Showing 75001 words to 78000 words out of 85238 words
Chapter 26 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
aiki, bayan ta shiga gefenta tayi wanka tare da zama dan ta shafa mai da sauri ta rufe dan taji warin mai din har kanta lokaci daya kuma tayi toilet tana kwarara amai a wannan halin ya shigo ya sameta hankali tashe yaita mata sannu idanta yayi ja dan wuya cikin tausayawa ya wanke mata fuska da baki sannan ya kamota suka fito waje bayan ya zaunar da ita ya koma toilet din dan ya gyara wajan, saida ya gama ya fito sannan ta kalleshi tace my one ka siyo min wani mai nawa yayi expire, yace ba akwai mai cikin akwatin dana miki ba tace oh na manta bude wardrobe yayi ya janyo mata akwatinan tare da budewa har ya bude namai ciki harda kalan wanda ta bude yasa ta amai shita dauka aiko Tana budewa ta jefar tare dayin toilet da gudu amai ta kuma sakewa shigo hankali tashe yace Baby muje hspt kai ta girgiza alaman a'a tace wannan ma yayi expire wari iri daya sukeyi dauka yayi ya duba expire date din yace da saura baiyi expire ba, bude mata Vaseline yayi na oil yace shafa wannan shiya fara shafa mata tace kaga wannan baya wari dariya yayi tare da fadin dama Mum tace yanzu abubuwanki ba irin namu bane sai kin zaba dariya tayi tare da ture mai hannu tace toh ba Baby dinka bane yasa na canza yace kar ayi ma baby dina shairi dariya ta Saki yanda taji yayi maganan wai nan ya kwaikwayeta ne, wayanshi ne yayi kara dauka yayi tare da karawa a kunne yace ok shigo bari ta sauko, kallonta yayi tare da fadin Zainab ce tazo gaidaki gabanta taji ya fadi amma haka ta daure tasa wata doguwar riga ta fito masu aikinta tace suje su jera mata kayanta cikin wardrobe na cikin akwati, a falo taga Zainab kallon2 sukama juna kafin indo tayi murmushi tare da fadin sannu da zuwa, amsawa tayi duk yanda taso ta boye kishinta saida ya fito domin taga indo ta kara kyau duk da sau daya ta ganta ran da sukayi rigima amma hakan bai hana ta gane ta kara kyau ba kishi kumallon mata bata wani dadeba ta tashi tare da fadin idan kina bukatan wani Abu saiki fadamin in Kawo miki dan nasan masu ciki akwai ciye2 indo dariya kawai tayi shiko gogan yaji dadi sosai Zainab na fita ta Fara kuka tare da alwashin saita zubar da cikin indo kota wani hali.
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
235to240
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Ranan Zainab taci kuka tare da tunanin hanyar da zata salwantar da cikin indo domin tunda ita bata haiyuba haka indo ma bata isa ta haiyu ba sai dai kowa ya rasa a hakan ma yata Kare balle ace aysha ta haiyu tsanar indo take taji tare dana Mum wacce take ganin duk ita ta shirya komai dake faruwa yanzu a hankali ta furta saina rabaki da dan naki inga ta tsiya haka taita kuka Tana sambatu
Indo kam duk wani kulawa Tana samu wajan mijinta da mum sai Zainab da itama take nuna mata ta2 irin kulawan duk da indo bawai ta saki jiki da ita bane, A Majeed yana lura da yanda aysha keyi ma Zainab ranshi nadan baci komai Zainab ta Kawo Mata bata ci domin ita ba yarda tayi da ita ba domin wanda ya kika da safe dan yace yana sonka da yamma karyane yaudara ne kawai, indo na zaune a falo Tana cin dankalin hausa dafaffe yasha mangyada da yaji sosai, A Majeed ya shigo kallonta yayi tare da nufanta ya kwace kwanon yace haba aysha wannan man gyadan da yajin yayi yawa bakya tunanin zai iya sa miki wani ciwon daban? Tace ni babu abunda zai samin dan Allah ka bani inci wlh yanzu fa na fara ci kuma tun jiya nake son ci sai yanzu na samu, yace gskiya bazan baki wannan abun kici ba, hawaye ta farayi tare da fadin nifa kasan yanzu ba komai nake ciba idan wannan abun ya fitar min a rai ban san Mai zanci ba yanzu, ido ya kura mata tare da share Mata hawayen fuskanta yace toh naji amma oil din yayi yawa da yajin bari a Kawo miki wani, tace ni wannan nake so babu yanda ya iya haka ya mika mata ta Fara ci kaman Tana cin nama har wani lumshe ido takeyi dariya ma ta bashi yace Baby ki barshi haka ai kinci da yawa, ido ta dan zaro tace nifa banci sosai ba da sauri ta fara ci dan kar yace zai amsa dariya yayi tare da fadin ci abunki a hankali, kitchen ya nufa tare da samun masu mata aiki yace su daina cika mata mai da yaji cikin abinci sukace ita da kanta take sawa yace toh su dinga fada mata yayi yawa in zata sa sukace toh, falon ya dawo yace Baby ban san kina shiga kitchen komai kike So kiyi magana a baki kinji kai ta daga alaman eh, saida ta cinye ta Fara kokarin shanye mai din ya tashi ya amshi plate din tare da fadin ya isa haka baki ta turo yasa hannunshi akan bakin tare da fadin wannan bakin ya koyi kwadayi dariya tayi shi kuma yakai plate din kitchen, bayan ya dawo tace yaushe zamu garin namu? Wani irin kallo ya mata tare da fadin ba yanzu ba,tace mai yasa? Yace taya zan bari kiyi tafiya kina dauke da babyna, tace wato nice baka so koh? Hancinta ya lakuta tare da fadin kinfi kowa sanin ina sonki Baby, kawai ban san muyi tafiyan ne yanzu tunda kina da ciki kiyi hakuri har ki haiyu sai muje, kinga hakan ma yafi koh, tace duk yanda kace ni mai biyayya ce, yaji dadin maganan ta tare da fadin Baby kwana biyu ban duba babyna ba ya kamata muje aban mu gaisa, dariya tayi tare da rufe fuska dan ta gane nufin shi Kin tashi tayi ganin yanda yake mata gashi masu aikinta zasu iya shigowa duk da in yana nan basa zuwa falon sai ya fita suke gyarawa amma tasa Su mata alale tasan zasu iya shigowa su gansu dan haka ta mike tayi daki shima ya rufa mata baya, suna shiga ya fara kissing dinta tako ina tare da shafa mata jikinta har suka kai gado kwanciyar da ita yayi tare da cire mata rigan jikinta yasa kunnenshi akan cikinta yana fadin Hello Baby is ur dad say hi to ur daddy dariya ta farayi ganin yanda yakeyi jin bakinshi tayi akan boob dinta yana tsotsa kaman swty ido ta lumshe daka nan akai mai gaba dayan saida suka dawo cikin hayyacinsu sannan sukai wanka tare tun Tana jin kunyan yin wanka Dashi harta daina dan ta saba yanzu *Note yin wanka tare da miji yana kara muku son junanku sosai yar uwa a cire kunya maganan aure babu kunya in kika tsaya jin kunya zaki dana sani domin duk ranan da mijinki ya kara aure ya auri wacce take mishi abun da bakya mishi kin bani*
Zainab duk yanda taso taga cikin indo ya zube tayi amma cikin na nan daram Dam har Magani tasha zuba mata cikin juice ta kai mata bata san indo bata sha ba, domin bata yarda da Zainab din ba duk da yanzu ta Dan Saki jiki da ita ba kaman da ba, cikin indo ya kara girma sosai idan ka ganta zaka dauka ya isa haiyuwa dan cikin yayi mugun girma sosai kuma kwata2 wata biyar yanzu cikin da yan kwanaki A Majeed siyan kaya yake tayi kaman hauka na mata dana Maza so yake ma su fita shida zainab dan ayi siyayya amma baya so abar aysha ita daya dan ko nan da can baya son yaje saboda aysha balle kuma yabar kasar yadai yanke zai sa a turo mishi kayan baby's kawai, bikin Abdul ya taso anata shirye2 indo kam jiki yayi nauyi A Majeed ya hanata yin komai dan karta wahala duk yanda indo taso tayi a bikin Abdul hakan ba dama dan jikinta yayi nauyi sosai duk da cikin ya mata kyau amma Tana jin nauyinsa sosai an mata scan ance guda daya ne Baby din, amma girman cikin naba kowa mamaki an Fara shagalin bikin Abdul A Majeed anata shirin zuwa kaduna dan daurin aure duk da bayaso yayi nisa da aysha amma tunda ga Zainab nan zai barta da ita hakan ko yayi ya shiga gefen zainab yace ta dinga kular mai da aysha karta bari tayi wani aikin wahala tace toh babu damuwa zaka dawo ka sameta lafiya, yayi dariya tare da shafa mata fuska sannan ya wuce bayan sunyi sallama da aysha sannan ya nufi kaduna shi daya dan Abdul shi yana can, tunda ya tafi indo ta rufe kofarta dan bata son damuwa domin tunda suka dawo gidan bai taba yin tafiya ba sai yau sai dai ya fita ko yaje office ya dawo, Zainab ce ta fito hannunta dauke da plate ta nufi gefen indo dashi nocking tayi tare da budewa taji kofar a rufe tsaki tayi domin tasa Magani cikin dambun da tasa a kawo mata dan taba indo ance idan mai ciki taci naganin wlh sai dan ya fito koda cikin yakai wata tara kuma babu rai zai fito, kara buga kofar tayi taji shuru komawa tayi Tana ta sambatu tare da fadin ai gobe na nan tsaki ta sake lokaci daya tunawa da tayi duka maganin ta juye bata rage ba wata zuciyar tace mata kiyi hakuri mana har dan yazo duniya sai ki bashi abu yaci ya mutu, da sauri ta girgiza kai alaman bazan iya ba haka taita tunanin hanyar da zata zubar da cikin.
Washe gari karfe daya da rabi aka daura auren Abdul da amaryan shi fatima Zarah a Sultan bello mosque dake kaduna, bayan an daura aurene akace za'a tafi da amarya hakan ko akayi ango ya dauki matarshi sauran yan uwanta kuma driver ya daukesu mota biyu suka je, shiko A Majeed ana daura auren ya wuce dan ya kosa ya koma yaje yaga ya Baby dinshi take, wajan karfe biyar saura ya isa Abuja, direct gefen indo ya nufa yayi nocking masu aikinta suka bude tare da gaidashi ya amsa tare da tambayan ina aysha sukace Tana ciki, haurawa yayi Sama ya ganta Tana ta faman Daura dankwali murmushi yayi tare da rike mata hannu kara ta saki dan bata zaji shi bane amma jin kamshin turaren shi da take mutuwar so da kuma dariyan shi yasa ta saki ajiyan zuciya tace shine baka fadamin ka taso ba yace sorry baby gani yanzu na dawo zaunar da ita yayi akan kujeran dakin tare da fadin bari in gaisa da Baby na nayi missing dinshi, dariya tayi dai2 lokacin yasa kanshi akan cikin nata yace Hello baby is ur daddy do you miss me dariya ta saki mai karfi tare da fadin tell your Baby yayi sauri ya fito yasa nayi girma sosai, hancinta yaja tare da fadin kin kara kyau sosai, tace an Daura aure lafiya ina ango? Yace lafiya qlau yanzu shirin dinner zanyi ma tace nima zani plz, yace nop babu inda zaki ban san yawo gashi bake daya ba tace plz bikin Abdul nefa dakyar ya yarda yace ta shirya suje bari yama Zainab magana itama fita yayi ya nufi gefen Zainab din ya ganta a zaune Tana danna waya daka gani chatting takeyi kallonshi tayi cikin kulawa tare da fadin saukar yaushe kuma? Yace ban dade ba ta mishi ya hanya bayan ya amsa da lafiya yace ta shirya suje dinner din Abdul tace yaje kawai kanta na ciwo nan ya fara tambaya tasha Magani tace eh haka ya fita ya barta tsaki ta Saki tare da fadin Magani bashi bane matsalata burina inga wannan yar iskan tabar gidan nan gaba daya, koda ya koma yaga aysha ta shirya cikin wani doguwar rigan material duk da batayi makeup ba tayi kyau sosai yace Baby kinyi kyau, ido ta lumshe lokaci daya kuma ta bude tare da fadin a haka yace Baby kona fada ko ban fada ba kina da kyau murmushi tayi cikin jin dadi domin Tana son yaban da mijinta yake mata kiran sallah magrib akayi yace bari inyi sallah sai mu tafi fita yayi itama tayi alwala tayi sallah tunda ya fita bai dawo ba har sai da aka kira isha'i yayi kafin suka tafi wani katon hall ne wanda an tsarashi sosai amarya itama tasha makeup tayi mugun kyau sosai A Majeed wajan Abdul ya nufa aysha na makale Dashi Tana dan tafiya dakyar nan indo ta mishi murna tare da addu'an zaman lafiya suka gaisa da amarya, nan suka sami waje ya zaunar da aysha shima ya zauna ana ta kida tare da ciye2 A Majeed ya lika musu kudi kaman ba gobe indo taso tayi likin itama ya hanata wai kar a bige mishi Baby haka ta hakura badan ranta yaso ba, sai wajan 10 A Majeed suka wuce taro dai yayi kyau anci ansha sai sam barka.
A kwana a tashi ba yuwa cikin indo ya cika wata tara Mum tace a dawo da ita gidan ta duk da baiso hakan ba amma babu yanda ya iya domin baya tsallake umarnin Mum, masu aikinta suke ta hada mata kaya ita kam Tana falo ita da gogan nata ya tamke fuska wai shi a dole baya so ta tafi, hannunta tasa cikin nashi tare da fadin my one plz kabar fushi kasan a gidan Mum zanfi samun kulawa sosai sannan idan Kana wannan fushin sai inga kaman bazan tashi bane inna zo haiyuwa da sauri ya toshe mata baki tare da fadin karki kara irin wannan maganan kin san bazan iya rayuwa ba tare dake ba, dan murmushi tayi tare da fadin haka zaka ce amma ni nasan zaka rayu ko bani danko yaranka zaka so ka rayu, yace aysha plz ki daina min wannan maganan bana son jinta, tashi muje in kaiki murmushi tayi kawai tare da tashi zata haura Sama yace ta zauna bari ya duba ko sun hada kayan haurawa yayi yaga sun gama hada komai yace Su fito Dashi sunkai komai mota sannan ta shiga gefen Zainab wannan ne zuwanta na farko, bayan sun gaisa indo tace Zan tafi gidan Mum nazo muyi sallama idan Allah yasa na tashi toh in kuma ban tashi ba ki rike min yara na amana dan Allah hawaye ne ya zubar mata a ido da sauri ta fita Zainab kam jikinta itama yayi sanyi, ta kasa ko motsi duk yanda takai da kin indo ba zata so ace ta mutu ba burinta kawai tabar mata mijinta, A mota ta sameshi yana jiranta ganin Tana hawaye yasa ya fara fada haba aysha wai miye haka ne mai yasa kike son tadar min da hankali ne plz ki barni haka inji da abun da yake damuna mana, shuru tayi Tana ajiyan zuciya ganin haka yasa ya fara rarrashinta tare da fadin aysha idan Mace zata haiyu bashi bane wai mutuwarta duk da yana da kyau mutum ya dinga Tuna mutuwa koda yaushe irin yanda kike yi yanzu baki san zaki Iya sa rayuwa na cikin wani hali ba aysha koh kin dauka son da nake miki wasa ne, wlh aysha ban taba jin son wata Mace ba kaman yanda nake jin sonki bana tunanin zan iya doguwar rayuwa ba tare dake ba Dan Allah aysha ki bar wannan maganan in baso kike ni in fara tafiya ba, shuru tayi ba tare da tace komai ba jiki ba kwari ya tada motar babu Mai cewa wani abu haŕ suka karasa gidan Mum, bude kofar tayi ta fita shima binta yayi a baya har cikin falon gidan mum na zaune ita da Dad suna fira sai gasu sun shigo mum tace sannu aysha ganin idanta a kumbure gashi yayi ja yasa ta gane tayi kuka tace aysha maiya faru dake haka, A Majeed yace Mum aysha nason sani cikin damuwa tun dazu take ta fadin wai kaman ba zata tashi ba shuru yayi yana hawaye da sauri yabar falon Mum da Dad suka bishi da ido Mum tace haba aysha ki daina fadin haka zaki tashi insha Allah dan murmushi tayi tare da gaida Mum da Dad suka amsa cikin kulawa sannan Mum tace ki zauna mana, zama tayi dakyar tare da tunanin halin da mijinta yake ciki yanzu, a yanda takeji Tana ganin kaman zaiyi wuya ta rayu domin ita tunda ta zama Dr tasan wahalan da mata ke sha wajan haiyuwa take tsoran ta haiyu gashi yanzu haiyuwa yanzu ko anjima ko gobe wani hawaye taji ya zubo mata tare da tausayin yaranta idan akace yau ta mutu bata raye wani irin rayuwa za suyi tunawa da tayi da rayuwanta na baya wanda maraici ne yasa ta haka,shiko A Majeed mota ya shiga amma ya kasa ja sai hawaye da yake ta faman yi sai driver mum ne ya kaishi Gida gefen Zainab ya nufa a falo ya ganta Tana hawaye Tana ganinshi tayi hugging dinshi Tana fadin komai dai lfya koh?wayanshi ne yayi kara dauka yayi yaga Dad ne yace son ka samemu asibiti aysha zata haiyu Da sauri yace toh Dad gani nan kallon Zainab yayi yace zani hspt aysha zata haiyu da sauri tace bari in dauko Gyale muje tare da sauri tayi daki jim kadan sai gata suka fita tare shine mai tukin kaman zai tashi Sama har suka karasa hspt din, koda suka karasa Tana