Showing 138001 words to 141000 words out of 175038 words

Chapter 47 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6863

da ita shi kuma ya mike tunaninta Tafiya zaiyi ya barta ta sake sai taga kida ma ya kunna abinsa yana yar rawarsa su Zanku Dance tare dasu Shaku shaku dama gashi yaci uban kana nan kaya na yan duniya,Ma'eesha ce ta fito palo basu da labarin ansa bikin Ameer da Meenat tazo kusa da Ameer itama suna ta rawar tare bai san ta zama kanwa kuma suruka ba,itama haka dama sun saba kusan kullum idan suna nishadi sai sun cashe,Meenat dai dariya take sha kawai Sabo da Ameer baya girma maybe ko da dansa ma rawa zaiyi, Su Khaleel ne suka shigo da Sallama Amma kida yasa ko jin Sallamar ba wanda yayi,Sabeer tun daga kofar ma ya fara cashewa Shima,Maeesha kuma taji kunya ta koma ta zauna kamar saliha dama da Ameer suka saba,Mujaheed ne kadai Baya rawa Amma Khaleel ma yana bi da baki yana yi a zaune wakar Olamide latest,Aliyu kuwa harda Handkerchief a hannunsa yana faman sarrafashi yana yi,da Haneefa akazo tare da Meenal dama aikinsu kenan a gida tun farko su kunna kida suyi ta rawa yau tsohon Tsuminsu ya tashi basu ji kunyar uban kowa ba suka dinga yi iri iri,Ameer yana dariya yace Haneefa kin fadi wannan step din Kije Ma'eesha ta koya miki ta fiku iya wannan,Maeesha kamar munafuka tayi kamar bata san ma mene ake nufi ba wai ita saliha, Ameer duk sun zauna suna magana,Sabeer da Aliyu kadai aka bari suna ta rawarsu suna bin Kidan da baki Suna haka sai gamu mun fito tare da Aayan ba karamin kyau muka sha ba kamar kasace mu,Shadda muka Sa me tsadar gaske fara me aiki da bakin zare,nasa dinkin na Maza nawa na mata,kowa ya kallemu sai ya kara kamar wasu wankin engine haka muka fito muna kamshi,dama sun saba ba kunya ce dasu ba bare Aayan da basa jin kunyarsa tun farko basu kashe Kidan ba kuma masu rawar su basu fasa ba da wanda sukeyi a zaune magana baza suyi ba sai hannu suke dago mana wai gaisuwa ce,ina zuwa na kashe Kidan nace haba komai dadin kida shuru ya fishi,Meenat tace gaskiya mu ki kunna rawa muke kallo,Musabiha sukayi da Aayan sannan suka gaisheshi nima haka,Maeesha na Yiwa magana ki kula da kowa zamu fita sai dare zamu dawo,kunyi kyau cewar Meenal,nace tnx Aayan ya sa hannunsa a waist dina yana fada musu su jira baza mu dade ba zamu dawo,ai da Sauri suka ce a dawo lfy,muna fita suka warare uban kida a speaker din katuwar gaske.

Ko da su Khaleel suka zo suna ta fadawa Ameer Ango Amma bai kawo da gaske suke ba tunani yakeyi ko dama wasa kawai sukeyi,tunda shi baiji daga bakin manya ba ko Aayan taya zai yarda, Abinci Ma'eesha ta kawo musu da kayan sha suna ci suna Santi cikin Santi Meenal tace Allah mun gode ma ku duba hakoran engine na Markade har washi ake kaisu kuma baka isa sunyi shekara biyu ba,haka zaka gansu duk karfe ne amma ya Zama Siri Siri ya gama sidewa amma kalli Hakorin dan Adam yayi tauna yana Markade abinci luwai luwai ba tare da karar komai ba,shekara da shekaru bai lalace ko ya daina kaifi ba,amma hakorin Engine kuwa ana zuba Abin Markade zaku ji karar tasa ma ta canja,Ameer yace ai fa gaskiya girki yayi dadi,kuma su hakoran mutum idan kana tauna ko kara basa yi ba kamar engine markade ba kaji kafkafkafkagkaf dariya sukayi gaba daya.
Ni da Aayan kuwa tunda muka fita bamu tsaya ko ina ba sai gidan Ammah mun dade a gidan muna tsare tsare bikin su Meenat,daga nan yace Muje mu gaida su Hajja ban so zuwa ba amma ganin Manyansu ne yasa banyi musu ba muka je,Sajeeda dake gidan ita ta saukemu bamu samu tarba me kyau wurin Hajja dasu Abbi ba dama kuma bamu sa rai ba,bayan mun danyi Jimm kadan muka musu sallama muka fito.

Bayan zuwanmu gidan su Hajja da kwana biyar kawai na wayi gari bana son Aayan ya rabe ni kwata kwata,ni ba tsanarsa nayi ba Amma bana so naje kusa dashi ko yazo kusa dani,idan kuma baya nan zanji kamar na cinyeshi na damu dashi ina ta damunsa da waya Amma da zarar ya dawo gareni to kuma sai naji duniyar tayi min kunci Bazan samu jin dadi ba har sai idan na bar gidan Aayan sai na samu kwanciyar hankali,d a dare ko Bedroom idan na canja sai na koma jin Kukan Dabbobi iri iri,Aayan ya kasa gane kaina gaba daya mum shiga damuwa babu me kwanciyar hankali a cikinmu,Saida muka kwashe wurin sati biyu muna haka ko Bed bamu hadawa da Aayan,tunda ya gane sai ya dan ja baya da lallabani dole sai mun hada shimfida,abin mamaki kawai yake bashi,ina dakin dana warewa kaina ni kadai 9pm Aayan ya shigo yasha wanka,ina ganinsa raina ya baci kawai naji wani bakin ciki marar misali kuma ni ba shi nake jin Haushi ba bansan me ma nake jin haushin ba,Zama yayi kusa dani Na kara daure fuska,kallona kawai yakeyi da mamaki,Hannu na ya riko na fisge abina,ya kara rukowa da Sauri na boye hannuna Ina shirin yin Kuka,a hankali ya zuba min ido cike da so da kauna nima haka shi nake kallo yana bani tausayi Amma na kasa canjawa ban san dalili ba,Muryarsa naji yace Mufeeda a hankali,Ba tare dana kalleshi ba nace Naam muryata tana rawa zanyi kuka nace dan Allah kayi hakuri wlh ni ban san me yake damuna ba,Karki damu na gane na san lallai akwai Matsala tunda komai baki fasa yi min ba,amma me yasa yau baki yi min abinci ba tunda nine bakya so na rabeki,kin san kuma ke zaki bani abinci naci ko? a hankali na daga kaina kayi hakuri jiya ne banyi bacci ba sai da rana ina ta jin Kukan Zaki dasu Damusa a gidan nan sai da Asuba nayi bacci.

Ko gida zaki koma wurin Ammah mu gani bana son ganinki a wannan hali Sweetheart,da Sauri nace na gode Na gode dan Allah ka maidani wurin Ammah anan kamar zuciyata zata fashe haka nake ji,Nima Ina da Meeting a Abuja gobe zan wuce sai nan da 2wks zan dawo naso ace tare zamu tafi sai kiga komai nawa na Abuja Sabo da so nake mu koma can da zama na gaji da nan kullum matsala iri iri, bari na dafa ma ko Indomie ce,no ki barshi naci abinci a waje karki damu,gobe ki shirya na maida ke wurin Ammah yana gama fadar haka ya wuce.

Kuka na saki sosai ina son mijina Amma kuma na rasa me yake damu na,yau ma da kyar na samu bacci sai da Asuba na samu bacci ya kwasheni,da sassafe na tashi bacci a idona na fito zan daura Breakfast,Aayan na gani ya dawo daga Gym room yace kije kiyi baccinki zan siyo mana abinci,Ba tare dana kalleshi ba na juya nace to sai bacci,Shirinsa ya gama yi fes ya jawo Trolley dinsa ya ajiye min take away dina iri iri tare da Short note cewar ya wuce ga Ameer nan zai maidani wurin Ammah karshe yasa I love u My Wife.

Sai 2pm na tashi da sauri nayi wanka tare da Sallah sannan na jawo take away naci na koshi ina tunanin mijina,duk naji gaba daya kamar ma ba ni ba,kamar bani da wani amfani a duniya ba tare da Aayan ba,tunaninsa kawai nakeyi iri iri ina jin da a raina wanda da ace yana kusa dani bazan ji hakan ba,Sai dai ma bacin rai,Shiryawa nayi na kulle komai na kashe kayan Wuta na kira Ameer a waya da katuwar jaka ta na hado kayana,Babu wanda yasan me yake damuna,haka Aayan ma ko Daddy bai sanar masa komai ba duk da cewar Daddy ya tafi U.s zai huta kafin bikin su Meenat zai dawo,Ammah ganina da katuwar Trolley sai da gabanta ya fadi,Su Meenat ma haka,Ameer shi kansa tunani yakeyi ko dai ba lfy ba,Sai da muka gaisa dasu Ammah tace lfy dai ko?murmushin karfin Hali nayi nace lfy lau Ammah ya tafi Abuja ne shine nace ya barni na dawo nan kafin ya dawo shima kuma yace to ba matsala,Ammah ta bata rai shine zaki dawo wajena?ko wacce matar aure ba haka take hakura ta zauna ba,shike nan idan baya nan sai ki bar gidan kema,ke da hakkinki ne kula da gidanki,dukiyarsa da komai nasa sai ki tattaro ki dawo,Jiya ma Aayan Yazo min ni banga Alamar lfy kuke Zama a tare dashi ba,matsala na hango sosai a tare daku,ki fada mana gaskiya ko ki tashi ki koma can gidan mijinki,Ma'eesha tace Haba Ammah ki Bari mana sai anjima ta fada mana,da bana raye ko bana garin nan gidan wa zata koma?dole tana gidan mijinta,Ameer yace nima ban yarda ba Ammah akwai matsala tun wurin sati biyu nake ganin Aayan cikin matsananciyar damuwa,a Office ma kasa komai yakeyi sai ni na koma ina aiki biyu naje nasa nayi a nawa,Har mutane frnds suna tambaya ko lfy? Ma'eesha tace nima Yarima ya tambayeni shi fa ya kasa gane kan Aayan,shuru nayi bance musu komai ba har suka gama cecekucensu,muna zaune a gidan har an kwashe 4days amma bance musu komai ba,tun suna tambayata har sun gaji,Aayan kuwa ko ya kira bana dagawa amma kuma da tuna ninsa nake kwana nake tashi,ina muradin mijina,ina son mijina amma kuma da zarar naga wani abu nasa sai na kasa cewa komai,naji bakin ciki ya addabeni,Meenat ce ta shigo Bedroom inda nake kwance sai tunanin Aayan nakeyi ina jin dadi a raina har Hawaye nakeyi,Sis lfy kike kuwa?da sauri na share Hawayena na Mike zaune nace lfy me kika gani,Ba lfy ba Sis dan Allah ko ni kadai ki sanarwa meke damunki ko za a samu mafita Ammah tana cikin damuwa akanki,kuka na fashe dashi sannan a nutse na sanarwa da Meenat duk abinda yake faruwa da abinda nake ji a raina, amma shine kika ki fada tun tuni ai da ko addua sai a tayaki da ita bari na sanarwa Ammah,bance mata komai ba har ta bar dakin,taje ta sanarwa Ammah komai har Ameer,mamaki ya kama Ameer ya shiga damuwa kowa zarginsa dai bai wuce Su Hajja bane sukayi tsafinsu, addua muka dage da ita,Ammah ta kira Aayan tace a kara dagewa da addua,Ganyyen magariya da addua Ammah ke bani ina sha kullum sabo da yana karya sihiri tare da Habbatussaudat.

Aayan yana Abuja kamar zaiyi hauka sabo da Missing dina da yayi,ga rashin Kulashi da banyi ko a waya,ga kewata tare da tsananin sona da sha'awata da suka addabeshi,ba yaso ya dawo ma yaga naki kulashi ko yaga na kasa bacci,ya ganni a damuwa shi yasa ma yaki dawowa,ni kuwa Adduar da mukeyi yasa yanzu na samu sauki a raina,ina iya baccina zanci na koshi,Rashin Aayan kawai ke damuna,sai ko gashi na danyi kibata da kyau,Ana gyaran Amarya Ma'eesha Ammah tace a gyara mata da Meenat harda ni ma ayi min,Me gyaran yar Maiduguri ce tazo gidan sai bayan biki zata koma,Meenat sai haushi takeji ita ba Amarya ba sai tsumi ake bata ana gyara mata skin duk sha'awarta ta tashi a banza.

Ameer yana Office yayi dogon tunani akan matsalata ni da Aayan zumbur ya Mike ya tafi can gidanmu har garden yaje ya koma Jikin bishiyar da yaga Nawwara sanda tazo tana Selfie,kuma yasan sanda tace ita kadai ma zata zaga gidan,a hankali yake kallon wurin da ko ina daga kansa yayi jikin bishiyar mango karaf idonsa ya sauka a saman wata laya katuwa da Zare a jikinta an makaleta a jikin bishiyar, ciro layar yayi yasa a aljihunsa ya koma ya kira wasu tsagerun yaransa wanda yasa suka tare Hajja suka kwace Maganin asiri,tare suka je Har unguwar su Nawwara ta dawo daga unguwa kenan taga Ameer a kofar gidansu,dadi taji ko wajenta yazo zaice yana sonta ai kuwa da tayi dace,da Mufeeda ba uwar da ta isa ta nuna mata itama,da fara'a Ameer yace muje mota na fada miki abinda ke tafe dani,ba shiri ta bishi mota irin taga me kudi,Sai ko ta shige mota tana shiga taga yan daba ne a ciki gaba daya,ta juya zata fice suka sa lock tare da figar Motar,Ameer kuma ya shiga tasa suka bar unguwar sunci Sa'a ba wasu mutane a layin.

Bayan sunyi nisa sosai sun shiga daji Nawwara kuka kawai takeyi tana basu hakuri,sai da suka isa inda ba kowa sannan suka yi Parking Ameer ya fito daga motarsa haka ma Guys dinsa suka Jawo Nawwara Waje,Ameer da katuwar waya a hannunsa me kauri da tsayi bai jira komai ba ya fara tsulawa Nawwara ta ko ina tana gunjin kuka ya fasa mata jiki sosai sannan yace Me kika saka sanda Kika je wajen Mufeeda,da sauri Nawwara jiki na rawa tace dan Allah kuyi hakuri wlh sharrin shedan ne,Mijin Mufeeda na ke so sabo da Kudinsa ina bakin ciki Mufeeda ta fini ci gaba,shine kawata ta bani shawara muka je kauyensu can Danbatta Lg wurin malaminsu ya bani laya yace na makale a jikin bishiya ko katangar gidan,shi yasa naje nasa wlh bazan kara ba na tuba dan Allah Ku yafe min karku kasheni.
Layar Ameer ya Ciro yace itace wannan?da sauri tace ae wlh itace a konata, nan take Ameer ya samu lighter ya kone laya a wajen.
Lokacin ni Mufeeda ina bacci na farka a firgice ina salati sai kiran Aayan nakeyi,Ammah dasu Meenat suna kaina ina kuka ni a nemo min Mijina,a gigice na dauki waya na danna masa kira,yana Meeting da wasu manya yaga kirana,hakuri ya basu ya dauki wayar, yana dagawa na fara magana ya zaka tafi Abuja ka barni dan Allah kayi hakuri ban san matsalata ba amma ni dan Allah ka dawo ko na biyoka Abj? Cike da Murna yana godiya ga Allah yace bari Ameer zai miki Booking Flight gobe sai ki taho,cike da shagwaba nace a'a ni yanzu nake so nazo wajenka nayi missing dinka,ba yanda baiyi ba kan na bari sai gobe amma naki yarda,Ammah tace ki Bari sai gobe Nace Ni a'a wlh tafiya zanyi ni,Ameer yana Zane Nawwara tana ihu Aayan ya kirashi yana murna yayi sauri yamin booking flight na biyoshi abuja,sai da ya ladaftar da Nawwara sannan ya basu Umarnin su kaita gidan Ammah wajena tayi bayani da kanta, haka naga Nawwara a firgice tana kuka ta durkusa har kasa tana bani hakuri na yafe mata ta fadi abinda ta aikata, bakin ciki da tsanarta ya kamani nace kije dan kanki Amma ni yanzu Bazan yafe miki ba sai ko nan gaba idan na huce Sabo da tuban dole na wahala kikayi bana Allah ba,nace a fitar mana daga gida ko wlh na kara miki wani Dukan, da Sauri tayi waje yaran Ameer suka ce ta shiga mota suka ajiyeta can gefen layinsu,

Ameer kuwa Da sauri yaje ya figi motarsa yayi min komai na tafiya Abuja,Su kuwa Yaran suna zuwa suka korawa Nawwara warning idan tace tasan Ameer ma kashe ta zasuyi,aiko a tsorace ta sa katon hijab dinta tace wlh bazan fada ba yanzu ma a gida cewa zanyi fada mukayi da wasu na musu rashin mutunci suka zanemin jiki,Good for u suka ce tare da Jan Motarsu suka bar layin ko da ta shiga gida kuwa haka tace wasu ta tsokana suka zaneta.

Ni kuwa ina Zaune an gama zana min lalle hadadde naje Saloon sharp sharp,Ameer yana zuwa ya zayyane mana labarin komai da Nawwara tayi,aiko na dinga tsine mata ba ji ba gani,Aayan ma sai da Ammah ta sanar masa komai yana ta mamaki da Hamdala,wato yanzu kowa Malami,harda yan mata abin yayi yawa,ba a son zama lfy sai haddasa fitina iri iri.
Ameer yana cin abinci Ammah sai albarka take Sa masa,Meenat tace anyi abin kirki sai wani murmushi kakeyi,Murmushi kawai yayi yace zan rama ne,Lokacin Lallena ya bushe na wanke sannan nayi wanka tare da shirin Tafiya Abuja ina fitowa da Akwatina na sallami me lalle nace Ammah na tafi ayi mana addua Ameer muje,Meenat tace zan biku Rakiya ta sa mayafinta muka tafi tare,Nace Ohh Nawwara ta Allah ba taki ba,shegiya zata rabamu harda wani Dan Allah kawata ki yafe min,akan me zan yafewa shegiya ai kuwa tayiwa kanta wlh da nayi niyyar bawa Ummanta Atamfa me tsada kyauta na fasa Bazan bayar ba ko unguwar ma na daina bi ta kusa da ita,Dariya su Ameer suke min yanda nake ta mita,Sai da na shiga jirgi suka tafi gida,tuni Aayan yana Airport na Abuja yana jirana,ina sauka ya hangoni da Sauri na karasa cikin takuna na birgewa Nace Nawwarace tsinanniya na fada Kirjinsa ina sheshekar Shagwaba,ya rungumeni tsam a kirjinsa yana lallashina,3wks fa kayi bama tare kuma kace 2wks zaka yi dole nayi Kuka ai,hmm kece bakya so na rabeki ya zanyi dake shi yasa nayi nesa ko zaki fi samun sauki gashi har kiba kikayi da kyau,tausayi ya bani Sabo da ya dan rame kadan,a hankali na rada masa muje yau dadi zamuji abinda ban taba yi ma ba yau shi zan maka ka dage a yau na samu Baby,
Dariya yayi sosai yana jin dadi yace Allah yasa,muje ki fara ganin gidajena na Abuja Amma a Hotel zamuyi 1wk musha Honey moon dinmu,a'a a bari sai gobe ka nuna min gidajen nan Amma yanzu ni nayi Missing dinka abun nan nake so kayi min kawai naji dadi na,Hanci ya lakace min yana dariya yace baki da kunya My Wife me zan miki? Nace hmm ka manta abinda nafi so ma? Allah ya shiryeki nace Ameen muna dariya muka shiga mota Driver ya jamu sai Hotel na gani na fada nan ya kama mana daki hadadden gaske.
Abinci muka ci da wanka ko gama shiryawa banyi ba yana Saman Bed ya takura nayi Sauri nazo mu kwanta yamma ba dare ba,Light na kashe na haura saman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login