Advertisement
Showing 60001 words to 63000 words out of 85238 words

Chapter 21 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

63

yayi yasa a washing machine ya wanke tare da busar dashi, harya dawo dakin bata fito daka toilet ba, kaman ya shiga ya dubata amma saiya zauna tare da fadin bari ta fito, yayi wajan 10mnt zaune bata fito ba, tashi yayi ya nufi toilet din, ganinta yayi ta kife kanta da giwa tana kuka, cikin tausayawa ya nufeta tare da dagota ya daura mata towel, sannan ya fito da ita, akan gadon dakin ya zaunar da ita, wata rigan Bacci ya kuma dauko mata, ganin bata da niyar sawa yasa ya saka mata Da kanshi, sannan ya kwantar da ita tare da rufeta da blanket, har yanzu Tana jin zafi amma ba sosai ba, shima kwanciya yayi akan kujeran dakin yana mai Tuna abunda ya faru, lallai mata suna suka tara irin nutsuwan da yaji tare da aysha bai taba jiba a wajan Zainab, lumshe ido yayi yana mai kara godema Allah daya bashi aysha a matsayin mata bacci ne ya daukesu duka basu farka ba sai wajan asuba, tashi yayi tare da nufan gadon hancinta Ya danja a hankali ta bude ido, murmushi ya sakar mata tare da fadin tashi kiyi sallah, kokarin tashi ta farayi ya kamota tare da mikar da ita, Jan jikinta tayi daka nashi ta nufi toilet tana tafiya a hankali murmushi yayi shima ya fita daka dakin.











Tunda indo tayi sallah, ta kwanta bata farka ba sai yanzu, ganin haske ta wajan window yasa ta gane gari ya waye sosai, wayanta ta tuna ta tashi ta fara tafiya jinta tayi fayau kaman an cire mata wani abu a jiki, wata jaka ta dauko ta ciro wayanta ta kunna karfe 10:35 ta gani a hankali ta furta Ashe lokaci yayi nisa haka, ji tayi anyi hugging dinta ta baya dan kara ta Saki alamun jin tsoro, dariya yayi tare da fadin morning my princess, banza Dashi tayi sai kokarin kwatar jikinta takeyi daka nashi amma ta kasa, a hankali yace muje kiyi breakfast, dan nasan you r hungry, dan tsaki tayi wanda bata san zai fito ba, murmushi yayi tare da fadin idan kina fushi bakya kyau my baby, ganin yaki sakinta yasa ta yarda ta bishi duk da rigan bacci ne a jikinta, dinning suka nufa bayan ya taimaka mata ta zauna ya hada mata tea tare da zuba mata farfesun naman rago, da chips nd egg, tea din ta fara sha, bata wani sha Da yawa ba ta ajiye ba tare data kuma cin komai ba, idanshi a kanta yace inzo in baki? Daure fuska tayi tamau, yace I should come, ganin zai iya kuma inya taso saiya bata yasa ta girgiza kai tare da fadin na koshi, tana maganan ne kaman za tayi kuka, yace toh kici naman ko kadan, babu yanda ta Iya haka taci tana gamawa ta tashi tayi daki toilet ta fada tayi wanka, tana cikin shafa mai sai gashi ya shigo fake ya mata a bayanta tare da fadin I love you my Baby baki ta turo tare da fadin mayaudari amma a cikin zuciyanta, zama yayi akan gadon yana kallonta yanda take abu cikin nutsuwa, harta gama ta tashi ta dauki kayanta ta nufi toilet dan tasa, dariya abun ya bashi sosai, harta gama ta fito wata doguwar riga tasa na yar kanti ya mata Bala'in kyau komai nata ya zauna das a cikin rigan, ta daura wani karamin Gyale a kanta, tunda ta fito idanshi ke kanta wani irin sonta ke kara shiganshi, wayanshi ya dauko ya fara daukanta hoto hannu tasa ta rufe fuskanta, dariya yayi tare da tashi ya nufota riketa yayi tare Da zaunar da ita akan kujeran dakin, hannun nata ya cire a fuskan ya manneta da jikinshi ya fara daukansu tare, duk da fuskanta a daure yke sunyi kyau sosai, nuna mata ya farayi, kallo ta farayi ta gefen ido, sai yanzu taga hasken data kara, gskiya hafsat da inna maryam sun Iya gyaran jiki, ji tayi ya kamo hannunta tare da kiran sunanta yace aysha what r you thinking? Ajiyan zuciya ta sauke tare da kawar da kanta gefe, tashi yayi ya dawo ta inda tasa kan nata yace Baby plz Luv me back, kallonshi tayi suka hada ido tayi sauri tayi kasa da kanta, yace aysha I love you so much plz ki daina tunanin komai ki yarda dani plz, shuru tayi tana nazarin maganan shi, amma ta kasa yanke wani hukunci akan shi, har yanzu zuciyarta taki gane Maita yanke.









A Majeed yana nunama indo tsantsar So da kauna wanda a cikin tsanar da take mishi ya ragu sosai sai dai har yanzu bata jin sonshi a ranta, yau satinta daya a gidan kuma har yanzu wani abu bai kara hadasu ba, dan yana jin tausayinta duk da a matse yake yana dauriya ne kawai, yau dai ya yanke zai nemi hakkinsa dan ya gaji da hakurin, indo na falo ita daya sai gashi ya shigo da basket daka gani daka gidan Mum ne, kaman ta tashi taje ta amso amma sai taki, ajiyewa yayi akan dinning tare da nufanta yana fadin Baby come and hug me am so tired, kin tashi tayi harya karaso inda take, zama yayi kusa da ita tare da daura kanshi akan jikinta yana fadin Baby na gaji yau, jin tayi shuru bata da niyan mishi magana yasa ya fara shafa mata boob dinta yana wasa dasu, da sauri tace ka bari plz, dariya yayi tare da fadin Ashe za kiyi magana, dan turo baki tayi tare da kokarin dagashi daka jikinta, amma ta kasa, ganin haka yasa ta hakura, janyota yayi ya hade bakinshi da nata Ya fara tsotsa tun tana kokarin ta hanashi harta sake ta barshi dan bazata iyaba jikinta Ya fara weak, shiko gogan lokaci daya idanshi ya kade, a hankali ya zare mata zip din riganta da yake riga da skirt tasa, aiko gaba daya kirjinta suka bayyana, dan sometimes bata sa bra dan a tsaye suke kam, kara rudewa yayi tare da daura bakinshi a kai ya fara tsotsa yana wani irin nishi, haka itama ta gefenta tunda yasa bakinshi akan boob dinta takejin wani abu tun daka kanta har kasan yatsanta, wanda lokaci daya ta kasa gane tana wani duniyar ne, hannunshi yasa cikin private part dinta ya fara wasa Dashi, lokaci daya ta Saki wani irin kara Wanda bata san ya fito ba, tare da kara matseshi a jikinta dan tana jin dadin abun, saida ya bari ta fita hayyacinta gaba daya yayi babban aikin baka jin komai sai karan TV dana nishin su sai surutan da yakeyi, Ya dade yana abu daya kafin ya barta, kwanciya tayi akan carpet din parlour tana mai sauke ajiyan zuciya, shiko kallonta yake tayi yana kara sonta, ya dade yana kallonta har bacci ya dauketa, ganin kaman tayi bacci yasa ya dauketa yayi daki da ita tare da kwantar da ita akan gado, ya rufeta da blanket, toilet ya shiga yayi wanka sannan ya fito yana gyara gashin kanshi, wayanshi ne yayi kara dauka yayi yaga Zainab ce da number dinta na Nigeria, tashi yayi yabar dakin dan karya tashi aysha dinshi, har wayan ya tsinke ta kara kira dauka yayi tare da fadin Hello, tace Kana ina? Yace ina gidan amarya na, tace ok tare da kashe wayan, zama yayi a falon yana kallo, nocking yaji anayi da karfi,tashi yayi yana fadin waye haka bude kofar yayi yaga Zainab ce cikin riga da wando ta yafa wani shara2 Gyale, tace gani nazo saika zaba ni koh ita, janta yayi suka koma baya, tace dallah sakeni munafiki ai wlh yau sai anyita ta kare sai ka zaba Zainab ko yar iskan daka aura kaida kanka kasan nafi karfin in zauna da wata Mace a matsayin kishiya, indo dake daki taji kaman hayaniya sama2 da sauri ta tashi ta leka ta window ta hangosu cikin tashin hankali da tsorata tace Zainab, lokaci daya kuma ta Saki wani irin kuka tare da fadin abunda take gudu kenan gashi ya fara faruwa, toilet ta shiga tayi wanka amma har yanzu tanajin hayaniyar tasu muryan Zainab kawai takeji tana fadin ya barta ta shiga ciki, da sauri indo tasa kaya tare da yafa gyale, fita tayi daka dakin, direct waje ta nufa ta bude kofar amma taji a rufe alaman yasa key ta waje, zama tayi akan kujeran dakin tare da takaicin abunda yake faruwa taso data fita data Kawo karshen abun dan sai tasa ya saketa yau domin bazata zauna Dashi ba gwara ya zauna da zainab dinshi kawai dan ita bata son tashin hankali, jin shiru yasa ta leka taga dukansu basa nan, jim kadan taji ana bude kofar tashi tayi taga shine ya shigo abunda taso ce mishi saita tsinci kanta dajin nauyin fada dan wani irin kwarjini taga ya mata, yace aysha kiyi hakuri da abunda ya faru yana fadin haka ya wuce dakinshi, sai taji ya bata tausayi a karo na farko kenan, zama tayi a falon duk sai taji wani iri tama rasa abunyi.












Taku maryam obam😘

[11/12, 15:17] Hassan Atk: *💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









205to210







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*








Daura hannu a fuska tayi alaman tagumi, toh ni daba ni akama haka ba nashiga damuwa ina gashi, zuciyarta ta fara mata tunani kala2 mai yasa baibi matarshi ba ya dawo nan, ina ita zainab din take? Tana cikin wannan tunanin taji hayaniya tare da buga kofar parlour din, bude kofar tayi Zainab ce tare da sodoji mata Da maza, kallo ta karema indo dashi Tana mamaki dama balarabiya ya aura, lokaci daya ta cakumi wuyan indo tare da fito da ita waje tayi jifa da ita, indo tayi tangal2 zata fadi amma sai ta fada jikin motar dake pake a wajan, Zainab tace dan ubanki sai kin koma kasarku da kafanki shegiya yar Iska can kasar taku kin rasa mijin aure ne da zaki aure min miji yar Iska, saina canza miki kamanni yau sai kin san kinyi babban kuskure nufanta ta kuma yi, ta wanketa da mari a dai2 lokacin A Majeed ya fito yaja Zainab da karfi tare da wanke mata fuska da mari itama kallonshi ta tsaya yi da mamaki abunda bai taba yi mata ba, kai zama ta iya rantsewa da cewa A Majeed bazai iya dukan ko wace mace ba domin baya daya daka cikin maza masu dukan mata, hannun indo ya kamo tare da fadin bata ji miki ciwo badai koh? Indo babu abunda take sai hawaye tare dajin takaicin abunda Zainab ta Mata yau, jan hannunta tayi daka nashi dai2 lokacin Zainab ta kuma zaburowa tare da fadin nika mara A Majeed akan wata Mace ka Manta wacece ni? Dan murmushi tayi tare da fadin u will regret it, kallon sodojin da tazo dasu tayi tace ku kama min wannan yar iskan kuyi ta duka har sai nace ku barta, matan ne suka fara tawowa alaman zasu bigeta din, A Majeed Ya daka musu tsawa tare da fadin get out of My house tare da nuna masu hanya, Zainab tace baka isa ka basu command ba sai abunda nace kallonsu tayi tace what r you waiting? A Majeed yace duk wanda ya kara wani step a cikinku sai an cire mai uniform dukansu suka tsaya domin sun rasa maganan wa za subi, A Majeed yace wlh idan kika kara wani abu I will teach you a lesson, tace kai waye baka isa kayi min komai ba kuma wlh sai sunci ubanta yau, indo zagin da ake mata ranta ya baci sosai dan idan da ta tsaya ana zaginta yanzu ba zata bari ba, nufan Zainab tayi tare da fadin ki kwantar da hankalinki indai mijinki ne gashi nan dan baya gabana tana fadin haka tabar wajan A Majeed kam ranshi ne ya baci dajin kalaman indo din, Zainab kam shewa ta Saki tare da fadin toh kaifa kaji saika sallameta ashe yar Nigeria cema shegia zabiya, A Majeed Da ranshi ya baci sosai baibi ta kanta ba ya wuce ciki, itama binshi tayi tana fadin ai wlh sai ka koro shegiyar tabar gidan nan, zama yayi a falo ranshi a bace, yama rasa abunyi gaba daya ga ranshi dake a mugun bace, tace kafa tashi kaje ka koro wannan shegiyar, indo ce ta fito ta yafa Gyale a kanta Zainab tace Yar Iska sai kinyi dana sanin auren min miji, sadaka yalla, indo ranta ya gama baci hakurinta ya kare abunda tai niyan yi saita tsinta kanta da fasawa, tace dafarko naga dai baki ganeni ba bari kiji nice dai kishiyar ki wacce aka miki tun farko yanzu kuma gani a gidanki a karo na biyu, Zainab kallon Indo take tayi tabbas sai yanzu taga kaman wani uban ashar ta saki tare da fadin dama na dade ina neman irin wannan daman da Allah zai hadani dake yanzu kam gani ga ki, cakuman indo tayi da nufin dukanta indo ta tureta da karfi tare da fadin karki kuskura yanzu bada bane sannan inaso ki sani ni aysha zan zauna a matsayin kishiyarki indai hakan kike so in kuma kin canza zan zauna a matsayin yar uwarki, Zainab tace yar uwar uwarki A Majeed tashi yayi yaja hannun Zainab yayi hanyar waje da ita ta fara kokarin kwacewa tare da fadin ka sake min hannu, saida ya kaita waje ya rufe kofar sannan ya dawo yace ma sodojin subar mai Gida fita sukayi tana ganin an bude gate din ta kara shigowa Da gudu tayi hanyar falon shima rufa mata baya yayi yana shiga yaga suna kokowa ranshi ya kuma baci ya fizge Zainab din tare da wanketa da mari har biyu wani uban ihu ta Saki tare da fadin akan wannan yar matsiyatan ka mareni abdul-majeed wlh ka mari Bala'i ke kuma ki jira dawowa Na, fita tayi fuuuuu tabar parlour shima rufa mata baya yayi tana fita ya kalli mai gadin yace karya kara barin kowa ya shigo mai Gida, yace ok sir ciki ya koma koda ya koma baiga indo ba bai bi ta kanta ba dan yana fushi da ita itama dan maganan data fada yafi mishi ciwo akan abunda Zainab tayi ni mijinki baya gabana, kwanciya yayi akan gado tare da lumshe ido yana mai jin zafin abun, itama ta gefenta kuka take tayi tare dajin haushin shi domin tana ganin duk shine yaja komai tunda ya nace saiya aureta gashi abunda take gudu ta fara gani, wata zuciyar tace kai karki ce haka yana sonki dagaske baki ga yau harda marin Zainab yayi saboda ke ba, ya kamata ki sallama kema ki soshi domin son tsakani da Allah yake miki, lallai hakane tunawa ta farayi da abubuwan da suka faru Baya duk abunda Zainab tace baya iya ce mata No, tuna abunda inna Maryam ta fada mata tayi tace kinga yanda zaki kwace mijinki inma kina tunanin wai yana son matarshi fiye dake, ki dinga mishi abubuwan da kika san bata mishi...... Misali kaman wajan kwanciyan aure duk wani abu da kika san yana so ki dinga mishi karki ji kunya ki zama karuwa number daya sannan kisan yanda zaki dinga magana da miji kar kice waike ranki ya baci bari ki fada mishi komai ko kice bari in tura mishi txt din rashin mutunci karki kuskura namiji baya mantuwa koda kuwa kun shirya zai dinga kallanki da abun wata rana koda kun samu rashin fahimta sai kiji yana fadin ina jiran sakon cin mutunci dama Kin saba kinga mutuncin ki ya ragu, sannan keda kike da kishiya idan kika lura ranshi a bace yake kisan hanyar da za kibi danki faranta mishi rai May be itace ma ta bata mishi ran kinga idan kina sashi cikin farin ciki koda baya gidanki zaiyi ta Alla2 Ya dawo gareki sannan kullum kina cikin ranshi, sannan koda shine ya miki laifi bishi ki bashi hakuri shida kanshi zaiji kunya gobe zai rage abunda ya miki sannan karki Bari mijinki ya kwanta cikin fushi kice aishi ya sani babu ruwana yar uwa kinyi babban kuskure a duk sanda kikaga mijinki na fushi bishi ki rarrashe shi har kiga Ya sauko irin haka zaisa miji ya kara manne miki dan yana samun nutsuwa wajanki.... Ajiyan zuciya indo ta sauke tare da tashi ta shiga toilet tayi wanka zama tayi tasa wata night gown gaba daya jikinta ana gani ga wani irin rikitaccen kamshi da takeyi saida ta gama ta bude kofa zata fita saita tsinci kanta dajin Kunyan zuwa wajanshi komawa tayi ta zauna dan bataji zata iya, tashi ta karayi ta dauko hijab tasa sannan ta nufi dakin nashi budewa tayi a hankali kofar ta bude akan gadon dakin ta ganshi yayi rub da ciki, jikinta a sanyaye ta karasa inda yake a hankali tace in Kawo maka abinci? Bai bata amsa ba sannan kuma bai dago ba, kara nanatawa tayi in Kawo maka abinci? Dagowa yayi idanshi yayi ja yace aysha mai yasa bakya sona? Aysha bani da abunda kike bugata gana mijin da kike burin aure ne? Mai yasa kika tsaneni haka? Aysha dan Allah ki fadamin miye bani dashi wanda bakya sona? Shuru yayi tare da kifa kanshi a kasa, jikinta taji ya mata sanyi ta kasa furta komai sai zuciyarta dake faman buga mata, a hankali yace aysha nine bakya so right? Plz kiban amsa yau inaso in kawo karshen komai koda kuwa Kin yanke hukuncin rabuwa dani ne, ni na yarda sonki ya kashe ni zan miki abunda kike so indai zaki farin Cik....... Karan kukanta ne yasa yayi shuru tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login