Showing 45001 words to 48000 words out of 175038 words

Chapter 16 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6902

nuna masa inda aka samu matsala,wani sai kaga gashi a wuyan rigarsa ya zuba,murmushi yayi Bai ce komai sai yace ai bakinki ne Gwauron gashi nan yi min naga iyawar taki kuma karki min da zafi,Ina murna nace ai nasan har kyauta yau sai kayi min,sunkuyawa yayi tare da miko min kan,nace zan gaji da wuri a haka,na zauna Saman Bed shi kuma na shimfida masa Sallaya nace zauna ka gani ni da nake me kitso,Kamar bazai Zauna ba sai kuma ya zauna,na ware cinyoyi kamar zanwa wata kitso dai yace ke hade wannan cinyar taki kina period,nace sai na fasa ma dan zan maka shine zaka fada min magana.

A hankali na dinga taje masa ina fesa masa abun gashin,sai wani lumshe ido yakeyi zaiyi bacci,nace kudi biyu zaka biya ga na gyaran gashi ga kuma na hannun mace yana taba ma kai kasan hannun mace daban ne sai an biya,wannan hannun naki kamar Dutse gwara na maza dashi,ni kaina ba wani yi nake ba kawai tajewa nakeyi ina wasa da gashin dama karya nake ban iya ba,bacci ne ya fara kwashe shi har na gama,nace na gama tashi ga abincin can,yana son yayi bacci na mika masa,yace Hannuna da Mai ban son tashi kisa spoon ki bani naci,ba da wani abu ya fada ba nima haka nasa spoon ina bashi har yaci ya koshi nace lemo zaka Sha?yace Ruwa ni ban fiye Shan lemo na kwali ba nafison fruits ko ruwa,ruwa na mika masa yasha,na kwashe komai na maida,su Meenat suna dawowa nace su shirya muje shopping,wanka muka Sha nasa doguwar rigar da Aayan ya bani nasa lokacin da ya kawoni wajen Family dinsa shiri mukayi sosai Meenat ce tayi mana kwalliya mun Sha kyau,mun fito nace suje jikin motar Driver yana can bari na fadawa Aayan.

Knocking nayi masa sannan nayi Sallama na shiga yana zaune yau magazine yake karantawa,nace zamu fita Shopping,hannu kawai ya daga min irin muje kawai,katon store muka je munsha siyayya sosai da sosai,Cosmetics,shoes,bags,mayafai,jelweries,Night wears,sai atamfofi kala biyar biyar,shadda kala Uku uku,sai materials tare da laces suma,Ready made dogayen riguna da riga da skert,mayafai dasu Inner wears duka masu kyau yan tsakiya dan yan tsakiya za ace baza ace masu tsada na karshe ba kudin baza su kai ba,wajen telanmu muka wuce duk Wanda za a dinka muka bayar,lokacin har dare yayi kusan ma 8:30pm,nace yau ba girkin dare nace Baba Driver dan kaimu Yahooza suya sai murna su Meenat sukeyi,mukaje na fita na siya mana muka zauna inda aka tanada don Zama ga masu son ci a wajen,muka ci abinmu muka koshi tare da ice cream,na siyowa Aayan ma nasa harda kilishin da suke siyarwa, Malam Garba ma na bashi nasa harda shi na siyawa,ya dinga godiya da addua,

Wasu sai kaga suna cin abu ma a gaban yan aikinsu wai baza a iya bashi yaci ba,bare aje dashi waje shima a dan siya masa ko kadan ne babu me kulasu Sabo da son kai su tunda talakawa ne suci irin nasu,
sai 9pm muka dawo gidan,a gurguje nayi wanka nasa rigar baccina kamar T-shirt take amma yar doguwa iya rabin cinya tsayinta,powder na murza nasa lipgloss sai dan turare na Amtek na shafa na dauki Take away na Aayan na wuce Samansa.

Da Sallama na shiga Yau ma yana saman Sallaya Sanye da Jallabiya yana karatun Qurani,ina zaune gefen Bed dinsa ya gama adduoin nasa sai lokacin ya juyo ya kalleni tare da cewa ya akayi? Ko ka tambaya mun dawo lfy? Gashi to na mika masa take Away,ledar ya bi da kallo sannan ya kalleni da baki ya nuna ledar tare da cewa bude na gani,da sauri na sakko kasa yace to Ustaziyya gyara Hijab din kina samun a fuska,Dariya nayi kawai na tsuguna tare da bude masa ledar duk kamshinsa ya cika min hanci me dadi ji nake kamar na fada jikinsa na shako kamshin da yawa,na bude yaga package na kilishi,daya ledar kuma Kazace da yawa tasha hadi,sai Fura da ruwa harda yoghurt,son jin dadi na da kwadayi na ya jinjina a ransa duk wata hanyar cin dadi na Santa har na iya na siyo masa wannan.

Muryarsa naji yace ina naku?nace ai mu a wajen muka zauna muka ci Namu kawai sabo da nafi so muna dawowa yaran nan suyi bacci su kyaleni na huta,Murmushin da bai shirya ba ya saki gaba daya ya tafi da Imanina don idan yayi murmushi wani masifar kyau yake karawa na musamman,ke ba yaranki ba amma feeling kikeyi kamar yaranki ne kika haifa sai son girma,

Fari nayi da Ido wanda ban san nayi ba nace ai ko Ammah na da rai nice kamar uwarsu,rufe wannan ledar bari na gyara farce na,nace au baka zuwa a yanke ma farce?yace a'a basa min yanda nake so ne a Abuja nakeyi ko kuma lokacin dana zauna a London,amma nan garin Sam nasu bai min ba tsoro ma nakeji kar su samin cuta,na kalleshi nace iyye kaji Manya Ashe har a London ka zauna uhm lallai dole kayi yanga,kallo na kawai yayi ya mike tare da dakko abun da yake yanke farcensa kalarsu ma daban ne, kawo na yanke ma kaji na iya sosai,Ba musu ya mika min na gyara Zama a gabansa, nace to fa sai ka koya min yanda ake amfani da kalar Nail cutter en nan ban gane ta ba,

gwada min yayi tare da cewa indai kika lalata min Nails sai kin biyani farce na in dai bai min kyau ba,ae naji kawo kafar to, kafarsa na jawo wani mugun laushi ba duk mace ba, na daura saman cinyata da na rufe da hijab, na mika masa take Away din tare da cewa to ci mana, naman ya fara ci ni kuma na dukufa ina yanke masa Farce,yana ci yana latsa waya yana murmushi ko chat yakeyi oho, ji nayi yana dariya nace mu gani me kake gani na dariya haka,ba komai kawai yace, da na dan shigar da zafi zai ce karfa ki yanke min precious skin dina, wannan kayan da kika cike min Bedroom dasu fa,nace au na manta ne na schl ne na kawo ma ka gani na bashi Labarin komai gobe ma zan fara zuwa,ba sai na gani ba kawai ki kwashe abinki,nace to ba damuwa.

Ina gama yanke masa na kafa ya gama cin abincin nasa,hannu ya goge da tissu ya miko min yatsun hannu masu shegen kyau dasu,na fara gyara masa farce ina cewa Dazu mun siyo kayan mun kai wasu dinki,du na karar da kudin Dubu uku ce kawai ta rage.

Ok yace ke kika bawa Malam Garba Abinci? Nace ae har ba dare ma,ya min waya yana ta godiya Ashe kina da hankali dai? Murmushi nayi nace Kai wai nufinka bani da hankali?to ba karamin Hankali da wayo ne dani ba,yace sai dai kiyi wa wani wayon na ki,harda kai ma zan mawa,Sau nawa nayi ma wayo kaine dai baza ka gane ba,a ransa yace lallai yarinya zan nuna miki baki da wayo soon,ina gama masa ya kalli yatsun tare da cewa uhm ba laifi,toilet ya fada yayi Brush dama yayi wanka kaya ya canja zuwa na bacci,yana fitowa yaga na kwashe kayan dana kawo du na tafi dasu,light ya kashe ya kwanta abinsa tare da Addua.

Washe gari ina gama aikace aikace na shiri nayi cikin riga da skert English wear nayi kyau na yafa mayafi na fita na tafi har part din Daddyn Aayan,securities basu barni na shiga ba sai da suka sanar masa matar Aayan ce yace daga yau indai itace a barta ta shigo kawai.
a saman Bed dinsa na ganshi an canja masa kaya yana kwance abinsa,cike da ladabi na durkusa har kasa na gaida shi ya amsa da fara'a,daga nan yace zauna ya ta,a gefen gadon na zauna,nace Daddy da har zan kawo ma abinci na tuna Ya Aayan yace ba komai kake ci ba,murmushi yayi tare da cewa ae ni abu me ruwa nake ci sai kuma vegetables sai ko snacks amma duk sauran abinci basu Dameni ba,tun farko haka nake ni dama abincinmu na Hausawa basu Dameni ba sai Fura da Kunu kawai amma na turawa nake ci,me girki na ma daban take yata,nace Daddy shi kuma Aayan ko yana yaro amma na Hausawa gargajiya yafi so,yace ai wannan kyaleshi kawai Uwarsa ya gado ta nan.

Kuna zaune lfy dai ko?ae Daddy lfy Alhmdllh,to idan ya miki wani abu kizo ki fada min kinji,nace to,idan kin samu lokaci kizo watarana zan baki labarin tarihin gidan nan namu kaf sabo da ki koyi Zama dasu,ranar da bani da schl zanzo,Allah ya kaimu,na mike nace na tafi zanje makaranta,yace na gode Mufeeda Allah ya taimaka,na fito a hanyar dawowa part dinmu na hadu da Ameer a hanya yana kallona zan wuce amma yaki matsawa sai ma hanyata da ya kara tarewa,na kasa gane masa kawai na matsa can na wuce abina tare da ja masa tsaki,a ransa yace zanyi maganinki.

1:30pm ina bedroom na fara shirin zuwa schl ina cikin sa sabon Uniform dina sai naji knocking ba zato,da sauri na zura hijab dina na fito da tunanin ko Aayan ne ya dawo to in ba shi ba waye zai min knocking a Bedroom,ina fitowa naga Dan iskan nan Ameer, ina ina ya fara ahm...ahm...abinci zaki bani,harara na maka masa nace banyi da kai ba don ba auro ni akayi dan na dafa ma abinci ba,na koma Bedroom tare da sa key,abin nasa ya fara tsoratani tun daga irin kallon da yake Bina dashi.

Cikin Uniform na fito ba karamin kyau nayi ba black and white komai nawa har jaka da takalmi kowa ya kalleni a uniform din sai ya kara nayi matukar kyau,Sallamar su Meenat naji Ma'eesha tana Faman Kuka,lfy Ma'eesha ina Meenat din na ganki ke daya,Sis wannan matan ne suka Mareni kuma ga Meenat can a Compound wai shoe maker ya tareta wai sonta yakeyi,wanne kuma me wankin talkami, wannan su Haneefa yake wankewa takalmin schl baki ganshi ba cikinsa kato hannunsa da jikinsa siriri kamar tsinke cikinsa kuwa katon gaske kamar zai fashe,sunce wai Meenat sai ta kulashi dole.

To shine kike mana kuka haka,to ai marina wannan Haneefa din tayi akan nace Meenat tazo mu tafi,ok wuce kiyi wanka ga abinci nan a Dining na tafi schl ni daga can zanga Meenat,maza Ku fara shirin Islamiyya,Bye Sis nace Bye, na fita rataye da jakata,saida nayi tafiya kadan sannan na Iske Meenat Tsaye tare da wannan mutumin me gyaran takalmi,ni tunda na ganshi ma dariya ta kamani don cikinsa girmansa ya isa ga jikinsa siriri kamar a bushe shi ya fadi,su Haneefa suna zaune suna faman latsa waya.

A fusace na karasa wajensu nace Malam mene haka lfy kazo ka tare min yarinya anan ko kunya baka ji idan kudin magani kake nema ai sai kayi magana a baka kaje Hospital,Meenat tace ba ke bace Sis nace ki bamu dama amma kince kar mu kula su ko me zasuyi mana dole kece zakiyi kawai,Yan matan nan ne suka taso kanmu,ke wace da zamuce ayi abu kice zaki hana wannan ya gani yana so kuma dole ta kulashi in dai tana gidan nan,sabo da shine dai dai ita,Haneefa tace au Ku nan har kunfi karfin wannan kuna yayan talakawa,dama kadan nake jira Mari lafiyayye na zabgawa Haneefa dama kin Marar min kanwa wlh ba wanda ya isa ya taba mana lfy ya kwana lfy,nasan in suka hadu zaneni zasuyi Marin ma da kyar nayi ta maza na shammaceta na fesa mata shi, Cikinsu Sukace KWAJA jeka ka dawo gobe dole sai ka auri wannan suka nuna Meenat,Meenat tayi dariya tare da cewa au dama sunanka KWAJA? Lallai Kaci sunanka ta kara sakin dariya,nace wuce to ciki yar iska idan kika kara tsayawa dashi wlh zan miki rashin mutunci,to ba ke kikace kar na dau mataki Kansu ba,motocin Aayan ne suka shigo ya hango Su Haneefa sun rike min Hijab gashi nayi kyau, har gabanmu yazo yace sake min mata yana gyara wayar Usb da ya Ciro a motarsa,Haneefa ya damko ya dinga tsula mata wayar tana kuka da ihu,su kuwa sauran tuni sun Arce,wlh duk ranar da kuka kara taba jikin matana sai na kusa kasheku a gidan nan kuma kinsan ba abinda zai faru,nasan kin san da haka,kallona yayi tare da takowa wajena zai damko ni nima na kwashe da gudu,ya biyo ni taku biyu ya damko ni Ransa a bace ya kalleni ido da ido sai yayi murmushi matsoraciya yi mata dariya zance shine kika gudu,aiko Nace Haneefa tana Kallona na kyalkyale da dariya nace wooo ayi mata gwalo,Aayan yace fara frog jump dan ubanki kafin nazo nan na halaka ki,da Sauri ta fara yi,yace yi mata dariya ke kuma Aiko na dinga yi ina wooo harda tsalle,muna Haka sai ga Hajja kakarsu ta fito kamar zata make mutane,Aayan yace jeki schl tana cewa tsaya dan ubanki Karuwa Amma ko kallonta banyi ba na shige mota abina Malam Garba yaja,ta glass tana Kallona ina kallonta na mata gwalo,Aayan ya daga min hannu bye,tana zuwa ta daga hannu da niyyar sharawa Aayan Mari ya rike hannun caraf tare da matsar da ita gefe ya wuce ya bata waje bai ce kala ba,Kuka da kara tare da ihu ta fara yi a gaban yan aiki,Sai ga Abbi yana huci an taba Uwarsa.

Tunda na fara zuwa schl yau Sati guda kenan lfy nake zuwa ina dawowa abina cikin jin dadi,haka su Meenat ma,Aayan kuwa tun daga ranar da ya Zane Haneefa ban kara ganin Sa a gidan ba,ashe wai ya tafi Umrah Saudiya bamu sani ba sam,koda kudina suka kare Bedroom dinsa na shiga na duba inda yake ajiye kudi na ebi dubu biyar idan ya dawo sai na fada masa.
A schl dinmu har kawa nayi yar gayu wayayya MARYAM ga hankali ga sanin ya kamata,kullim tunda taji ina da aure take fada min yanda ake Tafiya da Imanin me gida,nace ai ni kullum da Hijab nake zama a gida idan zanje unguwa ne nake Sa mayafi watarana,aiko ta dinga dariya tana wayar dani ni kuwa dan kar ma Aayan yace Dan shi nakeyi nace ko Ya dawo bazanyi ba.

Yau da yamma su Meenat sun dawo kenan daga Islamiyya KWAJA me gyaran takalmi ya biyota tun daga wajen gate,dama su Haneefa sun fadawa Securities in dai Kwaja ne a barshi ya dinga shigowa yana da budurwa a gidan bayan haka ma yana goge musu takalmin schl.
Direct Kwaja ya shigo yana wargaje baki da wata falkekiyar T-shirt,hannun rigar Sabo da ramarsa kamar skert hannu tsilili a ciki, kansa har wasu jijiyoyine ke tashi kamar me kwoshokwo, wuyansa kamar mirkin laima,dan kirjinsa kuwa kamar Allo,hakoransa guda biyu manya a waje na gaba,bakinsa yake dargajewa shi tunaninsa ai dole ma ya auri Meenat tunda yayyenta sunce sun bashi ita.
ta window din sama Na hangosu yana tsaida Meenat yana Meenatu Meenatu yan mata dan Allah ki tsaya,haba Meenatu so kike sonki ya kashe ni? Meenat ta ja tsaki tare da hararsa Malam Kaja mituncinka mun san darajar Dan Adam shi yasa nake daga ma kafa Amma tunda kaki ji zaka ga abinda zanma.
Kwaja yace ko me zaki min ni Bazan ji haushiba tunda ina sonki,da wlh ba da gaske nake ba Amma na yaba da hankalinki da nutsuwarki,gaki kyakyawa ni yanzu ba zancen yayyanki nake bi ba wannan da gaske ne daga makwallaton zuciyata a daina maganar wasa, to bana sonka kaja Life dinka ka kara gaba Malam cewar Meenat,Murmushi yayi yace yan mata bani da Lifan ni bana karya dan a soni,karki kiyi tunanin Ina da Lifan kice Naja Lifan dina na tafi wlh Allah ko Keke bani dashi idan zaki soni ki soni dan Allah nasan ku manya ne kun wuce ayi muku karya,Takaici ya kama Meenat tace ina ruwana da karyarka ka ja rayuwarka kayi Out a gidan nan,Haushi KWAJA yaji yace na fuskanci Ku kunfi son dan karya azo ana muku birga da mota kullum idan nazo zance na baki Dubu daya ko Dubu daya da Dari biyar koma fiye da haka,to ni ba haka nake ba gaskiya da gaskiya nakeyi wlh da zaki aureni kullum sai na dinga siyo miki kifin gona kina soya mana,watarana ma Miyar zabo zaki dinga yi mana,Taliyarmu guda da macaroni da wake gongoni guda ya ishemu na na kwana hudu zuwa biyar, tsaki Meenat taja tayi gaba ta barshi nan,ina jikin Window ta sama ina ta dariya gaskiya Su Haneefa yan Iska ne,Meenat ta shigo na dinga mata dariya,nace Allah sarki kanwata duk iya kwalliyar nan kuma taki sai ki kare a KWAJA tumburarre,Dariya tayi itama tare da cewa ai Allah ya tsinewa su Haneefa yanzu idan nayi wani Saurayin yazo ya ganni da wannan ai wlh rainani kawai zaiyi ya daina zuwa,ina ta dariya harda kwalla Meenat tace dan Allah ki daina,har dare muka kwanta ko farkawa nayi sai nace ta KWAJA tashi na baku lbr,banza tayi min tace wlh sai na fadawa mijinki idan ya dawo tunda haka kike min.

Yau nayi shiri tsab ba schl zanje wurin Daddyn Aayan ya bani labarin gidan nan da yace zai bani,koda naje Sallah ya idar daga kwancen,yana murmushi muka gaisa,nace Daddy yau na shirya a bani Tarihin naku. Yace to yata bude kunnuwanki kiji.


Next page is very Important readers ku tsaya ku karanta da kyau shine zamu san waye Aayan.
Raffa



Asma Baffa
[1/10, 10:37 PM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA






46-50






Official






By
AsmaBaffa








Page naku ne MADINA ALEEYU
MAMAN SAMHA
NAJA'ATU ALIYU

Jinjina gareku na wajena
MOMMY ARFAT
AYFA
MARYERM MUHD
HAJARANCY
HAULATU

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login