Showing 87001 words to 90000 words out of 175038 words

Chapter 30 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6881

Kamshi naji ya cika sashin ba tare da na juya ba nasan ma waye wani sanyin dadi naji a raina ban ma san Sanda na juya na kalleshi???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? ba cikin 3qtr da riga yayi matukar bala'in kyan da ban ma sanshi dashi ba sai yau, Na kalleshi kamar nace kayi kyau sai na fasa kar ya rainani,Shima yana ta kallona da kyar kamar dole yace u look Good,tnx nace tare da fari da idona ina wani wanashi warrr,bai san sanda yayi dariya ba yace naga wannan,Na kara waresu na lumshesu,murmushi yayi tare da cewa wannan ma na karba, na kara juya idona suka kalli up and down,Nice One yace dariya nayi tare da rufe idona da tafin hannuna yace wannan ma ba laifi na kara kyalkyalewa da dariya tare da fara zuba masa abincin.

Ameer ne gaban Hajja yana zaune tana tambayashi to Ameer yaushe zamu je ne wajen malaman karfa muyi sakaci,dan karta gane yace ah Hajja ai na gama shiga jikinsu ni dama Umarninki nake jira muje kawai Saturday ko Sunday ba matsala,Hajja tana ta murna tana yawwa yanzu naji magana bana kauna na bude ido naga yaran nan a gidan nan,wlh bana kaunarsu,babu wata mace dana tsana a duk matan da Aayan ya aura sama da wannan,nema take ma ta rusa min kan zuria ta,abinda na dade ina ginawa take nema ta rusa,Ameer yace gaskiya dai nima bakiga yanda nake jin haushin shiga part dinsu ba,ba a son raina ba,bana so ko kadan basu da kunya,Hajja tace ai babbar cikin itace duk shegiyar ita ke juya komai Mufeeda ba,Ameer yaji haushin zagin Mufee da Hajja tayi Amma ya danne sai yace a'a Hajja ai ta tsakiyar data karshe Meenat da Ma'eesha sune shegun,Hajja taja tsaki jibi wani suna na Aljanu malam,tun daga sunan ma kasan na aljanune wai Ma'eesha,Dariya Ameer yayi yace Hajja kenan ni na matsu ma muje a gama da yaran nan baki daya,Hajja tace Allah ya kaimu asabar sammako za muyi asubanci da wuri.
Ranar Asabar da wuri Hajja ta shirya tsaf ta nufi wajen Ameer, ta fara buga masa kofa yasan itace kawai sai ya koma kalar me cuta ya kwanta kamar me cuta ya fara numfarfashi kamar zai mutu,Hajja taji shuru ba a bude ba nan take ta tura kofar da kanta,ai ta hango Ameer na murkususu da Sauri ta shiga tana lfy dan nan ina can ina shiri ashe kana cikin wahala me ya sameka?ta furta kamar zatayi Kuka tana girgiza shi,Da kyar Ameer yace Hajja.....ba...na...boye..miki...komai...aure...nake...so...ciwon...sha'awa ne...Ya motsa...Me yasa baka fada min ba tuntuni idan ka mutu ka barni ya zanyi tashi muje asibiti,Ameer yace Nasha magani Likita ya kawo dazu yanzu zai daina,Hajja tace ai ko dole ayi maka aure ko da Sajeeda ne,Ni wlh idan aka bani Sajeeda sai dai ciwon ya kasheni bari zanyi ya kashe ni Bazan iya yin komai da wannan ba,Hajja tace to kwantar da hankalinka sannu kaji,mu bar tafiyar sai wani satin idan Allah ya kaimu,Allah baka lfy kaji,Ameer a ransa murna yake yace Ameen yana jin dadi an fasa zuwa.








AsmaBaffa
[1/21, 11:08 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA







86-90







Official











By
AsmaBaffa









AGAS, MMN HUSNA,AMINA AMINU, Mom Ammar page dinku ne domin jin dadinku.








Ameer yana ta rashin lafiyar karya sai Sunday yace ya warke da yamma ya feso uban Wanka sai part dinmu lokacin kawata Nawwara sarkin son jin Gulma da munafunci tazo min ziyara nasan badan Allah tazo ba,ganin kwakwaf tazo taje ta samu labarin fesawa,Kuma Alhmdllh taga gida iya gida,yau ta tabbatar da gaske gidan kudi nake aure ba abinda ban bata taci ba na jin dadi munyi mata babbar sauka, taci kwalliyarta ta masu rufin asiri tayi kyau kuwa ba karya, muna Hira a palo ta dameni sai ta gano Cikin Bedrooms nace to muje na rakata ko ina ta gani banda dakin Aayan,wai sai tace to dakin mijin naki fa ko duk yanda muke dake baza ki barni na gano kayan alatun ciki ba? Shuru nayi mata,tace kefa Amaryace gidan Amarya nazo gani kinga kuwa dole na ga ko ina,Nasan gulma ce kawai Allah kiyashemu mu abinda akeyi kenan yanzu.
Murmushi nayi nace banda dakin mijina ko baya nan baza ki gani ba bare yanzu da bacci yake ma,ina laifi da na nuna miki sauran me kike so ki gani?

Tabe baki tayi tare da cewa a hankali zamu shiga na kalla bazai tashi ba ta ya zai san mun shiga ma tunda bacci yake,Hmm Nawwara kenan ki hakura haka yafiye miki Bazan bari ki jawo ya tashi daga bacci ba,bai dade da farawa ba ma da kyar na samu ma ya kwanta Sabo da ya huta jiya bamu samu munyi bacci da wuri ba shine kuma zan bari a tasar min shi,ke a hankalinki ya dace ki shigarwa mace har dakin miji? Bada ni ba,Nawwara tace yaushe kika koma haka Mufeeda? Dariya nayi kawai na jata muka koma kasa nan muka hango Ameer ya shigo yana zaune,Ameer lfy kwana biyu kuwa? Murmushi yayi tare da cewa ai baku da kirki kunga shuru ko ku nemeni,Nawwara ta gaisa shi ya amsa tare da dauke kai can gefe,Nawwara sai gyara riga take tana kara bude mayafi tare da karairaya don kawai ta birge Ameer yace yana sonta itama ta shigo gidan kudi Amma ko kallo bata ishe shi ba, waye wannan fa?Nawwara ta tambaya, cousin din mijina,tace ok,muna haka sai ga Aayan yana sakkowa daga samansa yaci uban wankan Wani danyen yard Fari kar yanda ya hadu ba a magana ma,wani kishi ya soke ni bana so Nawwara ta ganshi kar taji tana sonsa nasan duk wacce taga Aayan sai taso ace shine mijinta,Aayan kuma shima bana so ya ganta Sabo da tayi kwalliya harda jambaki kar ya kyasa shine nake kishi sosai.

Nan take na bata rai kamar na boye Nawwara Amma ba hali,mikewa nayi da Sauri na Isa gabansa,Murmushi ya sakar min tare da cewa zanje wajen Daddy ne sai na fita wajen Yarima akwai wani abu da zamu tattauna a kai,Baki na turo gaba ina shagwaba ni...to wai me zaku tattauna? Kallo na kawai yayi ya share maganar yana kokarin wucewa,Nace dan Allah zamu je Saloon anjima,na aiki Drivers din gidan nan basa nan gaba daya kowa da inda na aikeshi, sai muje a Napep ko Ameer ya kaimu,a'a ke baza ki fita ba fa yace Direct,na marairaice pls kaji,ki ebi kudi ki bawa su Meenat Ameer ya kaisu Amma banda ke, ki wanke naki a gida mana, ina nuna kaina ni din?Yace kefa din,ya wuce zai fita bai ma kula ko da bakuwa ba har ina murna sai ji nayi Nawwar tayi shishigi tace Ina yini, lfy Alhmdllh ya furta da fara'a tare da tambayata frnd dinki ce? Nace ae tare muka taso a unguwa daya sunanta Nawwara,yace Ok thts Good Amma kina gani zan fita baki fada min ba,da Sauri na share zancen ina jin Haushi ana kalle min Aayan dina nace Zaka biya Office ne? Me zai kaini Office yanzu kuma,a dawo lfy Allah ya kaika ya dawo da kai lfy,yace Ameen kafin ya karasa na bude masa kofa kawai Sauri nake ya bar gidan Nawwara kar ta ganshi,yana fita na rufe kofar sannan na kalli Ameer nace Ameer Saurayi mijin yan mata,masu tashe da ji da kai,Allah ya hadaka da mata ta gari zukekiya Amma da ta sha kallon wanka da iyayi,Dariyar jin dadi Ameer yayi yau Ina yabonsa da kaina sai yace haba Aunty ai mijikinki ya fini,nace daga shi sai kai kusan irin halinku daya,wlh ya fini dan mijinki ne ba kya ganin laifinsa,nace uhmm to me kake so na baka kaci yau? tuwon danyar shinkafa miyar Kubewa danya da kifi Amma sai dare,Nace ka gani ko na fada ma irin halayenku daya da Mijina,Nawwara tana zaune tayi shuru sai tunanin Aayan take ya gama Tafiya da zuciyarta gaskiya zata dage da zuwa wajena kullum ko Aayan zai so ta ya kara ta biyu da ita ta shigo itama ta kwace gidan,ko hannunka ya rike ai ka dace wannan,cin Amanar Mata bama kawai a aureshi ba kawai a shigo a kwace gidan,a kori uwar gida ko a wulakantata su kuma su zama sune a gaba.

Ameer ka kai min su Meenat Saloon mana dan Allah,Ameer ya turo baki Amma Aunty kin san Meenat bata girmama ni ko dama Ma'eesha ce Amma wannan sai girman kai bana son kulata ni dai,kayi hakuri ka jira yanzu Meenat Zata dawo sai ku wuce Ma'eesha tana daki,kasan ina ji da kannena nafi so kullum na gansu sun hadu,Ameer yace ai ku dama Hadaddu ne Aunty,amma in kana da kyau ka kara da wanka.

Muna hira har dai Meenat ta dawo tana cin abinci nace su shirya,dama sun dameni zasu je Saloon,kudi na basu Ameer yace haba Aunty ina wajen sai kin basu kudi ina da kudi,Meenat tace mu dai a bamu kudinmu Sis Sabo da tsaro, na basu kuwa,tana karba ta Radawa Ma'eesha kinga munyi cuwa cuwa mun samu na kashewa mu kara a schl,shi kuma ya biya mana na Saloon babu ko sisinmu,Ameer yaji Me Meenat take fadawa Ma'eesha.

Ya kaisu hadadden wajen Saloon tare dashi suka shiga yaki fita wai sai yaga kalar gashinsu kamar na Maza ne ko dogo ne yanda zai musu dariya da kyau, Meenat ta zauna tare da warware gashinta Ameer ya dinga mamakin tsayinsa kamar na larabawa,haka Ma'eesha ma yace Allah ya taimakeku kuna da gashi yau da sai na dauki pics nayi status a social media,Meenat tayi dariya tare da cewa ta Allah ba taka ba to yaro,nine yaron Amma kin san na girmeki nesa ba kusa ba ma kuwa,Maeesha tace kaine ma Kwaja karewar girma nan suka fara dariyar Kwaja,yace zanje na dawo kafin a gama muku,Meenat tace a taho mana da me zafi tare da Me sanyi,fada kawai tayi sai ko gashi ana gama musu ya dawo,suna shiga mota suka ga Take away guda Wajen biyar wai duk nasu ne har Nima da nake gida,Gasassun Kifi da chips,sai Hanta lafiyayya taji hadi,ga su ice cream da yogourt.

Suna shigowa lokacin Nawwara ta min Sallama ta tafi har kudi na ebo cikin na Aayan na bata Dubu biyar da kayan kwalliya iri iri ta dinga murna tana godiya,ni kuwa Zama nayi na fara tunanin irin kyautar da nayi mata kamar wacce tazo da asiri na bata kudi masu Uban yawa haka kuma wai harda kayan kwalliya ma.

Su Meenat ne suka gyara min gidan ni kuma nayi girkin na shirya komai a Dining sannan na Shiga wanka ina tunanin Aayan yanzu suna can suna Hada min plan a raina nace duk kuyi Ku gama zaku San dani kuke zancen,yau ba Sallah nake ba shi yasa kwalliyar da nayi har da Nail paint nasa a farcena sky Blue nayi wani red wani Blue ba karamin kyau yayi min ba,nasa wando tight 3qtr me kyau baki,sai rigata Sky blue ta hadu gashina yasha gyara sai kyalli da kamshi nake ta ko ina ka rantse Balarabiya ce ni,na fito tare da Shiryawa Meenat Abincin Ameer a wani kwando me kyau nace ta kaiwa Ameer can part dinsu sabo da shi yace bazai dawo ba na bayar a kai masa abincin.
Meenat ta karba ba musu ta fita me aiki ce ta nuna mata ta shiga part dinsu su uku Mazan Ameer,Khaleel tare Mujaheed gaishesu tayi sannan ta ajiye a gaban Ameer tace ya Ameer gashi inji Sis,Yace na gode,ita kuma ta juyo zata dawo,Khaleel Kansu ya daure sai mamakin Ameer su ke yanzu abin nasa har ya kai haka? Gaskiya zasu fadawa Abbi me yake shirin faruwa kuma fa dasu aka cinye abincin nawa.

Sajeeda taga lokacin da Meenat ta shiga ta fito daga part din su Ameer shike nan ta dinga fesawa cewar Meenat bin maza takeyi abin har part din su Ameer,da sauri ta shiga sabo da kishi ta samu Ameer ai wlh Allah ya Toni asirinka dama abinda kakeyi kenan,to sai kowa yaji macuci yanzu har ajinka ya zube da zaka nemi wannan?ai gwara ko me kake so kazo wajena.
Khaleel da Mujaheed suka Mike tare da basu waje,Ameer ko kallonta baiyi ba har ta gama masifarta,yace ai ta fiki daraja da mutunci a idona ta kuma fiki class,asararriya me rabawa mazan waje,ke kike haka shi yasa kike tunanin haka kowa yake irinki,Sajeeda ta rushe da kuka tare da ficewa da Sauri.

Washe gari Sayyah kawata ce ta min waya zasu zo min ziyara tare da wasu kawayenmu yan Schl Mardiyya da Islaha,So nake Aayan ya bar gidan kafin suzo kar ma su ganshi wata ta soshi,5pm suka ce zasu zo ni kuma 4pm ina yin Sallah na bar kitchen na shiga wani Palo da nasan Aayan yana can sunyi wani meeting da abokan kasuwancinsa,Nasan ba kowa yanzu shi kadai ne,yana zaune ya baje yana cike wasu takaddun Office,Sallama nayi masa a hankali tare da Zama kusa dashi har muna gogar juna nace sannu da aiki,lemo ya kurba sannan yace Yawwa har kin gama aikin? A'a wai yau baza ka fita ba har yamma tayi? Tabe baki yayi tare da cewa no,nace yau fa Tuesday guda ai ya dace ace mutum yana aiki,Yau bazan iya fita bane shi yasa,Shuru nayi can na kara cewa gaskiya kana hutawa da yawa baka fiye fita ba jiya ma fa baka fita ba sai yamma liss,yau ma hakan take ai sai yamma zan fita,gashina na gyara na gaba nace yau muna tare kenan har dare? Bironsa ya ajiye sannan ya kalleni sosai yace korata kike?so kike na fita kenan anya kuwa kina da gaskiya tsakanin jiya da yau,jiya ma fa har murna kike na fita,a'a ni bance ka fita ba tambaya nayi na Mike zan bar palon ya riko min riga na koma na zauna amma sai nace aiki fa nakeyi kasan zanyi baki, je ki karasa aikin to,mikewa nayi na fita,har na rufe kofar na kara budewa a hankali tare da leko da kaina muka hada Ido na washe baki tare da cewa to ko zaka koma Bedroom dinka zan gyara nan? Wai wayo zan masa kar ya fito yace zaije samansa bakina su ganshi, ban san me kike nufi ba zo ki kwashi papers din sai na koma can din,Da murna nazo na kwaso masa ina bayansa yana cewa mutum da gidansa sai yanda akayi dashi ya zanyi,ina dariya har muka je Bedroom din na ajiye masa komai tare da cewa asha aiki lfy ranka ya Dade,murmushi ya saki yasan dana ce Ranka ya dade ko Yanlabai wayo na shirya masa wai zan masa.

Sai da na gama shirya lafiyayyan girki kala Hudu ga kayan Sha iri iri ko ina na gyara sai kamshi ke tashi,wanka na fada na tsantsara kwalliyata cikin fitted gown black and Silver,gogorona Silver na daurashi dan dagwas,sarka da abun hannu duka silver color wow ga red jambaki na saki gashi yalala.
Ina fesa turaruka naji sallamarsu suna knocking, fita nayi tare da bude musu su uku Sayyah,Mardiyya da Islaha yar gidan Wata babbar lauya, idanu suka zuba min yanda suka ganni kamar wata Queen,nan suka hau yabon kyauna Sayyah tace shegiyar kin ganki kuwa muna ganinki a Uniform muna rudewa Ashe kinfi ma haka gaskiya mijinki yayi dace ya huta,Mardiyya tace zai kwashi harkoki,dariya mukayi gaba daya nace kufa baku da mutunci,Islaha sarkin jiji da kai,bata kawa sai da me kudi,nima ganin mijin da nake aure masu kudi ne yasa ta biyo su dan ta tabbatarwa idonta,ta kuma taba ganin Aayan a TV tana sonsa sosai shine yanzu ta samu hanyar da zata ganshi face to face ko zata dace ni ko ban sani ba.

Zama mukayi a Palo suna kalle kalle duk sun Zama yan kauye suna kallon haduwa,Maeesha na kwalawa kira,yau sabo da na kara kankaro girmana bance Ma'eesha ba wai nima fa na Zama yar gayu sai da nayi zaman Hajiyoyi a kujera irin me ji da Hutu da Naira sannan na wani Kebe baki tare da cewa Angel...sai ga Ma'eesha ta fito da Headphone a kunnenta tana Jin waka cikin English wear riga da skert tayi kyau, da fara'a tare da ladabi ta gaishesu suka amsa Sayyah tace Ma'eesha ko,Marrdiyya tace gaskiya kuna da kyau Mufeeda,nace tnx Dear, Islaha kuwa sai wani cin magani take tana yanga sai danna waya take,tana kishi da bakin ciki.
Angel kawo musu ruwa,Maeesha ta cika musu gabansu da kayan abinci dana Sha iri iri,nace to ya akayi Frnds Gist me mene News?
Sayyah dama itace muke so close tace bari mu fara cin abincin Amarya muji ko kin iya,Nace ai kema kin sani yarinya,muna ta hira sosai banda Islaha,ko abincin taki ci sabo da bakin ciki,mu kuwa bamu San meke ranta ba ko ta kanta bamu bi ba.

Kamar Aayan yasan yau kankaro girma na da mutunci na nakeyi gaban Frnds,lekowa yayi ta sama tare da dafa jikin Karfen steps din sannan yace Baby ina kika sa min Envelop din nan,bana so frnds su gane min shi,amma munafuka Islaha tana Jin murya tasan shine da sauri kamar wata engine haka ta daga kai kamar kadangare tana ta faman kallonsa,wani haushinta na naji kamar na koreta daga gidana, gani nayi zai sakko kasa kuma yasha wanka da alama fita zaiyi, nace bari nazo na dauko ma,ina yauki da kisisina muka hadu dashi a steps,su Sayyah kallo kawai suke Sha,a gabansa na tsaya ina murmushi kamar zan shige jikinsa na zura hannayena na rungumo bayansa amma bamu hada jiki ba,kyakyawar fuskata yake karewa kallo da idanunsa masu kyau,hannu na zare tare da saka hannuna cikin nasa nace muje ka gani,ba musu ya Bini tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login