Showing 114001 words to 117000 words out of 175038 words

Chapter 39 - KASUWANCINA BOOK COMPLETE BY ASMA BAFFA.doc

25 Sep 2025

6879

iyee nanaye...Ayyeee riyalle duniya.....Haneefa dake kusa da ita tayi lamo a gefe sai yanzu take tunanin aure,da can me yasa bata samu cikin samarin ta masu kudi ta fitar da miji an mata aure ba ta zauna tace ita karatu sai tayi Masters, yanzu ko mijin ma ta fito dashi wa zai mata kayan daki? Mikewa tayi ta bar wajen Hajja ta koma dakinsu inda ta tarar da Su Meenal tare dasu Sajeeda sunyi jugum suna tunani,Kallonsu tayi tace ya akayi ne yan mata? Meenal tace hmm ke dai bari Wai yanzu Abbi yazo duk mu cire layin wayar mu mu basu harda masu computer kowa ya kawo tasa wai za a siyar a siya mana kana na Irin su Dagani Gara, harda wata waya Dagani Gara kuma? Ae mana tana nan wata me uban nauyi yar China ko Camera babu,Yanzu dan danna wayar ma da muke tana ebe mana kewa karbesu za ayi kwarai kuwa dan har an kwace ta yan mazan gidan nan tare da Sauran yara kaf za a siyo kayan abinci me yawa wanda zai dan Dade ana ci,Abbi kullum suna fita neman aiki duk tsufansu amma ba a dacewa.

Khaleel ne ya fito daga wanka ko Vaseline babu a dakinsu dakin su Haneefa ya shigo da gajeren wandonsa kai Ku miko min Vaseline na labta a jikina,Sajeeda tace kamarka da shafa Vaseline,to ya zanyi kawai a bani na labta haka,kune ance Ku samu aiki kunki ai da mun huta,Khaleel yace baki da hankali in mutum yayi aikin ma ai sai abinda Hajja tace wlh akan nayi wannan tsohuwar ta Dameni gwara na bar gidan nan na koma gidan frnd dina. Haneefa suna dariya tace nayi mamaki da yanzu kowa baya ragawa Hajja to ko dama wai tsafin nata can gidan ta binne su ne? Ita ta sani ai gashi tun ba a je ko ina ba sun jawo mana muna gane kurenmu gaba daya me yafi zaman lfy dadi Ameer tun wuri ya shiryu gashi ya huta Allah sai ya zareshi a cikin mu suka koreshi Ashe gata suka yi masa aikin banza ni dama ni suka kora wlh da wannan wahalar,Khaleel sai masifa yakeyi yana shafa mansa a dakin ya gama sannan yace to Ku ban aron Cumb,Meenal tace Cumb daya tal a gidan nan na Umma da ta zo dashi a jakarta shi yake yawo a gidan nan kowa dashi yake taje kansa mata da maza bari na karbo ma, yanzu wannan Sumar dana tara ta common Cumb ba bu bare man gashi da sauran kayan gyaranta ai kamar mahaukaci ma zan dawo soon zanje wajen me aski dole na sauketa, Sajeeda tana dariya tace haba gayu tana ma kyau, gyara ne yasa yanzu da babu zaki gani very soon dole ina ji ina gani na sauke ta, gaskiya Aayan baida mutunci Allah wadaran sa daya kore mu akan shegiyar Mufeedan nan,

Khaleel yace ah lallai baku fara nadama ba me tayi muku yanda haka kawai muke biyewa su Abbi da Hajja muka sasu a gaba musamman Ku,Aayan ko wacce shara shi ake turawa,tun bai San kasar nan ba Hajja ke tura masa asiri tun muna yara har muka girma,ki tuna takura da akayi masa shi da Ubansa,kalli matayen da aka sa ya aura kuma aka sa ya sakesu,kalli irin yanda ake nuna masa shi da Ubansa ko makiyinka ai baka yiwa haka ba bare dan Uwa na jini,Allah wadaran halin Hajja me zuciya kamar ta fir'auna danka da jikanka ka jefa su a wani Hali duk sabo da son kudi.

To mu ba irinku bane Sajeeda shekaran jiya dukkanmu Maza muka zauna muka tace tare da tankada mukayi rairayi munyi lissafi ya bulle dai dai dan haka mu Maza duk mun tuba wlh Allah ya ganar damu gaskiya kuma Aayan bashi da laifi yama yi kokari yayi biyayya,yana da damar da zai tattara su koma kasarsu amma ya zauna damu yana Shan bakin ciki,to mu dai yanzu ma Istingifari mukeyi ko mu nan ance miki Hajja haka zata barmu ba tare da ta asirce kowa ba, tunda tayiwa danta da ta haifa wa zata kyale kuma Uwa fa guda, yanzu kalli inda su Mommy suke mata rashin kunya kin San kuwa asirinta ne yake ta karyewa zai tonu,gamu dan muma mun gano gaskiya,da ai bamu gane ba musamman Ku mata masu karamar kwakwalwa,mu dai sai Aayan da Mufeeda,Allah ya bar mana Anty Mufee sai Mufee.

Sajeeda tace kato da kai kana kiran wata yarinya karama da Anty anji kunya,ai ke bakin cikin naki harda Hassada cewar Khaleel kinga tafi ki kyau,ta auri Aayan sannan Ameer ma maybe Kanwarta zai aura,Me yasa yanzu samarin naki yan iska basa zuwa? Duk sun gujeki wlh tun wuri ki gane gaskiya,Haneefa tana ji da sauran mata duk sunyi shuru Khaleel ya gogesu tas ya kara gaba abinsa.

Gaba daya sun hallara a Palo ana cin shinkafa dafa duka tasha manja tana tiri tiri sun saba da cin girkin yan gayu duk sai suka ji wannan ba dadi kowa turawa yake da hakuri,Abbi mamakinsa daya shine dare daya suka koma talakawa me yasa basu yi planning sun mallaki kadarori ba,a ransa ya tuna da fa talakawa ne su sai rufin asiri kuma aka samu Daddy ya basu aiki suka koma gidansa da zama,da sun San haka ne gwara a ginawa kowa gidansa daban da yanzu ba ruwansu,duk kudin kuma da suke samu a wajen bokaye suke karewa aikinsu kenan,kawai kudi suke kwasa a Companies suna abinda suke so basa tunanin su tattala sabo da gaba sai burin kawai su kwace Dukiyar Aayan data Daddy,Hajja kuwa ko a jikinta bata da niyyar tuba sai ma kwantar da hankalinta da tayi tasan dole Daddy zai nemeta ta dawo dasu dole su dora daga inda suka tsaya.
Meenal ce a palon tace duniya budurwar wawa,Abbi ya harareta tayi shuru,Abbi sani kuwa kallon Khaleel yayi tare da cewa dan ubanka baza ku aske Sumar nan ba ko sai kace kan mahaukata,Khaleel yace haba Abbi yawa kuke ba kudi ba komai me kuke so yan mata su gani a kanmu mu birgesu dashi yar wayar duk kun kwace kuma ya kuke so muyi shike nan mu baza muyi nishadi ba kenan, Mujaheed yace ni wlh aka sake barin gidan nan zanyi me ake min sai fada safe da rana da dare.
Hajja ta Galla musu Harara ba wanda ya kulata wanda ta tabbata da ace da ne da tuni sun bata hakuri,Hawaye Hajja ta fara tare da cewa an rainani bani da iko da kowa,shuru ba wanda yace mata kala,ta mike tsaye tare da cewa ai bani na dora muku talaucin ba da zaku tsaneni me nayi muku? Wlh in na gaji bar muku gidan zanyi,sai nayi magana ayi Banza dani wata tsiyar nayi muku da za a dauki karan tsana a dora min,to duk Wanda ya fasa baya kaunar uwarsa da ubansa,Abbi yace me akayi miki kuma wai? Gasu nan bani da iko nayi magana sai cin mutunci to wlh zan bar muku gidan nan, Hajja ta fashe da kuka, yaran gaba daya tsaki suka ja tare da mikewa daya bayan daya suka bar palon su Abbi ne ke bata hakuri.

Zaune nake a palon Sama na Aayan,naci uban kwalliya cikin English Gown iya cinya nayi kyau,Yau na samu Salama Da kyar Aayan ya fita zuwa wajen Yarima yana nemansa yace bazai je ba da kyar na lallabashi sabo da ya Dameni da fitina ko kasa bana sauka sai dai su Meenat ke yin komai kullum sai ya sani kuka yace zan saba ni dai yau 1wk kenan ban saba ba.
Abin mamaki 40mnt sai gashi naji sallamarsa har ya dawo, duk da damuna da Aayan yakeyi bana ganin laifinsa kuma bana jin ya isheni ko naji haushinsa Sam bana jin hakan sabo da sonsa da yayi min yawa bana jin akwai abinda zai nema na hanashi a duniya,Da ya fita ma duk sai naji ba dadi gidan amma jin sallamarsa wani Sanyi da dadi ya ratsani har na kasa boye farin cikina,. Tsayawa yayi yana kare min kallo yanda yaga na wani yi mugun kyau kamar a sace ni,murmushin da nasan yana kara min kyau na sakar masa tare da walwali da Idona cike da jan hankali ina daga zaune na bude masa Hannu ya kuwa karaso a hankali tare da shigewa jikina a hankali na mayar da hannuna tare da rungumeshi gwiwoyinsa suna kasa,Hannayena nasa tare da tallafo fuskarsa muka hada Ido nace sannu da zuwa kana na shiga tsotsar bakinsa kamar na samu Alawa me dadin gaske.
Hannu na daya na sa a cikinsa nace muji ko kana jin yunwa dariya yayi sabo da yanda nayi kamar irin dana din nan, ina Sonki My Queen ya furta yana dariya sabo da yanda nake masa cakulkuli a cikinsa, mikewa yayi tare da kwanciya saman doguwar kujera ya daura kansa a saman lumtsumemiyar cinyata wacce ke sheki da santsi ga tsoka da girma sai kamshi takeyi ta ko ina,Yar rigar dama guntuwa ce,Hannu yasa ya wara cinyata wai bude min Kingdom din taki na gani ya warke jiya fa sau daya kika bani tal, shagwaba na fara

nace Allah a'a amma ai ya dace ka dinga danne maitarka kullum ba fashi ka bari na warke sai na baka amma kullum kace Dan Dis,gobe kace dan Mitsili,gata kace kadan,nasan yau kuma cewa zakayi....kafin na karasa yace Dan Kucili, dariya mukeyi gaba daya yace tunda nake koyan hausa in baki labari wannan words din ne suke bani Wahala da dariya,abin dariya,wai Dan Kucili,dan mitsili,dan dis,dan kadan,dan Kis,Dariya mukeyi nace ai har dan Kucilili ana cewa,yana dariya yace to na yau Dan Kucili zanyi,nace naki sai na warke 1wk sai next wk,Ido ya zaro waje tare da cewa kawai mutuwa kike so nayi ni bazan iya ba,Ina wasa da gashinsa nace gidanmu na gado wai ya za ayi dashi ne? Aayan yace ki Bari kawai a gyarashi a sake sabon Gini sai a sa yan haya mu jira muji nan gaba ko Abbanku yana da rai ko ya rasu dole bincike za ayi first,nace to Allah ya kaimu,Ameen yace sai me kuma?nace uhm...uhm.. da dai zan fada kar kace ina da son kudi ne,fadi mana idan ma kina so waye baya son kudi kuma ai kudin mijinki kije so ko? Kai na daga ae,Lefe ni fa ba ayi min ba,dariya yayi tare da cewa duk kayanki? Ai wannan kawai siya mana kayi kuma ma ai har su Meenat lefe kuwa iya Amarya akewa, Ki kwantar da hankalinki idan ma har biki kike so sai ayi miki,nace a'a ni bana son biki ko wata Dinner kawai lefe nake so sannan ayi min Kamu, mene kamu kuma? Kamu da akewa Amarya idan ana gobe za a daura mata aure a sata a lalle,to ai gwara Dinner dashi,nace a'a ni duk wannan basa birgeni kawai Kamu za ayi min nima shine yake birgeni a duniya bazai yuwu ace ni har abada baza ayi min ba,kullum burina naga anyi min Kamu a biki sai kuma haka ta faru to duk da haka ban makara ba shi yasa nake jin tsoro kar na samu ciki ba ayi min Kamu ba,idan na haihu ai magana ta kare kuma na haifi dan dakan Kuka,Dariya Aayan yake tayi tare da cewa lallai har yau Kuruciya na nan,Dan dakan kuka kuma shege fa kenan,Dariya nayi nace ae ayi min Kamu ni dai ko idan na haihu nace dan dakan Kuka na haifo.

Jibi Birthday na sai a hada da kamuna,Waye zaiyi Kamun to? Zakiyi Birthday party ne? Nace a'a ba wanda zan gayyata Meenat da Ma'eesha sun isa su sani a lalle,ga Ameer da kai kuma Ango kun isa shike nan,Aayan yau dariyar Mufee kamar ta kasheshi da shirmena,yace to sai na gayyato Yarima ma yazo ayi dashi ko,nace to Allah ya kaimu,Aayan ya kalleni yace Amarya an kusa saki a lalle,nace haka yake next wk zamu koma schl ma,Nan Aayan ya hade rai yana jin haushin schl shike nan bazai dinga gani na ba sai yamma,yace a bari sai nan da 2wks ki koma kinga kin kara 1wk kenan ko? Nace ae Allah ya kaimu,Bazan iya yini ban ganki kusa dani ba, schl ta wani dawo ya furta tare da sauke ajiyar zuciya .

Na kalleshi nima nayi shuru sabo da bana so mu rabu ko na 1mnt,hannunsa naji ya tura cikin rigata yana Murza kirjina, sakon dai dai yake shigata babu gargada ban san sanda na shiga Maida masa da martani ba,daukana yayi cak yana rada min dan Kucili za a bani,banyi musu ba sabo da bana son na bata masa kuma kar ma yace na fiye Complain ba dama miji yace zaiyi wani abu sai mace ta fara Complain sai ki ga yana jin tsoron neman hakkinsa yana danne sha'awarsa sabo da yawan Complain,ko miji ya dinga zargin kansa Shi ba namiji bane ko bai iya komai ba baya sa matarsa taji dadi dashi sai kiga duk ya shiga damuwa da tunani baya birge matarsa shi.

Meenat ce zaune Saman sofa tana Shan ice cream dinta tana kallon American film a Tv,Ameer ya shigo ya zauna gefenta shima sanye da riga me gajeren hannu da 3qtr sai kamshi yake yi,yace San min na Sha Ice cream din,Dazu ya Aayan ya kawo mana da yawa yana fridge,bana iya Sha da daya ni kawai in zaki bani a naki ki bani,Meenat ta turo baki haka ta ebo a spoon tace duk zaka rage min quantity ni ungo ni karbi ya bude baki kuwa Meenat ta zuba masa ya shanye tana Sha tana bashi sai da suka shanye robar guda sannan Meenat tace kaji dadi hankalinka ya kwanta mun shanye da kai,karo wani mu shanye again ,au dama kana iya Sha da yawa dan kar nasha nayi kiba kazo ka raba ni dashi, Ma'eesha ce ta cakare ta fito kamar zata je Dinner,Meenat kawai sai ta hade rai tam, Ma'eesha tace Sis zanje wurin Yarima yana palon baki,Meenat sai lokacin ta saki ranta tace to maza ayi sauri a dawo lfy ki gaisheshi..me Meenat ke nufi da fushinta da farko? oho.

Kallon film dinsu suke yi sai katsam budurwa da saurayi suka fara kissing din juna a haukace,Americans ba kunya sai gashi ana tube kaya za a fara Sex,Meenat duk kunya ta rufe ta da sauri ta dauki remote zata canja Chanel,Ameer yace mene haka sai da kallo ya dauko dadi ai nan shine ainihin film din Horror movie ne ki tsaya ki gani abinda zai faru mana,Meenat tace ni ba yar Iska bace tana Satar kallon Tv kuma,tace haka kawai mu dan Allah ka kawo remote a canja ka wani kwace basai mutum zai kalla ba, Meenat taji ana shidewa a Tv Ameer ya ba da Amanna yana kallo ta dan kallo ta dauke kai tace yan iska kawai sai taga Masoya sun koma abin tsoro dama Horror film ne sai suka koma fada da zako zako hakora,mace ta bude bakinta wommm...Sai da Meenat ta buga kara tare da fadawa jikin Ameer, Ameer yana Jinta dan munafuncin Sa sai yace ai film din nan abin tsoronsa yayi yawa yanzu zaki ga ma sun koma kamar Dujal ance har mafarkinsu akeyi, na gani a BBC wani Horror rannan ana kallo a wani gida ya fito daga TV ya shiga jikin matar kin San Aljanune, Meenat ta kara kankameshi ta boye fuskarta a jikinsa taki dagowa,Ameer yana jin dadi a ransa a fili yaci gaba da cewa ai ba a barin irinku su kalli wannan sabo da idan suka ganku sukan iya Faso TV suzo wajenku,ni tsoro nake jiye miki dan yanzu zan fita sai ke daya bari na Canja Chanel,ya canja Chanel ya fara kamar zai Mike Meenat ta rikeshi kam ta makale a jikinsa tana roko Karya tafi,yace to sai dai ki dakko Ice cream ki dinga bani a baki sai na zauna idan ba haka ba tafiya zanyi.
Da sauri Meenat ta dakko tace bari na baka idan Ma'eesha ta dawo sai ka tafi kawai,nan ta zauna damfamfam tana bawa Ameer Ice cream a baki yana sha yana latsa wayarsa ya Zama dan gata,a ransa yace wlh aure zance Aayan ya min kwana nan na huta nima.






AsmaBaffa
[2/2, 12:41 AM] Asmabaffa:
KASUWANCI NA







107-108









Official







By
AsmaBaffa








HOUSE OF HAUSA NOVEL,TASKAR SURAYYARHMS,TASKAR FIDDAUSI SODANGI,UWARGIDA,ASMABAFFA FANS CLUB gaba dayanku gps na gode da Sharhi da kuke yawan yi kunfi kowa shi yasa wannan page naku ne.

Tnx etc da ake yawan fada basu damu Writers ba anfi son Sharhi Readers Ku daure kuci gaba munfi jin dadin typing da posting.Gp dina naga ana sanya da Sharhi ko an fara gajiya ne da Novel din a tafi Hutu?=?
?=?
?=?
? Love u all fans.













Ameer yana tunani ya zaiyi ma shima yayi auren nan ya huta,kwanciya yayi saman 3seater tare da Jan eriyar tunaninsa ya shiga nazari,Meenat na gefensa ta gama bashi Ice cream tana waya da kawarta ta schl,yawancin yan makaranta musamman yan Boarding schl idan suka hadu da kawayensu zage zage zaka ji yana tashi kawai ana shegiyar ya gari etc,yanzu Meenat ita da tayi Day schl ma wannan tsabiyar ta zauna mata Ameer na gefe ta daga waya kawarta tana dagawa Ameer yaji kawar ta duro ashar, Meenat tana dariya tace amma dai Allah ya tsine miki,Shegiya ai baki da mutunci,Kawar tace dan ubanki ke Hafsat Salisu ciki ne da ita daga biki, Meenat tace ke Dan Allah? ke Amai take yi,Meenat tace ai Hafsat Salisu matsiyaciya ce,ai Allah yayi yar iska a nan wajen,Kawar Meenat tace hmm ke dan uwarki Aisha Balarabe wai aure zatayi shegiya, Meenat tace ai tsinanniya ce Aisha ta kirki zamu je gidansu ai soon, duk wayar tasu a zage zage ta kare har suka gama wai nan hira aka Sha kuma sai gulmar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login