Showing 81001 words to 84000 words out of 175038 words

Chapter 28 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6856

ta gama shiga hannu zata ga wulakanci,sai suka tafa da Yarima,nan take naji jikina ya dauki rawar sanyi,tsoro da fargaba tare da bakin ciki ya dirar min,ban san wa suke nufi ba,ban san akan me suke maganar ba sai na fassara maganar da naji kawai ba bincike ban tsaya naji dalili ba ko da wa yake nufi kawai sai na yanke hukunci cewar ni suke nufi dani suke,wato ni ya gano ina sonsa wahalar da kaina nakeyi,ya bari na shugo hannu ya wulakantani,ni zai wulakanta ma tab lallai dan Adam,duk abinda nakeyi Ashe baya gani a banza sai ma mugunta da yake hada min,nan take na fara tunano tun farkon haduwarmu irin tsanar da ya nuna min,Ammah ta da suka kashe min tunda sune suka jawo duk so yasa na manta,har aurenmu irin abinda ya dinga min a farko na wulakanci ina ta binsa,so yasa na manne masa nake kai kaina har dakinsa na sakar masa jiki,nasa yaji dadi,na godewa Allah da yasa ba ayi sex ba.
Mata da dama suna irin wannan daga jin magana bata kai ta kawo ba,basu san ma akan me akeyin ta ba,amma da yake kullum a zargin mazajensu suke irin ko sun daina sonsu,ko suna kula wata,musamman ace suna da kishiya ko zai kara aure,ko wani dalili yasa dai taga mijin ya dan canja to zargi zata kasance a ciki iri iri,komai yayi laifi ne a wajenta,magana idan ta ji ko da abokinsa sai ta fassarata ta koma tashin hankali Babba,wata ma har abokin zata daina kulawa,ko ta masa rashin mutunci,miji na neman aure abokin dole shine a gaba wai dan me zaiyi nan fa zata kulla masa wata ma sai ta rabasu sun bata sun daina abotar,wata kuma duk abokansa ta daina kulawa ko ta ci musu mutunci wai sune suke zuga mijinta,duk da cewa ana samun masu hakan amma mata mu daure mu daina zargi tare da saurin yanke hukunci,ko magana akayi sai a dinga fassara ta bai bai sabo da ba a son zaman lfy.

Ni dai ina tsaye naji kamar ma zazzabi zan fara sabo da yanda nake son Aayan ko kaina ban so haka,bani da burin da ya wuce naga ya soni back amma sai gashi abinda naji ma daga bakinsa,Hawaye na share na daure na shiga palon fuskata ba walwala nayi Sallama suka amsa,Nan take Aayan ya kafeni da idonsa yana ganin yanda lokaci kadan na fita daga hayyacina,dazu lfy lfy muke,kamar ma kuka nayi,ganin yana kallona nayi kasa da kaina,tunaninsa ko yan gidansu ne suka yi min rashin mutunci ya tabbatar idan kuwa sune suka sa na dawo haka yau sai anyi yaki a gidan nan,baya son a taba masa ni yanzu ko kadan, kasa jurewa yayi yace ina zuwa Yarima yaja hannuna mukayi waje dashi muna fitowa a jikin kofar yasa yatsansa tare da dago da fuskata yana kallona sannan a hankali yace lfy? Me akayi miki? Nayi shuru,Hajja ce? Su Haneefa nan ma shuru sai Hawaye dake biyo min a kumatuna a raina ina kara cewa yanzu wannan zankadeden rabuwa zaiyi dani,shike nan baya sona? Yace am asking u me suka miki ya fada da tsawa,duk ya shiga damuwa lokaci guda ya rude Allah sarki So,so banza ne kawai sai ya bani tausayi kuma na batawa wanda nake so rai,har bana ganin laifinsa sai nawa sabo da Aayan baya laifi a wajena so hana ganin laifi,tunowa da maganarsu dana jine yasa na kara birkicewa,kawai nace ni ba wanda ya min komai kawai ji nayi bana son auren Kasuwancin nan ko nawa zan samu,ko yanke talauci ne wlh bana sonsa dan Allah ka sakeni na tafi, wani dum yaji maganar a bazata to ko dai itama sun mata wani asirin ne ko kuma sun sa mata wani abu taci ai ko wlh bazai iya sakinta ba har abada sai dai duk inda zata je da aurensa,jikin Bango ya Dafe kawai yayi shuru yana Innalillahi kawai yake maimaitawa duk zarginsa tunaninsa Su Hajja ne ko asiri ko kuma wani abu suka mata wanda baza ta iya zama ba, da kyar ya dago muka hada Ido sai da na rumtse Idona yanda bazan iya kallonsa ba ya Zama wani iri idonsa yayi jajir,Hannu na ya figa kamar zai tashi sama ya jani muka Haura samansa har Bedroom ni dai kawai binsa nakeyi,a ciki ya tsaya tare da rike kugunsa da hannu biyu kansa ya daga sama yana danne lips dinsa na kasa da Hakoransa yama rasa ta ina zai fara, maganarsa naji a hankali yace Mufeeda! na kalleshi tare da sadda kaina kasa,yace ki fada min me ya faru dake me kike ji me yake damunki ko kuma a gidan ne wasu suka ce miki wani abu ni dai nasan ban miki komai ba,ko kema sabo da bamuyi Xxx ba zaki tafi? Da sauri nace a'a wlh ba haka bane,yana kallona yace to ko bana Haihuwa kike nufi? Nan ma kafin ya rufe baki nace wlh ba wannan bane,to mene tell me,karki rufeni ko ki cuci kanki just tell me what's is going on? Ina Hawayena nace ni kawai na gaji da auren ne Bana son kudin yanzu,Wait bafa Business muke ba wannan wasa ne kema kin san aure ne na sunna aka yishi ba wai akan kudi ba,nace ae na sani kawai bana son auren ne nace ma ni bazan zauna ba kawai,ok yace ko gidan nan ne bakya so? Fada min sai na Canja muku gida,kai na girgiza a'a, yace ko Wacce kasa kike so fada min wlh zamu koma can indai kina so,a raina nace jibeshi kamar gaske salon ya kara mallake min zuciya yaji dadin wulakantani da kyau to bazan je ba,nace bazanje ba ni a fili,Abuja fa?nace ko villa ne banso,to kiyi Hakuri idan wani abu aka yi miki addua akeyi akan komai ba fushi ba haba yan mata nan ya dinga lallashina,sai nayi kamar zan Yarda naji tausayinsa sai kuma na fasa nace nifa bazan zauna ba.

Yana gajiya ya tamke fuska ba mutunci yanda na sanshi tun farko,nan take naji tsoronsa jikina ya fara rawa, tahowa yayi kamar zai makeni na fara ja da baya yana Huci yace bari kiji bude kannenki wallah kinji na rantse har uku bazan sakeki ba kuma ba inda zakije idan kika fita ma ko gate ne bada izinina ba sai munyi Shari'a dake a gaban Allah ban yafe miki ba,kiji ni da kyau ba wani Business auren za ayi as from today ni kuma duk Hakkin ki daga yau zan fara baki,yana gama fadin haka ya kwanta a saman Bed yana Dafe kansa dake Sarawa, tausayi kuma ya bani sosai yanda ya nuna ya damu a kaina gaba daya sai na tsani kaina me yasa nayi haka,amma dai zuciyata ta hanani na hakura,ido ya rufe sosai still yana Dafe da kansa ya rike sosai da alama ciwo yake masa da yawa,Hankalina ya tashi nima,mikewa yayi tsaye kamar wanda yasha giya yana maye da tangadi,haba ban san sanda tausayinsa ya gama rufeni ba gaba daya naga ya fini shiga damuwa yazo ya ratsa ta gefen zai wuce ya fita tuni na damko hannunsa ya tsaya cak tare da juyo da fuskarsa ya kalleni gabansa na koma tare da fadawa jikinsa na rungumeshi kam kam sosai da sosai kamar za a kwace min shi, baiyi hugging dina back ba,da kaina cikin kunnensa na rada masa Rug me back am so sorry, bai kulani ba babu zato naji bakinsa cikin nawa ya fara tsotsa ya rabani da kasa dan dagani yayi sama yanda tsayinmu zaizo dai dai ba sai yasha wahalar sunkuyoba,haka muke tsotse bakin juna kamar mun samu wani kayan dadi na tsotsa,wannan kiss din yafi na kullum dadi,gardi,tare da nishadi,yanda nakeji ya zarce na fada muku,muna ta yi ba ji ba gani kamar zamu cinye kanmu ko nayi kamar zan kwace bakina sai ya kara rikeni kam ya hanani sai da muka dauki dogon zango a haka sannan da kyar na zare jikina daga nasa,amma duk da haka kara jawoni yayi jikinsa tare da fara lashe min wuya,tsigar jikina tashi take kawai gaba daya ya gama kara min sonsa a zuciyata, da kyar nake iya tsaiwa da kafaguna shima haka,ya fara kokarin cire min kaya na tuna yayi maganar hakki dazu da sauri na rike masa hannu tare da cewa abinci still dai ban saki raina ba bana wani nishadi kamar dazu,kyaleni shima yayi fuska ba walwala yace let's go,sai da muka saita kanmu sannan muka sauka kasa,Gaba dayansu Har Yarima da Ameer suna Dining suna ta cin abincinsu muka sakko duk kayanmu ya nuna da gani anyi yamutse yamutse,ga T-shirt din Aayan Fara kar ce duk jambakina red da Powder a jiki duk na shafa masa ba tare da mun sani ba sabo da murzar juna,Yarima da Ameer duk sun gane me akayi,Meenat ma ta gane gani ba jambaki a bakina sannan duk ga wani nan a bata gefen bakina,Aayan harda digon jambakin a hancinsa duk sai yanzu ma muka kula da hakan,Yarima sai dariya yake kunshewa yana kallon Aayan, dan Iska wlh zaka bar gidan nan banza munafiki Cewar Aayan,Yarima yace to me nayi kuma? Bayan ka shanyani,Ameer kishi ya hanashi kallon kowa kawai tura abincinsa yakeyi,Aayan har yau yana cikin damuwa ya kasa cin abincin kuma yunwa yake ji,ni kuwa bakin ciki baya hanani cin abinci ko cuta nake sai naci na koshi haka nake bare kuma kafin naji Maganar da su Aayan sukeyi tun a kitchen muna girkin na cika tumbina, ganin ya kasa ci na Mike tare da Zama kujerar dake kusa da tashi zan bashi da kaina,kafin na fara Ameer ya ajiye spoon yace ina zuwa bari nayi waya ya fice da sauri zuwa part dinsu,Yarima yace nima tafiya zanyi Ma'eesha zo ki rakani mota nan yayi mana Sallama suka fita,Aayan yace sai nazo zanyi maganinka ya furta da alama kawai danne bacin ransa yakeyi,Meenat ma tuni tayi Bedroom zata fara karatu,daga ni sai shi ya Dafe kai tare da rafka tagumi da gani yana cikin damuwa me yawa.

Hannun da yayi tagumi na janye a hankali ba tare da nace komai ba na ebo abincin a spoon na fara bashi da kaina yanda yake ci zaka San baya jin dadinsa ko kadan,kamar kurame haka muke har yace ya koshi nace ko spoon biyar baka ci ba fa? Zan fara masa magiya ya Mike kawai ya haura sama ya barni a nan,ban damu ba na tattara komai na kai kitchen tare da gyara komai na shiga Bedroom dinmu nayi wanka da duk wani abu da zanyi nayi nasa Night gown dina da kawata Sayyah ta bani wai inji mamanta kala Uku hadaddu amma basu fiye tsaraici ba nasa light blue din masha Allah nayi gaskiya karshe na daura ta samanta na fita lokacin Ma'eesha ta dawo daga wajen Yarima tana nuna min chocolate masu Uban yawa da kudi masu yawa wai a bani inji shi,na karba nayi godiya nace bari na nunawa Aayan kafin Ku fara sha nayi waje zuwa Bedroom dinsa,gefen Bed na hangoshi a zaune yayi shuru kawai yana kallon sama da alama tunani yakeyi yaji Sallama ta,amsamin yayi kawai tare da kwanciyarsa saman Bed ya barni a tsaye,banji dadi ba ni kaina muna zamanmu lfy na jawo bacin rai kuma shi dama kafin a lallasheshi aikine.

Haneefa ce Zaune tare da Mommynsu suna hira,Mommy tace Ameer naga fa kamar kwanan nan ya Mannewa wajen yan iskan can a part dinsu ban san ko Hajja tasan labarin ba,Haneefa tace Mommy ki barshi ai da alama bata sani ba gwara ma da kika tuna min bari naje na fesa mata tayi maganinsa ya daina zuwa na tsani Su Mufeedan nan Shegu wai su masu kyau,Mommy baki ta tabe tare da cewa je ki sanarwa Hajja ni ma yau zan fadawa Abbi abin na Ameer yayi yawa, da sauri Haneefa ta tafi part din Hajja,ta samu Hajja sai Mulki take zubawa tana wani takama da isa tare da bawa yan aiki umarni.

Haneefa ta zauna gefenta tare da cewa Hajja wani labari na kawo miki marar dadi so sad wlh abin kunya ma,Ina jinki Hajja ta furta tana gadara,Haneefa ta gyara Zama tare da sanarwa Hajja yanda Ameer ya koma bangarensu Mufeeda.
Hajja da masifa tace to azukwi uwar munafunci me yasa kuke takurawa Ameeru ne,ina ruwanki Algunguma to nasan da zuwansa aikina yake ni na turashi,kinzo da guntun munafuncinki ai zai shigo ne zan fada masa me kika ce ya farfasa miki jiki,Haneefa ta fara bata hakuri daga fadar gaskiya sai a lullubeni da fada to daga yau bazan kara fada ba ko mene zai faru ya faru,Hajja ta dakko yar sandarta ta karfe tayi kan Haneefa da gudu ta fice ta bar Hajja na Masifa ta gaji da Gulmar Ameeru da akeyi a gidan nan.








AsmaBaffa
Loves u all d'=?
?
[1/20, 11:23 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA






81-85







Official







By
AsmaBaffa









Page din yan TASKAR SURAYYARMS ne wannan ina jinjina.


Gidiyata bazata irgu ba gareku Yan HOUSE OF HAUSA NOVELS
ASMABAFFA FANS CLUB
TASKAR FIRDAUSI SODANGI
UWARGIDA


Na gaisheku masu Sharhi a ci gaba.






Hajja tana nan tayi gaho da baki tana sauraren Ameer yazo suyi maganar komawa wajen Malamai tunda yanzu taga ya shiga jikinmu sosai zai iya aikata komai,Abbi sai Haushin Hajja yake ji ta hanasu aikata nasu ita kuma ta kasa komai ta biyewa wani Ameer.

Na dan Dade a tsaye ina tunanin me zance masa sai da na gaji nace gashi Yarima ya bamu,juyowa yayi yana daga kwancen,kudin na mika masa tare da bude masa ledar kayan zakin iri iri,a hankali yace ki basu kuje ya kyauta,To ka kirashi ka mishi godiya,Ba musu ya jawo faskekiyar wayarsa ya dannawa Yarima kira bugu biyu ya dauka suka fara suruntunsu na abokai naji Yarima yace to ya zamu shirya mata Plan din,Aayan yayi dariya tare da cewa ka bari sai mun hadu zanzo gobe ko jibi idan na samu time,ok anyway shaa cewar Yarima,Aayan yace dazu Ashe har wani wahala kayi na kudi da Sweets tnx, ban son Godiya Malam Good night I forget to tell u gobe Umma na zasu dawo tare da Abba, good to hear that sai nazo nayi missing girkin Umma tun muna London,Yarima yana dariyar Jin dadi yace ga matarka nan tafi ma Umma iyawa,Uhm gaskiya ne Night nan suka yi Sallama,ni kuwa na kuma jin ance ya plan dinmu a kanta nasan ma nice kawai na kara Jin haushi,Na kumbura kamar zan fashe da kuka,Kallo na yayi yaga yanda nayi a ransa yace to fa wannan na kasa gane meke kanta,ni kuwa Harda Haushin yace yayi missing girkin Babar Yarima wato nawa ni ba dadi bai dameshi ba har girkin wata yake tunawa yafi nawa ma wani haushi ya turnuke zuciyata naci gaba da tsaiwa a kansa rike da kudin tare da ledar kayan da Yarima ya bamu.

Kallo na ya karayi yaga kamar zance na shiga uku na lalace na hada girar sama data kasa na cokalo lips gaba kadan nake jira kuma na tsaya masa a kai, light ya kashe ba tare da yace min komai ba nima ban motsa ba kamar me gadinsa haka nake tsaye gefen bed din, mun dauki lokaci a haka yaga dai ko matsawa naki yi nan ya kara kunna light haske ya mamaye dakin,inda nake haka nake, kallona ya sake kare min ni kuma tunani nakeyi ba a sona ni ban san tsakin da Naja ya fito fili ba,a fusace ya Mike tare da dirowa daga saman bed sai da na firgita,ban kara tsurewa ba sai da naga ya zaro wata wayar wuta doguwa ya nufo inda nake da gudu na watsar da kayan na fice da shegen gudun da rabon nayi irinsa tun ranar dana je guess house Hon Chairman neman tallafi.
Dariya ma abin ya bashi dama gwadawa yayi yaga karshen rashin kunya, ban tsaya ba sai dai Su Meenat suka ji na banko musu kofa tare da fadawa Kansu,da gudu suka Mike daga baccinsu suka yi waje can Palo da gudu basuyi tunanin nice ba sabo da tunaninsu ai can nake kwana,Dariya suka bani na fito ina ce musu kai nice fa,Meenat ta manta ni yayarta ce sai da ta dura min ashar daga baya tace yi hakuri wlh na tsorata kin bani haushi muka dinga dariya Ma'eesha harda bige kafa da jikin Bed, ganinsu da kayan bacci nace ku koma Bedroom kar Aayan ya fito ya ganku a haka,Ko kunya kishinki yayi yawa cewar Ma'eesha,nace ae naji dai,suna shiga kafin na shiga suka banke kofarsu tare da Sa key wai sai da? na nemi wajen kwana.
Ni kuma tsoro nakeji na kwana ni kadai ban saba ba,lallabawa nayi na koma dakin Aayan kamar munafuka ko wacce taje yin sata haka nake sanda kamar Soja ana kwanton yaki,a hankali na tura kofar dakin Allah ya taimakeni ya kashe light ya kwanta saman Bed Amma ba bacci yake ba tunani na yakeyi gaba daya ya kasa bacci yanzu na gama sangartashi tare muke bacci idan bana kusa matsala ce a gareshi kasa bacci yake.
Lallabawa nayi yana tunaninsa baiji motsina ba har na hau saman Bed din gefe daya can na kwanta a hankali ina dauke numfashi na, nayi shuru kamar ansa wata na'ura me jawo ruhin mutum zuwa na dayan haka nakeji,gashi a kusa dani Na kasa sukuni burina na rungumeshi mu kwanta yanda muka saba,idan na taba shi kuma ina tsoro kar ya mike da fushi ya zaneni,Shi kuwa ya lula tunanina kamar yaje ya dakko ni,ji yake ma me yasa ya koreni gwara ai ina dakin ko banza ya dinga jin motsina.

A hankali nake matsawa kamar ana jana ban san sanda zuciyata ta Gaza hakura ba,idan na matsa sau daya sai na huta dan kar yaji,ji yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login