Showing 3001 words to 6000 words out of 175038 words

Chapter 2 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6896

na yarda na karba,shima sai da Driver ya nuna baiji dadi ba sannan na karba tare da zuba godiya na dauki kayana na shige gidanmu shi kuma yaja mota ya tafi,ina shiga gida Kannena Meenat da Ma'eeshah har sun yanka awarar suna jirana da gudu suka taso suna Sister Mufee me ya sameki?lfy?hatsari kikayi ko motace ta kadeki,kinga yanda kika koma kuwa,Da Sauri Ammah ta fito da Rarrafe kamar zata kifa Sabo da rudewa tana Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un shine Abinda Ammah ke furtawa tana Hawaye tare da cewa me ya samu Mufeedata?Me ya samu katangarmu? Kuka na fashe dashi me karfi tare da Rungume Ammah ina cewa ba komai Ammah a wani layi ne kare ya biyoni na dinga gudu na fada cikin kwalabati da kyar wani ya taimakeni ya kaini asibitinsa kinga an bani magani harda kudi dubu biyu na shan Madara da Maltina,Ammah tace wannan waye me kirki haka?Wlh Ammah wani ne Doctor ne Babban mutum ya sa Driver dinsa,to ku dai kiyaye da mazan zamani a tsare mutunci,Alhmdllh tunda komai yazo da sauki,Meenat ki dafa mata ruwan zafi ta gasa jikinta taci abinci tasha maganin ta kwanta,ke Ma'eeshah jeki kofar gida ki fara soya awarar kafin yan siya su fara taruwa, mikewa mukayi tare da aikata abinda Ammah ta ce.

Bayan nayi wanka na gasa jikina Mai na shafa sannan na Sa doguwar riga mara nauyi itama yar gwanjo ce,abinci na dauko tuwon da nayi dazu naci na koshi domin ni cuta bata hanani cin abinci,komai rashin lafiya sai naci na koshi nayi luf,bayan naci Ammah ta dinga ballo min maganin tana bani ina sha har na gama,tace kawo na shafawa na shafa miki,Ammah zan shafa ki barshi kinga ke ba lafiya gareki ba, bayan na shafa jikin Ammah na koma na kwanta ina tunanin Saurayin dazu tare da maganganun da naji sunyi nake ta faman tunani shi kuwa mene tarihinsa me mutanen nan suke nema dashi ne haka,tunowa da nayi irin rashin Imaninsa nan take na firgita tsoronsa ya kara shigata na kankame Ammah har bacci ya kwashe ni,. Washe gari da asuba da kyar na tashi na gabatar da Sallah tare da Azkhar kamar yanda muka saba gaba dayanmu,Bayan gari yayi haske naje da Sauri na hada wutar itace na daura ruwan zafi yana tafasa na dama koko sannan na kafa daya kaskon gefe daban na fara suyar kosan siyarwa ta,ana sallama ana siya sai kuma ruwan zafi ya tafasa na kwalawa su Ma'eeshah kira suzo suyi wanka su wuce schl,da Sauri sukayi wanka suka shirya tsab cikin Uniform dinsu wanda yasha wanki da guga,Kokon dana dama musu suka eba tare da kosan suka ci suka koshi sannan suka kaiwa Ammah nata itama,Nima ina aikin Suya kosan siyarwa ta ina shan koko da kosai na ,Sister ya jikin naki gashi kumburin ya baje,murmushi nayi tare da cewa Alhmdllh kuje kar kuyi late ayi karatu da yawa banda wasa,bani da burin da ya wuce naga kunyi karatu sisters ku dage cikinku mu samu lauya da Doctor dariya suka dingayi Ammah ma tana tayasu cike da tausayawa Mufeeda,kudin Break na mika musu nace gashi yau ba ashirin za a baku ba Hamsin Hamsim zan baku kuci me dadi,murna suka dinga yi suna tsallen murna tare da godiya,Nace kuje mana Gashi karbi Meenat kece babba kuyo mana Cefane muyi miyar egusi da tuwon shinkafa ki taho da nama na dari Uku muma muci dadi ko Ammah? Murmushin farin ciki Ammah ta saki tare da kallona tace Allah ya muku albarka dai yaran nan,

bayan sun tafi na gama siyar da kosai na ya kare kaf ,ina ta faman murna na lallaba jikina na gyara gidan fes na tattaro kayanmu har na Ammah da kannena na wanke su fes na shanya,Ammah wacce ta rarrafo ta zauna saman tabarma tace Mufeeda me za a dafawa yan makarantar ne yau? Na gaji taliya zan dafa da mai da yaji kafin dare sai muyi tuwon,eh hakan ma yayi ai tunda muna samun na sawa a bakin Salati ba kamar lokacin baya ba,tashi ki kokarta ki gama ke ma ki kwanta ki huta idan sun dawo yau ba Islamiyya sai suyi girkin daren,amsawa nayi da to na mike nayi abinda ta Umarceni,na hada mata ruwa na kamata har Nayi tayi wanka fes na koma na riko ta muka dawo naa tayata shiryawa tsaf muna hira.

ina gamawa na hada yaji me dadi yasha hadi na soya manja,na gyar dan kitchen dinmu wanda yake na karfen langa langa ne,Ammah na zubawa na kawo mata tare da ruwa,taimaka mata nayi ta zauna nima nasa hannu muka ci muka koshi muna Bada dunkulen Maggi star,Sallah muka gabatar ta Azahar,sai ko mukaji Sallamar Yan makaranta su Meenat,da gudu suka shigo suna sallama suka rungumeni,Ido na waro mene hakan? Sis wlh wani ne yace yana son Ma'eeshah mu kuwa muka zabgo da gudu,ke kin ganshi wlh in banda wari ba abinda yakeyi wai yanzu Ammah duniya ta lalace me kudi bazai Hulda da talaka ba komai kyanka indai ku talakawa ne babu me kulaka sai talaka dan uwanka,Ammah tace ai duniya haka ta koma idan da gate a gidanku to me mota ne zaizo idan babu kuwa sai dai dan uwanka talaka,Yanzu kalli irin kyawu da Allah ya zuba muku Amma babu me zuwa wajenku talakan ma ya gagara sabo da talakan ma gudun talakawa yake Allah kayi mana magani,dan baki na na turo Ammah ke komai kice aure wai shekarunmu nawa,dan gidanku gata nake nema muku yanzu ko idan da kunyi aure ai kuna da yancinku ko ba komai sai kiga kun huta shine burina,Ammah wa zai kula dake to aini aure bai taso ba a wajena Ammah wlh Bazan iya aure na barki a haka ba ko da kuwa zan dawwama ba aure ne a duniya,ki daina zancensa indai kina so hankalina ya kwanta,Maeeshah tace Sis manya bari muyi girkinmu,harararsu nayi nace kuje dai ku cire Uniform kuci abinci kuyi sallah ku huta sai kuzo ku fara aikin,ni yanzu kun san kasuwa zanje siyo kayan da nake siyarwa citta,kaninfari,barkono,wake,kanwa,Sabulu,omo,maggi kala kala,har su Aya duk siyarwa nakeyi duk wasu kana nan Abu na amfaninmu kayan girki ina siyarwa a gidanmu,haka ina saida su Aya,ridi,kantu,alewar Madara,albishir etc su Ma'eeshah nake sarowa suna Tafiya min dasu makaranta su siyar min,ina kosai na siyarwa,da rana na siyar da su Zobo kunun zaki da dare kuma nayi Awara,ina kitso da zanen lalle sosai kudi idan sunzo zanyi na karbi kudina,sannan ina cikin masu polio rigakafi,duk wani neman kudi na Sana'a kanana na gida ina yi,kusan komai ma siyarwa nakeyi,kullum bani da lokaci bana zama sam sai neman kudi dashi muke ci muke sha,muke Sutura tare da makaranta,

biyawa Ammah kudin magani,yanzu kasuwanci a duniya shine buri na wanda har ya kai ga dasa min matsiyaci son kudi tare da tattali,iya lissafi da planning,sabo da yawan Hulda da mutane yasa na kara gogewa na waye sosai,akan kudi ba mutunci ko bashi ya shiga tsakanina da mutum akan dan Kasuwanci na to fa zan iya rufe ido dole a bani ma,kamar zanyi sata haka nake matukar neman kudi.

Yau Monday Su Meenat suna schl na gama komai na fita naje wajen saro kayan Yara na sha,ina siyowa kala kala har su tuwon madara na wuce schl na kaiwa su Ma'eeshah domin su siyar,ina zuwa na hango Malam ya sa Ma'eeshah kamun kunne ya hanata ko shiga aji wai sun makara.




Ina matukar Jaje gareku fans da raguwar shekaru da muka samu domin ba karuwa shekarunmu suka yi ba raguwar suka yi,ana ta happy new year a daina addua ya dace muyi Allah yasa mun shigeta a Sa'a tazo lfy ta wuce lfy,Allah yasa ta Zama shekara me amfani a Rayuwar mu,ta zame mana farin ciki da samun ci gaba a cikinta,Allah ka kara mana lfy da Nisan kwana me amfani,Allah ka kara mana imani,Allah yasa muyi karshe me kyau idan tamu tazo,Allah ya azurtamu da mutuwar shahada,Allah ya rufa mana asiri duniya da lahira Ameen.





AsmaBaffa
[1/1, 10:20 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA








2-5






Official





By
AsmaBaffa











Wannan page naki ne HUMAIRA Allah ya bar kauna.











Wajen malamin naje da kyar na rokeshi ya kyaleta yace tayi Sauri ta karbi sakon ta shiga aji, nima ina mikata mata na kama hanya sai gida,washe gari kuwa da sassafe na shirya na barwa su Ma'eeshah suyar kosai da Komai nayi shirin Tafiya rigakafin Polio dama indai ina rigakafin nan to dole Meenat ce zata zauna tayi dukkan abin da nake siyarwa har na gama Polio sannan taci gaba da zuwa,Sabo da Ammah bata yarda da talla ba shi yasa Sam bama fita talla a gida muke sana'armu, Ma'eesha kadai ke zuwa yanzu kafin na gama Vaccine.

Inda muke haduwa da ma'aikatan unguwar da mukeyi naje na samesu cikin Napep na sauka cike da fara'a da murna muka gaisa da juna,sannan na dauki akwatin da kwalaben Allurar suke ciki ga kuma supervisor dinmu da sauransu,sabo da box carrier ce ni ba a biyanmu da yawa dubu hudu da dari biyar muke dauka idan an gama,bani da ilmin da za bani Babban matsayi,haka mune da wahala mune muke daukan kudi kadan,a kafa muke Tafiya muna shiga gidaje ana house marking,sai 2pm muka tashi,washe gari ma bangaren unguwan da mukaje daban,a kwana na Uku kuwa da muka fara GRA din nan da na taba ganin Saurayi Aayan ya zaneni yau gidajensu zamu shiga aikin Vaccine duk da cewar ban taba shiga gidan ba,amma bana fatan shigarsa,ina ji ina gani muka zo jikin gate dinsu,

takadda aka rubuta sannan akayi knocking,Sojoji sunfi biyar ne suka fito kamar zasu masgemu,sai da aka basu takardar cewar yan Polio ne suka zo ga me unguwa a tsaye kuma dole sai an digawa yaro dan kasa da 5years,takardar suka karba sannan suka koma ciki zasu nunawa me gidansu,tunda suka shiga muna tsaye a wajen gate har sai da suka kwashe fin hour guda sannan suka fito sukace ance mu shiga,ma'aikatan sai murna suke zasu gano haduwar gidan,ni kam cikina ya duri ruwa bana fatan shiga Amma ba yanda zanyi haka na fara binsu kamar kwai ya fashe min a ciki sanye nake da red hijab dina me hannu har kasa duk da cewa nayi kyau Amma sam na raina kaina,

Muna shiga muka firgita domin ma'aikata da Securities ne ko ina,gidan ko ina kamshi ke ratsowa yana sheki,ga wasu motoci sunfi ashirin a gidan lafiyayyu,har round ne a gida kamar wani Babban titi tsakiyar youturn din ruwa ke tsiri sama yana shararowa a kasa kuma yana komawa kasan yana fesowa,a film ake ganin irin wannan gida jen,can gefe ga wasu sweeming pool har kala biyu,ko ina flowers ne a gidan,duniya guda ce a gidan domin wani part din ma ya dace ka hau mota sannan ka Isa in kuwa ba haka ba zaka gaji,wani soja ke mana jagora muna binsa a baya har muka zo wani garden ba abinda babu a garden din nan domin har da filin ball da Sauran wasanni iri iri,kida ne na wakokin Naija ke tashi har tsakiyar kai a manyan speakers,yan mata su Uku kyawawa yan gayu ne sanye cikin English wears Wando short da yar vest suna ta faman taka rawa ,hannunsu rike da kantama kantaman wayoyi,gefe wasu Yara ne sunkai su hudu mace daya da Maza su Uku sun sha kyau cikin kana nan kaya yan yayi suna ta faman buga ball, abin mamaki ko kallon inda muke basuyi ba kamar ma basu san mutane sun wuce ba, haka muka ci gaba da Tafiya muna yin gaba kadan sai ga wasu Maza zaratan samari suma hadaddun gaske baza su wuce 29 yrs ba su uku suna zaune a wasu kujeru masu malafa a sama game kawai suke bugawa suna dariya,ko wanne yasha kyau cikin kana nan kaya kamar a England,kaina nidai yana kasa Amma suma samarin inda muke ma basu kalla ba balle musa rai za a kula mu,tafiya dai muke muna bin Soja can wani wawakeken fili ne fetal yasha tsari da haduwa carpet dan gaske ne a kasan wajen da wasu manyan pillows ko ina yasha flowers ga wasu grass carpet wata mashahuriyar Dattijuwa tsohuwa tukuf muka hango kwance tayi kwanciyar Isa kamar sarauniya fatarta lumis fara kar duk da cewa ta tsufa Amma akwai hutu kayan marmari sun ratsata.

Mu matan da muka shigo dama mu Uku ne,da hannu tayiwa Soja Umarni nan muka ga yace gasu nan yayi gaba abinsa,har kasa na durkusa na gaisheta cike da girmamawa,su kuwa sauran matan cewa sukayi ai ma'aikata ne wlh baza su durkusa ba duk wulakanci da akayi musu ba wanda ya musu ko sannu bare kallon arziki,gata ita wannan ta tsufa ma Amma bata saduda da duniya ba har wani jin dadi take.

Kallonmu tayi tsohuwar ko amsa gaisuwata bata yi ba tana yatsina fuska tana kebe baki tare nuna Isa ta fara magana kuje dan Allah kun tsaya min a kai wari yana hawa min kai,da mamaki muke kallon ikon Allah,can ta jawo waya ta danna kira tana jan tsaki,sai ga wata da Alama yar aiki ce harda Uniform dinta dauke ta fito da ruwan roba tare da wani liquid soap me kamshi tace kuzo muje ku wanke hannunku sai a diga musu polio,Tsohuwar nan cike da izza tace wlh badan Hukuma da suke hadawa da ita ba baza a digawa jikokina ba sam,kazanta abinda ana kaisu asibiti ayi musu me kyau ko kasar wajene ma sai suje a diga musu Amma a dinga turo mana kazamai gidaje jasu can kuje,ina jin haka na daga kaina ina kallon sararin samaniya tare da kallon tsayi da girman building din nasu kamar baza a mutu ba katanga ma tayi tsiri sararin samaniya kai kace Mala'ikan daukan rai bazai iya tsallakawa ba,a raina nace to yaje har fadar shugaban kasa ma ya dauke Yar Adua,yau Ina sani Abacha?

Ina wannan tunani sai ga wasu dattijan Maza farare suma su Uku sun fito harda Abbi wanda na taba gani zama sukayi kusa da tsohuwar suna magana,lokacin mu kuma an jamu part din yan aiki nan aka dinga dirje mana hannu sannan suka fito damu, wajen yaran dake Garden tare da yan matan nan masu rawa da Wando 3qtr muka koma,nan fa da kyar aka jawo mana yaran ana cewa Hajja ce tace ayi musu suka bude bakin su tas dasu cikin taka tsantsan na diga musu yanda akeyi sannan nace to Alhmdllh mun gama mun gode,me rubutu ta cike talley sheet din,muna jiranta tana rubutu yan matan nan dake rawa dauke da cup a hannu suna shan lemo suna rawa suna bige mu Amma ko kallon mu basayi bare mu Sa ran ko Sorry zasu ce,gefe dasu muka matsa,wata ce ta fito cikin shiga ta alfarma zata kai 40years da Alama da yaranta a ciki domin munga suna daga mata hannu bye Mum,tayi murmushi Tare da shigewa mota Driver ya jata ta daura kafa daya kan daya tana karanta Jarida,Numfashi ne ya kusa daukewa sakamakon wasu motoci da suka keto cikin gidan a kalla sun kai guda biyar suka Parker zunzurutun Securities ne suka fito tare da zagaye motar kamar wani Shugaban kasa ne zai fito,bude motar sukayi muna tsaye muna shan kallo Wani arnen takalmi ya zuro waje nan take kamshinsa ya cika gidan me dadi,ya dan jima a haka kafin daga bisani ya fito cike da takama kamar wani Sarki,cikin kana nan kaya yake yau ma farin Wando pencil sosai rigarsa Silver color da Golden rubutu,takalminsa Silver yasha masifar kyau,duk wanda ya ganshi zai rantse ba mutum bane Sabo tsabar baiwar sura da kyau,ga iya daukan wanka yanda yake matukar kyau,yan matan nan ne muka ji sunce Hi Ya Aayan,ko kallonsu baiyi ba sai ma wani kallon Banza da muka ga ya watso musu kamar yaga kashi,sabo da nima gwanar mugunta ce a raina nace Allah ya kara shegu ga ubanku a girman kai gwara haka,

Matar da muke aiki da ita wato Salima itace ta kalli yan matan tayi dariya wai irin ta tura musu haushi,ai kuwa ba zato muka ji karar Mari a fuskata domin suna rawa tunaninsu nice na musu dariya shine daya a ciki kawai ta daukeni da shegen mari wanda ya jawo hankalin wannan Saurayin da Sauran Ma'aikata kaina,Kuka na fashe dashi a wajen nan take na fadi a wajen na dinga shure shure,wanda muke Polio ne suke bani baki kan nayi shuru mu tafi,cikin kuka nace Wlh sai na rama mikewa nayi a hasale na cakumo daya a Cikin yan matan wanda ban san wace ta mareni ciki ba nidai na kama daya tare da makalkaleta na cisgo gashinta na murde na ja da karfi,sannan na dalla mata mari har biyu na sake ta na zura da gudu domin sunyo kaina da kwaben lemon me tsada da su??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ke sha zasu fasa min a kai,daya ciki ta jawo Hijab dina ta baya,Securities sun taho Saurayin nan ya dakatar dasu cewar a kyalesu,suna kallo sun rike min Hijab na sunkuya tare da zare Hijab dina na bar musu a hannunsu na Arce jikin gate ina rokon a bude min,Saurayin nan yace kar wanda ya bude min,Har yan matan nan suka zo kaina na kara runtumawa da uban gudu amma saida suka kamani suka rufarmin suka dakeni sosai naji jiki sai da suka gaji dan kansu sannan suka tafi ina yashe a kasa,sai Hawaye nakeyi abokan aikina suka dagani da kyar sannan naga wannan Saurayin yace a bude mana mu bace a ganinsa ya tsani mata ko da yan uwansa ne baya kaunar ganinsu,sai da na tabbatar an bude mana nasa kafa ta daya ciki daya waje sannan nace kai yan mata?duk kuwa suka juyo suna kallona nace Allah ya Isa kuma sai na rama watarana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login