Advertisement
Showing 36001 words to 39000 words out of 85238 words

Chapter 13 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

54

kala daka fari zuwa ja, ido suka hada gabanta taji ya fadi domin ganin Yana yinshi, tayi saurin kawar da idonta tana dan kallan abun, dai2 lokacin Mum ta shigo dakin hakan yama indo dadi, Mum tace aysha ya jikin nashi? Ni inaga muje hspt kawai, indo tace Mum VP dinshi ne yahau sosai, zaro ido Mum tayi tare da matsowa kusa da tilon dan nata tace Abdul Majeed, maike damunka haka da har jininka zai hau, idonshi a lumshe suke amma ji yake kaman yace ma mum aysha ce matsalata amma bazai iya ba dan inda zai iya da tun tuni ya fadama Mum din domin yasan shida kanshi bazai tunkareta da zancen ba dan abunda ya aikata... Mum ce ta katse shi da fadin son ka tashi muje hspt, kai ya girgiza tare da fadin a'a Mum aysha zata kula Dani, indo wacce sai yanzu ta kuma magana tace Mum za'a amso mishi magani bari inje driver ya kaini, da sauri yace No kiba driver din yaje, Mum wacce tasan kanin zancen tace rubuta maganin aysha sai driver ya amso mishi, tace To Mum, fita indo tayi daka dakin jim kadan sai gata ta dawo Mum tace ina takardan? Indo tace na bashi ya siyo dan murmushi Mum tayi tare da fadin maimakon kizo in baki kudi sai kika bayar, aysha shuru tayi ba tare da tace komai ba, A Majeed idonshi lumshe amma kirjinshi kaman ya fashe dan takaici, kishin aysha yake ji bai san dawa take mu'amala ba a hspt, jin kirjinshi na zafi sosai yasa hannunshi yana dan dannawa amma kaman karawa yakeyi, duk abunda yakeyi idon indo na kanshi ta dan tausaya mai ko Ba komai dan Mum ne dole ta tausaya mai, dan haka ta tashi ta fita jim kadan sai gata da Ruwa da Cup da kankara a cikin wani bowl ruwan ta zuba a Cup din tare da kankaran, wajanshi ta nufa jin kamshin turaren Nata kaman kusa Dashi yasa ya dan bude ido, fuskanta babu yabo babu fallasa tace ga Ruwa kasha zai rage maka zafin, kin amsa yayi sai ido daya kura mata wanda hakan Yasa take jin wani iri, Mum tace A Majeed ka tashi kasha mana, kai ya girgiza alaman a'a, indo cikin muryanta karama tace ka daure kasha zaisa kirjin ya rage maka zafin kafin a kawo maganin, ganin yanda take maganan kaman za tayi kuka yasa ya tashi yana cije baki ya amsa tare da shanyewa duka, kallonta yayi yana dan murmushi a hankali ya furta thank for care, bata bashi amsa ba sai barin dakin da tayi, jim kadan sai gata da ledan maganin lokacin Mum bata dakin idonshi a lumshe jin kamshin turaren da yake sashi cikin wani hali yasa ya bude ido dan yasan tana wajan, idanshi akan nata murmushi ya sakar mata fuskanta a daure tace ga maganin, kallonta yake yi yanda ta wani tamke fuska, sai yaga ta kara mishi kyau, mika mai maganin takeyi bai amsa ba sai fadi yayi plz bani ruwan da zansha, ajiye maganin tayi a gefe tare da bude goran faro ta zuba mai a cup, bashi tayi ya amsa jiki babu kwari kallonta yayi tare da fadin plz ki taimaka kiban maganin insha bazan iya budewa ba, dan tsaki tayi kadan wanda bata san zai fito ba har yaji, sai jinshi tayi yana fadin kiyi hakuri nasan na takura miki, but dan Allah za kiyi min, wani iri taji dan haka tayi saurin bude ledan maganin ta fara bashi yana sha, harya gama ya kalleta yace ngd da kulawa, tace no need ina maka hakan ne a matsayina na Dr wanda zan iya yima kowa ma hakan tana fadin haka tabar dakin, ido ya lumshe cikin jin zafin kalaman nata, zan iya yima kowa ma hakan, wani irin kishi yake ji tare dajin zafin maganan nata sosai, duk yanda yaso ya cire abun a ranshi ya samu yayi bacci ya kasa, sai juyi yake tayi ga kirjinshi na mishi zafi sosai dan ma maganin da yasha yasa ya dan ragu amma still yana mishi zafi.












Itako dakinta ta fada ta shiga toilet tayi wanka tare dayin alwala dan yin sallah magrib da aketa kira,bayan ta idar da sallah dinne ta zauna akan kujeran dakin tana tunanin kauyensu wani hawaye taji yana zuban mata Allah sarki inna jamila ko kina nan har yanzu a gidan mu? Abubuwan da suka faru a baya suka dunga dawo mata, gaba daya hankalinta taji yayi Gida ko Ba komai ya kamata ace yanzu taje duk da bata son zuwa garin amma kodan taga inna jamila dako sata sami labarin Dan uwanta dole taje,cikin wannan hakin Mum ta shigo ta sameta, kiran sunanta tayi tare da fadin wai ni kam aysha miye matsalanki ne kwana biyu nan, dan shuru tayi tana tunani tana son zuwa Kaduna da garinsu amma bazata iya fadama Mum yanzu ba saboda ciwan dan nata dan taga hankalin Mum ba'a kwance yake ba, kaman Mum tasan abunda take tunani tace aysha nasan kina Tuna baya ne bayan dazu mun gama magana, amma inaga ki shirya jibi sai kije garinku ki duba su inaga hankalinki zai dan kwanta, indo kai ta girgiza tare da fadin Ba yanzu ba mum sai nan gaba, Mum tace akan wani dalili kin fiso kiyi ta damuwa kullum koh? Tace Mum inaso inje amma zan bari sai A.... Shuru tayi wanda kuka yaci karfinta Mum tace kiyi hakuri aysha kibar wannan kukan, shuru indo tayi tana sauke ajiyan zuciya haka Mum taita bata baki akan ta shirya taje jibi din,tace Mum shikenan amma sai naga yanayin jikin nashi tunda ni nake duba shi, Mum tayi dan murmushi tare da fadin karki damu amma Idan kin bukaci hakan sai ki daga tafiyan, tace toh mum kiran sallah isha'i ne yasa Mum barin dakin indo tashi tayi dan yin sallah, bayan ta idar ta zauna amma saita tsinta kanta da zuwa duba A Majeed din dan haka ta tashi ta nufi dakin a zaune ta ganshi akan dadduma alaman ya gama sallah ne, kallo daya tamai ta kawar da idonta gefe tace kirjin ya daina maka zafi? Ido ya kura mata komai nata yana burgeshi a natse, yace ya daina sai dai ina cikin damuwa, kallonshi tayi caraf suka hada ido tayi saurin kawar dakai gefe dan murmushi yayi tare da tashi dakyar ya koma kan gadon dakin, cikin taushin murya tace gobe zan gwada maka VP din inga koh ya sauka sannan ka cire ma kanka damuwa indai Kana son lafiyanka,ido ya kura mata yanda take mai bayani abun har mamaki yake bashi, dan shuru tayi alaman ko zai ce wani abu jin shima din yayi shuru yasa ta juya zata fita, sunanta ya kira da aysha cikin wani irin murya tsayawa tayi ba tare da ta waiga ba, yace plz ki dan dawo ki zauna ko zan iya bacci, waigawa tayi tana mai wani irin kallo shiko murmushi yake mata, kaman bazata koma ba komai ta tuna kuma ta dawo tare da zama akan kujeran dakin tace zan zauna a matsayina na doctor mai burin inga wanda nake dubawa ya samu Lafiya, ido ya lumshe da alama maganan nata ya mishi zafi, amma saiya daure yace babu komai a hakan ma nagode, bata kulashi ba illa wayanta da take latsawa shiko idanshi na kanta ji yake kaman yaje yayi hugging dinta ko zaiji sanyi a ranshi, wayanshi ne yayi kara wacce yake gefen gadon, hannu yasa ya dauka bakuwar number ne, kuma na waje ko ba'a fada ba yasan cewa zainab ce tunda ta tafi bai kirata ba itama haka sai yau, dan haka ya dauka tare da sawa a Kunne, ban san mai take fada mai ba naji dai yana fadin kin san baki isa ki rabani da mahaifiya taba koh, dan haka ki dinga sanin kalaman da zaki fada a kanta yana fadin haka ya kashe wayan gaba daya cikin bacin rai, indo dake zaune tana saurara duk sai taji ya bata tausayi a karo na farko, dan tasan matarshi tafi karfinshi yana mata son daya wuce kima, dan lumshe ido tayi tana tuna abubuwan da suka faru lokacin datai zama a gidan nashi, haushin shi shida matarshi taji yana kara kamata, dan tsaki tayi kadan wanda sai kana gab da ita zaka iya ji, A Majeed da idonshi ke kanta yana lura da duk abunda takeyi jin muryanshi tayi yana fadin aysha dan Allah ki daina tuna baya ki bani second chance, ina mai baki hakuri akan...... Ya isa haka ta katse shi cikin bacin rai, shuru yayi yana kallonta taci gaba da fadin kar kaga dan daman dana baka yasa kaji koh akwai abunda nake nufi a kanka, karka yaudari kanka ya kamata ka bude idonka daka baccin da kake shirin yi, duk wannan abun ina makane a matsayina na doctor sannan kuma ka kasance kai dan Mum ne sai yasa har nake dubaka kar hakan ya baka daman wuce gonarka...... Wani irin hawaye taji yana zubar mata wanda yasa ta kasa karasa maganan dan haka tabar dakin da sauri......










Taku maryam obam😘


*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









140to145







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*











A Majeed idanshi ne ya kada yayi ja kaman garwashi ga kirjinshi na faman tafarfasa, gaba daya ji yayi zaman gidan ma ya isheshi domin magananta yake taji a kwakwalwanshi yana mai yawo, lumshe ido yayi yana mamakin irin son da yake mata Lokaci daya, hawaye ya fara zuba a idonshi tare da karayin nadaman abunda yayi mata, tabbas duk yanda kaga mutum karka taba wulakanta shi, domin baka san irin baiwar da Allah yayi mishi ba, tashi yayi dakyar ya fita daka gidan, security din gidan sunyi mamaki da suka ganshi dan sun san bashi da lfya gashi kuma yana tafiya dakyar, bude gate din gidan yayi, wani daka cikin security din yace sir where are you going in dis condition, bai kulashi ba dan bata shi yake ba, fita yayi daka gidan yana tafiya dakyar taxi ya tsayar dakyar ya iya furta mai inda zai kaishi, direct gidanshi aka kaishi zaro kudi yayi wanda bai san ko nawa bane ya bashi sannan ya karasa kofar gidan yana bugawa mai gadin gidan ya leko duk da dare ne akwai haske tako ina, ganin ogan nashi yasa ya fito da sauri yana fadin wlcm sir, baibi ta kanshi ba sai shigewa da yayi,dakinshi ya wuce direct ya fada gado yana hawaye kaman wani karamin yaro, tabbas Allah yakan jarabci bawa ta hanyoyi da dama, bai taba tunanin zaiso indo a rayuwanshi ba, sai gashi lokaci daya Allah yasa mishi azababban sonta tare da kishinta ada idan yaji labarin halin da masoya sukan shiga har haushi yake ji sai yaga kaman karya ne, sai gashi yau ya faru a kanshi, lallai ikon Allah ya wuce wasa, gaba daya ya kuma birkicewa ya koma abun tausayi duk saboda son wacce ya kira yar kauye wacce bata waye ba, gashi sonta na neman hallakashi, ido ya lumshe wanda hawaye ke zuba, tare da burin barin kasar ko zai dan sami sauki domin duk yanda yakai da sonta bazai matsa mata ba, tunda bata bukatar hakan, dakyar ya janyo wayanshi ya kira wata number, kana jin maganan shi kasan yana cikin wani hali, fadi yayi zan sami visa na London gobe nake So, ban san mai aka fada mishi ba ya jefar da wayan gefe tare da lumshe ido kanshi na mishi wani irin juyi.













Koda indo ta shiga daki itama kukan take tayi, wai mai yasa rayuwa yake zuwa mata a haka ne? Da farko nasha wuya wanda ban taba kawo wa zanji dadi ba, sai gashi nayi aure an kaini Gidan mijin da yake guduna yana kyamar nunama duniya ni matarshi ce, ya maidani baiwar kishiyata ya kirani yar aiki a gabanta tasa ni bauta kaman ba gobe, Allah ya kubutar dani daka gareshi mai yasa saida na fara jin dadin rayuwa na yake son fito min da wani bakon abu mai yasa hakan yake faruwa Dani ne...... Kukan da takeyi ne ya kara karuwa..... Dan shuru tayi yayin da wata zuciyar take ce mata haba aysha mai yasa zaki dauka da zafi haka aiko da zaki rama abunda ya miki bai kamata kiyi mai a cikin wannan yanayin ba, karki manta kefa doctor ce dan mai yasa zaki fadama patient dinki kalaman da zai kara samai wani ciwon da sauri ta tashi kaman an tsunguleta fita tayi ta nufi dakin da yake amma baya ciki dan zama tayi dan tana tunanin ko yana toilet jin ta dade a dakin bata ga ya fito ba yasa ta koma dakinta akan da safe zata dawo, koda ta koma kwanciya tayi tana ta juye2 sai tunanin da take tayi yanda zata Kawo karshen abun tun Kafin ya fito fili, lallai dole in fito da koma waye inyi aure duk da bata da burin yin auren a yanzu amma tana ganin hakan shine zai kawo Mata duk wani karshen matsalanta wanda A Majeed yake shirin tsokano mata domin indai harya furta abunda yake ranshi koda Mum bazata bada goyan baya ba, tabbas ita zata bada domin bazata taba gudun wani Abu na Mum ba, yanda take jin Mum babu wani nata da zaice yana son abu a wajanta ta kasa yi domin Mum Mace ce wacce babu irinta koda za'a samu sai ansha wuya, wani hawaye taji yana zubar mata a ido lallai ya kamata tasan abunyi.












Washe Gari da safe Mum ta shiga dakin da d'an nata yake amma bata ganshi ba, zama itama tayi dan tana tunanin ko yana toilet jin shurun yayi yawa yasa ta tashi ta nufi wajan toilet din, ganin babu alaman mutum yasa ta bude taga wayam, cikin damuwa take fadin ina yaje ne haka? Fita tayi a hanya suka hadu da indo tana kokarin zuwa dubashi tayi shiri da alama fita za tayi, Mum duk da tana cikin damuwa tace aysha fita za kiyi tace eh mum an kirani a hspt ne akwai wanda aka Kawo zan duba shi, Mum tace toh Allah ya taimaka, kinga A Majeed kuwa? Indo dan shuru tayi Kafin tace baya cikin dakinshi? Mum tace baya nan, indo taji wani iri amma saita daure tace kodai ya fita ne? Mum tace bari in kirashi shida yake jin jiki ina zashi kuma, kiran layin tayi akace switch off kallon indo tayi tace wayan ma a kashe indo taji wani iri musamman yanda taga Mum din nata, na cikin damuwa, toh ina zashi? Shida yake cikin wani hali ido ta lumshe gaba daya jikinta yayi sanyi, Mum ce ta katseta da fadin bari inje in tambayi security ko sunga fitan shi, tare sukai kasa ita da indo din tambayan security tayi ko sunga A majeed, bayan Sun gaidata ta amsa suke shaida mata jiya da daddare ya fita gashi kuma hjy kaman yana jin jiki sosai wlh, Mum shuru tayi amma ranta a jagule indo itama kasa magana tayi horn din da akeyi yasa aka bude gate din mai girma sanata ne ya shigo da mukarrabanshi, ganin matar tashi a tsaye ita da indo yasa ya fito yana tambaya koh lafiya? Nan Mum ta fada mishi abunda ke faruwa, kiran layin A Majeed din yayi amma a kashe, security dinshi ya tambaya ko akwai mai number din security din dan nashi? Wani yace yana dashi nan ya karanto ma senator bugu daya security din ya dauka tare da fadin Hello waye akan layi cikin turanci, Dad yace mahaifin A Majeed ne, cikin girmamawa kaman yana gabanshi yake gaidashi bayan Dad ya amsa nan yake tambaya koh A Majeed yazo Gida, yace eh amma gskiya sir yana cikin wani hali kaman bashi da lfya sosai wayan a speaker yake duk suna ji indo hawaye taji ya zubo mata da sauri tasa hannu ta goge hawayen Dad ya kashe wayan tare da kallon matar tashi bari inje inga halin da yake ciki, tace suje tare Dad yace ok Mum ta Kalli indo tace kije driver ya kaiki hspt din bari muje muga halin da yake ciki indo kafa babu kwari ta nufi mota driver yaja suma su Mum suka fita zuwa gidan dan nasu.












Koda indo ta karasa asibiti jiki a sanyaye ta shiga ciki, nan aka kawo Mata patient din da zata duba a kan keke kallon mutumin tayi cikin tausayawa tare da kallon wanda yake turashi din ganin yana mata murmushi yasa itama tamai tare da tunanin ina ta sanshi lokaci daya ta tuna da wanda ya biya mata kudin abinci dai2 lokacin wata mata ta shigo Office din daka gani matarshi ce bayanta wani saurayi ne ido indo ta kura mai da sauri ta nufeshi tana nunashi lokaci daya kuma ta rungumeshi wanda mamaki ya hanata magana sai kuka haka shima ta gefenshi yazeed dake gefe yana kallon ikon Allah tare da mamaki a ina tasan Yusuf ga zuciyarshi dake mishi zafi ganin irin runguman da tayi mishi ........












Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login