Showing 93001 words to 96000 words out of 175038 words

Chapter 32 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6873

dubu biyar biyar ita da Mardiyya,Badan Allah kika basu ba ke nan? Dan ki kankaro mutuncinki kika ce,kin basu kuma kina jimami kina tunanin kyautar da kikayi bata dace ba dama baki basu ba,kinga ba lada kenan kuma Sabo da suna miki kema shine kika rama musu,ba haka ake kyauta ba,iya wacce kikayi niyya ita zakiyi kuma da zuciya daya kisa Iklassi dan Allah kawai ba wani tayi min bari na mata ko ki Bada ki koma kina tinanin kudinki dama baki bayar ba,kinga ba lada sai ma ko Zunubi,kuma 10k ma tayi kadan nayi tunanin ma sunfi haka,amma abinda bana so shine indai kaya ne ni na siya miki to bana so baki amfani dasu ba ki bayar wata tayi,ke na siyawa ke nake so kiyi kwalliya dasu Sabo da ina so naje na siyo da hannuna wasu ma baki san tsadarsu ba shi yasa,idan kina son kyauta to ki karbi kudi wajena kije kisiyo ki ajiye duk wacce zaki bawa ki bata a naki,wanda na siya miki sai in kinyi amfani dasu ko na canja miki new sai ki bayar da wanda kike amfani dasu, haka akeyi ba a daukan kayan miji da ya siyo ki masa kwalliya ko amfani baki dashi ki dauke ki bawa wasu in kina haka Bazan kara bari Frnds dinki su zo.
Mata wasu don son gwaninta sai miji ya siyo miki kaya dan ki masa kwalliya ki birgeshi sai a dinga gayyato Frnds ana basu maza basa Jin dadin hakan.

Sai kuma tambayata yaushe kika je gi??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????dan su Sayyah ban san zancenba baki fada min ba? Jikina yayi sanyi nace daga schl rannan mun tashi frnds da yawa suka ce ba nisa daga schl zuwa gidan su Sayyah zasu je gaida Mamanta shine nima na bisu muka tafi tare,su basu da aure ai?ae duk yan mata ne,ke kuma fa? Ina da aure mana, sai akace miki matsayinku daya yanzu? Zaman kanki kikeyi da zaki je wani wajen ban sani ba? Da kika dawo baki fada min ba mala'iku na tsine miki,shi yasa mazaje da yawa basa so matansu suyi aiki ko makaranta idan sun aure su sai a fake da wajen aiki ko schl ayi ta yawo mara amfani,wasu ma daga can suke samun hanyar bin malamai da bokaye ko tarbiyyarsu ta lalace yanzu badan Allah ya kawo zancen ba baza ki fada min ba kenan? Kuka na fara yi masa to kayi hakuri Bazan sake ba tunanina ba wani abu bane,Shi yasa har kasuwa na raka wasu ma daga schl,munje gidajen wasu ma siyo wasu abubuwan da yawa Ban fada ma ba kayi hakuri na daina,kishi ne ya kama Aayan harda kasuwa ma gidajen mutane Maza nata kallonki kamar budurwa? A rude nace ai ban kula su ba Allah duk da yawa sun tareni wai suna sona nace ina da aure,Aayan takaici ya kara rufeshi ana gane masa mata wasu sunji muryarta ma yace daga yau ko an koma schl kin daina zuwa tunda bakya jin magana ni bana son irin wannan, kuka na nakeyi nace ni me nayi to dan Allah? Kayi hakuri Bazan kara ba daga schl wlh sai gida, na yafe miki ai Amma karki sake ki san kina da aure bana son irin shirmen nan na student,kamar an matse bakikin ki gashi kinzo kin fada min ana miki fada ki fara wani kuka,

nace to yanzu duk abinda kaine ka siya min kar na bawa kowa? No ba haka nake nufi ba,sai kinmin kwalliya dashi sosai idan na canja miki wasu sai kwashe sauran ki bayar tht's what I mean, na gane Insha'allah ba matsala,dama kana son kwalliyar tawa ne? A'a kawai dai ke kiyi kyau,wani haushi ma naji kawai nayi shuru har bacci ya kwashemu.
Sati biyu tsakani Meenat ta gama Exam tare da Ma'eesha suka shirya zasu tafi can kauyen Ammah wajen dangi za suyi sati daya daga can su Wuce Maiduguri nan dangin Abba za suyi sati daya, na hada musu goma ta arziki tare da Driver suka tafi abinsu,ni kuwa ina gida tare da Aayan,sai Ameer da yake dan shigowa idan yaga dama bai son yazo yaga muna tare da Aayan kunya yake ji,na tambayi Aayan ya bani kudi na fara zuwa gidan su Sayyah wajen Mum dinta gyaran jiki,haka take gyaran tana bani kayan tsumi,duk na kara cikowa skin dina sai sheki,santsi tare da kyalli ga uban laushi.

Nawwara ta min waya zata zo min again nace bana gida munyi Tafiya bana so tazo,amma Sabo da naci yau Saturday ina kitchen Aayan ya ce na mishi Shawarma na gane yana son Kalar tawa,knocking naji sai da na leka ta yar kafa naga Nawwara ce,abin ya daure min kai to uban me tazo yi nace mata bana nan ana dole ne,komawa nayi kitchen naki budewa tayi ta danna Door Bell shuru.
Khaleel yazo wucewa ta wajen ya ganta a tsaye tsawa ya buga mata wanda ta kusa sumewa uban me kike mana a gida kamar na ubanki anki bude miki ki tafi mana kin cika mana gida Nonsense,jiki na rawa Nawwara ta kama gabanta,Haneefa tana kallonta ta saman Bene tunaninta daga wajena take zata tafi shine taji Haushi an fara cika musu gida da baki,Sajeeda ma tana wajen suna kallo akwai ruwa a hannun Sajeeda roba guda ta dakko zata sha sai ta fasa sha ta saita kan Nawwara ji kake Gaf zafi ya ratsa Nawwara tunaninta Bom ne ya fashe ta kurma ihu ta fadi kasa tana Bom...Bom...ta mike da kyar tana faduwa tana tashi da Rarrafe ta Isa bakin gate,Haushi ya kama masu gadi ta ruda su tana Bom tsawa suka buga mata tare da turata waje suka jefar kamar wanki suka kulle kofa.
Nawwara tana karasawa gida ta fada Toilet tare da barkewa da zawo ga gefen gashinta ya fashe.

Na gama hada masa Shawarma na shirya komai a tire na wuce Bedroom dinsa zan kai masa na bude zan shiga kenan Naji Aayan yana amsa gaisuwa da Alama da mace suke waya da Sauri na shiga Amma sai naji yaci gaba da wayarsa, kwana biyu kiyi Hakuri Ban kira naji ya kike zama a kasar ba,Da Sauri na zauna a gefensa tare da gwara kaina da nasa na jonesu waje daya wai so nake naji Muryar macen ko Budurwa ce Amma bana jin komai,Ya matsa nima na kara matsawa jikinsa,ya matsa na kara matsawa again,kasar akwai dadi yana Murmushi harda wani Ladabi yakeyi na musamman ina jinshi ya gama wayar sannan yace min Allah ya shuryeki nace Ameen ina turo baki idan wayar gaskiya ce a fadi sunan wacce ake waya da ita Mana aji,yace to yar Us ce Sarkin zargi, wa kake dashi a can me jin Hausa na furta nayi kicin kicin,ki bari zata zo Soon kasar nan zan kawo miki ita idan tazo sai ki fada mata haka in kin Isa, baki na turo tare da cewa ni mutunci gareni an cema Allah bata Isa ta zo nan gidan ba ko wace sai na balla yarinya,murmushi ya saki tare da cewa ai ni zan tare mata fadan,da kai zan hada ai sai na mayar mata da fuska ta koma baya,keyarta ta dawo itace fuskarta,Dariya yayi yace Allah ya kaimu dan baki san wace ba shi yasa, ki shirya min kayana zanyi tafiya,gaba na ya fadi rass nace ina zaka je?Us daga can zan wuce Saudiya,Hawaye na fara tare da turo baki cike da shagwaba nace yanzu ni kadai zaku bari? Amma kasan Tsoro nake ji ko ni kadai ban iya zama a gidan nan,Ga Ameer nan zai dinga zuwa yana tayaki Hira Amma da dare kuma sai dai ki kwana ke daya,Yarima na jirana tare za mu tafi zanyi 2-3wks, ganin kamar bai damu dani ba nima kawai na share shi nace a dawo lfy bari na hada ma kayan, zuciya ta a jagule gaskiya baya so na ya kasa sanar dani zai Tafiya sai yau da zai tafi kuma ko ajikinsa irin bai damu da rabuwa dani ba,Allah ya gani nayi kokari na da zan iya,da ace bana sonsa da tuni na fita daga harkarsa Amma zuciyata ta kasa hakura dashi na rasa me yake damuna gaba daya,shi kuwa shawarmarsa ma yake ta ci ko a jikinsa dama Already naga yayi shiri tare da hadewa cikin kana nan kaya.
Harda goge yar kwallata ina hada masa kayansa na gama komai tsab yanda ya dace na ajiye a gabansa, yana cin abincinsa na dauki paper da Biro nayi dan dogon rubu a takardar me Santayana mutum zuciya amma fa ba na love ba,na adduar Tafiya sannan na Sa a tsakiyar kayansa ba tare da ya sani ba.

Yana gama ci ya mike yana kara shiryawa ni kuma na sauka kasa ina palo a zaune saman kujera duk raina a bace yake kadan nake jira sai gashi ya sakko cikin shiri ya kalleni tare da zuwa gabana ya zauna a gefe na jikinmu na Gugan na juna a hankali yace zan tafi Baby, ban san sanda na zabga masa uwar harara ba nace Ina ruwana to ni na nasan da wata tafiyarka ne,Kallona yayi tare da cewa shirya mu tafi tare am serious wlh i wl be missing you is Better na tafi dake,Harara na kara watsa masa ae ai dole kace haka tunda zaka tabe min jiki to Bazan je ba,ba Us ba ko birnin Sin ne Ban zuwa,Har fa Germany? ban san sanda nace Allah yasa Agadaz zamu je hhh ya dinga dariya in bake shashasha ba kin taba ganin inda Agadaz tafi Germany zaki Hada Niger da Germany ne,ina turo baki nace to ko Birkinafaso ce ehe,Dariya yayi yace ke ana maganar Europe kina kawo ?frica,nace to ko Egyft ce harda Morocco kai ko Algeria ce,nan ma yana ta dariya,yace to Saudiyya fa? Nace ko Qudus ce,dan Allah shirya a yau za miki komai mu wuce bana son bana ganinki kusa dani,uhm sai kayi kuma zancen kake so Karuwa taji me Wa'azi tace aiki ne bai isheka ba, Marairaice min yayi sai da nayi mamakinsa kamar wanda ke so na da yawa, wai sai kuma naji tausayinsa Amma na rantse Bazan bishi ba,nace ni Bazan je ba fa,wai harda jin haushina ya juya tare da fara Tafiya,nace Aayan... Juyowa yayi nace zo pls,tunaninsa zance zan bishi ya dawo nace nasan me kake so a jikina tattaba ka tafi abinka kaji,wani haushina yaji me nake nufi?au tunanina ma jikina yake so shi yasa yake taba ni etc Amma tunda haka nake tunanina zai nuna min,tsaki yaja ya juya abinsa,nace a dawo lfy Allah ya kiyaye Hanya ayi addua me yawa Sabo jirgi zaka shiga ba dabara ga wanda aka kwashewa kafafu kasan duk wanda aka kwashewa kafafu kana sama to dabara ta kare sai du'ai,dariyarsa ya danne kawai yayi gaba,Yana fita Ameer ya shigo nasa Katon Hijab dina,jefi jefi muke hira yana ta bani labarin yan matansu da suke yaudara muna dariya, gaskiya Anty gidan ba dadi Ba Maeesha da wannan yarinyar da na sani ma na bisu munje tare naga Kauyen,Bani Address na bisu Allah zanje,Ni kuwa ya ban mamaki kawai dai na bashi Address din, tun daga Lokacin Ameer yacewa Abbi da Hajja tare da yan gidan kaf wai ya tafi Abuja interview Zai nemi Visa a wani Embassy idan ya samu,Hajja tace bazai tafi a mota ba Amma yace a mota zai je,Nufinsa tunda Rimin Gado zai bi su Meenat sai ya kaisu a mota har Airport su shige jirgi sai Maiduguri gaba daya har da shi,Hajja ta damu ita bazai je har Abuja a mota ba sai a jirgi haka ya hakura Driver ya kaishi har Airport,Driver na Tafiya ya shige Napep har inda zai hau motar Rimin Gado ya shiga Drop fyalleliyar mota karama ya biya kudi shi kadai har Cikin kauyen Rimin Gado can rugar fulani.

Da tambaya ya gane gidan da su Meenat suka sauka yan fulani sukace yan matan Larabawa yan birni ga gidan can,Ameer sai wani make jiki yake yana karkabe kayansa tare da tabe baki yana kyankyami wai,a kofar gidan ya tura yaro wai Meenat da Ma'eesha suzo inji Ameer dan Birni,Meenat ce ta fito kofar gidan tasha Atamfa riga da Zani me style tayi kyau,tasha mamaki ganin Ameer ne da gaske to ko lfy ko Mufee ce wani abu ya sameta Meenat ta tambaya da tsoro a fuskarta, kin wani tareni da tambaya zuwa nayi naga kauyenku to Anty ce ta bani Address bakwa gida duk ba dadi shine nazo,Murmushi Meenat tayi tare da cewa kayi Kokari bari na fadawa Inna to,
Wajen Inna tsohuwa tazo ta sanar mata,Inna tace to kuma sai ki barshi a waje gidan tsohuwa ne kice ya shigo,Maeesha ce ta fita tana dariya tace lallai ya Ameer kayi Kokari ina motarka?ke zan mareki ko wacce sai tambayar tsiya,shugo to ciki,Ameer yabi Bayan Meenat suka shiga gidan,komai na kara ne dakuna Uku irin na ruga,Tsohuwar yayar Ammah ce ita kadai ce a gidan sai jikanta babba kuma ya tafi kiwo can wani daji sai shekara ta zagayo zai dawo gida tare da shanunsu.

Gidan Babba ne me dan fadi tare da katuwar bishiya a tsakar gidan,yasha shara tsaf dashi,Ameer da Ladabi ya gaisar da Inna,da Fara'a ta Amsa sannan tace to ajiye kayan naka ga dakin da zaka zauna can,ke Meenatu kai masa kayansa,Meenat ta rakashi dakin tabarma ce katuwa sai katifa yar siririya dai dai mutum daya ko juyi sai da? ka mike sannan ka juya,Ameer ya dinga dariyar katifar tare da cewa sai kace ta jarirai wannan har katifa ce,ni Yanzu ya zan iya kwana a nan kato dani? Daki yasha tsafta dai ba laifi Amma katifar nan gaskiya kice ta canja min wata,Meenat da Sauri ta sa Hannu tare da toshe masa baki tare da cewa rufa mana asiri kunnenta kamar micijiji yake masifaffiya ce wlh ta gaske bar ganinta haka kunyi faran faran yanzu tayi mana tatas a gidan nan.

Hannunta ya janye a saman bakinsa tare da cewa ke baki da kunya ni kamata zaki toshewa baki kamar yaronki kato dani,ni gaskiya ki fada mata ta canja min katifa,Ai ko karaf a kunnen Inna sai muryarta suka ji tace Iyyeeeeeee... Kai kake bani kudin?ko jikana yana gari ai bazai canja ma katifa ba,duk girman wannan makekiyar katifar yo ni Allah na tuba duk ranar dana kwana a saman ta kasa Sallar asuba nakeyi,har makara nakeyi sai rana ta fito nake tashi Sabo da laushi da girmanta,ba karamin daraja mutum nake Ba zan barshi ya kwanta saman wannan katifar tawa,ai wlh ko su Meenatu basu Isa ba,amma zaka nuna min kai dan birni ko kinibibinka ne? Murmushi Ameer yayi jin yanda take ta mita tana yabon katifar da take duk ta jeme duk ta side tudun babu Sabo da taci duniya ta gaji gata siririya ta gaske,Ameer ya fito wajen Inna yace Inna ta dakina da nake bacci a birni sai tayi girman tsakar gidan nan gaba daya,kinga Bed dina kuwa like...Hannu Inna ta daga masa kaji shakiyin yaro yo ko Sarki ne ina zai samu katifa kamar girman tsakar gidan nan in ba karyarku ta yan boko ba,sai dai ka shiga gidan Radio a Sa zancenka a labarin nishadi na tatsuniya Amma ba a wajena ba baza ka samu karbuwa ba

Dariya Ameer yayi tare da cewa dan kawai baki sanni bane Inna kalli fatata fa kalli kyauna, me yasa kasan da haka baka Sako gadon naka a mota ka taho dashi ba karka dameni kaje kayi wanka ga abinci miyar harda Naman Zabo,Maeesha sai dariya suke har suka kai masa ruwan wanka bayi,yaga bayi ba rufi ba komai fayau ko murfin kofa babu gashi na kara da Ameer ya fito tare da cewa shi ya fasa wankan Tafiya gida zaiyi kar dare yayi masa bazai iya amfani da toilet dinsu ba,Toilet ce kadai zata koreshi daga kauyen,rokonsa sukayi yamma Liss yayi Manage zuwa gobe sai ya tafi,ya shiga haka ba yanda ya iya kayansa ma daya cire sai ta saman katangar ya mikawa Meenat ta rike masa su,

Ya mike yana wanka jikinsa duk kumfa wata yar fulani da kwaryar nono ta bayan gidan zata wuce sukayi ido hudu da ita ta kalleshi ya kalleta Amma iya kansa zuwa kirjinsa take iya hangowa ta wajen gidan,Ameer yaga taki dauke idonta ya ware mata hannu alamar zagi dakuwa yace karbi wannan kan Uwarki,bata gane ba ta tsaya tace me kace yace baki gane ba? Hakan nana yana ware mata yatsu wai yaren mutan kauyen ya mata na zagi Haka nanan,Tace ni yace a'a ubanki nake nufi baza ki bar nan ba sai na fito na fasa miki baki,Yar fulani tace yo ni ina ruwana da kai dan zanje tallana, ko tsirara na kalleka me zai firgitani,Kaga naga kalar ta Iro,Nasan ta Ja'e,har gaisawa na kanyi data Lawalli duk ranar kasuwa iya kaci kace ta wani fara ta wani ba to duk cikinsu ta Ja'e ce Baka wuluk me zaka bude min ido dashi ta ja tsaki tayi gaba,Ameer ya zaro ido waje tare da bude baki yana mamaki yace Ana iya shege a kauye ba kunya ba komai,ana cewa yan Fulani masu kunya etc ashe duk karyace, ya kwalawa Meenat kira ta bashi kayansa nan ma sai kanta ta sadda kasa sabo da kunya kar ta hango kirjinsa.
a gaggauce ya karasa wankansa ya karbi kayansa ya fito,Abincin ma ba dadi kasa ci yayi yace shi wlh gobe zai tafi da Safe,Gari na wayewa ko karya wa yace bazai yi ba,dama tun jiya ya karbi number din me motar da ya kawoshi jiya yace ya dawo gobe da sassafe ya daukeshi,Me mota yaji yanda ya samu kudi da Sauri ya Amsa, ai kuwa 8am sai gashi yazo daukan Ameer back to Cikin Gari,Ameer da murna ya dauki jakarsa tare da basu kudi da yawa har Inna sai godiya take tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login