Showing 42001 words to 45000 words out of 85238 words
Chapter 15 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
nata dan ta faranta ma bare, wani hawaye ya kuma zubar mata mai zafi dan harga Allah bataji zata Iya aurenshi a karo Na biyu domin har yanzu ta kasa cire abunda ya faru a ranta ,jin kaman yana magana Yasa takai kunnenta dan taji mai yake fada dayan hannunshi yasa ya riketa dole yasa ta kwanto a jikinshi wanda maganan da yakeyi kaman mafarki ne tunda bacci yakeyi, wani irin kasala taji ya kamata ta fara kokarin tashi amma sai taji ya kuma rikota yasa dayan hannunshi ya rungomota dakyau kirjinta ya shiga bugawa da Sauri........
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
155to160
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Saukan numfashin shi take taji akan fuskanta, fuskanshi ta kalla ta gefen idonta amma taga idonshi a rufe alaman dai bacci yakeyi bai san abunda yakeyi ba, dan ajiyan zuciya ta sauke tare da rike dayan hannunshi ta sauke daka rikon da yayi mata, tazo zata sauke dayan taji yana magana kadan2 saida ta saurara dakyau taji yana kiran sunanta Aysha I really love you, da sauri ta cire hannun nashi daka jikinta ta tashi ta koma kan kujeran dakin Tana mai sauke ajiyan zuciya, kanta ta kifa a kasa tare da lumshe ido anya A Majeed ba gamo yayi da aljana mai sunanta ba, wannan wani irin So ne wanda ban taba jinsa ba sai a film koh a littafan hausa, dama hakan yana faruwa dagaske mutum ya zauce akan Mace kaman yanda marubuta suke fada a littafin su, wani irin hawaye taji yana zubar mata data tuna da maganan mum, gskiya Mum ta cika uwa ta Gari Wanda irinsu kalilan ne, wata uwar zata iyasa kowa cikin kunci dan nata yayi dariya, sai gashi ita Mum dan wani takeso yayi farin ciki akan nata, A Majeed yakai namijin da duk wata Mace zatai burin aure sai dai kash matarshi tafi karfinsa dan yana mata son da baya ganin laifinta koh kadan, wani hawaye ne ya kuma sauka a kan fuskanta tunawa da yanda ya kaskantar da ita a gaban matarshi wai yar aiki ya Kawo mata, jin karan bude kofar ne yasa tayi saurin goge hawayen fuskanta tare da dago kanta, Mum ce ta shigo dakin ganin fuskan aysha yasa Mum tace aysha lafiya Kuwa? Indo tace lafiya Mum? Mum kallon gadon dan nata tayi wanda yake bacci har yanzu dan Dr yace zaiyi baccin wajan awa 6, sannan ta maida idonta kan indo wacce take dan murmushin yake dan kar Mum ta zargi wani abu, Mum tace haba aysha ai duk wanda yaga fuskanki yasan kinyi kuka, nifa mahaifiyarki ce dan mai yasa zaki dinga boyemin damuwar ki, indo tace Mum babu komai kawai ina kukan murna ne yau naga dan uwana, Mum da sauri ta zauna kusa da indo Tana tambaya a ina? Nan indo ta bata labarin inda suka hadu, Mum ta taya ta murna sosai tare da fadin ina fata dai baza'a gujeni ba koh? Dan murmushi indo tayi a dai2 lokacin A majeed ya farka yana mika tare dayin salati, gaba daya idonsu ya sauka a kanshi wanda shima din su yake kallo, da sauri Mum ta tashi ta nufeshi Tana fadin son ya jikin naka? Dan murmushi yayi ba tare da yace komai ba, Mum ta tashi tare da fadin bari in kira Dad dinki, indo ganin kallon da yake mata yasa ta karaso wajan gadon Tana fadin sannu ya jikin naka? Yace ai baki damu da kisan halin dana shiga bah yana maganan ne cikin murya irin na mara lafiya dake jin jiki, za tayi magana su Mum suka shigo dakin, Dad zama yayi kusa da dan nashi yana tambaya son ya jikin naka hope ka warke? Kai ya girgiza alaman a'a yace Dad bana tunanin zan warke har sai na samu abinda nake So, Dad kallon Mum yayi kalan kinga ni koh, Mum yi tayi kaman bata jiba, Indo kuma wani hawaye ne ya zubo mata wanda yasa tabar dakin da sauri, ganin indo tabar dakin yasa Dad fadin kinji dai da kunnanki koh? Mum tace dan Allah kabar wannan maganan mu nemi lafiyar yaron nan kawai, A Majeed da baisan akan me suke maganan ba yasa ya lumshe ido, Mum matsawa tayi kusa Dashi tasa hannunta a gashin kanshi wanda duk ya yamutse tana shafawa bude ido yayi a hankali Mum tace son muje gidan mu saika zauna acan kafin muyi arranging na fita dakai waje, kai ya girgiza tare da fadin No Mum am OK ni nasan miye matsalata babu Dr din da zai bani Magani sai Dr aysha ki bari ita tai treatment dina, Mum taji tausayin dan nata sosai, duk da tasan shiya jama kanshi yanzu ga matar tashi nan da yake Bala'in so bata ma san baida lafiya ba tunda bata kirashi ba ko Mum taji ya yake ba, Mum taji zuciyanta na mata suya, mum dakyar ta lallaba shi akan yazo su koma gidanta toh, security din Dad ne suka kamashi akai mota dashi, wanda indo dake zaune Tana kuka a wajan ganin an fito dashi yasa hankalinta ya tashi, Mum tace mata tazo su tafi jiki a sanyaye tace ma Mum bari in dauko abu a ciki ledan maganin data shigo dashi ta dauko sannan ta shiga motor da Mum ta shiga wanda shima A Majeed din yana cikinta, Mum ce kusa dashi yasa kanshi a jikinta, gaba daya kamshin turaren Indo yake ji a motar duk da yasan tana ciki wani irin mugun sonta yake karaji yana shiganshi, sai dai yasan duk santa da yakeyi a yanzu bazai iya matsa mata akan ta soshi dole ba, itako indo gaba daya jikinta yayi sanyi, sai dai duk da haka bata tunanin zata iya aurenshi domin tana ganin kaman Akwai abunda yake shiryawa akanta shida matarshi tana ganin kaman So yake ta koma gidansa yaci gaba da azabtar da ita a matsayin yar aikin su shida matarsa da yake Bala'in so, wani hawaye ya zubar mata wanda tasa hannu ta goge da sauri dan kar a gani, idan A Majeed dake kwance cikin Mum yana ganin duk abunda takeyi wani iri yaji domin baya son ganin damuwanta a yanzu, bayan Sun karaso aka shigar dashi har dakin da yake da, Dad bai shigo ba dan anata kiran sallah magrib ya tsaya yayi sallah, itama indo alwala tayi dan tayi sallah,bayan ta sallame ta tsinta kanta da yima A majeed addu'a akan Allah ya bashi lafiya, bayan ta shafa addu'a ta dauki wayanta da ledan Magani tare da sauran kayan aikinta ta nufi dakin, Mum na ganinta tace yauwa dama So nake naje nayi wanka da sallah tunga gaki bari ki zauna Dashi kafin in dawo, tace toh Mum, bayan fitan mum ne indo ta matsa kusa dashi tana fadin yanzu mai kake ji yana damunka? Yace ke, tace mene? Yace ina nufin kece matsalata aysha nasan ban kyauta miki ba, kuma duk wani hukunci da kika dauka akai na kinyi dai2 dan na fusknci hukunci fiye da abunda kike min a yanzu, sai dai ke a wajanki ba komai kike daukan hakan ba, amma ni a wajena hakan da kike min..... Dan shuru yayi alaman ciwo na damunshi kafin yaci gaba da fadin hakan zai iya shafan rayuwa na, da sauri ta kalleshi dan ta tabbatar shi dinne yake magana ganin ita yake kallo yasa tayi kasa da kanta, aysha a da ban taba tunanin zanzo wata mace ba sai zainab, amma a yanzu Allah ya jarabce ni da sonki wanda ko Dashi aka barni na horu ban taba jin kishin wata Mace ba kaman yanda nake jin naki sai yasa na bada aikin gina miki asibiti dan banso kina aiki a karkashin wani namiji sai dai ayi a naki, dan shuru yayi yana kallonta ganin Tana hawaye yasa yace aysha dan Allah ki yafe min koh Allah muna masa laifi ya yafe mana, jikinta yayi mugun sanyi ganin ita yake kallo ysa ta daure tace zan gwada maka VP in gani ko yyi normal, dan murmushin yake yyi tare da fadin No ki barshi kawai bana bukata, kallonshi tayi taga idonshi a rufe, tace lafiya shine komai mai yasa kake son horar da kanka da ciwo? Idonshi a rufe yace bani nake son horar da kaina da ciwo ba kece kike neman horar dani da ciwo aysha ko kin san sonki zai iya zama ajalina? Bazan iya rayuwa in ganki da wani namiji ba Face ni ba, cikin siririyan muryanta da tasha kuka tace A majeed ni nasan ba sona kake ba akwai abunda kake nufi dani amma daka yau ina tunanin zan bar gidan nan May be idan nayi nesa dakai zaka tashi, amma ina rokan ka da kabari in duba ka,jin yayi shuru yasa ta matsa kusa da gadon tare da zama akai bude ido yayi wanda suka hada ido wani irin shock taji tayi saurin kawar da kanta gefe, yace Aysha keda za kiyi nesa dani mai yasa kike son dubani? Baki damu dani ba mai yasa kika damu da ciwo na? Aysha kiban amsa? Tace saboda ina son ka warke kaci gaba da rayuwa kaman da dan Allah karka kara tambaya na ka bari in duba ka, yace bana bukatar wani koh ke ki duba ni, har sai kin fada min amsan tambayar da zan miki, jin hanunshi tayi cikin nata wani abu taji tun daka sama har kasa, kokarin cire hannunta tayi daka nasa amma ya rike sosai dan haka ta hakura ,yace aysha ki kalleni ki fadamin cewa bakya so na, indai kika min haka na miki alkawarin zan cireki a raina har abada tare dayin nesa dake, kuka ta fara mai sauti gashi hannunta yana tare da nashi babu daman tabar wajan, shiko jin kukan yake har cikin ranshi amma babu yanda ya iya dole yana bukatan amsar ta,cikin kuka tace dan Allah ka sakemin hannu, baice komai ba haka kuma bai saki ba, Dad ne ya shigo dakin ganin Dad yasa ya sakar mata hannun to tashi tabar dakin da sauri tana kuka, dakinta ta nufa ta fara hada kayanta domin bazata iya ganinsa a hakan ba kuma ba zata iya yarda da abunda yake bukata a wajanta ba duk da har yanzu ta kasa gane mai zuciyarta to yanke akai amma d Best tin shine tabar gidan cikin daren nan hakan zai bata daman ci gaba da rayuwa cikin salama shima idan yaga ya daina ganinta tasan zai tashi yaci gaba da rayuwa.... Hmmmm ku biyoni sannu a hankali
Taku Maryam Obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
160to165
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Gaba daya ta gama sa abunda zata bukata cikin akwati, duk da ba komai ta dauka ba, fita tazo yi amma saita tsinta kanta da kasa bude kofar dakin, domin tunanin alkawarin da tayi ma Mum ya fado mata, bani da yawan dangi koh yara, naso ki zauna dani har abada sai dai hakan bamai yuhuwa bane dan za kiyi aure May be Ma mijin da kika aura ya hanaki hulda dani, sakan akwatin tayi tana kara rusar kuka, tunawa tayi da amsan da taba Mum, bazan taba barinki ba mum duk mijin dazan aura dole ya soki a matsayin Mum dina, zama tayi a wajan tana kuka gwanin tausayi, mai yasa talaka bashi da gata mai yasa wanda bashi da iyaye yafi shiga irin wannan matsanacin rayuwan mai yasa, A Majeed mai yasa kake son Sani cikin kunci koda yaushe mai yasa maina maka, ni nasan bawai dan kana sona dagaskiya kake wannan abunba, kanayi ne dan wata manufa taka ta daban, dan shuru tayi kaman Tana dan nazari lokaci daya kuma ta lumshe ido hawaye na zuba jin karan wayanta ne yasa to bude ido Bros taga an rubuta da sauri ta dauka tare dayin sallama, bayan ya amsa yace sister lafiya Kuwa? Naji muryanki kaman mai kuka, dan murmushi tayi na karfin hali Kafin tace lafiya qalau bros, yace ya mai jikin da fatan dai da sauki koh? Tace eh Alhmdlh da sauki bros, nan suka taba dan fira kafin sukai sallama akan cewa gobe zaizo gidan, yana kashewa kiran yazeed ya shigo wayanta, kaman karta dauka harya kusa tsinkewa ta dauka tare da fadin Hello, daka gefenshi shima ya amsa da fadin barka da dare, dan lumshe ido tayi tare da fadin barka kadai, yaka koma Gida? Ya amsa da lafiya dan shuru ya biyo baya, jin muryanshi tayi yana fadin aysha tun ranan dana ganki Allah yasa min sonki a raina, sai dai kuma a lokacin baki bani lokaci ba dan kin nuna kina sauri, amma haka zuciyata taci gaba da tunaninki duk da ban san inda zan kuma ganinki ba, sai dai nabar ma Allah komai sai gashi kuma ya kara hadamu cikin sauki wanda ina fata wannan karan zai zama shine hanyar da zamu kasance har abada, domin dai ni bada wasa nazo ba, dagaske nake aurenki zanyi sannan bana son ya dauki Lokaci mai tsawo, amma fah inkin amince dani, dan shuru yayi alaman yana jiran amsa, kanta ne ya kulle tama rasa abunda zata ce mai jin muryanshi tayi yana fadin ban samu karbuwa bako? Tace a'a yaya yazeed na amince Allah yasa hakan shine alkhairi, cikin jin dadi ya amsa da ameen, tare da fadin insha Allah zaki farin cikin kasancewa mata2 sannan dan Allah inaso kar aja da tsawo inaso ayi komai nanda wata biyu, bata iya cewa komai ba dan tama rasa abunda zata cemai tadai yardan mishi ne kawai badan tana sonshi ba ko Tana jin wani abu a kanshi ba, sai dai auren nashi zaisa tabar gidan nan gaba daya hakan zaiba A Majeed daman tashi tare da wargajewar wani abu da yake nufi a kanta, jin tayi shuru yasa yazeed ya kira sunanta tare da fadin gobe zanzo sai muyi magana, tace Allah ya kaimu tare da kashe wayan, Mum ce ta shigo dakin ta ganta a bakin kofa ga akwati a gefenta, kallon akwatin tayi sannan ta Kalli indo wacce fuskan ta tayi ja ga idonta duk ya kumbura dan kuka kun san farar Mace, Mum tace aysha lafiya kuwa? Maiya sameki wannan akwatin fah? Badai kina nufin Zaki barni bane,? Wannan tambayar duk a lokaci daya Mum ta mata shi, indo gaba daya kunya ya hanata magana dan bata so Mum ta shigo dakinba ba tare data maida komai wajanshi ba, mum ta tsugunna tare da kiran sunan aysha tace aysha mai aka miki da zakiyi irin wannan danyan aikin, koh wani ne ya bata miki rai? Indo kuka ta kuma saki tare da fadin Dan Allah mum kiyi hakuri wlh na rasa abunyi ne, gaba daya komai ya jagule min Mum dan Allah karki min wani fahimta ta daban.... Kuka yaci karfinta dan haka tayi shuru ba tare data karasa abunda tayi niyan fada ba, Mum janyota tayi jikinta Tana shafa mata baya tare da fadin aysha na fahimce ki, amma mai yasa ba zaki iya fadamin abunda yake damunki ba, saiki yanke hukunci dakanki? Cikin murya mai sanyi tace Mum A Majeed yana son kara bata min rayuwa Mum...... Shuru tayi dan tunawa dawa take magana, jin muryan Mum tayi Tana fadin aysha kiyi hakuri A Majeed bai isa yasa kiyi abunda baki niya ba, bashi da iko akanki, sannan ba zamanshi kike ba, kiyi shuru ki daina damuwa da komai kinji, bazan bari ya kara miki wani magana makamancin hakan ba, sannan idan kina da wanda kike So ki bashi dama ya fito kinji? Ido kasa amsa ma mum tayi dan gaba daya jikinta yayi sanyi, tare dajin kunya yau gashi Tana nuna bata son jinin Mum, wani hawaye mai zafi ya zubo mata sai dai hakan bazai sa ta canza ra'ayi ba, dan tasan bawai sonta yake ba, yaudara ce kawai irin tashi, shida yake da zee mai zaiyi da ita, gata yar masu arziki nida ba yar kowa ba, bazan iya kishi da itaba .... Wata zuciyar tace mata sai kace ba Mace ba, ai indai Mace ce ko wacece zaki iya zaman kishi da ita, ido ta lumshe ba tare data gamsu ba, Mum ce ta katse mata tunani tare da fadin tashi kije kiyi wanka ki sauko kici abinci, tashi tayi ta nufi toilet Mum kuma tabar dakin, ta nufi dakin dan nata dan taga ya yake ciki.
Mum bayan ta shiga dakin taga dady a kusa dashi yana dan mishi fiffita duk da akwai AC a cikin dakin, amma zufa yakeyi, cikin damuwa tace zafi yakeji? Wajan gadon ta nufa taga yanda yake zufa, hannu tasa a fuskanshi Tana share mai zufan fuskan nashi, tare da fadin son, idonshi dake lumshe ya bude, ya kura ma mum din ido, gabanta ne ya fadi ganin irin ramar da yayi lokaci daya, tace mai yake Damunka? Dad yace wannan wani irin tambaya ne fatima bayan kin san komai, tace dan Allah ka bari yaban amsa domin inaso inji da bakinshi kuma cikin hayyacinshi, Dad shuru yayi amma ranshi