Advertisement
Showing 27001 words to 30000 words out of 85238 words

Chapter 10 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

61

daka yau ba matarshi bace, ta Kalli A Majeed tace ka rubuta min takardan aysha kuma saki uku nake So yanzu ka ban, Zainab da sauri tabar wajan jim kadan sai gata da takarda da biro tana mikama A Majeed, bai amsa ba bai kuma yi mata magana ba, illa Mum ce data karaso wajan ta amsa takardan cikin takaici ta mika mai, amsa yayi ga mamakin Mum sai gashi ya fara rubutu, harya gama ya mika ma Mum tare da fadin Mum kiyi hakuri naso in zauna da ita amma na kasa sata a raina domin bata cikin tsarin macen da nake so.... Mum jan hannun indo tayi wacce take ta faman kuka suka fita mota Suka shiga driver yaja, gidan su na abuja suka nufa, Mum Tana shiga ta zaunar da indo ta fara mata nasiha akan tayi hakuri haka Allah ya tsara mata, sannan tana rokan indo akan taci gaba da zama da ita karta ce zata barsu, indo ta kasa magana sai kuka mum ta janyota jikinta ta rungumeta itama tana hawaye, dakyar ta samu ta rarrashi indo tayi shuru, ranan zazzabi ne ya kama indo sosai Mum ta tsorata dan haka suka nufi hspt Dr yace damuwa ne ya mata yawa tana bukatan hutu, nan ya bata Magani sannan suka dawo, washe Gari suka dawo jalingo, Mum ta fadama his excellency abunda ya faru tun a waya ranshi yayi mugun baci, koda su Mum suka dawo yace ta bashi takardan amsa yayi ya Fara karantawa kaman haka *NA SAKI AYSHA SAKI DAYA MUM KIYI HAKURI BAN TABA SON AYSHA BA, BANA SON FUSHIN ALLAH A KAINA DAN ALLAH MUM KI GAFARCI DANKI* his excellency bayan ya gama karantawa yace Allah yasa haka shine alkhairi yace Mum ta kira mishi aysha din, Mum ta tashi ta kirata bayan tazo his excellency yace aysha naji abunda ya faru da farko dai zan baki hakuri akan abunda ya faru sannan in nemi alfarmanki akan ki zauna damu har Allah ya fito miki da wani mijin, tace insha Allah sannan ban rike komai a raina ba komai ya wuce, his excellency yaji dadi sosai yana ta sa mata albarka, tare da fadin zai zamo mata uba ta dauka tana tare da iyayenta, taji dadi sosai, bayan indo ta fita Mum tace akira A Majeed ya karasa ma indo sauran sakin, his excellency yace babu kyau saki uku duk da daya yayi mata bana ma tunanin zai dawo da ita tunda ya tsaneta kawai ki barshi .










A kwana a tashi babu wuya indo ta gama idda, kuma tana zuwa makaranta ta kara kyau da girma sosai komai nata ya fito domin Mum Tana tsaye a kanta wajan gyarata da bata abubuwa masu gina jiki, farin indo na asali ya fito har wani sheki takeyi dan haske, gashi babu laifi tana jin turanci yanzu dan bada wasa take karatun ba, tun Mum da Dad na fishi da dan nasu har suka hakura sai dai tun daka ranan daya rabu da indo bai kuma ganinta ba, sai dai abun yana dan damunshi dan bazai taba manta sanda yaga kirjinta a waje ba har yanzu abun na idonshi ya kasa mantawa duk da kuwa lokacin ana cikin tashin hankali, Abdul yaji abunda A Majeed yayi ya kira indo ya bata hakuri sannan yayi fushi da abokin nashi sosai.






Wasa2 dai indo an kammala karatu anyi waec ta sami 8 credit, nan Mum ta fara mata kokarin fita zuwa Egypt Alhmdlh indo ta sami gurbin karatu a kasar masar wato Egypt inda ta sami medicine duk da indo taso ta karanci political science amma bashi aka bata ba, tare da Mum indo aka daga zuwa kasar misra, wai indo a jirgi first time in history😂 abun mamaki kuma batai kauyanci ba, kodan yanzu an waye ne oho, amma fah ta dan tsorata kawai ta dake ne irin ita Big girl din nan😁 koda suka sauka a kasar Egypt driver yazo ya daukesu nan iyayen Mum sukai ta murnan ganin yar tasu kaman zasu cinyeta dan murna, ummi tana ta jan indo jikinta domin taji tana son indo, haka shima baban ummi din da Mum ke kira da abba, nan sukaci Suka sha, ummi da turanci take ma indo magana dan bata jin larabci, kwanansu biyar suna yawo a Gari kafin Mum ta fara ma indo kuciba2 harta gama mata komai harda islamiya aka saman mata, washe gari driver din su ummi yakai indo ta fara lecture, haka idan ta fito zaizo ya dauketa in zata islamiya ma haka, indo an fara sabuwar rayuwa watan mum daya ta dawo Nigeria, Indo karatu take sosai babu laifi tana ganewa, tayi wata kawa balarabiya mai suna fatima suna shiri sosai indo tana dan jin larabci kadan2 duk da yawanci maganan da turanci sukeyi danko a islamiya ana hada musu da turanci, suna Waya da abdul jefi2.










A Majeed gaba daya ya kasa gane Zainab domin tunda indo tabar gidan rabon da wani abu ya shiga tsakaninshi da Zainab dan tace hala ma wai ya hada jiki da indo din karya shafa mata cuta, wai sai anje anyi gwaji, ganin yana cutuwa yasa ya yarda akayi duk da yana ta rantse mata babu abunda ya faru shida indo din amma taki yarda anyi test bashi da wani cuta, ta dan sakar mai amma ba sosai ba, gashi yanzu ta karo wulakanci sai tabar kasar tayi wajan wata daya bata nan, gashi idan ya mata magana ta inda take shiga ba tanan take fita ba, wata rana tayi tafiya watan ta daya da sati daya tunda ta tafi sau biyu sukai waya shima daka ta dauka sai tace tana aiki zata kirashi idan yaji shuru saiya kirata taki dauka, daka baya ma yaji wayanta a kashe, koda ta dawo ya mata magana wai ita fah Karya takura mata ta fara business ne, ranan hakurin A Majeed ya kare yace mata nifa mijinki ne ina da hakki akanki kin maidani kaman wani hoto, nifa mutum ne ba dutse ba, ina da Sha'awa,tabe baki tayi tare da fadin to ni mai ya dameni da Sha'awan ka? Idan kaji abun ya dameka basai kasha Magani ba, ranshi ya kuma baci yace tunda haka kikace ki sani bana zina kuma ba zaki sa in fara ba ina da bukatar Mace dan haka zan kara aure, wani uban ashar ta saki tare da fadin wlh baka isa ba, karka manta wacece ni, bari in fada maka wacece Zainab yar president babana ne na daya a kasar nan banga wata wacce zan iya kishi da itaba a cikin kasar nan ko wacce iyayenka sukai gigin hadaka da ita fita tayi ta barni, danma ranan mamanka ce ta kwace ta da tayi rayuwa a prison ita da iyayenta yanda babu mai kuma yimin shishigi, ina da kudi ina da ikon da zan hanaka auren ko wace Mace dan haka ka cire wannan abun a ranka ni Zainab ni daya ce matarka a cikin duniyan nan so you have to be very careful akan abunda zaka dinga fada,tana gama fadin haka ta wuce ta barshi zama yayi yana mamaki dama haka Zainab take? Sai yau ya gano abunda Mum take nuna mai lallai yaba Zainab dama da yawa, tunawa da indo yayi nan take yaji nadaman abunda yayi mata lallai wayewa da yawa Bala'i ne, yau yaga illan wayewa wanda gashi matarshi tana nuna kaman itace keda iko Dashi, tuna kalaman abdul yayi da yake cemai yafi son ya auri yar talaka wacce ko mai ya mata zatai godiya ta amsa hannu bibbiyu baya son macen data waye sosai, nan take ya Tuna da maganan Mum da take fadin na maka gata son amma ba zaka gane ba sai nan gaba,.hmmm muje zuwa











Taku Maryam obam😘


*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









110to115







*DEDICATED THIS PAGE TO....*

*AYSHA BAGUDO INA YINKI IRIN TOTALLY DINNAN😍*










A Majeed ya dauki lokaci mai tsawo a zaune, tare da tunanin abubuwan da suka faru a baya, Zainab kam tana shiga daki toilet ta fada tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da wando tayi kyau sosai, zama tayi a dakinta Kana ganinta kasan ranta a bace yake tabbas in bata tashi tsaye ba A Majeed yana son ya nuna mata wuyanshi yayi kauri, dan murmushi tayi lallai wannan karan idan da gaske yake muddin ya kara aure sai tasa yayi dana sani, domin tana son mijinta kuma ita daya zata zauna Dashi, har yau tana ganin auren indo da aka bashi a matsayin an mata wulakanci a rasa wacce za'a bashi sai yar matsiyata har yanzu bawai ta kyale indo bane inda zata ganta koh tasan inda take dasai ta koya mata babban darasi yanda babu wata Mace da zatai gigin auran mata miji nan gaba, amma koh yanzu bata baci ba tana jira taga wace mace zai Kawo a matsayin mata inma dagaske yakeyi haka itama taita tunani.















Zabe yazo anyi zabe his excellency yaci zaben senator yanzu su Mum sun dawo abuja da zama, sannan mahaifin Zainab ya kara cin mukamin shi na president domin mutumin kirki ne mai tausayin talakawa, Zainab an kara fasowa gari tare da karo wani sabon wulakanci, yau tana can gobe tana can A Majeed tun yana magana har ya daina yasa mata ido, sai dai abu daya dake damunshi yanda zaiga indo ya bata hakuri akan abunda yai mata dan akwai sanda yaje wajan mum yana bata hakuri akan ta yafe mishi tace ta yafe mai duniya da lahira, yaji dadi sosai yai shuru na wani lokaci sannan yace Mum dan Allah ina zanga aysha?mum tamke fuska tayi tare da fadin ban sani ba, kamo hannun mum yayi tare da fadin Mum plz,mum tace ni bamma gane aysha da kake nufi ba, dan shuru yayi domin yasan Mum ta gane kawai dai so take taji daka bakinshi dakyau, yace Mum matar da kika aura min, Mum tace ban san inda take ba yanzu, may be ma tayi aure jin kalman tayi aure abun ya dan taba shi domin a yanzu yana ji zai iya zama da indo ko dan faranta ma mum da kuma irin hakurin yarinyar tashi yayi ya fita jiki a sanyaye Mum ta bishi da kallo tare da fadin Ai aysha yanzu tafi karfinka kaje ka karata da matarka wacce ta waye









BAYAN SHEKARA HUDU


wata doguwar yarinya na gani a tsaye da wani akwati kusa da ita, tasa jallabiya black ta yane fuskanta da gyalen jallabiyan ga glass tasa a fuskanta kallo daya zaka mata kace balarabiya domin irin farinta da kyanta kaman nasu, doguwa ce amma ba sosai ba, ga kirjinta a cike, duk da jallabiyan da tasa bai kamata ba kana kallonta kasan tana da diri mai kyau, gani nayi anyi hugging dinta Mum ce sai yanzu na gane Ashe indo ce😱 cikin jin dadi aysha ta kara rungume Mum, Mum tace aysha barka da dawowa nan driver ya amshi kayan aysha ya tafi Dashi, Mum na rike da aysha kaman wata jaririya suka nufi mota, motoci har biyar akazo daukan aysha indo, direct gidansu Mum suka nufa dake abuja, bayan Sun karasa cikin makeken gidan su, nan sukai ciki Mum takai indo dakinta, indo taji dadi sosai domin ganin wannan ne dakinta an kayata mata shi, komai Pink, harta Cotton din da bed din, dakin yayi kyau sosai Mum fita tayi dan tabar indo ta kimtsa toilet ta fada tayi wanka, tasa wata doguwar riga mai kyan gaske, ta feshe jikinta da turare bata shafa mai ba, ta daura dankwali ta nufi falo inda abinci ke jiranta a dinning, zama tayi Mum tayi saving dinta, indo ta faracin abinci cikin natsuwa da kwarewa, Mum sai kallonta take tana mamakin irin kyan data kara da girma, har indo ta gama nan suka fara fira da Mum, suna cikin haka sai ga Abdul yazo indo ta dan bata fuska, Abdul ya gaida Mum ta amsa cikin Fara'a, sannan ya kalli indo yana murmushi tare da fadin aimin afuwa plz naso inzo in daukeki aka kirani emergency daka office, indo cikin hausanta wanda zaka tadauka tana larabci ne tace aini yaya abdul nayi fushi dakai ka barni a airport inata jira, yace sorry my sister, dan turo baki tayi irin na shagwaba wanda ita bada hakan tayi ba, dariya Suka Saki su duka harda Mum, abdul ido ya kura mata yana ta kallonta yana mamakin irin kyan data kara da girma wanda shi tun asali yana ganin kyanta, ga wani irin wayewa da tayi, gashi magana daya biyu sai tasa turanci da larabci hausan ma kaman bata wani iya sosai ba, haka sukai ta fira har abdul ya tashi yayi musu sallama indo tashi tayi tabi bayanshi domin tana son suyi magana, bayan Sun fita tace yayana wai ya maganan auren naka? Yace hmm ki bari kawai akwai dan matsala ne amma inaga komai ya kusa zuwa karshe, indo tace wani irin matsala kuma? Nan ya fara fada mata yarinyar kaman wacce take rikonta ba yarta bace so kaman bata so yarinyar tayi aure tafi son taita mata bauta, indo shuru tayi tana nazari lallai mata da yawa za suci wuta, dan tuna rayuwanta tayi a baya da yanda yanzu ta sami canji duk saboda Abdul lallai ya kamata itama ta taimaka mishi, nan dai tace bari idan ta dan kwana biyu ta huta za suyi shawara akai, motar A Majeed ne ya shigo cikin gidan, indo kallo daya tamai ta gane shi, dakanshi yake tukin, kawar da kanta tayi taci gaba dayi ma Abdul magana, A Majeed da Tun shigowanshi ya ganta gabanshi yaji ya fadi tare da fadin tsarki ya tabbata ga Allah domin bai gane indo bace dan tayi mugun canzawa, danshi a tunanin shi wata daka cikin yan uwan Mum dinshi ne, bayan yayi parking ya fito ganin yana nufo su yasa indo tayi ma Abdul sallama ta wuce, A Majeed da ido ya bita yana tunanin inda ya santa, Abdul ne ya katse mai tunani da fadin yanzu wajanka nake son zuwa, A Majeed yayi ajiyan zuciya tare da fadin ya akayi Abdul yace maganan zuwa Kaduna, A Majeed yace kai har yanzu kana nan da wannan yarinyar duk da iyayenta sunce sun mata miji, Abdul yace wlh basu mata miji ba kawai dai uwar rikonta ne keda matsala, nan suka tautauna amma gaba daya hankalin A Majeed yana ga yarinyar data shiga yanzu dan haka yace ma Abdul su shirya suje Friday sannan ya shige ciki, koda ya shiga Mum kawai ya gani a falo, bayan sun gaisa ya dan sosa kai tare da fadin Mum kinyi bakuwa ne? Mum tace wace bakuwa kuma? Dan shuru yayi can yace wacce ta Shigo yanzu kaman yar kasar ku ce dai, Mum tayi murmushi tare da fadin au kodai aysha kake nufi, cikin razana ya furta aysha tabbas itace dan yanda yake tunanin a ina ya santa sai yanzu yaga kamannin sak.....










Taku Maryam obam


*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









110to115







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*











A Majeed gaba daya ya shiga cikin rudani tare dayin daya sani, tunawa yayi da Mum ta taba gaya mishi hala ma tayi aure, hada hannunshi yayi ya buga da karfi, Mum ta kalleshi tace lfya kuwa, idonshi lokaci daya ya kada yayi ja wani irin zafi yake ji kirjinshi nayi, Mum ganin halin daya shiga yasa ta tashi da sauri ta nufo shi tana fadin maike damunka? Dakyar ya furta babu komai Mum kawai kirjina ke ciwo, tashi yayi ya fita Mum ta bishi da kallo yana fita abdul ya kira yace Abdul kana ina ne? Abdul yace ina Gida, kashe wayan yayi ya shiga motarshi ya nufi gidan abdul, bayan Mai gadi ya bude mai gate yayi parking, kai tsaye falon gidan ya shiga abdul na falo yana cin abinci cikin take away, A Majeed zama yayi akan kujera tare da lumshe ido abdul da ido ya bishi bai dai ce mishi komai ba, A Majeed yayi wajan minti biyar kafin yace abdul aysha tayi aure ne? Abdul yace wace aysha kuma? A Majeed yace matata mana, abdul yace toh kai ina ruwanka da ko tayi aure koh batayi ba, A Majeed yace plz ka bani amsan tambaya na kawai, dakyar Abdul ya fada mai cewa batai aure ba, A Majeed wani irin ajiyan zuciya yayi cikin jin dadi domin yasan komai zai zo mishi da sauki tunda batai aure ba, abdul ne ya katseshi da fadin A Majeed mai yasa amma kake son sanin hakan, dan murmushi yayi tare da fadin saboda ina son in dawo da matata mana, abdul yace amma dai wasa kakeyi koh? A Majeed yace wasa fah kace, toh inma wasa kake gani toh ka daina dauka hakan, abdul yace inda zan baka shawara kar kayi gigin furta wannan maganan domin aysha ba ajinka bace ko ka Manta ne, itafa yar aikin matarka ce, ganin abdul na son bata mai rai yasa yabar gidan cikin fushi, Abdul ya girgiza kai tare da fadin Allah ya ganar dakai abokina.











Indo suna falo suna breakfast harda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login