Showing 6001 words to 9000 words out of 175038 words

Chapter 3 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6894

idan kanwata ta zama Doctor ko Lauya,kallon banza suka min tare da tabe baki,nace zaku gani wlh kyaleki nayi dan ba a kan KASUWANCI NA kuka tabo ni ba,rigimar ba akan kudi bace Amma da akan kudi ne ai da sai da? a mutu a gidan nan shegu,tsinannu tambadaddu,arna,jahilai,dabbobi kuma dukkan yan gidan nan na zaga na nuna Saurayin nan dake tsaye nace harda kai da wannan tsohuwar dake zaune a carpet a sanar mata dazagina da iyayenku baki daya,sannan kuma ina tunatar muku Mala'ikan mutuwa na nan zuwa watarana,sojoji ne suka yo kaina na Arce da uban gudu tare da cewa Allah ya isa dana gaishe da tsohuwar nan kekakashashiya,na dinga zura uban gudu Allah yasa time din tashinmu yayi kawai na fada Napep ina haki sai gida tazarce kawai tun daga Cikin gidan nake gudu har nazo bakin titi na hau Napep,su kansu abokan aikin nawa dariya suke min da kyar wani cikin wanda ke jiranmu a waje ya karbi box din hannuna Sabo da uban gudun da nake kamar na fanfalaki.

Bayan na koma gida sallah na gabatar tare da fara harkar kasuwancina har Awara nayi ta dare bayan na siyar na gyara komai tare da irga kudin na cire ribar na zuba cikin asusun da nake tarawa Ammah kudin asibiti na magani tare da ware na gida da yan abubuwa,washe gari haka muka je wata unguwar mukayi polio abokan aikina su Salima sun sani gaba suna min dariyar abinda ya faru damu a gidan masu kudin jiya,sai dariya muke muna Bada labarin,Salima tace ammafa sun hadu da yawa a gidan kowa me kyau ga iya kwalliya musamman dan Iskan da yasa aka dakeni domin ni tunanina shine yasa a Zane ni tunda shi ya hana a bude min gate,Salima tace lalle Mufeeda ashe haka kike da rashin kunya idan an tabo ki,kina da Silent falava wlh,u like too much falava,murmushi nayi kawai domin bana jin wani turanci ni kam,karatun Hausa da Arabic kawai na iya Amma Ilmin turanci sai dai kalmomi dai dai domin bani dashi,h akan ma don ina dagewa ne su Meenat suna koya min amma da ba karamar dakikiya za ayi ba ni kam.

Yau cikin nishadi muka gama Polio na dawo gida da Sauri naci abinci na shirya sai kasuwa siyayya ina tsoron bi ta cikin GRA Kawai sai na hau Napep naje na dawo lfy, bayan mun gama suyar Awara mun siyar wanka muka kara yi tare da Sallar Isha,Su Meenat Assignment sukayi na schl tare da karatu nima na zauna suna koya min karatun turanci da rubutu haka Arabic ma duk da ina da Ilmi domin Uzu na ashirin cif haka wasu litattafan duk nayi wanda Kannena su Ma'eeshah sunyi Sauka tuni littafin da suka sani kam ko kafarsu ban kama ba danma ni gwanar jin wa'azi ce nasan duk wasu hukunce Hukunce na addini da dama Amma su suke koya min karatun,da badan haka ba da anyi kungurmar Jahila ni,

Part of speach suke koya min common adjective sun sha fama dani kafin na iya fada Sabo da ba laifi kwakwalwata da saukin ja tunda ni dai iyakacin Jss 2 makaranta ta gagareni Allah ma yasa Makarantar Arabic da boko mukeyi a hade shi yasa muke dana addini,su Meenat kuwa ai akwai Ilmi,shi yasa da munyi fada zasu ce to Sis me kika sani ma in ba neman kudi ba musamman Meenat uwar iyayi da son kwalliya domin duk wata kwalliya ta yan Zamani ta iya ta komai nata na harkar son gayu,Maeeshah ma haka suyi ta faman iyayi ni kuwa sai dai na siya musu kayan yi suyi ta zuba kwalliya ina kallo tunda har cosmetics na talakawa ina siya musu iri iri,kayan wanke gashi na talaka ni dai barni da jarabar tsafta amma ba ruwana da wata kwalliya gani nake bata lokaci ce kawai kudi nake nema dan mi tsira da mutuncinsu,
ni kullum sai da? na labta Hijab na fita neman kudi ba sauki wanda yanzu Unguwarmu sun samin suna Yar Kasuwa,sabo da bani da lokaci sai na neman kudi akan kudi ba daga kafa.

Duk inda naji wata Sana'a ko harkar samun kudi to fa yanzu zan cusa kaina ciki dole sai na samu domin mu samu na ci da sha tare da Sutura,ina da karancin wannan shekarun Amma na shaku da kudi,yanzu abinda ya dameni bai wuce kai Ammah Hospital ba domin dubu Sittin da biyar zamu je da ita za ayi mata wani aiki a Ciwon dake kugunta zuwa kafafunta shi yasa na gigice yaki Halak yaki Haram haka nake tara kudin,
Akan wannan yanzu kam na koyi ha'inci a Sana'a ta domin Awara da ina yinta me kyau da dadi Amma yanzu dan na samu riba da yawa na daina alkintata idan na tashi tacewa Bazan matse ruwan da yawa ba,kadan nake dan matsewa kana ci zaka ji ciki lumtsum da ruwa da mai,haka yajin na daina me dadi sai na gabza uban gishiri a ciki dan yayi yawa,haka ake siye Sabo da tsaftarmu Amma sun daina karba da yajinmu,haka kosai na ma da wata taba da ha'inci ya taso min sai na siyo garin kwaki tare da jar kala bayan na dauko markaden saina zuba garrin kwaki a Cikin markaden waken kosan nawa tare da jar color yayi wani jajir sannan kosan ya kumbura yayi sutu sutu dan na samu riba na samu kudi sai kiga ana ta siye Malam kosai yasha kayan miyar color gashi har wani Danko yake Sabo da yaji garrin kwaki ciki ba a sani ba ayi ta siye ina samun riba tunanina dai dai duk kuwa da cewar nasan ba kyau sai da? nayi Istngifari domin ko Ammah da kannena basu san tabar da nake aikatawa ba gara awarar gida idan zan soya musu daban nake tace ta tas tsam ba ruwa sai su zata ma wacce ake siya haka take.

Hattana Alewar madarata dasu kwakwimeti tare da kafi tsire in dai zanyi sai na san tabar dana yi a ciki Sabo da kawai na samu riba me yawa,gullisuwa idan zanyita sai na tankade garrin masarara me Laushi na kara a cikin Madarar Sabo da tayi yawa,haka ma Zobo na siyarwa sai na samu jar color na tafasa zobon kadan na narka uwar Color a ciki nayi hadinsa a ganshi kamar gaske ayi ta zuka ba a san rabi color ce kawai da ruwa ba,kuma bana sa sugar dan zaki wato sugarin nake dan yafa kadan sai kaji zaki cai.

Ina zaune kusa da Ammah ina tufke mata gashinta muna sauraren Radio kawai sai muka ji cewar Gomnati zata raba tallafi ga marasa karfi Naira dubu sha biyar biyar tare buhun shinkafa da taliya sugar da man gyada tare da waken Suya a ja jari,nan take na mike zumbur naji kudi,Ammah ta kalleni tace sarkin neman kudi dan Allah ki hutawa kanki zafin nema baya kawo samu haka duk kin damu kanki Allah yana rufa mana asiri dan Allah ki rage takurawa kanki ayi amfani da abinda ya samu,baki na turo Ammah kina gani kudin maganinki har yau basu hadu ba fa,to ta wacce hanya zaki bi ki samo mana tallafin? Ammah wajen counsilor din Unguwarmu Adamu zanje na nemi Alfarma ya nemo mana hanya,ai yana da kirki Amma fa kija mutuncinki duk da nasan irin tarbiyyar da nayi muku ki kiyaye Mufeedata sannan kinga girma ya fara kamaki idan kika bari Namiji ya rike miki ko yatsa shike nan kinyi ciki an gama,da Sauri na zaro ido waje a tsorace nace Ciki Ammah?ae ai indai Namiji ya rike maka ko farcene to shike nan ciki ya shiga,da tsoro na firfito da ido waje,nace Ammah su Meenat nake tsoro bari su dawo na fada musu gaskiya kar suje su yarda da Maza su rike musu hannu.

Su Meenat suna dawowa na taresu da Sauri tare da jansu dan Bedroom dinmu nace dan ubanku karku bari Namiji ya rike ko yatsanku,Meenat tace Sabo da me?ba kyau kuma Ammah tace ciki ake dauka,Dariya naga Meenat ta kyalkyale tare da cewa Allah ya bamu kudi Sis ki koma schl kema wlh ba haka bane ke baki da labarin abinda ake a aure ana samun ciki,ai Ammah wayo ta miki kar mu kula Maza mu lalace shi yasa ta fada haka Sabo da taga mun fara girma,shuru nayi ina Nazari Amma naki yarda da Meenat Sabo da nasan Ammah baza ta fada mana karya ba,kyalesu nayi kawai na fita abina naci gaba zuba kwakwimeti na ? leda,bayan na gama na fara daura su citta dasu kanwa,kaninfari etc,kusan duk makwaftanmu a wajena suke siyen kayan miya,idan suka siya kawai sai su zauna a gidanmu suce bari su daka kayan miyar ko jajjage da sun shiga gida kawai sai da? su fara girki,sabo da son kudi na nace to daga yau na kafa doka cewar ko wacce idan zata yi daka a turmin gidanmu to sai ta bayar da Naira goma kudin turmi,ganin haka yasa Bazan basu tabarya ba sai an miko goma shike nan suka daina daka a gidanmu,Muna da wata Kura da yake gidan mu akwai rijiya idan guganmu ya fada da ita muke amfani mi Ciro gugan,mutane suna zuwa aro sosai nan ma nace kudin aron Kura Naira talatin wasu haka dole suke bayarwa suna dauko Guga,Ammah ta hanani Amma naki ji,su Meenat ma dole suyi abinda nace ko bana nan idan aka zo to fa sai an Bada kudin nan,komai nawa idan zaka taba na kudi ne.

Haka na kama kafa naje har gidan Adam counsilor neman Alfarma a sani cikin masu tallafi,yace Mufeedata ki. Makara wlh an gama daukan sunaye amma na miki alkawari akwai na wani watan kizo Office ki sameni a secretariat zan sa sunanki a wasu da za fara bayarwa na manoma,ban kawo da wata manufa ba kawai na dinga Murna ina godiya cewar zanje in Sha Allah.

Bayan kwana goma Zaune muke gaba daya tunda anyiwa Su Meenat hutun schl muna ta Hadin Zobo nan nace suje su ebo robobi a wanke suna Tafiya na watsa Maroon color tare da makawa Zobo ruwa na hadashi da su Flavour yasha uban Barkono a ciki,sabo da aji yaji sosai sai na zuba citta da kaninfari kadan na ebi Barkono na watsa a ciki na tafasa dashi Sabo da aji yajin ya fito sai ka rantse yajin cittane da kaninfari me uban yawa,gaskiya na iya taba sosai ni kaina ina jinjinawa kaina yanda nake tabka tsiya a sana'oi na ba a magana watarana nakanji haushin kaina nima ba da son raina nakeyi ba Amma Sabo da neman rufin asiri,su Ma'eesha suna kawo robobi Meenat tace sis wannan uban zobon fa dazu fa dan kadan ne bai kai rabin botiki ba amma yanzu ya cika botiki,Maeeshah ma tace nima haka na gani kamar na Aljanu,Harara na zabga musu sannan sukayi shuru.

abin takaicin da kyar na hada dubu Sittin da Bakwai kudin Ammah na asibiti,haka nace su shirya mu tafi,har kofar gida na kira Napep muka hadu tare da daukan Ammah muka sata cikin Napep muka kulle dan gidanmu da yar kofar da ta kusa ballewa ma haka na zarge ta muka shiga Napep Sai Asibitin Murtala na cikin Kano,Munje Dr Naseer ya duba lafiyarta ya dinga fada me yasa ba a kawota da wuri ba tuntuni yace a kawota ayi aikin to gashi ciwon nata ya kara karfi yanzu dole wasu magunguna zasu rubuta mana mu siya na dubu Hamsim da biyar sannan idan ta shanye bayan sati Uku mu dawo da ita za ayi mata aiki.

Bakin ciki da tsoro tare da firgici suka kamamu gaba daya,nayi Zuru Zuru kamar wacce ta shekara taana zawo haka na koma nace Doctor yanzu nawa ne kudin aikin? Yace ai kudinku da yawa,likitan da zaiyi mata aikin nan baya zama a kasar nan sam Sabo da aikinta zaizo yayi mata ya koma,don haka idan yayi muku sauki ku biya dubu dari takwas da Hamsim domin ciwon ya girma,da ace tun farko kun kawota da tuni baifi ku kashe dubu dari ba Amma yanzu danma da wannan Doctor dinne Amma wannan aikin kasar waje muke tura mutane masu irin cutar ayi musu aikin anfi dacewa,a nan kuwa sai dai mu dage da addua,kuje ku dawo lallai nan da 3wks tare da kudade in ba haka ba kuna kallo wlh zata kasa ko motsa yatsa dake gabarta nan gaba sankamewa zatayi ku daure ku dawo ayi mata aikin kunji.

Likita na bayani Hawaye na sintiri a fuskata tunanina ina zan nemo kudin nan ko kaina zan siyar wlh bazan yi wannan kudin ba,Innalillahi nake maimatawa Doctor kuma na kwantar min da hankali yana cewa cuta jarabta ce daga Allah,idan Allah ya jarabceka sai hakuri aci gaba da addua Amma tana cikin hadari,Meenat dake kusa dani itama Hawaye takeyi,da kyar na Lallashi kaina nice babba Amma kuma nice me raguwar zuciya bana iya rike Hawaye na saurin kuka gareni ammafa a bangaren abin tausayi,ko ya naga abin tausayi yanzu zan yi kuka,kanmu da Ammah nake tausayawa kawai,Meenat karki fadawa Ammah me Doctor yace kawai kiyi shuru da bakinki Sabo da bana so hankalinta ya tashi,muce kawai aiki za ayi mata nan da 3wks sai kudin zamu fada mata,amma karki fada mata Doctor yace zata iya rasa ranta ba lallai ta tashi ba kinji,ok Sis Bazan fada ba cewar Meenat dake shesheka,hawaye na share mata nace muje kawai muk ayiwa Dr sallama muka tafi,Ma'eeshah da Ammah suna jiranmu a can waje, magunguna muka siya sauran kudin na siyo mana wasu kayan abinci da Cefane,Su Meenat kuwa tuni na hadasu tare da Ammah nace suje gida zanzo daga baya,Ina cikin Napep kawai tunani nake ta ina zan samu kudin nan,lallai Zafin nema baya kawo Samu,gashi dai na gama Ha'incina a sana'ata na cuci mutane da dama ta hanyar siyar musu da gurbataccen abun ci kuma karshe kudin anfaninsu kadan ne a wajenmu abinda nayi don shi ba a dace ba,amma duk haka ban hakura ba kuma ban damu ba matukar zan samu kudin da Zan nemawa Ammah lfy.

Tunani nake bana ganin komai bana ji har Napep ya saukeni a gida na shiga da kaya Niki niki,Meenat ta karba ta shigar dasu ciki,tsabar bakin ciki da muke ciki yau bamu iya daura kaskon Awara a kofar gidanmu ba,duk muna zaune kowa da tunanin da yake banda Ma'eeshah da yake ita ba wani girma da hankali tayi ba sosai bacci ma takeyi,abincin da muka dafa ba wanda ya iya kai ko loma daya bakinsa,musamman ni gaba daya na rude na rikice,idan kuka ya taho min sai na shiga toilet naci uban kuka na wanke fuskata na fito haka na kwana inayi kafin Safiya tayi idona ya kumbura yayi jajir, ga addua muna tayi, mura ta kamani muryata har ta dashe Sabo da Hawaye na kawo Mura yawan kuka,da sassafe kamar me aikin Gomnati 8am nayi shiri da kumburarren idona tare da jansa na maka hijab kowa ya ganni yasan ba lfy,tunani nake ina zanje neman kudi Office din yan siyasa ko gidajen masu kudi?ko kuma kasuwa zanje wajen masu kantina,domin banyi tunanin kaiwa gidan Radio ba ko wani waje,kaf makwaftanmu haushina sukeji Sabo da kan Sana'a ta ba mutunci idan maganar kudi ce ba kawaici don haka ba da wanda muke shiri sai da? daiku duk sunfi jin haushina,don haka babu me bamu shawara ko gidan Radio ko wani waje to idan ba business ba babu abinda ke hada mu dasu Sabo da ba a kula mu ance dan munga muna da kyau sai mu dinga yanga mu ba yayan uban kowa ba,sannan tunaninsu ma ni yar Iska ce Sabo da yawan fita da nake kullum ina gantalin neman Kudi tunaninsu ai iskanci nakeyi kullum ina titi,haka suke zagina ba abinda ba ce min.

A fusace na fito daga gida ka Rantse mutanen garin ne suka min abin haushi domin kowa haushinsa nakeji kamar zan make mutane haka nake tafiya fuuuuuuu fuska ba annuri,duk motar dana gani sai na harareta na harari na ciki dake tuki irin ga mutane da kudi ba taimako,common arna ko church kaje a tallafa ma amma musulmai ko a masallaci basa iya bada Sadaka me tsoka sai biyar,goma,ashirin katon me kudi kaga ya mika Hamsim,mafi akasarin Hausawa haka suke bare har wani ya dauki nauyin karatun wasu ko ci da Sha bare na magani sai dai dai ake samun masu haka,amma arna sai kaga mutum daya ya kwashi yan unguwa da yawa ya fitar dasu kasar waje karatu etc.






AsmaBaffa
[1/1, 10:20 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA






6-10







Official






By
AsmaBaffa







AUTA kema wannan page Sadaukarwa ce gareki.







Tafiya nake ina tunani har na Isa bakin titi ina jiran na shiga Napep shuru shuru ba taxi ba Napep kowacce a cike suke,wata dalleliyar motace tayi parking a gabana tunanina Namiji ne irin samari yan iska masu ragewa mata hanya a nemesu nan take na kara tamke fuska na dauke kaina na kalli can gefen hanya,wani kamshi naji ya cika wajen sakamakon bude murfin motar dake Saitina da akayi sai lokacin na kalli me fitowar ba kowa bane face yan matan nan na gidan Saurayi Aayan wanda suka min dukan tsiya sune su biyu suka fito a zafafe kida na tashi a motarsu sunci uban kyau ko ina zasu je oho,ina cikin wannan tunani sai ji nayi an sharara min ruwa a jikina me sanyi,a firgice na kallesu da mamaki,nan suka sheke min da Dariya dayar ta fusgo min Hijab tare da shakeni,dayar ta duro min ashar tare da cewa ubanwa kika zaga har gidanmu?dama nace wlh duk ranar dana ganki sai kin San

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login