Advertisement
Showing 84001 words to 85238 words out of 85238 words

Chapter 29 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

58

takeyi ga azaban da takeji tace wlh ban zubar ba banyi komai akan cikin nan ba fita yayi fuuuuu yaranshi ya kwasa dake waje sukai mota ya fita fuuuu daka gidan Zainab kam murna ya kamata tare da fadin Alhmdlh, indo dakyar ta tashi tayi toilet ta gyara jikinta tasa pad tare da daukan wasu kaya dasu ATM dinta da kudaden dake wajanta duk wasu abu mai amfani ta dauka dakyar take jan akwatin ta fita daka gidan Zainab na kallonta ta window tana ta tsallan murna burinta ya cika yau, shiko koda ya fita yama rasa inda zashi kai yaran yayi wajan snack yasai musu sannan ya dawo Gida ranshi a jagule koda ya shiga gidan bai ganta ba dakin yaran ya kaisu yasa musu kayan bacci yace su kwanta, dakinshi ya shiga ya kwanta tare dajin zafin abunda aysha tayi mai yasa mai yasa aysha mai yasa kika zubar min da jini na Aysha mai yasa kika tsaneni har haka laifin da na miki shine har yanzu kika kasa yafe min aysha mai jini na ya miki kika zubar min Dashi bayan ni zaki hukunta bashi ba kuka yake sosai tare da takaici ranan ko bacci ya kasa sai tunani duk da yana so ya cire ma kanshi tunanin ina ta nufa yanzu amma ya kasa, ita ko indo koda ta fita hotel ta kama washe Gari da safe ta shiga motar taraba ta nufi garinsu wanda har an gama gyaran gidan sai wajan karfe 4 takai nan mlm musa yayi murna da ganinta yace aysha ina yaran damai gidan? Nan tasa mishi kuka cikin damuwa yace aysha lafiya kuwa nan ta fada mishi abunda ya faru tare da rantsewa akan bata zubar da cikin ba, yace kai abu baiyi dadi ba amma kiyi hakuri muga zuwa nan da kwana biyu zan nemeshi dan nasan yanzu yana fushi kiyi hakuri insha Allah zai fahimta kema aysha dole ya zargeki ai tunda kin nuna bakya son cikin amma kiyi hakuri komai zai wuce tace toh Baba, ginin gidan anyi 2bed room sai daki daya a waje da toilet nan indo tace zata dinga kwana akwai gado a dakin gidan yayi kyau sosai inna jamila kullum Tana gidan dan mijinta ya dade da rasuwa kullum Tana kwantar ma indo hankali tare da bata baki Mlm musa ya amshi number din A Majeed ya jishi a kashe wasa2 yau satin Indo biyu wayan A Majeed kuma a kashe, indo ta rame ga kewan yaranta da take yi, indo kullum Tana jin wasu abubuwa a jikinta ta fadama inna jamila tace suje asibiti hala cikin bai zube ba dan yana haka aiko indo ta shirya suna zuwa asibiti aka duba ta tare dayin scan nan aka gano cikin na nan bai zube ba amma sun bata bedrest dan Tana bukatar hutu saida tayi sati biyu aka sallameta tare da bata Magani jikinta yanzu ya mata karfi ta dai rame ta kara haske dadinta daya da cikin bai zube ba, Abu daya ke damunta yanda yaki bata uzuri yaki sauraranta gashi yanzu ya shareta wayanshi a kashe wani hawaye taji yana zubar mata dama ba sonta yake ba, sallaman Mlm Musa ne yasa ta fito ganin wanda suke tare yasa ta koma daki da sauri Tana kuka yaranta ne suka shigo dakin suna fadin Mummy suna tsalle najin dadi, jim kamshin turaranshi yasa ta gane ya shigo dakin rikota yayi ta baya yana fadin am so sorry nayi kuskurem da ban saurareki ba duk da a lokacin kona saurareki bazan yarda dake ba dan abunda naji nan ya bata labari tare da fadin yanzu ma Zainab Tana gidansu na saketa Saki daya cikin kuka tace mai yasa yace saboda na gano itace ta baki drink kika sha tasa miki Magani Da sauri tace taya ka sani yace naji Tana fadama kawarta ne, indo tace wlh ranan taban kunun aya nasha yace naji komai kiyi hakuri ki yafe min tace naji amma saika yarda zaka dawo da Zainab zan hakura bata fuska yayi tare da fadin plz kar kisa nayi abunda banyi niya ba, tace plz My One Zainab na sonka kuma san naka yasa tayi duk abunda tayi dakyar tayi convincing nashi yace zai dawo da ita din mlm musa ya kara musu nasiha inda indo tace Baba ina neman alfarma yace name fah tace Baba zamanka babu mata hakan yana sani cikin damuwa babu mai kula da Gidan da gyarawa yace hakane aysha nida na tsufa ina ni ina aure tace Baba dan Allah ka auri inna jamila dariya yayi na manya yace toh saiki mata magana inta amince indo tashi tayi ta nufi gidan jamila duk da A Majeed bai so ta fita ba ta mata bayani dakyar inna jamila ta yarda wai ita ta wuce aure a ranan mai gari ya daura aure A Majeed yaba mlm musa kudi masu yawa wai ya fara Sana'a dasu a kalla yakai million biyar itama inna jamila ya bata kyautan kudin, a ranan ya dauki matarshi suka koma Abuja kwanansu biyu tasa yaje ya dawo da Zainab wacce a yanzu tayi dana sani kuma ta gane duk wani abu da zata kulla ko tayi bazata canza yanda Allah ya tsara ba gashi duk kudin nata da mulkin babanta gashi Tana zaune da kishiya wacce take ganin tafi karfinta gashi duk kudinta da mulkinsu bazai bata yara ba ko soyayyan miji wanda tasan yanzu baya sonta kawai dai yana zama da ita ne sai yanzu tasan kudi da mulki bashi bane komai mutunci yafi kudi tunda kudin nata bai tsinana mata komai ba saima tozarci.











Bayan shekara uku indo yanzu yaranta 7 zarah arfan irfan, sai kuma ta kara yan uku duka maza adnan farhan anan, sai Mace daya yar auta yusra yanzu zarah ta koma wajan Zainab wacce yanzu ta dauki indo matsayin kanwa kuwa abokiyar shawara indo tayi suna sosai ta kware wajan aikinta Tana daya daka cikin doctors din da ake alfahari dasu a Nigeria, Zainab da indo kuma sun hada kasuwanci sunayi tare, Abu itama tayi aure ta auri yazeed itama yanzu an waye kuma ta shiga makarantar never give up harta gama ita yaronta daya aka samai musa sunan babanta suna kiranshi da aryan, matar Abdul ma yaranta biyu sunyi ma indo takwara aysha sai muhd,sulaiman ma A Majeed ya samar mishi aiki, yusuf shima yanzu ya kara kudi ba kaman da ba, A Majeed ya Kara samun kwanciyan hankali ga kudi sosai da yake samu yanzu dan yanzu yabar aiki ya koma kasuwanci kudi kota ina suna shigo Mai ga kwangilan da mahaifinshi ke bashi da wasu ma, ya gina musu wni mahaukacin Gida babba gefen yara daban ga wajan kayan wasan su nan kala2, indo ce zaune ita da A Majeed tace nikam ina son zuwa Egypt inga ummi da abba yace gskya ya kamata kam nan aka musu visa harda Mum da yara duka da Zainab suka wuce Egypt sunyi yawo sosai indo har gidan kawarta fatima taje sukai zumunci sati biyu sukayi suka dawo indo taji dadin ganin ummi da da abba duk da sun kara tsufa sosai, haka a taraba mlm musa da jameela suna zaman lfya suna cin mai kyau su sha mai kyau dama ance *TAMBARIN TALAKA* cikin sa, sai yanzu yasan yayi aure, rayuwan indo da mjinta sai dai muce Alhmdlh nima dai a nan zance ALHAMDULILLAH.





Sai mun hadu a next novels very soon

Taku Maryam obam😘

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login