Advertisement
Showing 6001 words to 9000 words out of 85238 words

Chapter 3 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

40

bayan mayyar can yace yana so, Abu tace wlh Tani bazan yarda ba nifa shi zan Aura Kin ganshi ne dan gayu, gashi sai kamshi yake yi, ga mota, ni wlh Tani kisan yanda za kiyi in aureshi, Tani tace toh naji Abu na kwantar da hankalinki kaman kin aureshi kin gama, Abu ta wangale baki tana murna, indo na daki Tana kuka gwanin tausayi lokaci daya zazzabi ya kuma rufeta, babu abunda take tunani sai dan uwanta yusuf shine kawai yake sonta ta tabbata inda yana nan da yanzu yana ta rarrashinta yana bata hakuri, yanzu ko ina ina oho, yana da rai ya mutu duk bata sani ba, kuka ta kuma Saki mai ban tausayi,ta dauki lokaci tana kuka har dare ya tsala sosai bacci da yake barawo ne yai awon gaba da ita.










Tunda asuba ta farka, duk da jikinta baya mata dadi haka ta fito ta share gida sannan ta dauki roba domin dibo Ruwa, gidan kusa da gidansu basa nan, dan haka ta nufi rafi, ta dibo ruwan tana kokarin daurawa a kanta, taji an rike mata kugu, da sauri ta waiga taga dan jummai ne saurayin Abu, tayi saurin matsawa da baya tare da sakin ruwan ya zube, dariya yayi yace haba yan mata miye abun jin tsoran nifa taimakonki zanyi, indo ta dauki bokintin da nufin ta wuce ya janyota ta fara ihu, ya fara dariya tare da fadin ihunki banza domin babu mai jinki, dan babu kowa a nan kinga gwara ki yarda kiban hadin kai, nifa taimaka miki zanyi, kuka ta fara tana rokanshi akan yayi hakuri ya barta amma ina bai masan Tana yiba, da yaga tana mai ihu yasa ya toshe mata baki da dayan hannunsa, tare da kokarin cire mata riga, tana ta kokarin tureshi amma ta kasa, riganta ya farka nan kirjinta da suke tsaye kyam Suka bayyana nan dan jummai idonshi ya kada tare da kara rudewa, kokarin kai hannu yayi yaji anyi jifa dashi ta gefe, nan aka fara dukanshi ganin dukan bana wasa bane kuma ya gane yaron mai gari ne yasa ya gudu, indo rufe jikinta tayi da dan kwalin kanta tana kuka, sulaiman ganin yanda tayi yasa ya cire Rigan shi ya bata ya koma daka shi sai singlet, mika mata yayi yace gashi kisa, da sauri ta amsa ya juya baya ta saka, yace ta tashi ya rakata gida, bata tashi ba kuma bata mishi magana ba, sai kuka da takeyi, sulaiman jin kukan yake har ranshi domin tunda ya ganta yaji yana sonta, zama yayi kusa da ita yace esha dan Allah kiyi hakuri kibar wannan kukan kizo muje in raka ki gida, kai ta girgiza alaman a'a, yace saboda me, dakyar ta iya furta za'a bigeni, yace kaman ya? Cikin kuka tace dan Allah kayi hakuri karka kara kulani domin inna tace duk sanda na kara kulaka saita kashe ni, daukan bokitin tayi ta diba ruwan, har tayi gaba ta tsaya tace zan aiko maga da riganka nagode, Sulaiman kasa cewa komai yayi domin gaba daya abun ya daure mishi kai, wai wacece Indo? Koma dai wacece ina sonta kuma bana tunanin zan iya rabuwa da ita, tashi yayi domin ya nufi gida dama ya fito gudu ne,ya biyo ta rafi shine yaga wannan aika aikan, koda indo ta nufi gida bata ga kowa ba, hakan ya mata dadi ta nufi daki ta cire rigan Sulaiman da yake ta kamshi mai dadi ta dauko wata kodaddar rigan atamfanta tasa, sannan ta boye nashi rigan, yanzu gari yayi haske makotansu sun bude kofa dan haka nan taje ta dibo ruwan ta cika ko ina, sannan ta hada murhu tasa ruwan kunu, kaman dai kullum, yau da wuri ta hada wainar rogo, gashi Tani ta hanata abinci haka ta fita tallah, tare da rigan Sulaiman inta ganshi ta bashi, amma har takai tasha bata ganshi ba, tana ta yawo wajan motoci tana fadin asai wainar rogo, babu laifi an dan siya, kadan ya rage, har takai yamma sauran bai Kare ba, dan haka ta nufi hanyar gida ga yunwa tana ji, muryan sulaiman taji yana fadin esha, kaman karta tsaya sai dai dole ta tsaya kodan ta bashi rigan shi, tsayawa tayi ya karaso inda take, mika mishi rigan tayi tare da fadin kayi hakuri ban wanke maka ba dan kar inna ta gani, kallonta yake yi yana murmushi, yace Ai yanzu ba nawa bane naki ne rigan, kai ta girgiza alaman a'a ni bana so, yace toh nima dai bazan amsa ba, ajiye mai tayi a qasa tayi gaba binta yayi yana fadin ta tsaya suyi magana, ganin bata da niyan tsayawa yace shikenan anjima zanzo gidan naku, cak ta tsaya tana hawaye tare da rokanshi akan karya zo, ganin tana hawaye yasa ta bashi tausayi yace toh shikenan indai bakya so inzo to kizo mu zauna a can muyi magana, bata musa mishi ba ta bishi, a dan wani dakali Suka zauna, yace esha ina son ki fadamin ke wacece, nan indo ta fad'a mishi tare da fadin dan Allah tunda kaji koni wacece dan Allah ka rabu Dani, Sulaiman idonshi ne ya kada yayi jaa, tabbas ya tausaya mata, ita indo tana ganin idan yasan ko ita wacece zai rabu da ita, amma sai taji sabanin hakan, yace esha tunda nake ban taba ganin macen da naji inaso ba sai ke, labarinki da kika bani yasa na kara sonki sosai, esha inaso kimin alkawari komai zai faru baza ki gujeni ba, har ranan da za muyi aure, tabbas an zalinceki keda dan uwanki, ni na yarda dake bazaki aikata wani abu mara kyau ba, zan tayaki neman dan uwanki har Allah yasa a dace, nidai so nike kimin alkawarin zaki yarda ki aureni sannan ba zaki taba gudu naba komai zai faru, indo shuru tayi domin tabbas karyane tace bata son sulaiman duk da shi din ba Sa'an auranta bane, kaman yasan abunda take tunani yace shi so babu ruwanshi da kudi ko mikami, dan Allah ki amince dani, rufe fuska tayi tare da fadin nima ina sonka amma bazan taba aurenka ba, cikin tashin hankali yace saboda me? Tace Inna ba zata bari inyi aure ba., sulaiman yace karki damu zan ma mahaifina magana duk yanda mukayi zan fada miki, murmushi tayi tare da fadin to ni zan tafi kar ace na dade, yace toh yanzu sai yaushe kuma ko inzo gida anjima zare ido tayi, ganin haka ya fara dariya tare da fadin wasa nake miki amma lokacin da zan fara zuwa ya kusa kinji My esha, bata ce komai ba sai murmushi kawai yace gobe in kin fito diban ruwa sai mu hadu, rufe fuska tayi ta ruga da gudu dan ta tuno abunda dan jummai ya mata......











Yawan comment yawan posting












Taku Maryam obam😘

💅 TAMBARIN TALAKA 💅






NA


MARYAM ALHASSAN DAN'IYA




🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝






Vote me on wattpat @maryam-obam


WWW.maryamobamnovels.com









35to40







DEDICATED DIS PAGE TO...

Maryam Obam novel grp😘

Ina yinku irin sosai din nan One luv❤










Murmushi sulaiman yayi, tare da girgiza kai, yana mamakin son da yake ma yarinyar Lokaci daya, koda indo ta shiga gida, Tani da Abu suna tsakar gida akan tabarma suna cin tuwo, sallama tayi babu wanda ya amsa mata, dan haka ta nufi inda tani take tace inna gash..... Tani tace yanzu sauran da kika dawo dashi ubanki ne zai siye yar iska, indo tace inna wlh ina ta yawo dashi amma yaki karewa naga yamma tayi shine na dawo gida, Tani tace maza ki dauka ki fitar min Dashi wlh kar inga ko daya a roban nan, indo dauka tayi ta fita waje tama rasa ina zata dashi, can tace bari taje gaban layin su domin Akwai inda maza ke taruwa suna fira, nan ta nufa ta zauna a gefe da wainar rogon, harta gama zamanta ta gaji babu wanda ya siya, ganin dare nayi yanzu wajan takwas da wani abu, da sauri ta tashi domin ta tuna tana da canjin da suilaiman yabar mata, gida ta nufa tana dan sand'a Allah yasa babu kowa, dakinta ta shiga ta juye wainar rogon duka na saba'in ne, ta kirga kudin ta fito,dakin Tani ta nufa inda ta gansu ita da mlm musa suna yar fira, kanta a 'Kasa tace inna ga kudin, amsa Tani tayi ta kirga taga sun cika dai2 dauko sauran tuwan da suka rage tace gashi, amsa tayi tare da fadin ngd, sannan ta fita, ruwa ta diba a kofi ta nufi dakinta, wainar rogon ta cinye sannan ta hada da tuwan, ranan saboda koshi cikinta kaman zai fashe, haka ta kwanta cikin jin dadi.










A Majeed ne kwance a bedroom dinshi, ya lullube da blanket, sai rawan sanyi yakeyi, ga wayanshi na ringing amma babu daman dauka, dan bazai iya tashi ba, yau kwana biyu yana daki bashi da lafiya, ga Abdul yana Kaduna daya tabbata da yazo ya duba shi, bude kofar akayi aka shigo d'akin, Mum dinshi ce cikin sauri ta karaso kusa dashi tana fadin son maiya sameka, tabashi tayi taji jikinshi zafi radau, cikin tashin hankali ta kira security din gidan tace suzo su sashi a mota, bayan an sashi a mota direct hspt Suka nufa, nan aka amsheshi aka fara duba shi, Dr yayi wajan 30mnt Kafin ya fito, ya kalli Mum wacce kana ganin A Majeed kasan danta ne, domin suna mugun kama, da turanci ya mata magana dan baya zaton ma tana jin hausa, yace suje office, bayan Sun shiga Dr ya fara mata bayani kaman haka..... Hjy wannan yaronki ne koh? Mum tace eh yaro nane, Dr mai yake damunshi? Dr yace sperm ne ya tarun mishi a mara,yana da karfin Sha'awa sosai, shine ya haifar mishi da zazzabi, hjy inaga dai matsalan yaran ki shine ku mishi aure gskya, Mum shuru tayi amma ranta yayi mugun baci dan me wlh ba zata sabu ba, bazata bari a kashe mata gudan dan nata bat, dole ma ya kara aure, miye amfanin auren nashi matarshi kwata2 bata da lokacinshi, dr ne ya katseta da fadin anyi mishi alluran bacci nan da 1hr zai tashi, mum tayi mishi godiya sannan ta nufi dakin da dan nata yake, yana kwance yana bacci, kanshi ta fara shafawa cike da tausayi sai taga ya rame mata, kun san d'a da uwa, wayan Mum ce tayi ringing daukan Jakarta tayi ta ciro wayan, mijinta ne dauka tayi tare da fadin Habibi... Katseta yayi da fadin har kin kai? Yana dai lafiya koh? Mum tace gamu dai a asibiti, cikin tashin hankali his excellency yace maiya faru, nan Mum ta bashi labarin komai da yanda Dr ya fada mata, his excellency shima baiji dadin abunba amma saiya boye nan yaita kwantar ma matarshi da hankali akan gobe zai dawo kasar dan baya nan sunyi tafiya da president, tace Allah ya kaimu ya dawo min dakai lfya, ya amsa da ameen sannan sukai sallama, tana nan zaune tana ta saka irin yanda zata mishi wannan karan domin wlh ba zata sabu ba, a kashe mata yaro duk da tasha mishi maganan karin aure yana zullewa amma wannan karan bada wasa zata mishi ba.











Abdul ya taso daka Kaduna, kai tsaye taraba ya nufa, direct kauyensu indo, nan ya shiga yaita yawo amma baiga mai kama da ita ba, har yanzu fuskanta yake gani tana kuka, murmushi yayi tare da juya motarshi domin ya shiga jalingo ya kwana gobe ya dawo da safe nemanta, ko Allah zaisa a dace.










Yau dambu Tani tayi, domin tace a canza sana'a, duk a roba aka jera aka rufe da leda baka, indo ta dauka bayan Tani ta mata kashedin karta dawo mata dako kadan, kai tsaye tasha ta nufa nan da nan aka siye, ta juyo, tazo tsallaka titi taga mota tasha gabanta, komawa tayi da baya, tare dayin dan tsaki su masu kudi basa daraja talaka, fitowa yayi yana sakar mata murmushi tunani ta fara a ina tasan fuskan shi, lokaci daya itama ta sakar mishi murmushi domin tuno da ko waye, tabbas ya mata babban taimako tare da ceton rayuwanta, karaso wa yayi inda take, yace sorry, wlh kar ki bace min ne yasa na tawo da sauri, murmushi tayi tare da fadin ina wuni, amsawa yayi da lfya, sai kika gudu rannan ko sunanki baki fadamin ba, tace kayi hakuri, yace toh ya sunan? Tace indo, dariya yayi tare da fadin aysha koh? Tace eh, nan yaita dan janta da fira duk da ya lura tana sauri,yace inane gidan ku? Tace idan kabi can ka mike sai kayi kwana ka kara wani kwana sai ka mike..... Dariyan da yake yi yasa tayi shuru itama tana dan murmushi, yace haba aysha ai wannan kwatancen bazan gane ba, yanzu dai kizo muje sai in kaiki kinga sai inga gidan koh? Shuru tayi can tace kayi hakuri ba'a zuwa gidan mu, abdul yace saboda me? Tace inna ta hana zata bigeni idan kazo, yace niba tadi zanzo ba, ke kanwata ce, ya fadan mata hakan ne dan ta yarda ta nuna mai, tace itafa inna bata so kowa yazo dan Allah kayi hakuri kar kasa ta bigeni, yace toh yanzu ina zan dinga ganinki? Tace a nan cikin tasha nake Kawo tallah kullum, Abdul yayi dan murmushi tare da fadin ina zuwa,mota Ya bude ya dauko wata leda, ya mika mata tare da fadin gashi, girgiza mai kai tayi tace ka barshi ngd ,yace haba aysha nifa yayanki ne, dakyar ta amsa tare dayi mishi godiya, yace ni tunda baki son sanin sunana shikenan, tace kayi hakuri inaso, yayi murmushi yace toh yaya abdul, yace bari in barki ki tafi gobe zan koma abuja zanzo muyi sallama, tace toh sannan ta wuce, hanyar gidansu ta nufa tana jin tsoran shiga da ledan duk da bata ma san miye bane a ciki, koda ta shiga gida lambo ta farayi tana lekawa ji tayi ankira sunan tah cikin tsoro ta waiga......











Taku Maryam obam😘

💅 TAMBARIN TALAKA 💅






NA


MARYAM ALHASSAN DAN'IYA




🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝






Vote me on wattpat @maryam-obam


WWW.maryamobamnovels.com









40to45







DEDICATED TO....

HABIBA SALEH❤









Jameela ta gani, ajiyan zuciya tayi,jamila tace lafiya indo kike ta rabe2, Tani bama ta gidan, Jameela da tun shigowanta sai yanzu ta lura da ledan dake hannunta mai kyau, tace indo ledan nan fah, indo mika mata tayi tare da fadin dan Allah gashi ki ajiye min, kai jamila ta girgiza tare da fadin sai kin fadamin inda kika samo shi, indo tace toh Inna jamila, muje d'akin ki kar inna ta dawo ta gani, jamila tace muje, bayan Sun shiga d'akin jamila sun zauna, jamila ta Kalli indo tare da fadin ina jinki indo, shuru indo tayi domin bata san ta inda zata fada mata ba, uwa uba kuma tana jin tsoran abunda zai biyo baya, jamila kaman ta lura da hakan, yasa ta fara fadin indo karki damu inaso ki fadamin komai domin ni innan ki ce, nan taita gayama indo magana mai dadi, kun san babba ya iya kwantar ma yaro da kai koda yaron baiyi niyan fadin abu ba, sai kuji yana fad'a, nan Indo taba jamila labarin komai harda haduwanta da sulaiman da yanda sukayi, jamila ajiyan zuciya tayi duk da shima Abdul ta fahimci yana son indo dinne, amma tunda bai fada mata ba, itama ba zata ce Komai ba, numfashi ta sauke tare da bude ledan turare ne kala2 dasu chocolate da biscuits, jamila tace kai wannan kaya haka, yanzu dai abunda za'ayi ki dauki Turare daya ki boye saiki dinga amfani Dashi, inya Kare sai kimin magana in kara miki, amma fah ki boye kar tani ta gani, daga kai tayi alaman toh, sannan jamila tace ta diba chocolate din, diba tayi tace ma jamila ta rike sauran, jamila tace a'a sunyi yawa kwara daya kawai ta dauka, ta ajiye mata sauran, jamila ta kira sunanta da indo, amsasa tayi sannan jamila tace inaso ki bani hankalinki duk da bani da iko dake amma zan baki shawara, ki fadamin tsakani da Allah kina son sulaiman, ido ta rufe tare da daga ma jamila kai, dariya jamila tayi, tare da fadin shikenan yanzu sai ki jira amsa daka Sulaiman din tunda yace zai fadama mahaifinshi, nan taita ba indo shawara akan yanda zata dinga tafiyar da rayuwa cikin sauki, sun dauki lokaci Kafin Indo ta fito dan kar Tani ta dawo ta ganta a nan.










Mum na zaune har A Majeed ya farka, ganin Mum kusa dashi yasa abun ya bashi mamaki dan haka ya kare ma dakin kallo, ya tabbatar yana asibiti ne, lumshe ido yayi tare da fadin Allah yasa Dr bai fadama Mum matsalata ba, jin hannun Mum yayi tana shafa gashin kanshi, bude ido yayi a hankali, murmushi ta sakar mai tare da fadin Alhmdlh, son ya jikin naka? A hankali yace Mum da sauki, yaushe kika Zo? Tace dazu nazo na ganka cikin wannan halin, bari in kira Dr, fita tayi jim kadan sai gata ita da Dr, nan Dr ya dan duba shi,sannan ya fara dan tsokan shi, Oga ya kamata ayi aure shine maganin matsalan, ji yayi kaman yasa ihu gashi a gaban Mum duk kunya ta rufeshi, shiko Dr ko a jikinshi, nan Dr ya rubuta mai wasu Magani da za'a bashi kafin su wuce, A Majeed yasan Mum tasan komai haka ya tashi jiki babu kwari bayan an

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login