Showing 21001 words to 24000 words out of 85238 words
Chapter 8 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
tace kunga shegiyar wai kuka takeyi, nan saudat taita zungurin Abu dake kuka, Abu ta tashi ta cakumi saudat da nufin ta rama nan suka tarun ma Abu suka mata lilis, sulaiman ya shigo yaga ana jibgar Abu nan yaita Bala'i akan me zasu dukar mai mata, mai gari jin hayaniya shima yazo gefen yaron nashi, nan yaga kannan sulaiman da yayyinshi mata mai gari ya tambaya mai ke faruwa nan sulaiman ya fada mishi abun da sukai ma matarshi mai gari ya musu fada sosai akan idan basu fita daka lamarin matar sulaiman ba sai yayi mugun saba musu, nan suka fita suna fadin an mallake musu dan uwa, shima mai Gari fita yayi, nan sulaiman yaita rarrashin Abu, amma ina taki yarda wai ita saiya saketa ta auri mijin indo, sulaiman dai ranan a waje ya kwana dan tashin hankali.
Washe gari Mum da indo suna dinning suna breakfast sai ga A Majeed ya shigo falon kamshin turaren shi ya cika wajen, yace morning mum gaban indo yahau bugawa tunda ta ganshi, Mum tace morning, ganin indo yasa ya tamke fuskat dan shi yasha ma ko ta koma kauyensu, yanzu wannan yar ficiciyan ake kokarin manna mishi, To inyi me da ita, duk da yaga ta dan canza akan da amma shi yasan wannan ba tsaranshi bace domin shi sai babban Mace irin zee dinshi, Mum ce ta katse shi da fadin lfya naga ka tsaya kerere? Yace Mum ni zan wuce Abuja yanzu, Mum tace ok Allah ya kiyaye hanya, ya amsa da ameen, tare da fadin yaushe Dad zai dawo tace gobe insha Allah, yace ok tare da fita, indo sai da taga ya fita ta sami nutsuwa.
A Majeed ya koma abuja, koda ya nufi gida Zainab ce zaune a falo ita da wasu mata guda biyu daka gani kawayenta ne, nan Suka gaisa da A majeed, ya zauna kusa da madam din tashi dako kallo bai isheta ba, yace swty am back, ta tabe baki tare da fadin I though ai a can zaka tare, domin naga mamanka tana kokarin raba ni dakai, bini2 kace tace tana nemanka am tired of this, bazan dauki wannan ba wlh, daya daka cikin kawayenta tace hmm ai sai yasa gwara ka auri wacce mum dinshi ta mutu mother in low ar wicked wlh dat Why ni bazan auri wacce Mum dinshi ke raye ba W........ Tas saukan mari taji akan fuskanta A Majeed ne ya kai mata mari tare da fadin how dare u zaki dinga fadin irin wannan maganan akan Mum dina, Infact ma wa yasa bakin ki get out of My house ya nuna mata kofa, daukan jakanta tayi dayar ma ta tashi tayi waje zainab na kiransu amma suka wuce, Zainab ta kalli A Majeed tace u try ka nunawa duniya kafi son mamanka akai na dan haka yau sai kaban takarda na in yaso sai kaje ka zauna da family dinka......
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
90to95
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*SIS AYSHA MAMAN HUDA😍*
A Majeed shuru yayi ba tare da yace mata komai ba, ganin kaman ya maidata wata Sauna tana magana baya kulata yasa ta matsa kusa dashi tana fadin A Majeed tun muna mu biyu ka sakeni, kallon ta yayi cikin fushi tare da fadin kin ci darajan abu guda biyu amma da yau saina sakeki kaman yanda kika bukata, cikin gadara tace bana son inci darajan komai ni nafi karfin kace naci darajan komai wlh sai dai ni ince kai ne ke cin daraja ta da iyayenka, domin kasan mahaifina shine No 1 a kasar nan dan haka yau ko mai kasha sai ka sakeni tas ya sauke mata mari tare da fadin bansha komai ba zan nuna miki cikin hayyacina nake, saki dai kike bukata koh? Shuru tayi hannunta nakan fuska tana mamakin marin da yayi mata gashi taga kaman zai iya sakin nata domin duk wannan abun da takeyi cika baki ne bawai so take ya saketan ba, ganin karya aikata yasa tabar falon da gudu tana kuka, shima ganin haka yasa ya fita daka gidan gaba daya domin kanshi yaji yana juya mai har ga Allah yana son Zainab sai dai a yau ya fara ganin halin nata mara kyau da Mum dinshi ke fada tana Dashi, wanda shi a da komai ta mishi baya ganin laifinta duk da kuwa tana mishi abunda yafi haka, kodan yau ta taba Mum dinshi ne yasa har yaga laifin nata, tabbas hakane domin yana son Mum dinshi fiye da yanda mai karatu yake tunani, dan tsaki yayi tare dajin haushin wannan kawar Zainab din wai mother inlow are wicked, tunda yabar gidan sai dare ya dawo a falo ya ganta taci uban kwalliya da English wear, top din da tasa gaba daya ta kameta kirjinta duk a bude abunda A Majeed yake masifar so kenan duk da ba wani girma nata suke dashi ba amma tasan yana rudashi, da sauri ta nufeshi tayi hugging dinshi tana kuka tare da fadin am So sorry my swt, kara matseta yayi tare da shafa bayanta cikin kunnan ta ya rada mata stop crying my baby, cikin kissa tace Baby yanzu baka So na ka canza min ta dan janye jikinta daka nashi,A Majeed da ya riga ya fara fadawa da sauri ya matsa kusa da ita yana fadin ba haka bane baby I..... Da gudu ta tafi dakinta tana kuka da sauri ya bita a kwance ya ganta akan 'katon gadon ta tana faman kuka nan hankalinshi ya tashi ya shiga rarrashi dagata yayi ya fara kissing dinta tare da shafata tako ina itama tuni ta fada ranan dai A Majeed yaji dadi domin rabonshi da wani abu ya hadasu harya manta duk da wani lokacin daki daya suke kwana, Zainab ita da kanta tasan samun namiji irin mijinta zaiyi wuya ga kyau ga kudi duk da kudin ba matsalanta bane domin tana dasu wanda bata san nawa ta mallaka ba ma,ita burinta ta sami mijinta ita daya a kullum tana tsoran yaje jalingo ko Egypt kasar mum dinshi kar yaga balarabiya yace zai aura ko Mum dinshi tace ya auri wata daka danginta, domin balarabiya ce kawai zai aura take ganin zata yi kishi da ita dan tasan suna da kyau amma babu wata yar Nigeria da zatai gigin auran mata miji ma ta zauna lfya, domin tana matukar kishin mijinta dan zata iya aikata komai a kanshi sannan bata son yana yawan sex da ita dan a ce wanta yana saurin tsufar da mace hmm tabdi jam ban taba jin haka ba sai a wajan zee🤣.
Mum tayi shawara da Maryam akan mai ya kamata tayi ma indo dan rayuwanta ya in ganta, Maryam ta bada shawaran a sata a wata makaranta na mata wanda ba suyi karatu ba mai suna NEVER GIVE UP IN LIFE, za kayi karatun wata biyar zasu koya ma boko yanda zaki kula da kanki da tsafta da sauran su, Amma ko wanne fanni2 ne Maryam tace a sa aysha a fannin boko dana girki, Mum tayi na'am da batun kuma taji dadi sosai sannan kuma idan mutum ya gama za'a bashi certificate na primary school sannan idan an fara waec da mai bukatan ci gaba da karatu suna da center mutum yana biya yayi amma in za kayi waec sai ka zauna harna shekara daya Kana karatu in kuma primary certificate ne wata biyar, Mum tace aysha shekara daya za tayi domin zata ci gaba da karatu, mum tasa anyi ma indo komai da komai, fara zuwa kawai ya rage shima cikin satin nan zata fara zuwa,.
A Majeed na office yana duba wani abu cikin system sai ga Abdul ya shigo, bayan ya zauna ya kalli A Majeed tare da fadin angon aysha ya amarya da uwar gida, tamke fuska yayi tare da daina danna system din yace kasan nasha fada maka ka daina min irin haka, kawai ka fadamin abunda ya kawo ka, in kuma ba komai ya kawo ka ba ka tashi ka koma office dinka, Abdul yace Allah ya baka hakuri ango kasha kamshi A Majeed kara tamke fuska yayi tare dayin banza da abdul, ganin haka Abdul yace na samo wata yar Kaduna ina so musa rana muje ka ganta, A Majeed tabe baki yayi tare da fadin ina wannan yar kauyen da kace Kana so da? Abdul murmushi kawai yayi tare da fadin abar dai wannan zancen wancan tayi aure, kawai nidai yaushe kake da Time muje? A Majeed yace bari muga Next Week sai muje ko ran Friday, Abdul yace OK Allah ya kaimu tare da tashi dan ya koma office dinshi.
Indo an fara zuwa makaranta, tun safe inta fita bata dawowa sai 4, tana dawowa zata islamiya, in tayi sallah taci abinci lesson teacher yazo, ran lahadi ne kawai take dan samun hutu,domin babu Skul sai islamiya da lesson, kuma babu laifi tana fahimtar karatun dan tana son itama taga tayi ilimi, sai dai kullum burinta taga dan uwanta yusuf, Mum Tana kula da indo sosai ta gefen sutura kayan kamshi da sauransu, ga abinci mai gina jiki da take samu yasa jikinta yake murmurewa ga girma tana karayi, Mum ta lura tana da girman jiki amma rashin cin abu mai kyau yasa bata girma sosai amma yanzu Alhmdlh komai ya fara bayyana, gashi sunyi wani irin shakuwa da Mum duk da indo na jin kunyan Mum, suna zaune suna fira mum take fada ma indo inta gama karatun ta Egypt zata taci gaba sai ki zauna wajan ummi na, indo taji dadin hakan sosai tare da kudiran kara dagewa da karatu.
Zabe yana ta gabatowa domin his excellency wannan karan Senate yake son zuwa, anata campaign, Mum Tana Bussy kwana biyu domin akwai masu taya mijinta campaign mata da ita take basu duk wasu abu da suke bukata, indo itama takan taya Mum da bata shawara musamman da taji his excellency yace yana son a kara yawan titi ayi a layi2, indo ta sami Mum a daki tana zaune ita daya, Mum tace aysha dazu nazo ai naga kina bacci, indo tayi murmushi tare da cema Mum barka da hutawa, Mum ta amsa da yauwa, nan indo tace ma mum akan titi din da his excellency taji yana fada idan aka karayi zaisa talakawa suji dadi, indo tace Mum inaga shi talaka baya bukatan titi ta kofar gidansa indai akwai a babban hanya, shifa *TAMBARIN TALAKA* rumbun sa, indai talaka zai ci ya koshi bashi da matsala domin shine burin shi, inaga da ayi wannan titin gwara an raba musu jari koh da babu yawa, Mum da tunda indo ta fara magana take kallonta da mamaki yanda har tayi wannan tunanin mai kyau, Mum tace kai aysha gskiya kinyi tunani mai kyau, anya ma Ba political science zaki karanta ba? Indo dariya tayi kawai, Mum tace hakan za'ayi gobe zan kira meeting sannan anjima kadan zan gayama his excellency wannan shawaran, koh da Mum ta sanar ma his excellency wannan shawaran yaji dadi sosai tare da cewa gskiya kinyi tunani mai kyau, Mum tace bani nayi wannan tunanin ba aysha ce, yace wace Aysha? Tace matar A Majeed, yace yauwa suna nan lfya dai koh, dan ina tsoran wannan yaron, kwanaki yazo ya sameni akan a raba auren naki yarda, mum taba his excellency labarin abunda yayi tare da gaya mishi yarinyar tana nan gidan, ranshi ya baci sosai tare Da fadin dan mai yasa Mum bata gaya mishi ba sai yanzu, daukan wayanshi yayi ya kira A Majeed, bayan ya dauka yana gaidashi amma his excellency bai amsa ba sai ma fadin da yayi kazo jalingo gobe da safe sannan ya kashe wayan, his excellency yace ma mum tunda ya aureta dole ya zauna da ita ban yarda da zancen saki ba, gobe dole ya tafi da matarshi in yazo Mum za tayi magana ya dakatar da ita tare da fadin ban san jin komai naga In akabi ta Yaron nan saiya zubar min da mutunci tashi yayi tare da cema Mum ina da meeting sai na dawo.
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
95to100
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*ZAINAB ZEE BABY😍*
Mum shuru tayi tama rasa abunyi, harga Allah itama Tana son indo ta koma gidan mijinta sai dai tana gudun irin zaman da za tayi a abuja din, haka taita tunani kala2, tare da tausayama indo din, domin tasan tunda A Majeed ya iya bude baki yace baya sonta a gabanta tasan tabbas idan aka matsa mai akan indo din zai iya yi mata wani abun ko matarshi, Mum gaba daya ta kasa sukuni zama tayi tana jiran mijin nata ya dawo suyi magana, koda his excellency ya dawo Mum ta mishi magana akan a bar indo a nan yace hakan bazai yihu ba, bawai an aurota bane dan ta zauna dasu ba, dole gidan mijinta zata zauna, ganin tashin hankalin da matar tashi ta shiga yasa ya kamo hannunta yace kiyi hakuri babu abunda zai faru nasan abunda kike gudu, insha Allah babu abunda zai faru zanja mai kunne sosai karki damu, Mum ajiyan zuciya tayi ta danji dama2.
A Majeed duk da yau monday amma haka ya tawo jalingo tare da tunanin lfya dad yake neman shi, karfe goma da wani abu ya sauka a jalingo, gidan shi ya sauka sai da ya kimtsa domin baya tunanin ko yaje gida zaiga Dad dinshi yanzu, wajan 12 ya nufi gidan nasu koda ya isa anata kiran sallah masallacin dake kofar gidansu ya nufa mutane ancika sosai ciki harda mai girma governor, bayan an idar, his excellency yana ta gaidawa da mutane yana jin matsalan su, wanda hakan ya zame mai jiki kullum in yana kasar yana sauraren kukan mutane, tare da dan nasa Suka shiga gida, a falo suka sami Mum a zaune tana karanta news paper, A Majeed wajanta ya nufa yana fadin sannu da hutawa my mum, mum murmushi tayi tare da fadin yauwa ya hanya? Ya amsa da lafiya his excellency zama Yayi Mum ta tashi ta nufi kujeran daya zauna tare da fadin food is ready fah, yace ok tashi yayi Suka nufi dinning wasu manyan kuloli ne Sun kai goma akai kana ganin hummer din kasan masu tsada ne, abinci kala2 na gida dana waje, Mum ta zuba ma mijinta da dan nata, suna ci suna taba fira sama2 A Majeed shidai ya kosa yaji ko miye Dad ke neman shi, har Dad ya kammala ya kalli A Majeed yace ka sameni falon sama inka gama, Mum ta tashi tabi mijinta saman itama, A Majeed kasa cin abincin yayi tare da tambaya toh maiya faru wata zuciyar tace may be Akan campaign dinshi zasu tattauna dan haka yaci gaba dacin abincin shi, sannan ya haura sama, A kan kujera yaga Dad Mum na gefenshi, shima samun waje yayi ya zauna, Dad yace Abdul-majeed Ashe baka da kirki? Dam A Majeed yaji gabanshi ya fadi dad yaci gaba da fadin dama har yanzu baka hakura da maganan aurenka ba, toh wlh baka isa ba domin ba zaka maidamu mutanan banza ma, mum dinka tamin bayanin komai dan haka in zaka tafi zaka wuce da matarka sannan wlh kar inji kar in gani in naji ka mata wani abu wlh sai nayi mugun saba maka, Dad yaja mishi kunne sosai daka karshe yayi mishi nasiha, A Majeed gaba daya takaici ya isheshi koda zai koma gidansa Dad yace su tafi tare da matarsa babu yanda ya iya, nan Mum tasa indo ta fito su tafi tare dasa masu aiki su hada mata kaya, gaba daya an hadama indo kayanta, Mum tace ta tafi da kadan sauran driver zai kawo Mata abuja din Indo babu abunda take sai kuka domin bata son rabuwa da Mum ga karatun ta,sannan bata san zuwa gidan A majeed, domin harga Allah tsoranshi take ji sosai, Mum tayi mata nasiha sosai tare da fadin komai ya mata ta kirata ta fada mata, ta dauko waya taba indo tare da fadin akwai number dina a ciki, indo ta amsa tare da godiya,mum tace zata sa a bata transfer na skul dinta sai ta farayi a abuja, indo taji dadin hakan sosai, har mota Mum ta rakata A Majeed yana mota a baya fuska daure kaman ance mamanshi ko babanshi ne wani ya rasu, Mum baya ta bude ma indo itama ta shiga tare da fadin aysha komai aka miki ki kirani ki fadamin kinji tana fadin haka ta rufe musu motar, driver yaja, indo kuka take kasa2, A Majeed wani irin takaici yake ji gashi baya son yin wani abu a gaban driver direct gidanshi Suka nufa, fita yayi ya shiga ciki da sauri, itama fita tayi ta dauko akwatin ta karami taja tai ciki, dakinta na gidan ta shiga, ruf da ciki tayi akan makeken gadon dakin tana kuka, tare da tunanin wani irin rayuwa za tayi a gidan A Majeed, karan wayanta ne yasa ta dan tsagaita kukan tare da dauka taga Mum ce ,shuru tayi tare da kara goge hawayen fuskanta ta dauki