Advertisement
Showing 45001 words to 48000 words out of 85238 words

Chapter 16 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

52

a bace yake dan gaskiya abun yana matukar damunshi wai tilon dan nashi ne yake kwance babu lafiya gashi yaki bari a kaishi asibiti, duk da ya bayyana matsalanshi amma Mum tana nunawa kaman bata damu ba, lallai komai ya samu danshi laifin Mum ne.... Jin muryan A Majeed ne ya katseshi da yake fadin Mum babu abunda yake damuna Just kawai ina son inbar kasar jibi shine kawai nake So, Dad yace son indai zaka cire komai a ranka a gobe ma zaka sami flight, yace yes Dad plz inason fita london, I need to rest for some month , Dad yace shikenan amma sai kamin promises zaka ga Dr a can? Yace I promise Dad, cikin jin dadi Dad din yace shikenan saika shirya,gobe 6 in d morning zaku tashi, inda badan dare yayi ba da yau zaka tashi, A Majeed yaji dadin hakan duk da zuciyarshi a tunkushe yake yana son ganin aysha ko zaiji dadi sai dai bazai nemeta ba dan Yana son yayi nesa da ita ko hakan zaisa ya Manta da ita, dan lumshe ido yayi yana mai jin zafi a ranshi, Mum kam kasa magana tayi gnin Dad ya fita daka dakin yasa ta kalli dan nata tace mai zaka ci son?kai ya girgiza alaman babu komai, Mum tace haba son ya zaka zauna kana ciwo kaki cin komai, plz tell me mai kke son ci? Yace aysha plz am o.... Bai karasa ba yayi shuru dan jin sunan daya kira Mum din nashi dashi, Mum dan murmushi tayi tare da tashi ta fita daka dakin, tashi yayi dakyar ya nufi toilet, ya dade a ciki sai gashi ya fito da towel a kanshi alaman dai yayi wanka, yana tafiya kaman babu jini a jikinshi domin gaba daya babu kwari a jikin nasa, jallabiya yasa, tare da zama akan gadon kayan aikin indo ya gani da sauri ya kawar da kanshi Dan baya son gninsu dan So yake ya manta da komai nata, duk da yasan hakan ba abu bane mai yuhuwa, kwanciya yayi ta baya yana ganinta a idonshi yana cikin haka Mum ta shigo dauke da tray a hannunta ajiyewa tayi akan Side drawer, tace son tashi kaci abinci koh kadan ne kaji? Tashi yayi yana kallon Mum sannan yace Mum bana jin yunwa, tace Abdul-majeed ka daina horar da kanka, wannan abunda kakeyi bashi zai kawo maka karshen wannan matsalan da kake ciki ba, kallon Mum yayi da sauri ta daga mai kai alaman eh, zaiyi magana tace mai Ya Isa haka tare da bashi Tea din data Kawo mai da snack, amsa yayi ya fara ci tare da tunanin mai Mum ke nufi, suna cikin haka Abdul ya shigo dkin hankali a tashe, ganin A Majeed din yana shan Tea yasa ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin kama warke Ashe, karaso wa yayi ya gaida Mum, inda take tambayanshi kwana biyu yace wlh Mum naje Kaduna ne amma wannan karan anyi nasara komai ya daidaita yayar yarinyar Ashe wai Tana tsoran bata mai kudi ne saboda gudun wulakanci dakyar dai aka shawo kan matsalan, ni da farko ma nasha ko rikonta take Ashe yayarta ce, Mum tace toh Alhmdlh yanzu saura musha biki kawai, dariya yayi ba tare da yace komai ba, Mum fita tayi ta barsu,Abdul matsawa yayi kusa da abokin shi, yace kai Man irin wannan rama haka gskiya kaji jiki fah, wai maike damunka ne haka? A Majeed yace aysha, Abdul yace aysha kuma? Kai ya daga mai alaman eh, Abdul dariya yayi tare da fadin wai mai kake nufi ne? Kodai ka sami wata chicks ne, dan tsaki yayi kalan na mai jin jiki, kafin yace kana da matsala Abdul wace aysha nake nufi inba matata ba, abdul yace wannan yar kauyen? Cije baki A Majeed yayi tare da ajiye Cup din Tea din ya kwanta, Abdul yace haba Man magana zaka yi, A Majeed cikin murya irin name jin jiki yace, Abdul joke apart ina son aysha sosai duk wannan abunda nake ciki saboda sonta nake cikinsa, ban taba jin wani abu akan wata Mace ba kaman yanda nakeji akanta, Abdul nayi nadaman abubuwan dana mata duk da a lokacin wani abun bada san raina nake mata ba, dan Allah ka tayani bata hakuri dan nasan zata iya jin maganan ka, bance lallai saita soni ba amma ta yafe min,ta cire komai dana mata a ranta duk irin son da nake mata bazan matsa mata akan dole saita soni ba, dan bazan iya auren macen da bata jin wani abu a kaina ba, am not dat selfish, koda sonta zai kashe ni bazan matsa mata dole ba dat Why na yanke decision akan inbar kasar ko zan manta komai duk da nasan ba abu bane mai sauki, but I will try, domin gaba daya bata san ganina kaman yanda na fahimta indai nesa da ita da zanyi will make her happy, I will do anything just to c her happy .... Dan shuru yayi domin jin zafin da kirjinshi yake yi, Abdul ne ya tabashi tare da fadin karka damu Man zan mata magana and I knw baza tayi rejecting dinka ba, abunda naji dadi shine ka fahimci abunda Mum take nuna maka akan aysha din,wanda tun farko kaki ka fahimta saida lokaci ya kure but i will try inga komai ya koma normal insha Allah....... Toh fah ku biyoni kuji ynda zata kaya...



Taku maryam obam😘


*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









165to170







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*










Dan murmushin karfin hali yayi tare da fadin I wish so, abdul yace plz Man kabar maganan tafiyan nan, I promise zan Kawo ma karshen duk wani damuwanka, but saika tashi ka fara komai kaman da zaka sami aysha tunda naga ka fada sosai, wani irin kallo A Majeed yayi mishi tare da fadin bana tunanin haka domin she really hate me, abdul yace kiyayya na zama so ai kaima gashi ka gani tunda gashi ya faru akanka, lumshe ido Am yayi tare da fadin hakane but sai nake ganin kaman...... Abdul ya katse shi da fadin karka damu just kawai kayi Cancel tafiyan ka, A Majeed girgiza kai yayi tare da fadin No Abdul dole inyi tafiyan nan gobe, Abdul Shuru yayi yana tausayin abokin nashi, tashi yayi tare da fadin bari ni zan wuce sai gobe zan shigo, A Majeed yace flight din 6 zanbi zadai muyi waya kawai, abdul yace tare da kokarin fita daka dakin muryan A Majeed yaji yana tambaya ya wannan yarinyar da kake so da ta taraba dinnan, Abdul wani iri yaji amma saiya dake yace tayi aure, yana fadin haka yabar dakin, A majeed gaba daya ya kasa bacci sai juye2 yakeyi tare da tunanin indo wanda yayi kokarin ya cire amma ya kasa.










Haka itama ta gefen indo din sai kaiwa da komowa take a daki, tama rasa maiya kamata tayi, gaba daya kanta ya kulle zuciyarta ta tunkushe da tunani kala2 tama rasa maiya kamata tayi,wani hawaye taji yana zubar mata tare da fadin Allah sarki mahaifiya mai dadi yau inda mahaifiyata na raye da itace zata zamemin abokiyar shawara amma gashi yanzu na rasa mai bani shawara, kwanciya tayi akan gadon dakin tare da lumshe ido, magananta da yazeed ne yake ta dawo mata, a halin yanzu Tana da bukatan hutu wanda Tana ganin yin auren ne zai Kawo Mata Karshen duk wani wahala da take ciki, sai dai kuma Tana da bukatan ta auri wanda take so yake sonta, mai yasa nayi saurin amsa ma yazeed bayan banajin wani abu a kanshi, wata zuciyar tace haba aysha karki Manta da cewa kin amince mai kuma ya yarda da hakan, kodan abunda yama dan uwanki aiya kamata ki soshi, wani hawaye taji yana zubar mata yanzu idan na amince mishi A Majeed fah ya zanyi Dashi? Anya banyi butulci ba, zuciyarta taita tuno mata abubuwan da suka faru a baya, gskiya Mum uwace da babu irinta a kullum ina neman hanyar da zan saka mata da irin abubuwan da tamin na alkhairi a rayuwa na, nan zuciyarta tace inko hakane ki yarda da bukatan danta domin shine babban alkhairin da zaki mata sannan hakan zai sata farin ciki, kaita girgiza tare da fadin Mum hakan bazai sa taji dadi ba tunda ta nuna itama bata sona dashi, kuma ta fadamin hakan, lokaci daya kuma ta tuna maganan da taji Mum da Dad nayi inda Mum ke fadin nima harga Allah ina son aysha da A Majeed sai dai hakan bamai yuhuwa bane, kenan Mum tana sona Da A Majeed? Toh mai yasa ta nunamin a gabana bata sona dashi? Gaba daya kanta ya kulle tama rasa abunyi, ranan dai bacci barawo ne yayi gaba da ita.










Washe gari kaman yanda Dad yace haka akayi, A Majeed ya danji karfin jikinshi duk Da zuciyarshi a tunkushe take dason ganin aysha, amma babu yanda ya iya dole ya tafi, itama ta gefenta tunda ta tashi da asuba tayi sallah, sai tunani take tayi kala2, tsintar kanta tayi dason zuwa kitchen dan ta hada breakfast tasan A Majeed zaici indai tayi, tunda ta lura bawai wani abinci yake ciba, koba komai dan Mum ne dole in nuna kulawa Na a gareshi, ta fito zata kitchen shima a dai2 lokacin ya bude kofar ya fito, nan suka tsaya kallon juna,yaji dadin gnin nata, shine ya fara kawar da kanshi, ganin haka yasa taji wani iri, a hankali ta furta ya jikin ka?mai makon ya bata amsa sai matsowa da yayi gab da ita yana mata magana kaman mai rada amma ba radan bane kawai ciwo ne yasa muryan ta dashe, yace aysha am leaving now I just want to see you happy am leaving d country just to c you happy, sai dai all I want u to knw is...... Dan Shuru yayi kaman yana nazarin abunda zaice dan ja baya yayi kadan tare da kallan fuskanta idanta a lumshe kura mata ido yayi tare Da yaba duk wani abunda ke jikinta yace just keep dis on ur mind dat I love you, my life is nothing without you, yana fadin haka yabar wajan a falo ya tarar da Dad shida Mum daka gani jiranshi suke yana tafiya ne kaman mai rangaji, Mum tace son dan Allah kabar wannan tafiyan ka zauna anan sai kaga Dr, dad yace a'a ki barshi yaje nama Dr magana idan ya sauka ma direct hspt zashi, har airport suka kaishi tare da daya daka security din dady suka tafi, babu abunda ya tafi Dashi na kaya dan yace acan zai siya, saida jirginsu ya daga su Mum suka dawo Gida, indo koh tunda taji ya tafi zuciyarta ta kara tunkushewa mai yake nufi ina zashi? Gaba daya ta shiga wani irin hali daki ta koma jiki a sanyaye, wayanta ta dauka ta kira Abdul bugu uku ya dauka tare da fadin aysha lafiya kuwa? Tace Abdul dan Allah A Majeed zaiyi tafiya ne? Abdul yace eh, tace ina zashi? Abdul yace aysha nima ban san inda zashi ba yayi tafiyan ne dan yayi nesa dake, cikin tashin hankali tace saboda wani dalili? Abdul yace bari zanzo anjima kadan muyi magana, yana fadin haka ya kashe wayan, indo sai juyi take akan gado to maina tsare mishi da zaiyi tafiya saboda ni? Haka taita tunani har wajan karfe Tara ta kara kiran Abdul yace gani a bakin Gate fito plz banso in shigo, tashi tayi tasa hijab, sai kuma ta tsinci kanta dajin kunyan fita, domin bata san haduwa da Mum koh Dad amma hakan ta fito cikin sanda tayi Sa'a babu kowa a falon, ta fice a cikin mota taga Abdul, bude gaba tayi ta shige, bayan ta shiga ta gaidashi, amsawa yyi tare da fadin haba aysha ashe haka kike da riko ban Sani ba? Tace yaya Abdul Mai nayi? Yace A Majeed duk ya fadamin abunda ya faru, haba aysha mai yasa bazaki iya yafe mai ba bayan ya roki gafaran ki, karfa ki manta ko Allah muna masa laifi ya yafe mana sai mune zamu ce ba zamu yafe ma wani ba danya mana abu, ko badan shiba aiko dan Mum yaci albarkacinta, aysha nasan waye A Majeed tunda kikaga ya shiga wannan halin har yana rokanki akan ki yafe mishi wlh duk abunda ya fada dagaske yake har cikin zuciyanshi, aysha ina sonki Da Abdulmajeed domin shine wanda ya dace dake koh kin san saboda sanki yasa yake wannan ciwon? Har yabar kasar nan dan yace bakya son ganinshi a kusa dake, haba aysha aiko dan Mum zaki tausaya mai shine dan Mum fah guda daya data haifa bance dole kiso shiba amma ya kamata ki yafe mai, kuka ta fara Tana fadin yaya abdul wlh na yafe mai saidai bana tunanin zan iya aurenshi a karo na biyu saboda matarshi yaya abdul matarshi bata Da imani koh kadan har yau na kasa mantawa Da abunda tamin, amma indai Mum za tayi farin ciki zan aureshi, Abdul yace haba aysha ina ruwanki Da matarshi zamanta za kiyi koh zaki bari ne ta kara miki wani abu? Sannan idan kika amince da auren Mum sai tafi kowa murna, sannan bana So ki aureshi saboda Mum dan soyayarshi zaki aureshi kunya taji tare Da dan rufe ido tace yaya Abdul na yarda zan aureshi, abdul yace Alhmdlh, Allah yasa hkan shine alkhairi wannan karan ba zakiyi dana sani ba insha Allah, nan ta bashi labarin gnin yayanta ya taya ta murna sosai inda ya bukaci ta bashi number din dan uwan nata domin ya kirashi, bayan ta bashi ta fita tare dayi mishi sallama, koda ta koma dki kuka tasa domin tunawa da alkawarin da tama yazeed, anya bazai ce ta yaudare shiba? Sai dai bata jin komai a kanshi hankalinta yafi kwanciya da auren A Majeed duk da shima din bawai Tana sonshi bne dan Mum da yayanta Abdul zata koma gidansa, cikin wannan halin Mum ta shigo ta ganta, cikin damuwa take fadin aysha Maiya faru? Kunyan Mum ne ya kara kamata cikin kuka tace Mum dan Allah ki yafe min na yarda zan koma gidan..... Shuru tayi domin jin nauyin maganan da take son fada, Mum tace aysha gidan wa? Rufe fuska tayi tace gidan A Majeed, Mum wani irin farin ciki ne ya ratsa ta, amma saita ce mata aysha karki yanke hukunci da sauri ko dan tunanin wani abu, rayuwan aure anayi ne na har abada bawai ace yau anje an dawo ba, ya kamata ki nutsu, tace Mum har cikin raina na yanke wannan hukuncin, Tana fadin haka ta tashi ta shige toilet Da sauri, Mum dadi ne ya kamata, tashi tayi tabar dakin dan ta fadama mijin nata dake fushi akan Mum ce ke zuga aysha din, a daki ta sameshi yana danna śystem, zama tayi kusa dashi Tana fadin maganan bikin aysha da A Majeed sai ayi ma dan uwanta magana ayi komai cikin watan nan, kallonta yayi cikin mamaki tare da fadin ban gane ba, nan ta fada mishi yanda sukayi da aysha din tare da fadin abunda yasa kaga naki bada goyan baya bawai dan bana son auren bane saboda yarinyar zata ga bamu mata adalci ba,zata ga kaman munfi san namu akanta, kadai ga abunda ya faru a baya ,Dad yace hakane kin san ganin halin daya shiga yasani shiga damuwa, tunda ta amince yanzu Alhmdlh, sai ayi komai Mum tace hakane, Dad yace saiki amso min number din dan uwan nata in nemeshi, Mum tace ok tare Da fita, dakin indo ta koma ta ganta itama zata fito, tace ina zaki? Yaya yusuf ne yazo Mum tace shine baki gaya zai zoba? Dama number dinshi nazo amsa, shigo dasu ciki, tace toh Mum, koda indo ta fita ta ganshi tare da yazeed jiki a sanyaye ta gaidasu tare da fadin su shigo yazeed idanshi akan indo yana ta sakar mata murmushi...




Taku Maryam obam😘


*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









170to175







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*










Har cikin babban falon gidan ta kaisu, nan masu aikin suka cika musu gaba da kayan ciye2, indo sama ta haura dan ta shaida ma mum sun shigo, bata karasa zuwa wajan dakin Mum dinba sai gata itada Dad sun fito, indo cikin jin kunya take gaida Dad, ya amsa tare da fadin sun shigo? Tace eh, nan suka koma tare, Yusuf yana ganin Dad ya tashi domin girmamawa Dad ya mika mai hannu suka gaisa sannan ya mika ma yazeed dake zaune yana kallonsu, Dad cikin sakin fuska yake fadin aysha koh ban tambaya ba wannan shine dan uwanki danga kama nan sai dai kin fishi fari, dariya duka sukayi sannan Dad yace ma yusuf ya zauna mana, bayan sun zauna yusuf ya fara yima Dad godiya akan rike mai yar uwa da sukayi, Dad yace haba2 ya isa haka ai babu zancen godiya tsakanin mu, sai dai fatan daurewan zumunci muke fata ya kasance na har abada, Mum tace hakane domin a gaskiya ban san rabuwa Da Aysha

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login