuwa wlh ana kallo zai mutu ba kudin magani,

tagumi Khaleel yayi yace Shege Ameer yana can Allah ya Zabe shi,Haneefa tace idan zamuyi aure yayi mana kayan daki,Khaleel yace a yau naga dama sai na nemo inda Ameer yake wlh amma bazan nemo shi ba duk muci wahalar tare sai kowa ya gane kurensa a gidan nan,Mujaheed yace wlh ana nemoshi tsohuwar nan dasu Abbi zasu koma takurawa mutane kyalesu iyakaci idan mun gaji mu fece wajen Ameer mu barsu.
Sajeeda tace sai na fadawa Abbi,Khaleel yace fadi dan Allah wlh da sai na barar dake a gidan nan dama cike nake da zafin talauci,Hajja ce ta fito tare da cafko wuyan rigar Sabeer tare da cewa ina kudina dan Ubanka,Sabeer yace Hajja wai ance miki kudi ne suka makale a Internet zasu zo ta rigada ta turo su suna hanya,Hajja tana zaro Ido tace yaushe zasu iso? Aliyu yace nan da kwana Uku ko hudu,Hajja tace Allah ya kaimu wlh idan basu zo ba sai nayi maganinku,Su Khaleel suna ta dariya Hajja tace zaku ci ubanku gaba daya a gidan nan wlh sai nayi maganinku,dariya sukayi gaba daya tare da cewa hooo Hajja Rayuwa sai Imani, Banza tayi dasu sannan tayi gaba zuciyarta na suya,

A kwana a tashi tun su Khaleel basa tunanin neman aiki har suka yi shawara gwara su nemi na Kansu wahalar ta ishesu haka,amma kuma ta ina zasu fara neman na kan nasu.
Waye ya daukar min takalmina?Mujaheed yana cigiya,ya fito da masifa Haneefa tace Aliyu ne yasa ya tafi schl,tsaki yaja yanzu sai na jira shi ya dawo gidan nan dan masifa idan kana da abu kowa sai yayi amfani dashi,hakuri zakayi lokacin da muke gidan jin dadi wa yake kula kayan wani kowa da nasa cewar Abbi dake zaune yana jinsu.

Yau Saturday ba schl tunda dama mun koma hutu,Meenat kuwa tayi Candy wata za a nemo mata University, Ina wajen Daddy Muna hira yace 'yata ki daure kiyi min wani aiki,nace Na mene Daddy? Aayan zaki sa ya dawo dasu Hajja gida tare da yan uwansa,bai dace hakan ba,babu wanda ya isa ya shiryar da wani sai Allah,kuma ba lallai wahala ce kadai ke sawa a shiryu ba,wasu wahala bata sawa su shiryu sai Allah ya so,tunda Allah ya kare mu kawai ya kyalesu a kwai lokacin da komai zai wuce,kuma yanzu ko sun dawo ba abinda zasu iya yi,baza mu zauna gida daya dasu ba kawai ya dawo min dasu kowa ya koma bakin aikinsa abinda nake roko a wajenki kenan tunda yana daukan shawararki watakil idan kece sai ya yarda,Sai da Daddy ya kashe min jiki da nasiha tare da nuna min Muhimmancin yan Uwa da iyaye dole nace Insha'allah Allah zasu dawo Daddy ka daina damuwa.
Haka muka rabu da Daddy ina tunanin ta ya zan iya sa Aayan ya hakura yanda yayi fushi dasu Haka.
Ameer na kira a waya nace yazo ina nemansa,da wuri kuwa sai gashi yazo,bayan mun gaisa nace kasan inda su Abbi suka koma?Ameer yace ae mana na sani kusan kullum ma ina wucewar ta layin kuma ina bibiyar halin da suke ciki,amma baka shiga wajensu ba?yace ae wlh sabo da bari nayi su kara dan nutsuwa sai na fara zuwa wajensu kawai sai naga Ameer yana Hawaye,nace subhanallah Ameer lfy? Allah Anty tausayi suka bani baki ga halin da suke ciki ba,sabo da ko kayan sawa Aayan bai bari sun dauka ba,suna cikin wani Hali,yan uwana ne mun shaku dasu sosai tare muke komai dole bana jin dadin ganinsu cikin wannan yanayi wlh musamman su Khaleel,ni kaina sai naji tausayinsu duk da ban gansu ba ganin yanda Ameer yake ta hawaye,yana fada min halin da suka shiga ga Iyayensu mata sunyi yaji yana gama fada min ya goge Hawayensa yace Anty dan Allah kisa ya dawo dasu ko me zasu yi Kansu Allah yana ganin komai bare nasan yaran gidan duk sun shiryu su Abbi da Hajja ne kawai ban sani ba.
Numfashi Naja tare da cewa tsaya mu tafi gidan nasu,waya na dauka tare da kiran Aayan nace My Man ya aiki?yace alhmdllh Babyna kinyi missing dina?nace sosai ma,dan Allah unguwa Ameer zai kaini idan ka yarda,idan na dawo zan maka bayani inda muka je kaji,ba damuwa sai kun dawo.

Godiya nayi sannan na shirya tare da daukan wanka cikin tsadajjen lace kamar a saceni nasa glass na yayi brown me tsada nayi kyau sosai kai kace yar Gomna ce gaban motar Ameer na shiga muka tafi har gidan dasu Abbi suke,a kofar gidan mukayi parking,Ameer na kalla har ya fara shirin zubo da hawaye wai na tausayin yan Uwansa,nace dan Allah karka karya musu zuciya pls ka daure kamar ba namiji ba,bazan iya shiga gidan ba Anty jeki ki fito ina jiranki,wucewa nayi ina taku dai dai kwas kwas,tun daga tsakar gida na fara Jin tausayinsu ganin su Haneefa kwance saman tabarma jikin bishiya duk sun rame sunyi duhu gashi duk gayun nan babu sunyi shuru sunyi tagumi,kallo daya sukayi min suka ganeni,da Sauri suka mike zaune,da fara'a suka ce sannu da zuwa Mufeeda,kece yau a nan?wa ya nuna miki gidan?da Ya Aayan kuke tare? Nace a'a ni da Ameer ne nace ya kawo ni tunda ku baza kuzo mana ba,da Sauri suka jani har palo,suna kiran kowa na gidan Maza da matan,Kahaleel duk iyayi da gayu babu naji tausayinsu kowa da fara'a da mutunci muka gaisa muna Hira,abinda bamu taba yi dasu ba kenan,Ruwa suka kamfato min a cup na roba,na karba ba tare da na nuna kyama ba nasha haka,sai murna sukeyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login