Advertisement
Showing 39001 words to 42000 words out of 85238 words

Chapter 14 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt

14 Mar 2026

57

145to150







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*










Kuka take sosai dan sake shi tayi ta dago da fuskanta ta kalleshi wanda idanshi na kanta shima tace mai yasa baka nemeni ba tsawon wannan lokacin yaya yusuf, Yusuf yace aysha, indo da sauri ya kara riketa yana hawayen murna dan sakinta yayi tare da fadin Alhmdlh, aysha.... Yama rasa abunda zaice murmushi take tayi tare da komawa ta zauna dan ta duba wannan bawan Allah da yake zaune akan kujera,dan kallonshi tayi tare da fadin Baba maike damunka? Matar tace hawan jini ne yake fama dashi kwana biyu yaki sauka na rasa mai yake tunani haka, dazu muna tsaye kawai ya fadi kasa, koda ya farfado ya kasa koda daga hannu... Ta karasa maganan cikin damuwa, nan indo ta tashi ta nufi inda mutumin yake ta dan dubashi, sannan ta dawo inda take tayi yan rubuce2 sannan ta kalli mutumin tace Baba ina yake maka ciwo, da baki yake magana amma baya iya daga komai nashi, yace gaba daya jikina bana jin dadinsa ji nake kaman jikina baya tare Dani, magani ta rubuta mai tare da fadin za'a dinga Kawo shi duk sati daya ana mishi gashin kafa domin jikinshi ne ya shanye amma idan akayi Sa'a ...... Matar kuka tasa cikin damuwa nan yusuf ya karaso inda take yana fadin kiyi hakuri ummi komai zaizo da sauki insha Allah zai warke, indo ta amshe da fadin insha Allah kawai abunda za'ayi yanzu shine ku dinga bashi Magani akan lokaci, sannan ku dinga Kawo shi duk sati dayan, duk wani abu da zai sashi tunani a kauce ma abun nan taita basu shawara shiko mutumin babu abunda yake sai hawaye, abun ya daure ma indo kai ganin dan uwan nata shima yana hawaye toh miye alakansu da wannan mutumin? Jin muryan yusuf din yasa ta dawo daka duniyar tunanin data shilla, yace Sis yanzu sai kizo mu tafi tare koh? Dan ya kamata ki dauki excuse, tace dama saboda duba wannan bawan Allah aka kira ni, nan suka fita tare wannan karan yusuf ke tura mutumin, har wajan jibgegiyan motarsu mai kiran jeep yusuf da yazeed suka kamashi suka saka shi cikin motar, matar ta shiga gaba yusuf wajan driver, indo suka shige baya ita da yazeed domin kalan jeep din nanne mai shigen seyana, mai kujera baya tsakiya da gaba, yazeed kallon indo yake tayi tare da lumshe ido yana jin kamshin turarenta a hankali yake jin sonta na kara kamashi gashi yau yana farin ciki sister din abokinshi ce duk da yana cikin rudani akan ya suka rabu, itako ta gefen indo murna take sosai na ganin dan uwan nata gefe daya kuma tana tunanin wani hali A Majeed yake ciki, jin an taka birki ana horn yasa ta kalli inda suke wani katoton Gida ne sukai parking lokaci daya mai gadi ya wangale Gate din suka shiga, Nan masu aikin gidan suke ta faman zuwa gaida Alhaji da matar tashi, yusuf bayan ya fito haka itama indo da yazeed, kama mutumin sukayi Suka shiga cikin katon falon gidan, har zasu kaishi ciki yace a ajiye shi a falo zaiyi magana hakan koh akayi wata yarinya ce ta fito kyakyawa hannunta dauke da Baby daka gani bata dade da haiyuwa ba, da sauri ta nufi wannan mutumin tana mai sannu daka gani babanta ne, Alhaji yace kowa ya zauna, zama sukayi su duka banda yazeed da yake musu sallama akan zai wuce, mutumin yace shima ya Zauna a gabanshi za'ayi komai, kallon yusuf yayi yace miye tsakaninku da wannan dr din ko itace kanwar taka? Yana magana ne amma daka ji yana jin jiki, yusuf yace eh kanwata ce abba itace indo da nake fada muku, yusuf ya kalli indo yace aysha ban taba tunanin zan sake ganinki ba a rayuwa tun da nabar taraba na shigo garin abuja na fara wanki da guga ina samun albashi duk da bawai yana isana bane tunda a ciki nake ci insha, domin basa bani abinci, gashi ina dan tara wani abu dan inci gaba da karatu, kullum da tunaninki nake kwana nake tashi gashi bani da ikon inje in ganki dan gargadin da mai Gari yayi min wanda shairi aka kulla mana ni dake wani hawaye mai zafi ya zubo mai a fuska, sannan yaci gaba da fadin gidan da nake wanki wata rana ina dakin da aka bani saiga matar mai gidan ta turo a kirani koda naje dan shuru yayi na wani lokaci kafin yace ta nema in bata hadin kai naki amincewa, na nuna mata hakan haramun ne tare da dan mata nasiha shuru tayi kaman ta dauki nasihar sai ji nayi tace wlh dole saina biya mata bukatan ta yana magana yana hawaye, da dai taga bazan yarda ba tasa masu gadin gidan suka Fara jibgata da yake sodoji suke gadin gidan, summin duka sosai ba tare da tace musu ga abunda nayi mata ba , mijinta baya zama washe garin ranan sai gashi ya dawo gari nan yasa a kamani a kara min duka dan shuru yayi yana kuka Kafin yaci gaba da fadin ranan na daku sosai har da karaya suka min wai naje ina son inma matarshi fyade, haka suka daukeni suka jefani cikin daki aka rufeni ga karaya a kafa da hannu, gashi babu abinci balle ruwa indo kuka tasa sosai dan tausayin dan uwan nata, yaci gaba da fadin Allah yasa inada sauran kwana a gaba, ranan dana cika sati suka daukeni suka jefar Dani a bakin titi tare damin kashedin karsu kara ganina, Ashe duk abunda ya faru lokacin da aka jefar Dani a idon Abba ne lokacin zai koma Gida nan yasa driver dinshi ya faka, dan a zaton shi yan yanka kaine suka kamani sukayi tsafi Dani amma ganin ina numfashi yasa suka kamani shida driver dinshi suka kaini asibiti nan Dr suke ta fada akan ya za'a bar mutum ya karye har a barshi Ya dauki lokaci ba'a daurashi ba, nan abba yaita basu hakuri, Dr ya fadama abba idan akayi daurin Allah yasa yayi abba yace dan Allah suyi ko nawa ne zai biya amma daurin yayi kyau, nan Dr suka ce babu damuwa gobe za'ayi, abba ya tausaya min ranan shiya koma Gida shi daya driver dinsa yasa ya kwana dani, washe gari sai gashi da matarshi da yarsu sunzo lokacin har an fara min daurin nasha wuya sosai lokacin harna gwammaci in mutu, haka akayi daurin na koma gidan abba ina zama ana jinya na, yarinyar abba wacce ita daya ya mallaka zaliha kullum tana dawainiya Dani ita da ummi, nayi zaman jinya sosai lokacin da aka kwance ni hannun ya gyaru amma kafar akace akwai matsala sai an sake min aiki, haka aka sake min wani aikin aka sa karfe a wajan nasha wuya sosai lokacin har zan iya cewa gwara na farkon ma, na jinyatu sosai, kuma duk wannan zaman da nakeyi a gidan abba bai san ko daka ina na fito ba, tunda ya tambaye ni iyayena nace mishi sun rasu bani da kowa, haka naita zama ana jinya Na, har Allah yasa na warke, lokacin ne nace zan tafi domin inzo in nema kudi inje inga yanda kike ciki koda kuwa za'a kashe ni tunda a lokacin na cire rai da duniya dan nasha wuya, Abba ya hanani tafiya inda ya nemi yasan daka garin dana fito ban boye mai komai ba na fada mishi harda abunda akamin lokacin daya sameni, nan ya tausaya min yace kar inje garin namu yanzu in zauna na wani lokaci a nan, haka naita zama yana sani cikin harkan kasuwancin shi na canji da saida motoci ganin yanda na rike Mai amana gashi na iya kasuwanci yasa ya kara sona gashi Mace daya Allah ya bashi bai kara haiyuwa ba yasa ya turani london karatu inda na karanta kasuwanci a nan muka hadu da yazeed komai tare mukeyi yazeed yayi min taimako sosai wanda ban san damai zan saka mishi ba, dan ya wuce abokina ya zama dan uwa Na, shekara uku na dawo Gida, cike dason inje in ganki lokacin dana dawo abba yaban jari sosai inda muka hada da yazeed duk da kudinshi yafi yawa ninkin nawa wajan uku, amma idan aka samu riba biyu yake rabawa yaban rabi shima rabi haduwan da nayi da yazeed yasa na samu kudi sosai domim bashi da mugunta ko kadan samun irinshi sai an tona....









Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*






*NA*


*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*




*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*






*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*


*WWW.maryamobamnovels.com*




https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/









150to155







*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*









Dan shuru yayi sannan yaci gaba da fadin lokacin da naje taraba direct gidan Mai gari na nufa lokacin bai ganeni ba, saida na mishi bayani yayi mamaki kwarai dagaske tare da bani hakuri akan abunda ya faru, nan yake shaidamin kinyi aure ya bani labarin yanda abun ya kasance nayi takaici lokacin sosai haka nabar garin ba tare da naje Gida ba, domin nasan har yau babu abunda ya canza daka zuciyar kawu akan kiyayyar da yake mana, duk da mai gari ya fadamin wanda kika aura hankalina bai sa ya kwanta ba lokacin saida nayi bincike sosai akai naji dan sanyi kullum ina da burin inje in ganki amma babu dama domin shiga gidan governor ba abu bane mai sauki, haka na hakura duk da a lokacin inda na fadama abba zaisan yanda za'ayi in ganki amma sai nayi shuru nabar abun a raina, ana cikin haka abba yaban auren zaliha muka tafi london saboda karatun ta, inda nima naci gaba da masters dina a yanzu haka mun kammala ta haiyu yau kwana biyar jibi suna, indo cikin muryan kuka tace gskiya yaya yusuf kasha wahala a rayuwa sosai amma Allah da yake mai rahma ne saiya hadaka da masu tausayama, ta Kalli abba dake zaune tace Allah ya saka maka abba samun mutum irinka zaiyi wuya a rayuwa Allah ya baka lafiya, duka Suka amsa da ameen, sannan ta kalli yazeed tace yaya yazeed kaima Allah ya biyaka, murmushi yazeed ya mata, sannan ta kalli ummi tace ummi Allah Ya saka muku da gidan Aljanna, tashi tayi da sauri ta dauki yaron yayan nata dake hannun zaliha, Tana kallonshi cike da kaunar yaron dan uwan nata, tace anty zaliha yaron da yaya yake kama zaliha murmushi tayi tare da fadin kai sister wannan son kai haka, dariya duka suka sa, yusuf yace sister yanzu a ina kike yaranki nawa? Dan shuru tayi tare da hawaye tace yaya yusuf bani da aure yanzu, yace mijinki fah maiya faru? Nan ta bashi labari da irin abubuwan da suka faru tun daka kauye har haduwanta da Abdul da irin taimakon daya mata shida Mum, amma ta boye musu irin abunda A Majeed ya mata sai dai tace sun rabu ne a bisa kaddara wanda haka Allah ya tsara yazeed jin haka yasa ya saukar da ajiyan zuciya wanda tun sanda yaji yusuf yace an Mata aure ya shiga damuwa, yusuf yace gskiya sister kema kin hadu da mutane musu kirki tabbas na Allah basa karewa duk da akwai marasa kirki amma Na Allah sunfi yawa marasa kirkin kadan ne,sai dai Sunfi kaurin suna, yau ina cikin farin ciki mara misaltuwa daya sake hadamu, indo ce ta tashi tare da fadin Bros inaga zan tafi sai gobe zanzo, kallonta yusuf yayi tare da fadin sister har zaki Iya tafiya kibar ni Ai bazan yarda da hakan ba, zadai kije ki dibo kayanki ki dawo Gida na, sannan Kafin ki dawo zanje inyi musu godiya duk da nasan kalman godiya tayi kadan, sai a lokacin ummi tayi magana tare da fadin haba yusuf ai hakan inaga ba daidai bane ace lokaci daya tabar su, ai hakan ba adalci bane, abba yayi gyaran murya shima yace hakane ka barta tayi shawara da kanta Akan abunda ya dace tayi, yusuf yace shikenan abba, indo tayi dan murmushi tare da fadin Bros yaron Mum ne bashi da lafiya nan ta basu labarin yanda ta fito ta barsu, yusuf yace subhanallah Allah ya bashi lafiya kije kiji yanda ake ciki gobe nima zanzo insha Allah, yazeed ne ya tashi shima Amma ranshi a dan jagule dan ya gane A Majeed shita aura suka rabu kuma gashi Tana wani nuna damuwa akanshi dan baida lfya... Yusuf ne ya katseshi da fadin kaima tashi kayi, yace eh nan sukai sallama indo da yusuf da yazeed suka fita, yusuf yace ya ajiye indo a Gida plz baya son barin abba shi daya hakan akayi motar yazeed ta shiga bayan sunyi exchanging number da dan uwan nata, Tana gaba yazeed na tuki yana ta dan janta da hira sama2 take bashi amsa har suka karaso inda ya nemi ta bashi number dinta shima bata musa ba ta bashi sannan sukai sallama ta shiga Ciki.












Kai tsaye falon gidan ta shiga babu kowa, haurawa sama tayi bata ga kowa ba, dan haka ta kira Mum bugu daya ta dauka tare da fadin aysha..... Indo tace Mum na dawo ban ganki ba, Mum tace aysha wlh gani gidan A Majeed tun dazu muke fama dashi akan muje hspt yaki, kana jin muryan Mum kasan Tana cikin damuwa, wai babu inda zashi aysha na rasa gane mai yake nufi..... Indo tace gani nan zuwa Mum, indo jiki a sanyaye ta fada toilet tayi wanka tare dayin alwala tayi sallah La'asar dan ankira tun dazu batayi ba, wata doguwar riga tasa ta fita taxi tahau bata jira driver ya kaita ba kai tsaye gidan aka nufa da ita, jiki a sanyaye ta fita taba mai mota kudin, tayi wajan minti uku Tana dan tuna abunda ya faru baya a cikin gidan hawaye ne ya silalo mata tasa hannu ta goge ta nufi Gate din Tana bugawa kirjinta nata dukan uku2,mai gadi ne ya leko duk da bawai ya santa bane ya bari ta shiga, a falo taga dady yasa hannu akai alaman damuwa, indo ta gaidashi cikin sanyin jiki, yace aysha sannu tare da fada mata Mum na ciki direct dakin ta shiga wanda yau ne ta taba shiga duk zamanta a gidan a baya, Tana bude kofar ta hangoshi kwance akan gadon da alama bacci yakeyi daka shi sai singlet Da 3quater jeans ya rame lokaci daya hannunshi an makala mai drive, wani hawaye ne ya zubo mata a fuska lokaci daya tare dajin tausayin shi, dai2 lokacin Mum ta waigo tace aysha karaso mana, karasa shiga tayi tare da fadin Mum ya jikin nasa? Mum tace toh da sauki dai na musulunci, tunda muka zo muke ta fama muje asibiti yaki yarda wai mu barshi kawai..... Hawaye ne ya zubo ma Mum cikin damuwa taci gaba da fadin aysha A Majeed shi daya gareni gashi a kwance yana fadin a barshi kar'a kaishi asibiti wai mutuwa zaiyi, indo itama hawayen take, Mum tace dakyar ya bari akasa mishi wannan Drive din wlh aysha A Majeed yayi mugun d'agamin hankali a yanda muka sameshi yanzu anyi mishi alluran bacci tunda akamai har yanzu bai farka ba, indo tace Mum kiyi hakuri zafin ciwo ne kawai insha Allah zai tashi babu abunda zai sameshi, mai Dr yace akai, nan mum ta bata wata takarda da Dr yace za'ayi mishi scan da test din da Dr yayi mishi da dan rubuce2 da akayi, indo amsa tayi ta fara dubawa, kallon Mum tayi kaman za tayi magana kuma tayi shuru, wata nurse ce ta shigo dakin danta duba ko ruwan ya kare, indo tace mata ta bata number din dr din nurse din ta fadama indo ta rubutu, fita waje tayi dan ta kira Dr din, dialing number din tayi bayan an dauka ta fadama Dr din koh ita wacece inda ta rokeshi akan ya tura mata sauran bayanan ta email dinta yace mata ok, jingina tayi a jikin motar Dad, Tana tunani, lokaci daya tace no hakan bazai faru ba, nasan dai matsalan matarshi ne yake damunshi duba wayanta tayi taga an tura mata dan haka ta fara karantawa harta gama, fita tayi daka gidan, bata dade ba sai gata ta dawo da leda a hannunta, Dad yana falo har yanzu yace aysha zoki zauna inada magana dake, zama tayi a gefen kujeran tare da sunkuyar da kanta a kasa, Dad yace aysha miye tsakaninki da A Majeed? Dam taji gabanta ya fadi dai2 lokacin Mum ta fito Tana fadin aysha tashi ki shiga ciki, Dad ido yabi Mum Dashi cikin mamaki indo tashi tayi Tana mamakin mai Dad yake son Sani, bata karasa dakin ba taji Mum na fadin haba mai yasa za kayi haka, karka manta irin abubuwan da suka faru a baya nida kaina ina son aysha da abdul-majeed amma dan Allah karka fada mata karta daukemu marasa adalci masu san kammu da yawa, duk da a yau ina cikin damuwa ga tilon dana a kwance rai a hannun Allah bazai sa ince aysha ta aureshi ba, tunda nayi hakan a farko maiya haifar koda kaji yana fadin aysha ina sonki karka manta yana cikin zafin ciwo ne bai san inda kanshi yake ba....... Indo data tsaya tana ji da sauri ta shige dakin da A Majeed din yake an cire mai drive din, yana kwance abunshi, kuka ta fara mai tsuma zuciya zama tayi a kan gadon Tana kallonshi yayi mugun ramewa sosai jin hannunta tayi cikin nashi ya rike da sauri ta kalleshi amma taga har yanzu bacci yakeyi, kallon hannun Nata tayi wanda ya rike da karfi, wani hawaye ya zubar mata mai zafi lallai Mum ta cika uwa ta Gari mai sadaukar da ran

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login