Showing 48001 words to 51000 words out of 85238 words
Chapter 17 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
dan tana da hankali da nutsuwa, yusuf yaji dadin yaban da sukema kanwar tashi yanda ya fahimci su Mum mutanan arziki ne, nan Dad yace musu bismillah naga baku ci komai ba, Yusuf ya dauki drink Ya zuba a cup tare Da zubama yazeed shima, nan Dad yaita jan yusuf da fira Mum tace ya mai jego gobe suna koh?dad yace waye ya haiyu nan Mum tace matar yusuf Dad shima barka yamai, Dad saida yaga yusuf ya kammala sannan yayi gyaran Murya, a dai2 lokacin wayan yazeed yayi ringing ya dauka tare Da fita daka falon, Dad yace ina mai bada hakuri akan abubuwan daya faru a baya na rabuwan auren aysha da mijinta, wanda rashin fahimta ne yaja hakan, amma yanzu sun fahimci juna ina mai rokan a barta ta koma dakinta, yusuf dan shuru yayi tare da kallon indo wacce take ta kasa Da kanta ganin irin kallon da yake mata yasa tabar wajan da sauri, murmushi yayi wanda a dai2 lokacin yazeed ya dawo inda yusuf yake fadin cewa babu komai tunda sun yanke zata koma gidan mijinta Allah yasa hakan shine alkhairi ya basu zaman lafiya, nan mum ta amsa da Ameen, yazeed dai bai fahimci abunda ake nufi ba saida Dad yace banso a dauki abun da tsawo danshi yana London inda So samu nema a daura auren sai tabi mijinta yusuf yace duk yanda kuka tsara koh kuma ince yanda aysha din suka tsara gaban yazeed ne ya fadi tare da shiga cikin wani irin hali, bai kara tsinkewa bama saida yaji Mum tace aida an bari ya dawo sai ayi bikin koh? Dad yace a'a baza'ayi haka ba, nan Dad ya zaro kudi cikin aljihu yace mlm yusuf ga sadakin aysha nan,yusuf yace dady inaga da an bari dan abbana zan wakilta akai yace toh shikenan kayi tunani mai kyau Allah yayi albarka yusuf ya amsa da Ameen, yazeed gaba daya ya shiga damuwa mai yasa aysha ta amsa min bayan ta daidaita da mijinta? Wani iri yaji yana ji dan haka ya tashi yace ma yusuf inka fito ina mota, sannan yama su Mum sallama ya fice,dad yace zaizo wajan abban Yusuf din, shima yusuf din bai wani dadeba ya fito inda Mum ta kira aysha dan suyi sallama, a waje ta gansu yazeed Na cikin mota shiko yusuf na waje bayan ta fito Yusuf yace amarya bakya laifi, dan rufe fuska tayi tare Da fadin kai bros, dariya yayi tare da fadin dama naso muje taraba So yanzu sai mu bari bayan bikin ki koh gwara kije kina da aure nima ga ciwon abba bana son yin nesa dashi, tace toh yaya yusuf duk yanda kace hakan za'ayi, ya jikin abba din? Yace da sauki Alhmdlh tunda ya fara shan Magani yace ya rage jin zafin jikin, tace Alhmdlh bari ya gama sha muga yanayin jikin sai ku dinga Kawo shi gashin kafa duk sati din, Yusuf yace insha Allah, yazeed dake mota gaba daya ji yayi kaman yasa ihu dan takaici, sallama sukayi da dan uwan nata sannan ta leka cikin motar tace yaya yazeed sai anjima kai kawai ya daga mata, sannan yusuf ya shiga yaja suka wuce, ta shiga Gida jiki a sanyaye su Mum na falo ita da dad, Mum tace aysha ko kina da wani abun da zakiyi na bikin naku? Tace a'a Mum duk yanda kuka yanke nima yamin, Mum taji dadi sosai indo dakinta ta wuce Tana tunani kala2 wayanta ne yayi kara alaman shigowan message, budewa tayi ganin yazeed ne ta fara karantawa *haba aysha mai yasa kikamin haka? Ko kin san yanda naji a lokacin da ake maganan za kiyi aure a gabana bayan kin amince min, dama zaki iya yaudara na aysha namiji bashi da tabbas duk da ban san maiya hadaki Dashi ba har kuka rabu tun farko ba, komawa gidan nasa bakya tunanin zaiyi miki abunda ya faru baya, aysha mijinki da zaki aura bawai sonki yake ba inda yana sonki da tun farko bai rabu dake ba kiyi tunani akai karki lalata rayuwanki a banza* wani hawaye taji yana zubar mata akan fuska lallai maganan yaya yazeed gskya ne A Majeed bawai yana sonta bane tunda a baya ya gujeta bana tunanin yanzu zai soni sai dan wani manufa nashi, lokacin da nake indo na ya nuna yana jin kyamana tare da gudu Na saida yaga na zama wani abu zai nuna min So, anya banyi babban kuskure ba na komawa gidan nasa ba, kuka ta Saki mai sauti tunawa da tayi da sulaiman mai sonta tsakani da Allah tun bata wayewa yake sonta lallai Sulaiman kaine masoyina na gskiya duk da kaima ka juya min baya, amma har gobe ina jinka cikin raina, kiran yazeed dinne ya shigo waynta kashe wayan tayi gaba daya dan bata son damuwa dan shima Tana ganin bawai yana sonta bane inda Ya ganta a yanda take da tasan koh kallonta bazai yiba, kwanciya tayi tare dajin haushin yazeed din Da A Majeed wanda tafi tsana a yanzu, zazzabi ne ya rufeta ta kudun dune a bargo, Mum jinta shuru yasa ta shiga dakin taga halinda take ciki cikin tashin hankali take tambaynta lafiya kuwa ,indo tace Mum zazzabi nakeyi cikin rawan sanyi Mum tce bari muje hspt indo tace a'a zata sha paracetamol kawai Mum dauko mata tayi ta taimaka mata tasha, sannan ta koma ta kwanta, Mum ranan taita zirga zuwa dakin dan taga jikin indo din, babu laifi zazzabin ya saketa sai dai damuwa dake damunta domin tunda taga sakon yazeed taji bata san auren da zatayi duk da dama ta amsa ne badan tana so ba, anya bazan fadama Mum na fasa ba? Wata zuciyar tace karki kuskura ma ki kara wannan tunanin, ranan dai a daki ta wuni washe Gari dakyar ta shirya suka tafi sunan yayanta ita da mum, inda aka amshesu cikin mutunci Mum tayi ma baby siyayya da yawa,haka akaci suna yaron yaci sunan abban zaliha suna kiranshi Da irfan, indo jiki a Mace domin tunani taitayi Mum duk Tana lura da ita, amma ta bari sai sun koma Gida zata mata Magna indai auren ne bata so sai a fasa, koda suka dawo Gida mum ta sameta a daki ta zabga tagumi tace aysha bataji ba har saida ta tabata, tayi firgit, Mum tace aysha anya lafiya kuwa tun jiya da akayi maganan aurenki kika shiga wani hali dan Allah aysha idan bakya son wannan auren ki fadamin karkiji komai ko nauyi Na wlh bazanga laifinki ba duk hukuncin da kika yanke, aysha hawaye ne ya zubo mata tace Mum bazan taba kin jininki ba, koda kuwa ya yake mum kinmin abunda bazan taba mantawa Dashi ba a rayuwa bani da abunda zan saka miki Dashi Mum sai addua Mum tace ya isa haka,tare da rungume indo Tana sa mata albarka.
Yau alhamis kuma a ranan dady ya hadu da abban yusuf ashe sun ma san juna nan suka tattauna bayan saduwa inda dady yake tambayan abba maiya sameshi, abba yayi ajiyan zuciya tare Da fadin wlh jarabawa ne ya sameni na tura wajan rabi Da kwata na kudina a kawo min kaya har an shigo Da kayan costume suka rike wai an sami hodar iblis a ciki gashi driver din ya gudu, nida aka Kawo min motoci maiya hadani da wata hodar iblis, nan dady ya jajanta mishi tare Da fadin zaiyi wani abu a kai insha Allah, sannan Suka fata tattauna akan maganan daya Kawo su inda abokin dady Da sukaje tare ya bada sadaki abba yace gobe juma'a sai a daura auren, hakan koh akayi, Dad bayan ya koma Gida yake tambayan Mum sunyi waya Da A Majeed kuwa yakira? Tace wlh bai kira ba gashi babu number dinshi tacan Dad dan shuru yayi tare Da fadin gobe za'a daura auren nasu, Mum tace haba aida an bari an shirya, Dad yace No gwara a daura dan harna turama mutane Da txt kawai kiyi addu'a kawai Mum tace Allah ya sanya alkhairi yasa ayi a sa'a, Dad ya amsa Da ameen.
LONDON
A majeed bayan ya sauka direct asibiti ya wuce gado suka bashi ana kula Dashi, kwananshi uku ya dawo gidan da zai sauka tare Da Magani Da aka bashi, kwata2 baya son kiran koda iyayenshi dan So yake ya manta komai amma abun yaci tura dan kullum aysha Tana ranshi ganin kaman a nan din yafi tunanin nata yasa ya fara tunanin dawowa Gida, duk da yayi alkawarin yin nesa Da ita amma yaji bazai iya ba yadai yanke gobe zai dawo Gida ko zaiga ayshan shi yaji dadi.
Yau juma'a bayan an idar Da sallah juma'a aka daura auren A Majeed Da Aysha a central mosque dake abuja, daurin auren Da mutane da dama suka shaida ciki harda president dan shima Dad ya mishi bayani kuma ya hallara sai dai addu'a zaman lafiya.
Hmmmm muje zuwa
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
175to180
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Duk wannan abunda akeyi indo bata sani ba, balle shi A majeed din,bayan Dad ya dawo Gida yasa Mum ta kira mishi indo din, bayan tazo ta gaida mum ta zauna tare da dan takurewa Mum tausayinta take dan Tana ganin kaman bata san auren ta daiyi ne kawai danta faranta musu, duk ta rame, Dad ne ya katse Mum daka tunanin data fada yace aysha yau aka daura aurenki keda abdulmajeed, Dam taji gabanta ya fadi dan batayi zaton za'ayi auren a wannan lokacin ba, toh amma mai yasa aka Mata haka? Hawaye taji yana son zubo mata tayi saurin goge idon dan karya zubo, wayan Dad ne yayi kara ya dauka tare da fadin shigo mana yusuf, bayan Yusuf ya shigo ya gaida Mum itama indo gaidashi tayi ya amsa ,bayan ya zauna ya dauko kudi tare da fadin Aysha ga sadakin ki nan tashi yayi ya mika mata, tace a'a yaya yusuf ka barshi a wajanka, yace a'a wannan ba Hakki na bane naki ne, amsa tayi tare da zubar da hawayen da take makalewa, yusuf murmushi yayi tare da yima su Dad sallama, Dad yace a'a ya tsaya suci abinci, yace Alhmdlh yana So yaje yaga abbanshi ne, sallama yayi musu ya fita, indo tashi tayi tabi bayanshi itama, har wajan motarshi, tsayawa sukayi a gefe, ya kalleta fuskan duk ta cabe da hawaye, sunanta ya kira da fadin aysha kin san zaman aure hakuri ne, basai na fada miki miye hakuri ba ke zaki fadama wani ma miye hakuri idan kin tuna rayuwanki a baya, So inaso ki kara akan nada, dan Allah sis karki bani kunya mutanan Da alkhairi suke sanki ki duba yanda suka rikeki kaman yarsu ta cikin su, dan Allah a wannan karan kema ki nuna yar halak ce ta hanyar Hakuri da kawar da zuciya nesa, sannan nasa ayi oder din kayan dakinki duk da dady yace a barshi amma nafi son a kawo miki yace yasa komai a gidan dan wani saban gidanshi ne daya gina zaki zauna keda mijin naki, kayan idan an Kawo za'a ajiye miki a wani waje, Allah ya bada zaman lafiya, kuka yaci karfinta ta kasa magana ganin tana son karyan mai da zuciya yasa ya shige mota ya wuce yana tausaya mata, saida ta goge fuskanta sannan ta shiga Gida, a falo ta tarar da mum, har zata wuce Mum ta kira sunanta ta amsa Mum tace kizo kici abinci, kaman zata ce ta koshi komai ta tuna kuma ta nufi dinning ta zuba abinci kadan taci, baifi 3spoon taci ba ta tashi ta wuce dakinta Mum duk tana kllonta amma bata ce mata komai ba, koda ta shiga daki babu abunda take sai kuka domin tana ganin kaman da wani manufa Ya aureta lallai hakan nema maganan da yazeed ya fada mata, dafarko ya nuna baya sonta yanzu kuma mai zaiyi da ita, shida yake da kaman Zainab a Gida mai zaiyi da ita, haka taita tunani tana kuka.
Karfe biyar dai2 jirgin su A Majeed ya sauka a airport, mutane suka fara fita ciki harda A Majeed kallo daya zaka masa kasan ya rame ya kara haske da kyau, kaman balaraban kasar dubai, direct wajan motarshi ya nufa dan yama driver magana akan yazo Ya daukeshi, baya ya zauna security din dady na gaba, kai tsaye gidansa yace a wuce dashi, bayan sun karasa ya shiga cikin falon duk yayi kura, dan tsaki yayi dan baya son kazanta ko kadan, fita yayi ya shiga mota yace a kaishi gidan Mum din nashi, kai tsaye gidan suka nufa, wayanshi dake kashe a hannunshi ya kunna message suka fara shigowa har zai share sai yaga na Abdul dan haka ya bude, *man ya zaka tafi baka kirani ba har yanzu kasan bani da number dinka na can, To congratulation aysha an daura muku aure yau* da sauri ya kara karanta message din yana mamaki dan yasan basa irin wannan wasan da abdul, fita yayi daka motar tare da doka ma Abdul kira inda yaji line busy, tsaki yayi tare da kara duba message din da aka turomai duk na congratulations ne akan auren nashi, da sauri ya shige cikin gidan nasu dan yasan duk amsan da yake nema zai samu a ciki, babu kowa a falon dan haka ya haura sama direct dakin Mum ya nufa, mum na zaune akan gado tana waya, taga mutum ya shigo Da sauri ta kashe wayan tare da tashi tana fadin son, sai kuma tayi shuru tana dariya da sauri ta nufeshi tayi hugging dan nata tana fadin mai yasa baka kiramu ba son? Dan sakinshi tayi tana kare mai kallo tace son ka warke kuwa? Dan murmushi yayi tare da fadin da sauki Mum, ina Dad? Tace yana dakinsa muje hannunshi rike da nata suka nufi dakin mahaifin nashi, inda suka sameshi yana danna system, shima ganin dan nashi yasa ya tashi yana yar dariya irin ta murna, yace son ya jikin naka? Yace Dad bana tunanin zan warke har sai abunda naji ya tabbata, Dad Da Mum suka Kalli juna lokaci daya kuma suka kalli dan nasu, Mum tace mai kaji, babu kunya ko tsoro yace Mum aysha wai da gaske an daura...... Shuru kuma yayi tare da sosa kai, Mum ta sakar mai harara Dad yayi gyaran murya tare da fadin zauna son, gabanshi yaji ya fadi bayan ya zauna Dad yace son hakane yau aka mayar Da aurenku kaida aysha, wani irin ajiyan zuciya yayi har iyayen nashi naji, Dad yaci gaba Da fadin son inaso kaji tsoran Allah kayi adalci a tsakanin matanka, ka daiga abunda ya faru baya, da irin abubuwan da suka faru yanzu, aure ba abun wasa bane..... Dad dai yayi mishi nasiha sosai mai ratsa jiki, inda Mum ta amshe tare da fadin ka dai san bazan yarda a wulakanta min yaba koh, wlh idan naji wani abu saina saba maka, itama ta daura da nata nasihan, inda Dad ya bashi keys din gidan da zasu zauna, ya amsa yayi godiya mum tace tarewa kuma sai nan Da sati biyu, wani iri yaji danshi harga Allah yanzu yaso a bashi matarshi, anya zan iya jira har sati biyu kuwa, Dad ne ya katse shi da fadin naji ance kana gina asibiti? Kai ya dan sosa tare da fadin eh Dad na aysha ne bana So tana aiki a karkashin wani, Dad yayi dariya irin tasu ta manya yace hakane hakan yana dakyau, tashi yayi dan yaje ya huta Mum tace Gida Zaka tafi? Yace No Mum ina nan zanje in huta ne, tace badai a gida naba koh? Yace Mum can gidan yayi kura kin san babu kowa a ciki, Mum tace matar taka har yanzu bata dawo ba? Kai ya daga alaman eh dan baya so ayi mishi maganan Zainab din dan yana ciki da ita sosai tunda ta kirashi sau daya bata kara kiranshi bah, shima haka bai nemeta ba, fita yayi daka dakin Mum ta girgiza kai tare da fadin Allah dai ya kyauta Dad yace da akayi me? Tace ina mamakin irin wannan auren Na abdulmajeed, na rasa wani irin So yake ma Zainab da baya ganin laifinta baya iya kwaba mata idan tayi ba dai2 ba, Dad yayi murmushi tare da fadin ki kawar da idanki a kansu ki masa addu'a kawai, Mum tace toh Allah yasa mu dace, Dad yace ameen.
Koda A Majeed ya shiga daki murna yaitayi wai yau shida aysha suna matsayin mata Da miji, ikon Allah, wayanshi ya dauka ya kara kiran Abdul ringing daya ya dauka, abdul yace angon aysha yaushe ka dawo? A Majeed yace yau wlh Kana ina? Abduk yace ina gidana, A Majeed yace ya kamata kazo kasa ta fito in ganta, Abdul dariya yayi sosai tare da fadin kaida matarka, A Majeed yace plz ka bari ni nasan halin kayana sai an lallaba, nasan har yanzu bata sauko ba wai ya abun ya kasance ne ma wlh mamaki nakeyi, nan Abdul ya bashi labari, A Majeed wani irin nishadi yake ji tare da fadin Abdul wlh tunda naji an daura mana aure da aysha naji kirjina ya warke kaman an cire min wani dutse, Abdul dariya yayi sosai tare da fadin kace yau akwai cin amarci, dan tsaki A Majeed yayi tare da fadin Mum tace sai nan da sati biyu zata tare,ni yanzu kawai kazo ka daukeni muje inga gidan da Dad yaban in babu wani abu in kara dan yace yasa komai, abdul yace ok gani nan zuwa, yana kashe wayan aka kirashi da No