Showing 18001 words to 21000 words out of 85238 words
Chapter 7 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
da murmushi, indo cikin dashewan murya tace mata ina wuni? Matar ta amsa da lafiya yata, ya naganki haka fuska babu kwalliya maza shiga toilet kiyi wanka kinji, indo ta fara zare ido To inane cholit kuma, kaman daka sama taji matar tace zo ki gani, nan ta bude wata kofa a cikin dakin indo baya tayi da sauri dan tsoro toilet ne, nan matar tayi dariya dan Mum ta bata labarin indo bata san komai ba Tana son ta koya mata, tace yata zo ki gani kinji? Indo girgiza kai tayi alaman a'a, ganin haka matar ta kamo hannunta tace shigo kiga yanda ake amfani Dashi, ihu indo tasa tana fadin dan Allah karki shigar dani, amma bata saurare ta ba, har saida ta shigar da ita, sannan tace ma indo ki nutsu yata babu wani abu, nan ne bayi, indo ta danyi shuru amma tana hawaye, nan ta nunama indo yanda ake amfani da komai na bayin sannan ta fita tace tayi wankan, indo sharp2 tayi domin har yanzu a tsorace take, matar tace badai har kinyi wankan ba, tace eh nayi, nan taba indo wata doguwan riga tace tasa, rigan yayi ma indo yawa kadan bayan tasa, tace suje falo Tela zai gwada ta, Tela ya gwada indo sannan matar tace sunanta Maryam indo hawaye ya fara zuba a idonta jin sunanta daya da mamanta,matar tace lafiya aysha? Indo tace naji sunanki daya da inna ta, matar tayi dan murmushi tare da fadin To saiki dinga cemin Mama koh?indo ta daga kai alaman eh cikin jin dadi,tun daka wannan lokaci indo take kiranta da mama.
Kaman yanda A Majeed yace hakan ko yayi ya sami mahaifinshi akan a rabashi da matar da Mum dinshi ta bashi, Dad dinshi ya nuna shima bai yarda ba tare daja mishi kunne akan karya fara cewa zai saketa domin bazai zubar mishi da mutunci ba, A majeed haka ya koma gida cikin takaici, washe gari da sassafe ya nufi gidan nasu domin yayi ma mum sallama akan zai wuce, lokacin Mum na kitchen domin indai his excellency na gari ita take mishi abinci da kanta, gaida Mum yayi ta amsa babu yabo babu fallasa, yace Mum zan wuce ne gobe akwai Office, Mum ta danyi shuru can tace ok amma da matarka Zaka tafi dam gabanshi ya fadi........
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
80to85
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*DADIQA ISAH*😍
Domin baiyi zaton mum zata mishi maganan tafiya da wacce ake kira da matarshi ba, yace mum bada ita zani ba, Mum tace wannan kuma bazai taba faruwa ba dole ka tafi tare da matarka, dan shuru yayi na wani lokaci kafin yace Mum ita a nan zan barta ta dinga zama sai in dinga zuwa, Mum tace sam hakan bazai taba yihuwa ba, ganin Mum ta dage kuma taki bashi fuska yasa yace shikenan mum, amma da an barta Friday zan zo sai mu koma tare kafin nan nasa an gyara inda zata zauna, Mum shuru ta danyi tana nazari kafin tace shikenan hakan yayi, Allah ya kiyaye hanya, ya amsa da ameen, sannan Mum tace ka dai sallameta koh, dan naga kaman da shiri ka fito, yace eh Mum munyi sallama da ita, Mum taji dadi sosai har tana ce mishi ya tsaya yayi breakfast, yace No mum ina so in kai da wuri tace ok tare da bashi dambun nama da drink, fita yayi driver ya ja, suka daga abuja, A Majeed rabonshi da ganin indo tunda Mum tazo jiya kenan bai kara ganinta ba, amma yace ma Mum sunyi sallama.
Indo ita da Maryam wacce take kira da Mama yanzu suna zaune a falo, Mama tana koya mata yanda ake canza channel indo an rike remote ana dannawa, idan ta canza channel daya sai tayi dariya irin ta canza dinnan, Mama babu abunda take sai dariya tare da mamakin irin kauyancin indo, haka indo taita canza channel Tana dariya, Mama ganin abun bamai karewa bane, yasa tace tazo su zaga gidan taga ko ina, tashi indo tayi ta bita suna shiga ko wani lungu da sako, gidan kato ne sosai domin falo uku ne a cikin gidan akwai guda biyu a kasa sai daya a sama, daki uku a kasa, biyu a sama da falo babba, indo dai baki da ido ta bude tana kallo, Mama Tana ta mata bayani,har suka zo kitchen dake kasa, indo tace Mama ni kam tsoran nan nakeji wlh, Mama tayi dariya tare da fadin ki daina jin tsoro aysha, nan kitchen ne, indo kasa fadan kitchen tayi dan haka tace mai kenan? Mama tace wajan yin girki, indo ta zaro ido cike da mamaki, nan ne wajan yin girki tabdi, to ya banga murhu ko dutse ba ko akan me akeyi oho, mama ce ta katse mata tunani tare da fadin matso ki gani, nan indo ta matsa Mama ta kunna Gas sai ga wuta ya kawo indo da gudu tabar kitchen din tana fadin mun shiga uku,mama da sauri ta fito tana dariya tare da cewa indo tazo su koma ciki, indo taki yarda sai fadi take wutan ya mutu? Mama tana ta dariya babu yanda batai da indo ba akan su koma kitchen din amma taki yarda su koma, domin abun ya bata tsoro.
Mama tana taimaka ma indo sosai musamman wajan yin tsaftan jiki, domin a rana sau biyu take sata yin wanka, wanda ada sai tayi wata batai wanka ba, suna zaune a falo suna hira, Mama tace wai ni kam aysha kullum kanki a rufe,bude mu gani, indo ba tare da damuwa ba ta cire dankwalin kanta, nan Mama tasa salati ganin kan a dangare ga wari na tashi, tace aysha haka kanki yake, Indo dai bata ce komai ba, mama waya ta dauka ta kira Mum, bayan Mum ta dauka Sun gaisa take cema Mum ya kamata aysha taje Saloon, Mum tace ku shirya zansa driver yazo ya daukoku sai a mata a nan, Mama tace toh ranki ya dade, nan Mama tasa indo ta kara yin wanka, tare da fito mata da wani riga da skirt tace tasa, indo ta fito wanka tasa Mama ta bata powder ta shafa, babu laifi ta danyi Kyau, Mama ta bata gyale ta yafa, basu dade ba driver yazo ya daukesu akai gidan mum dasu, indo anata kalle2 har Suka shiga ciki, a makeken falon gidan suka zauna, basu dade da zama ba aka cika musu gaba da kayan motsa baki, Mum ce ta fito cikin shiga ta alfarma fuskanta dauke da Fara'a, tace sannu Maryam, maryam tayi murmushi tare da fadin yauwa ranki ya dade nan ta gaida Mum, itama indo ta gaida Mum, cikin Fara'a Mum tace aysha zo mana tare da miko mata hannu, alaman tazo inda take, tashi indo tayi ta nufi inda Mum take, nan Mum ta fara tambayanta ya kwanan bakwanci? Indo kunyan Mum takeji bata amsa ba sai murmushi, mum daukan wayanta tayi tasa a kunne tare da fadin kizo ciki, bata dade da ajiyewa ba, wata mata tazo cikin riga da skirt baki da baby hijab fari, tace yauwa hafsat ga Aysha nan ki gyara mata kai da gyaran jiki, hafsat ta amsa da ok ma, Mum ta kalli indo tare da fadin aysha tashi kuje, indo tashi tayi tabi bayan hafsat din, bayan sun fita Mum ta kalli, Maryam tace mai kika fahimta a gidan? Maryam tace ranki ya dade tunda naje gidan ban kara ganin shiba, haka kuma ban ganshi wajanta ba, mum tace ya wuce abuja, amma ai yazo sunyi sallama koh? Tace a'a bata ganshi wajanta ba sai dai in a waya ya mata, Mum shuru tayi amma Kana ganin fuskanta kasan ranta a bace yake, can tace ma Maryam inaga zaki koma ki dibo ma aysha kaya da dai abunda zata bukata sai ta zauna a nan kafin ya dawo dan tare nake so su tafi, maryam tace ranki ya dade inda zaki dauki shawara na aida an barta a nan sai a sata makaranta in yaso sai ya dinga zuwa, domin naga aysha bata san komai ba,nan taba Mum labarin abunda indo tai tayi Mum dariya tayi sosai sannan tace hakane gskya tana da bukatan tasan wani abu, bari zansa a duba mata makaranta duk da tayi girma ,maryam tace gskya hakan ya kamata nan sukai ta tattaunawa.
An wanke ma indo kai, gashinta har gadon baya kun san Fulani ba baya ba wajan gashi, gashi an Mata gyaran jiki tayi kyau fuskan ta tayi dan haske kadan, ita kanta hafsat din tayi mamakin gashin indo, nan tace ma indo suje ciki, bayan sun shiga wajan Mum, Maryam tace kai Masha Allah, mum tace kai aysha kinyi kyau sosai, Maryam tace muga gashin indo ta cire dankwalin, maryam ta saki baki domin ganin yawan gashin, Mum tace Masha Allah sai kace balarabiya wajan gashi su Maryam sukai dariya, nan Mum tace ma hafsat yanzu gyaran jikin zuwa nan da yaushe za'a daina? Hafsat tace za'a mata kaman na sati biyu, dan naga fara ce sosai idan aka mata farinta zai fito sosai, nan Mum tace ok, tun daka wannan ranan indo ta dawo zama gidan mum ga tela ya kawo mata wasu kayanta dinkin dai2 jikinta Mum tasa ana koya mata abubuwa da dama irin su girki da makeup, ranan da indo zata fara shiga kitchen anyi drama har sai da Mum tazo kafin ta shiga.
A Majeed tunda ya tafi sati biyu kenan bai zoba, Mum Tana zaune a falo, ita da indo tana fada mata zata fara zuwa islamiya gobe, indo taji dadi dan tana son karatu kuma ko ba komai tasan addininta, wayan mum ce tayi ringing ta dauka ganin bakuwan No kuma na waje yasa tayi mamaki ko waye kuma bana kasar su bace Egypt, dauka tayi muryan A Majeed ne yace Mum barka da warhaka, tashi tayi daka falon ta nufi Daki,tace lallai A Majeed ka kyauta kana ina yanzu? Yace Mum ina London Zainab na raka wani meeting da za suyi, ran Mum ya baci sosai tace wlh na baka nan da jibi ka dawo gida kuma direct jalingo zaka tawo, tana fadin haka ta kashe wayan tare da takaicin abunda dan nata yayi, tana ta kiranshi No dinshi a kashe Ashe ya tafi London da matarshi, lallai saina saba ma A majeed sosai.
Indo an fara zuwa islamiya tana karatu, sannan Mum tasa wani Mlm na koya mata a Gida but islamiya da boko, yau indo da ciwon ciki ta tashi da alama period za tayi, a daki ta wuni Mum jin shuru yasa ta nufi dakin indo din, ta ganta a kwance tana juye2, nan Mum ta karasa da sauri tana tambaya aysha lfya kuwa? Indo ciki ta nuna mata alaman yana mata ciwo, nan ta kira dr ya fara dubata, ya bata Magani tare da cema Mum period ne za tayi, Mum tayi mishi godiya tare da sallaman shi, Mum tasa aka hada ma indo Tea ta tasar da ita tana bata indo tasha sannan ta bata Magani tasha, taba indo pad tasa, Mum ita ta fadama indo yanda za tayi amfani Dashi duk da indo tana jin kunya amma Mum ko a jikinta, bayan indo tasa pad din ta kwanta bacci ya dauketa.
*Kuyi manage da wannan zuwa gobe muga dawowan A Majeed yanda zai kwashe da mum*
*plz ku dinga sharhi akai domin yana da amfani*
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
85to90
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*SAD'ASH*
*1 DIN BA 2 DIN BA😝*
Indo sai wajan 4 ta farka babu laifi ta danji dama2, Mum ta shigo dakin ta ganta a zaune tace sannu aysha, ya cikin ya daina koh? Tace eh da sauki, mum wayanta ta danna tare da sawa a kunne tace ki kawo Min paper soup din chicken da abu mara nauyi, ina sama, tana fadin haka ta kashe wayan, ba'a dade ba sai gashi an kawo chicken soup din da snack, a tray Mum tace haba ba snack zaki kawo ba mara lfya zata ci, abinci nake So, ki bata ko dankali ne, tace ok ma, ta ajiye ma indo chicken din,har matar zata fita Mum tace ta tsaya tare da kallon indo ko a Kawo miki tea ne? Indo tace eh, Mum tace ta kawo snack din sannan ta hado Tea din, ta amsa da ok ma sannan ta fita bata dade ba sai gata da Tea din, Indo taci ta koshi harda ragewa, haka Mum taita kula da indo ranan bata je islamiya ba, sai dai da lesson teacher dinta yazo ta fita duk da mum tace ta zauna tace ta warke.
Mum na zaune a falo sai ga A Majeed ya shigo, zama yayi a inda take ganin ta daure fuska babu alaman wasa yasa ya shiga tai tayinsa, gaidata yayi bata Amsa ba sannan bata kalleshi ba,yace Mum plz am so sorry nasan nayi kuskure amma dan Allah kiyi hakuri fushin ki Bala'i ne a kaina, jin haka yasa jikin Mum yayi sanyi, tace kasan da haka kake kin bin umarni na, kake yin abunda ya maka dai2? Yace Mum kimin afuwa dan Allah, kun san d'a da uwa,tace shikenan naji zan hakura amma sai kabi abunda na tsara ma,yace insha Allah my Mum tare da kara matsawa kusa da ita, tace A Majeed akan matarka aysha yarinyar alkhairi ce a gareka amma ba zaka gane ba sai nan gaba domin yanzu giyar son matarka na kanka baka gane tayi dai2 da ba dai2 ba, komai tayi a wajanka dai2 ne, nasha fada maka wlh ina son matarka har cikin raina, sai dai halayenta da bana so, yau shekaran ku nawa da aure amma har yanzu ban taba ji kace tayi batan wata ba, duk da haiyuwa na Allah ne, amma kwata2 matarka inaga bata da burin haiyuwa yanzu, bani da yawan dangi ko yara amma ina son inga jikoki na, bawai na maka auren nan dan in kuntata maka bane a'a kawai dai dan na lura Kana da bukatan hakan ne, A Majeed ya rike hannun mum dinshi yana dan murmushi yace Mum ngd amma dan Allah kiban umarni in saki yarinyar nan in yaso sai in auri wata...... Mum tace ya isa haka ta dakatar dashi, dan shuru tayi tama rasa abun cewa Can tace A Majeed miye illan wannan yarinyar toh da baka sonta? gyara zama yayi dakyau sannan yace mum akwai abubuwa da yawa, kinga ni mutum ne Mai san Mace yar gayu kyakyawa wacce ta waye, mai ilimi sosai wannan yarinyar yar kauye ce bata da ilimi da wayewa gata karama wlh Mum abun kunya ne a gareni ace wannan yar kauyen mata tace, nayi miki alkawarin zan auri mata har uku in kina bukata amma ki barni in rabu da wannan plz mum, Mum ajiyan zuciya tayi tare da fadin shikenan naji duk matsalanka, amma ka bani lokaci kadan zan bukaci ka rabu da ita da kaina, cikin jin dadi yace thank My Mum tare da rungumeta, Mum murmushin takaici kawai takeyi wato shi Mace yar gayu wayayya yake So bayan ga daya nan a gidan shi yana shan wuyanta amma bai daddara ba, shi babu ruwan shi da tarbiya sai wayewa lallai A Majeed yayi nisa,katseta yayi da fadin Mum yunwa nake ji sosai wlh, tace ga abinci can a kan dinning, tashi yayi ya nufi dinning din, indo da tazo zata sauko falo taji suna magana jin zai nufo wajan tabar gun da gudu tana hawaye, daki ta shiga tana kuka, tabbas gaskiyan shine, ita ba ajin shi bace, taya za'a hada mai tallah da dan gwamna aure ai wannan abun ma kowa yaji yasan bamai yuhuwa bane, tabbas dan mai kudi sai yar mai kudi, yar tallah sai dan talaka dan uwanta wani hayewa ne ya zubo mata, tare da fadin dama dan jummai ta aura da yafi mata kwanciyan hankali duk da tasan auren nashi ba hutu bane domin badan Allah zai aureta ba, amma shine dai2 da ita duk da har gobe sulaiman ne a ranta amma shima tasan yafi karfinta, haka taita tunani tana kuka.
Koda A Majeed yayi ma Mum sallama akan zashi gidan shi bata hana shi ba, sai cemai tayi sai da safe, ya fita cikin jin dadi domin ya kusa rabuwa da matar da aka jajibo mai, Mum tashi tayi ta nufi dakin indo, jin karan bude kofa yasa indo ta kwanta kaman tana bacci, Mum ganinta tayi a kwance ta kura ma fuskan indo ido, bata ga munin yarinyar ba, domin kuwa indo tafi Zainab dinshi kyau nesa ba kusa ba, domin indo ita bata makeup din da matarshi takeyi inda itama za tayi da sai an dauki indo da gudu Kafin matar tashi da yake ji da ita, mum bayan ta gama tunaninta ta fita daka dakin cikin tausayin indo , jin ta fita yasa indo ta bude ido tare da ci gaba da kukanta.
Abu bayan an tafi an barta taita kuka, Yan uwan sulaiman suka shigo dakin suka ganta tana aikin kuka, kanwar sulaiman saudat wacce Sa'ar Abu dince kuma kawarta ce