Advertisement
Showing 30001 words to 33000 words out of 85238 words

Chapter 11 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

59

dady, duk da tana jin kunyan dady amma yana janta a jiki kaman yarshi domin yana tausayama yarinyar, dady yace aysha yaushe za'a fara aiki ne? Kallon Mum tayi alaman tayi magana, Mum tace babu abunda zance gwara ki fada dariya sukasa, indo ganin Mum taki cewa wani abu, yasa tace dady koda yaushe a shirye nake, yace toh Alhmdlh na bada komai naki dama Office dinki na jiranki, indo tayi godiya, dady yayi gyaran murya tare da fadin aysha ya kamata ki shirya kije kiga Gida ki gaidasu koda kwana biyu kiyi musu, Mum tace hakane ya kamata taje taga yan uwanta nima abun yana raina, indo ji tayi kaman an soka mata wani mashi, bata kaunar zuwa garinsu abubuwan da Suka faru suka fara dawo mata, har yau sulaiman na ranta sai dai kuma tana son taji ko anji labarin yusuf, wannan tunanin yasa taji tana son zuwa, nan sukai ta dan fira, A Majeed ne ya shigo gidan idanshi nakan indo daure fuska tayi ganin ita yake kallo, Dad ya tashi tare da fadin zani majalisa yau akwai zama sai na dawo aysha ki shirya Monday sai ki fara zuwa office, A Majeed Dam yaji gabanshi ya fadi domin baya son ta fara aiki kar a mishi kwace amma yasan yanda zaiyi, bayan Sun gaisa da Dad din nashi ya wuce, zama yayi akan dinning din shima ya fara cin abinci, wayan indo ne yayi kara dauka tayi tare da fadin ina nan ina zani, dan murmushi tayi tare da fadin haba fatima ai Nigeria yafi dadi ina tare da Mum dina duk da larabci tale maganan wani kuma da turanci, A Majeed ido ya kura mata yana kallon ta yana mamaki, harta gama wayan, tashi tayi tabar wajan ido A Majeed ya bita Dashi yana mamakin irin yanda ta canza, wayan Mum ne yai kara ta dauka tare da fadin an Kawo ne?ban san mai akace mata ba tace gani nan zuwa, tashi tayi ta nufi dakinta jim kadan sai gata ta fito da Gyale ta kalli A Majeed bari inje in dawo yanzu bazan dade ba, yace ok Mum, bayan fitan Mum indo jin karan kaman an rufe Gate ta dauka A Majeed ne ya fita dan haka ta fito falon, tana sauka ta ganshi wani iri taji kaman ta juya sai taga hakan bai dace ba dan zai dauka ta damu dashi ne, mai makon ta zauna a falon saita nufi kofar fita wajan bukka taje da yake yana bayan gidan, dan kwanciya tayi akan kujera mai kaman lilo tana danna wayanta, jin kaman ana kallonta yasa ta tashi ta zauna ido suka hada kauda kanta tayi taci gaba da danna wayanta, zama yayi kusa da ita, kamshin turaren shi ya bugi hancinta, Tana so ta tashi tana gudun bashi dama domin idan yaga ta tashi haka zai dinga mata, daure fuska tayi, kiran sunanta yayi cikin wani irin murya kirjinta taji yana bugawa da karfi, aysha nasan nayi miki kuskure a....... Tashi tayi tabar wajan da sauri, A Majeed gaba daya jikinshi yayi sanyi wani irin sonta yaji yana kara shiganshi, itako dakinta ta shiga tasa kuka tare da Tuna abunda matarshi Dashi kanshi sukai mata wani irin tsanarshi taji yana shiganta jin an bude kofan dakin yasa ta rufe ido kaman mai bacci Mum ce ta shigo dakin domin ta dawo bata ga A Majeed ba, tana so taji ko ya tafi ne, ganin Indo tana bacci yasa ta koma tare da fadin toh ina ya nufa dan taga motarshi, ko data gidansu ya fita oho, shiko A Majeed kasa tashi yayi yana tunanin yanda zai shawo kan indo ya dauki lokaci mai tsawo a wajan Kafin ya fito yaja motarshi ya tafi,gida ya koma a falo yaga zainab ita da wata kawarta ko kallansu baiyi ba ya wuce Zainab tabe baki tayi kawarta dai bata ce komai ba sai kallon yanda Zainab take wani tabe baki takeyi ita kawar tana fadin inda ita take da wannan Guy din da anga luv, kawar tashi tayi tare dayi mata sallama ta wuce, Zainab daki ta wuce inda taga A Majeed zaune yana danna laptop tace wai A Majeed mai kake nufi kwana biyu kana ta wani shan kamshi, bai kulata ba yaci gaba dayin abunda yakeyi, ganin ya maidata Sauna yasa ta kwace laptop din ta jefar tace ni nafi karfin in dinga maka magana kana kyaleni, kana mantawa da ko wacece Zainab, dan murmushi yayi tare da fadin bani da time dinki fita yazo zaiyi ta tare mai hanya tare da fadin babu inda zaka sai da yarda na, shuru ya mata ba tare daya kuma cewa komai ba, ganin kaman rigiman take so yasa ya barta ya koma ya kwanta tana ta surutai tunani yake tayi very soon zanyi maganin ki kwata2 duk ta fitan mai a rai duk yanda yake sonta....










Taku Maryam obam😘


*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









120to125







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*







Plz nayi mistake a page 115to120 sai nasa 110to115 ayi hakuri plz, yanzu sai a fara daka page 120to125











Zaune take a wajan bukka tana danna wayanta, daka gani tana jin dadin wajan, dan tsaki tayi tare da ajiye wayan ta kwanta akan kujeran lilo din dake wajan ido ta lumshe kaman mai bacci amma idonta biyu,ba komai take tunani ba illa halin da Abdul yake ciki, tare da tunanin ta yanda zata bi ta taimakeshi, domin Abdul yana daya daka mutanan da suka taimaketa wani irin zafi taji ranta na mata tuna irin wahalan da tasha da wanda bata fata koda makiyinta ne ya fada irinshi, kamshin turaren da taji yasa tasan A Majeed yazo wajan domin irin kamshin turaren shi taji, bata motsa ba balle ta bude ido, tayi wajan minti uku tana shakan kamshin ba tare data motsa ba, A Majeed wanda tun zuwanshi ya kafa mata ido yana kallonta yanda take kwance idonta a lumshe, wani irin yanayi yaji yana shiga mai wuyan misaltuwa, ganin idan yaci gaba da kallon nata zai iya shiga wani hali yasa yabar wajan cikin wani yana yi, tafiya yake amma kaman bayayi dan tafiya yake a hankali dan gaba daya jikinshi ya mutu, baiko shiga Gida wajan Mum ba yabar gidan, jin ta dade a haka kuma bata daina jin kamshin turaren ba, yasa ta bude ido amma bata ganshi ba, mamaki ta fara toh ina yake, kodai bashi bane yazo? Amma kuma kamshin shi naji, dan shuru tayi na wani lokaci can tayi tsaki tare da fadin koma dai shine ba damuwa na bane, jin kamshin turaren kaman yana kara mata yawa yasa tabar wajan dan bata son duk wani abu daya dan ganceshi, koda ta shiga ciki bata ganshi ba abun ya daure mata kai tare da tunanin mai yasa toh take tajin kamshin shi, tabe baki tayi alaman bai daman ba.











Mum da indo suna zaune suna fira,mum tace jibi dai za'a fara zuwa office, indo dariya tayi tare da fadin harna kosa in fara Mum na gaji da zama waje daya babu wanda na sani balle inje ziyara, Mum tace ai nima dai zaman naki Gida baya min dadi gwara ki fara aikin ko a can kya samo min siriki na, dai2 lokacin A Majeed ya shigo wanda yaji abunda Mum ta fada fuska tamke ya zauna bayan yayi sallama ciki2 mum ce kawai ta amsa amma ita indo cikin ranta ta amsa, wayanshi yake ta dannawa tunda ya gaida Mum bai kuma cewa komai ba, amma gaba daya hankalinshi na wajan Indo, Mum tace ya kamata kije kiyi shopping abubuwan da zaki bukata Dan nasan masu aiki suna bukatan kayan makeup dasu Turare sabo da shiga cikin al'umma, A Majeed Wanda tunda ya shigo baice musu komai ba sai yazu yace haba Mum miye nayin wani makeup dan mutum zai shiga Al'umma, gwara mutum ya zauna yanda Allah yayi shi bawai yaita ma fuska fenti ba sai mutum ya koma kaman aljani, yana fadin haka yai shiru tare daci gaba da danna wayanshi kaman bashi yayi wannan dogon zancen ba, Mum dan murmushi tayi tare da fadin ai kowa da irin choice dinshi naga wasu masu yin shafe2 din suke So dan sune suke ganin Sun waye, shuru yayi bai kuma cewa komai ba domin yasan Mum magana ta fada mishi, indo da tunda ya shigo falon take a takure tashi tayi tare da fadin Mum bari yau in shiga kitchen, Mum murmushi tayi cikin jin dadi tare da fadin kice yau za muyi dinner da abincin larabawa, dariya tayi wanda saida dimple dinta ya lotsa A Majeed wani irin sonta yake ji yana fisganshi ganin ta shige kitchen duk sai yaji ya takura da zaman, dan tsaki yayi wanda bai san ya fito ba, Mum ce ta daga kai ta kalleshi tare da fadin kai kuma lfya kuwa, yace lfya fuska a tamke irin na shifa asan abunyi Dashi, Mum tashi tayi tabar falon, ganin haka shima yabar gidan gaba daya cikin wani irin yanayi,tuki yakeyi yana tunanin ta hanyar da zai shawo kan Aysha wanda ya lura kaman baya gabanta dan yanda take nuna mishi kaman Dashi da babu duk daya wani iska ya furzar mai zafi tare da daukan wayanshi ya kira Abdul cikin murya irin na wanda baya san magana yace Kana ina? Abdul ya amsa da ina Kaduna dan tsaki yayi tare da kashe wayan, juya kan motarshi yayi ya koma gidan Mum domin in yana ganin indo yana shiga cikin nishadi ko ba komai ganinta na sashi cikin farin ciki da annashuwa, koda ya koma gidan bai shiga ciki ba wajan bukka ya nufa inda yaga wani littafi a wajan an rubuta the doctor, dan shuru yayi bayan ya karanta sunan tare da fadin kenan Dr ce yanzu, wani iri yaji tunawa da a asibiti zata fara aiki ranshi yaji ya baci dan yasan da mutane zata dinga hulda manya da kanana, gashi yasan babu wanda zai ganta bai loraba wani takaici ya kuma ji tunawa da yayi babu aure a kanta, kenan kowa yana da daman yi mata magana, ya dauki lokaci mai tsawo yana sakawa da kullawa jin kiran sallah magrib ne ya gane ya dade a wajan dan haka masallaci ya nufa yaje yayi alwala aka fara sallah, koda aka idar mutane sun fara fita wasu kuma suna nan zaune domin suna jira lokacin sallah isha'i yayi idan sukayi sai su koma gaba daya cikin masu jira harda A Majeed wanda yake ta faman addu'a akan Allah ya mallaka mai aysha a karo na biyu har aka kira sallah aka idar sannan ya fito ya shiga gida, a dinning yaga Mum da indo wacce take cikin wani doguwan riga Red material ne kayan saman ya kamata kasan kuma ya bude, ga dan kwalin kayan ta dan yafe kanta Dashi duk da babu makeup a fuskanta tayi kyau sosai kun san jan abu da karama mutum kyau ido ya bita dashi wanda ta dago suka hada ido da sauri ta kawar da kanta tare dajin haushin hada idon da sukayi, shigo murmushi ya sakar mata da suka hada idon zama yayi akan daya daka kujeran dinning din, Mum tace au dama baka wuce ba?yace eh har na tafi na dawo dan inyi dinner a nan, cikin ran indo tace inda tasan zaiji da batai girkin ba domin bata son duk wani abu da tayi yaci ko ya yaba wani abu nata dan haushi yake bata sosai..... Jin muryanshi tayi yana fadin aysha plz samin abincin ba indo ba harta Mum tayi mamaki indo kaman ba zata sa ba amma ganin Mum a wajan yasa ta tashi tare da zuba mai ta tura mai gabanshi ta kalli Mum tace Mum good night, Mum tace tun yanzu aysha Allah ya tashe mu lfya, daki ta wuce bawai dan tana jin bacci ba kawai dan kar taci gaba da zama da A Majeed ne yasa tabar wajan, koda ta shiga daki tsaki tayi tare dajin haushin zuba mai abincin da tayi, shigo tana barin wajan yaji ya kasa cin abincin danshi ba abincin yake bukata ba ita kawai yake son gani, irin kallon da Mum take mishi yasa ya fara cin abincin yaji dadinshi sosai, harya gama ya tashi tare da fadin Mum bari in tafi in Dad ya dawo a gaida shi, tace OK sannan ya fita da ido Mum ta bishi tana takaicin halin dan nata yau shekara nawa da aure amma har yanzu baida da ko daya, wanda ita koda yaushe burinta bai wuce ace taga jikanta ba,amma tunda haka yake so sai yaje yaita yi.









Indo ce cikin atamfa tayi kyau sosai saman kayan tasa kalan rigan likitoci, dan karamin gyale ta yafa a saman kanta, falo ta fito inda taga Mum tana zaune cikin shiri Mum tace yauwa sai kizo muje in kaiki domin in raka ki zuwa Office, indo tayi dariya cikin jin dadi sannan suka fita, driver ke tuki indo da Mum suna baya har katon asibitin da zata fara aiki, bayan driver ya faka suka fito duk wanda ya gansu zai ce indo yar Mum ce ta cikinta domin irin kyan da suke Dashi, har cikin asibitin suka shiga inda Suka je wajan wanda Dad yace su nema nan ya amshesu da murmushi tare da raka su har Office din indo din, office din babba ne ciki harda dan karamin gadon duba mara lafiya ga AC da TV dake manne sai kujeran zamanta da guda biyu na zama, office din dai irin na Dr babba, indo gefen hawan jini da sugar da zuciya ta karanta, sai yasa Office dinta yake da girma, Mum bayan ta gama gani ta mata murna sannan ta wuce tare da fadin driver zaizo ya dauketa inta gama, nan aka shigo ma indo da file na marasa lafiya babu bata Lokaci tace a fara shigowa, wani tsoho ne ya fara shigowa wanda kallo daya zaka mai ka gane mai arziki ne sai dai ciwo yasa duk ya rame, nan indo ta mishi umarni daya zauna bayan ya zauna tace maike damunshi nan ya fara mata bayani, tana rubutawa harya gama ta fara mai tambayoyi yana bata amsa, wanda yake fada mata dakyar yake tafiya kafanshi ya kumbura, tace yahau gadon dake dakin ya bude kafan ta gani, bayan ya zauna ya bude kafan taga yanda ya kumbura kuma guda daya, Magani ta rubuta mai tare da fadin idan ya kare ya dawo, fita yayi wani ya shigo haka taita duba mutane a ranan ta duba mutane sun kai ishirin, sai wajan 8 ta gama Wanda driver yazo ya dauketa sukai Gida suna shiga A Majeed na shigowa, ganin kayan dake jikinta yasa ya tamke fuska da sauri ya nufeta Kafin ta shiga ciki, tare mata gaba yayi tare da fadin aysha inason magana dake, shuru tamai ba tare data kulashi ba fuskanta a daure, ga kamshin turaren shi da yake tashi, haka shima ta gefenshi jin kamshin turarenta yake yi gaba daya ya fara kashe mishi jiki, cikin wani irin murya ya kira sunanta bata amsa ba sai daka kanta da tayi alaman ya matsa mata ta wuce ido suka hada wanda saida gabanta ya fadi da sauri ta kawar da kanta gefe ta juya da baya zata bar wajan dan bazata iya tsayuwan ba, riganta ya rike ta baya wanda yasa ta tsaya cak......









Taku Maryam obam😘


*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









125to130







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*







*NGD DA KIRANA DA KUKAYI AKAN LAFIYA BANYI POSTING JIYA BA DA MASU YIMIN MESSAGE DUK NA GODE LAFIYA NA QALAU SAI DAI CIWAN KAI DA YASA NI GABA TUN JIYA HAR YANZU DA NA DAURE DAN INGA NA FARANTA MA MASOYA NA RAI SOSAI NAKE JINKU KAMAN YANDA KUKE KAUNAR NOVEL DINA INA MUKU ONE LUV❤*









Zuciyanta taji yana tafarfasa tare da fadin wai mai yake nufi da ita ne haka, cikin fushi ta waiga amma ganin irin kallon da yake mata yasa ta kasa yi mishi masifan da taso tamai, tsaki ta danja tare da wucewa ta gefenshi ba tare da taji abunda zai fada mata ba, wani irin iska ya furzar cikin wani yanayi mai wuyan misaltuwa,shima cikin ya shiga, koda indo ta nufi falo a nan taga Mum harda Dad suna dan fira, da sallama ta shiga duka Suka amsa, Mum tace a'a likita bokan turai, dan rusuna wa tayi ta gaida Dad da Mum, cikin Fara'a suka amsa Dad yace ya office din dai2 lokacin A Majeed ya shigo yana sallama yana magana kaman baya son yi, amsawa sukayi, zama yayi kusa da Dad din nashi wanda shima Dad din kallonshi yake tare da fadin yauwa kai dama nake nema, wai ya maganan contract dinne? Kayi signing kuwa? Yace eh nayi Dad tare da tashi yana fadin bari in dauko maka, indo tashi tayi ta shige daki, toilet ta fada tayi wanka,tare da alwala bayan ta idar da sallah isha'i tasa wata doguwar rigan bacci ta kwanta tare da lumshe ido, koda A Majeed ya dawo baiga ayshan shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login