Showing 102001 words to 105000 words out of 175038 words

Chapter 35 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6898

wasu zakiji suna wancen ina ba yar manya bace Bazan iya ba na tsani me roko etc.

Ma'eesha na dawowa Ameer yace matso nan Hajiyata ki bamu mu musha,Meenat tace Sis Mufee kin gansu ko,Mufeeda tace nima baza kunne nayi yarinya, Babbar banza cewar Aayan,dukan wasa na danyi masa kadan tare da kwanciya a cinyarsa , Ma'eesha tace kai Allah ya bawa Meenat farin jini samari iri iri tun daga Rimin gado yan fulani suka dinga cika kofar gida.

Farko mun fita siyo pure water muka hadu da wani zai je kiwo da shanunsa ya tare mu yana washe baki idan kun ganshi abin dariya yana busa hayakin wiwi Yace hooai Yan Birni aradu wagga Bingel tana Burgeni, wannan ke nake so ya nuna Meenat tare da cewa Sunana TSITO, nan muka fara dariya jin sunansa Ma'eesha tace in kun ganshi wlh yaci sunansa Tsito wani siriri ne kamar a busheshi gwara Kwaja ma yana da Katon ciki Amma Tsito shi ba dan cikin ma,Meenat tace to Dan Uwarki ai Tsito yafi Kwaja lfy da ganin cikin Kwaja ai na cuta ne,kuma Tsito kyakyawa ne,Ameer yace mu dai ba ruwanmu Tsito muka sani,Ina dariya nace karki kara zagar mana Uwa akan kice dan Uwarki gwara kice dan Ubanki Better,Make min baki Aayan yayi shi Abban shine ba a so ba kyau,baki na turo cike da shagwaba nace da zafi fa...Zan rama ne.

Ma'eesha tace Daga Tsito kuma sai NA AGWAGWAJI shi kuwa a yan fulanin ma dan Daba ne duk wanda yaga Meenat tayi masa magana sai ya farfasa masa jiki,Ameer yace kice dan karamin yaki ta hada,Meenat tace Allah ya bani ya zakuyi dani ehe,Dariya muka dinga yi Jin har Dan karamin Saniya Na Agwaji ya bawa Meenat tana can gidan Inna an daureta za a sata cikin Shanu ana kiwata mata ita,Nace Business Sabo Sarkin Kasuwanci cewar Aayan jin yanda nake ta murna Meenat ta samo Saniya zata girma ta Haifo yayanta.
Ma'eesha tace Arzikin Meenat bai tsaya a nan ba kullum samarinta suna hanyar kawo mana kaji da zabbi muna yankawa mu sha farfesu iri iri,Na ciji yatsa nace me yasa kika cinye a ciki banzaye maimakon ku siyar ku tara kudin ku kawo min ko dankunnen Gold na siya muku dan karami,Aayan ya kalleni baki bude yace da kudin kajin? Nace of Course.

Ameer yace inye to wannan buhun kayan naku fa? Ma'eesha tace duk Samarin kauye ne suka tara mana su danyar Gyada,gero,wake etc,A Maiduguri kuwa samarin Meenat harda Conductors na mota,yan Napep etc me dubu daya me dubu biyu haka muka cinye musu kudi,Nace to ke kuma fa in haka ne kece me bakin jini,Meenat tace tsakani da Allah duk wani me kudi indai kinga rantsatsiyar mota ta tsaya to ba shakka wajen Ma'eesha aka zo zance,ni dai Meenat ina ga asiri akayi min daga me kaji sai me Saniya,gyada da gero tare dasu waken Suya hhhh muka dinga dariya,Aayan yace sorry Sis zaki samu wanda yafi kowa kudi kuma na gari kema,ni kuwa nace Meenat haka Allah yake lamarinsa ni kam Ruwa ta sha aradu,Rankwashi Aayan ya zuba min,Ameer yace ni wlh ji nayi gwara haka ita ba iyayi ba dama Allah yasan manufar jaki shi yasa ya hanashi kaho.

Meenat ta gaji da abinda Ameer yake mata ta mike cike da shagwaba tayi kansa wai zata kwala masa spoon ya mike suka fara zagaya mu a palon muna zaune, sai da na gaji nace Meenat kun damemu can u stop ths Nonsense pls? Meenat tace ai kuna jinsa abinda yake ce min kun kasa yi masa fada,Maeesha ce abar duka ai ba Ameer ba tunda ita ta fada mana,Haushi Meenat taji ta jefar da spoon din tayi Bedroom abinta .










AsmaBaffa
[1/28, 10:00 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA







101-102








Official









By
AsmaBaffa








Mun dan jima muna hira bayan tafiyar Meenat sannan na mike nabi bayan Meenat Bedroom dinsu,Maeesha ma ta shigo,Ameer ma ya tafi shirin bacci,Aayan yana samansa jirana yakeyi nazo mu kwanta,Ni kuwa yau dakin su Meenat nake son kwana Sabo da musha hira ta ganin juna,Meenat tace ban gane ba?Ya zaki zo nan ki Kwanta mana mijinki fa?Nace hira zamuyi,Maeesha tace shike nan mun shiga Uku Meenat baza muyi bacci ba yau,Meenat dariya tayi hmm ai mijinta zan kira mata idan mun gaji,ina kallo sukayi shirin bacci nima na mike na feso wanka na shafa turarukan kamshi iri iri sannan na kwanta gefe,Maeesha tace wai Mufee har yau baki ciki ba? Gaskiya ya kamata ace kina da cikin Aayan,baki na tabe tare da cewa mu ba yan iska bane a kujera yake kwana ina Bed,dariya sukayi Ma'eesha ta kalle ni lallai Sis maida Karuwa yar Iska ni mamakina Banga kinyi rashin ko yar lfy ta first night ba,nima kullum zura ido nake Amma ai nasan tuni Su Mufee an san kan harkar Cewar Meenat, zanci ubanki wlh ni sa'arku ce wai dan kunga kunyi saurin girma,so kuke ko me na kwashe na fada muku? Meenat tace mu ina muka Isa daukan wannan maganganu na manya ki rike abinki dama shawara zamu baki munga ko kamar Aayan yana da matsala ne shine muka samo mafita a Maiduguri.

Masifa na fara wacce mafita uban wa yace muku mijina nada matsala idan banda ta Family nifa bana son Sa ido Meenat ku kiyayeni,Allah baki hakuri ai gani mukayi mu da ke duk daya ne ba wanda ke boye maganar dake damunsa yaushe Mama Mufee ta dawo mana haka bamu sani ba bayan Ammah ta bar mana wasiya rike zumuncinmu,yau miji yafi mu daraja shike nan.
Jikina yayi sanyi nan nace ai kune wlh bakwa ji sam Amma akwai matsala Meenat,lokacin Aayan yana can yana ta faman jira nazo muyi baccin mu Amma shuru shuru sai tsaki yake faman ja yana juyi.

hannun Meenat na rike muna kwance nace Meenat kuji ni ina cikin neman taimako na addua Asara ta hauni,na tafka babbar asara,jikina da kyauna duk nema yake ya kare a banza,jibi uban Hips dina,kalli tun ina karama Allah ya hore min na shanu masu kyau da birgewa,kalli skin dinmu,amma a haka aka ce idan kana da kyau ka kara da wanka kalli yanda nake zabga uwar kwalliyar da shiga iri iri a gidan nan,yanda nake kashewa jikina kudi bai tsaya a nan ba sai da na dangana ga zuwa gidan gyaran jiki na biya makudan kudi an tsunami nasha an gyara skin,lungu da Sako anyi masa filla filla Amma ku kanku da kallona kun san na kara kyau da canjawa,kalli yanda nake sheki da walwali,kalli yanda nake kamshi ko abu na rike sai ya tafi da kamshi na,kalli ku kanku yanda kuka rude da kyauna gashi komai ya kara cika duk da cewa kun sanni Amma sai da kuka Koka yanda nake sheki da uban kyau,

Meenat tace mun gane,to asarar tayi muni da kashe kudina yayi yawa Amma kun san Aayan asiri na jikinsa har yau bai warke ba,bazai iya komai ba sai tabe tabe,kinga ko ba komai Sabo da lafiyarmu ma ya dace ace an daina taso da sha'awa kuma taki kwanciya,kamata yayi ace mijina yana alfahari dani kamar ko wacce mace,amma ni kaina nake zargi ko nice ban iya yanda zansa yayi amfani dani ba,bayan wannan asarar kudin gyaran jiki so nake nima ace kwalliya ta biya kudin sabulu ace mijina yana yabo na yana susucewa a kaina,amma ace ina sheka Ado bana ganin ya zauce ina kanta.
Dariya Ma'eesha tayi tare da cewa wlh ya susuce kece bakya ganewa kinga yanda yake binki da uban kallo duk inda kika Gilma,kuma kin gama zautar da shi,bakya ganin yanda yake kishinki me kike so kuma? Meenat tace akwai matsala ace mijinka bazai biya bukatarsa da kai ba,kuma ribar soyayya da aure a hayayyafa,to ki kwantar da hankalinki kinga Wani Saurayina a Maiduguri dan gidan gawurtaccen malamin Sunna ne Malamine na Sunna basa tsafi ko shirka addua zasu baka kayi suma su tayaka kuma ba kwandalarku ana dacewa,Maeesha kin tuna Masa'udu Shekare wanda akace yayi shekara da shekaru a Cikin Uwarsa kwantacce kafin a haifeshi? Wanda ke zuwa kusan kullum yana damun mu da Fassarar Hadisai? Ma'eesha tayi dari tare da cewa au wai Shekarau kike nufi? Dalla Shekare yake ba Shekarau ba,ae gaskiya ne kam malamai ne,ni kuwa nayi tsalle na dire cewar Bazan tonawa mijina asiri ba gaskiya,Meenat tace to kin gwammace ya zauna da cutar wani abun sai ana fada ake samun mafita,ai ba wanda yafi karfin cuta a duniya ba a kunya a cuta gwara a daure a fada muji shawara ina da Number su,kinga ko a nan talaka cikin Samarin za suyi rana,shi yasa ba a raina dan Adam kowa da ranarsa kuma da baiwarsa,nace haka ne Meenat Allah ya kaimu gobe sai a kirashi.

Da haka muka fara baccinmu bilhakki,Aayan yana can yana fama da rashina,sai faman jirana yakeyi har ya gaji da latsa waya da laptop ya mike nan take ya sakko kasa tare da nufo dakin su Meenat,Yana zuwa knocking ya shiga yi yaji shuru sai da kyar Meenat ta farka taji tsoro ko abin cutarwa ne tace Mufee ku tashi yan Fashi ne,Da Sauri na fada lungun Bed nayi flat,Maeesha ta fado kaina itama,Meenat ta mike tare da bude sip ta shige ciki ta dunkule waje daya,jikinmu na rawa gashi sai bugawa akeyi,Da kyar nace waye? Nine naji Muryar Aayan,Nan Naja tsaki ina tsinewa Meenat dake fitowa daga Cikin Sip,Maeesha tace Amma kin cuce mu saura kadan hawan jini ya kamamu,a hankali na bude kofar kawai naji yayi sama dani ya tura kofar da kafa ya daukeni kamar Jaririya haka muka je har Bedroom dinsa, nace me ya faru muna baccinmu wlh ka Tsorata mu,Murmushi yayi tare da cewa akwai wani babbar kyauta da zan miki amma ba yanzu ba,tunanina kudi ne na fara Murna nace sai yaushe? Hararar wasa ya min tare da cewa nasan kyautar tafi kudi tafi komai na duniya a wajenki Amma sai ranar nima da nake cikin nishadi wanda soon nake Sa rai,a kirji na cijeshi kadan tare da cewa Allah ai ni babu abinda yafi kudi a wajena a yanzu ko mene shi tunda ba kudi bane na daina murna.

Murmushi yayi me sauti tare da cewa wannan kayan baccin fa? Karki kara Sa min su sunyi nauyi da yawa gashi sun matseki sosai Bazan iya ciresu da wuri ba,Ai yau banyi niyyar kwana nan ba dumin yan uwana nake ji, a kunne ya rada min pls ciresu ni ki daina Sa su bana sonsu kawai,suna miki kyau Amma wahalar cirewa zasuyi harda wani Wando me tsayi fa, kunya nake ji bana son na cire sai na daga zan cire sai na fasa shi kuma ya kafe ni da ido yana faman kallon kirjina tun kafin na cire ma,nace ka kashe light to na karasa a shagwabe kamar zanyi kuka,Kara wani kishingidewa yayi kamar Sarki yana kallona dai dai tare da murmushi,a hankali naji muryarsa yace Babyna kin san me? Nace a'a sai ka fada yace Kinfi kowa kyau a duniya wanda na taba gani komai kin hada Allah ya baki,Murmushi kawai nayi nace hmm tun baka je Palace din ba kenan ka gano haka,Baki ya bude dan baiyi tunanin nasan harkar ba ma,idona na rufe ina dariya hannuwa na biyun ya rike kam yana kare min kallo harda wata Palace da ake zuwa dama? Nace uhm am just kidding u fa,Sai kin fada min naji,Nace to kaima ka sani ai Kingdom kenan ai me matakan tsaro,au wani sunan ne wannan? Nace ai Baza ka gane ba sai ka tsallake border Amma ai kaima yaron ne tunda ba sani kayi ba sai lbr kamar ni.

Ido ya dan ware kadan tare da cewa bacci nake ji pls cire kayan mu kwanta,jikinsa na kalla daga shi sai Boxers dan gutsul,Haka cike da kunya na fara zare rigar tun kafin na zare ya fara Murza Albarkatun Kirjina.

Abbi an dawo ana jiran Boka Shakylgancy ya aikata Aiko sai waya da sukeyi,Cikin dare Boka ya Cillo tsafinsa zuwa jikin Mufeeda sai akayi dace Aayan yasa munyi wankan tsarki don shi ba a ko kara 1hr da najasa a jiki ko na Sunna ne,Yace to Ki daure muna Nafeela ko raka'a biyu ne duk dare mu daina bacci ,Mufee ba musu na bi bayansa muka fara Nafeela,lokacin Boka yana ta jefo tsafinsa baya Tafiya,ya buga ya buga shuru,bayan mun idar sai da sukayi dogon Azkhar lokacin boka yana ta faman jefo bala'insa Amma shuru,Har ya hakura yace sai gobe zai kara yi.
Washe gari da sassafe ya fara tsafin irin ko muna baccin Safe kawai lokacin nan ma azhkar mukeyi na Safiya,da rana bai samu nasara ba lokacin karatun Qur'ani Meenat take kara min,yamma ya gama shiri tsab lokacin kuma Azhkar na yamma nakeyi zuwa Magrib,still daga Magrib zuwa Isha duk bashi da sa'a.
Kwana na biyun kuwa na fara period Amma ko yaushe ina da Alwala,ga addua a bakina har kitchen ni ba wake wake nakeyi ba sai addua nan ma boka ba labari,lokacin kuma mun kira Saurayin Meenat Shekare ya hada mu da babansa na bashi labarin komai nan Malamin ya bamu adduoi ta waya da yanda zamu yisu, na fara ma yau kuma Ma'eesha ta tuna min zamu je gidan kawarsu ana bikin yayarta,haka na damu Aayan ya barni naje da kyar ya yarda yace Amma sai da? Ameer ya kaimu,Haka muka ci uban kwalliya bana cikin sahun matan aure,a gaban Aayan sai nasa Katon gyale Amma muna shiga mota na cire gyalen na ajiye a bayan motar Ameer gashina na saki jelarsa,abinda mata keyi yanzu kenan Ba a gane wace matar aure,nima sai na birge kawai,muka je Dinner wurin 9pm ana ta rawa da kade kade,Har wurin 11pm muna ciki ana cashewa na manta da wata addua ma gashi nasan mijina bai so a kalle masa ni,amma na zalunceshi bai sani ba na bari Maza na kalle min sura tare da gashina wanda nasa ne shi kadai Allah ya halitta masa,tunanina na masa wayo ban san kaina nayiwa ba,har shiga filin rawa nake muna gogaggaya da matan manya kowa ya ganni yasan matar hamshaki ce ni ko yar gidan wani ce yanda nake zubar da Naira.
Abin haushi Boka shi aikinsa yakeyi dama aikinsa ne kullum ta nan yake samun kudinsa kamar yana Office ne,kuma basa saurarawa kullum aiki sukeyi suna gwada sa'arsu ko zasu samu wata dama daya tak su samu nasara musamman yare da zaka ga sunfi Musulmin bahaushe Amana basa karya alkawari.
Wufff Ya turo min Aljani ta tsafinsu yana zuwa yaga na shagala ya samu dama nan yayi wuf zai shigeni Amma ba ta inda zai iya shiga jikina da wuri ai tuni ya ankara cewar Gashina gashi nan a waje nan fa yayi wuf ya bi ta gashin ya shiga jikina,nan take naji kaina ya fara ciwo sosai sai nayi tunanin ko Gajiya ce,kawai nace suzo mu tafi,haka muka dawo gida ina fama da ciwon kai me tsananin gaske kamar kaina zai tarwatse,na fara Hawaye na samu Aayan a daki yana jirana yana ganina haka yace mene lfy?,nace kaina ciwo kin gani ko sai da nace karki je kika ki yarda,zo ki kwanta na baki magani,kafada na make tare da cewa Bazan sha ruwan gidan nan ba,indai ruwane na gidan nan Bazan sha ba,Aayan ya zata tsokanarsa nakeyi yayi dariya yace kwanta,nace na rantse Da Allah me Rahma in na kwanta a gidan nan yau Allah ya tsine min albarka,bude baki yayi yaga fa da gaske ne dan ba alamar wasa a tare dani,yace to ina zaki kwana nace wani gidan Amma ba wannan ba,kaina na dafe nace wlh ni a fitar dani daga gidan nan idan na zauna a gidan nan shegiya nake,wlh in dai na kara kwana a gidan nan Allah ya tsine min albarka wannan tsinannen gidan dukka ma tsinannu ne ku yan gidan,Aayan ba a kanta ya fara ganin hakan ba tunda Mommynsa tayi da suka mata asiri haka matarsa Nafisa tayi itama da Ruky, Amma ai munyi alkawari dake baza ki bar gidan nan ba,Alkawari? Amma ka cuceni Allah ya Isa me zanci da wannan gidan,nan na sauka kasa da gudu na fara hado kaya ta ko ina,nace Meenat ku tashi mu tafi,sis lfy? Zanci kutmar ubanku dan uwarku dan ubanku ku tashi mu tafi wlh idan baza ku taho ba ku zauna,Ba yanda su Meenat basuyi dani ba Amma zagi kawai suke sha iri iri,haka Ma'eesha tace mu Bita Meenat kar a samu matsala ta fada hannun bana kirki ba,haka suka kwashi akwati har Uku,Aayan tuni ya fito ya nemi Ameer ya kora masa bayani,nan Ameer yace shawara ka bawa Meenat key din Wani gidan naka can daban sai na kaisu can su zauna,Haka Aayan a gigice ya mika masa yace kuje dayar sabuwar GRA ka gane gida Dana siya last wk pls ko me Mufee na take so a bata, kar ka dawo gidan nan ku zauna ka kula dasu kafin nazo,Ameer yanda yaga Aayan ya fita daga hayyacinsa gaba daya abin ya bashi tausayi kamar ya masa kuka ya ma rasa me zaiyi gaba daya baya hayyacinsa za a rabashi da Mufee dinsa wayyoo.

Yana gani Yanda Mufee ta gigice sai gumi take hadawa ta fita da gudu har Jikin mota hakanma da kyar Ameer ya lallaba ta hau motar tasa cewa tayi in dai motar ta gidan ce baza ta hau ba,Aayan ya Kira Meenat da suke kuka ganin abinda Mufee keyi ya zarta hankali,kwantar musu da hankali yayi tare da cewa karku kara kuka kinji ko,kai kawai Meenat ta daga Masa Kudi ya mika mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login