Showing 78001 words to 81000 words out of 85238 words
Chapter 27 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
labour room A Majeed gaba daya ya kasa zama haka Mum da Dad Zainab kam kuka takeyi domin ta tausaya mata bata so ta mutu, ta dauki lokaci mai tsawo Tana nakuda amma shuru Dr ce ta fito tace gsky sai an mata Cs dan bazata iya haiyuwa da kanta ba jikinta yayi weak, A Majeed akaba ma takarda yayi signing dai2 lokaciñ Yusuf da zaliha suka zo hspt din gnin irin tashiñ hankalin da suke ciki yasa suka zauna suma amma basu ce komai ba, an Fara shirin aikin indo tayi wani irin nishi mai karfi sai ga yaro ya fado lokaci daya kuma tayi wani nishin yarinya ta fado can kuma ta sake wani sai ga yaro ya kara fadowa lokaci daya kuma ta Saki hannunta komai nata ya tsaya cak.
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
240to245
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Kwashe yaran akayi ganin kaman bata motsi yasa aka sa mata oxygen amma baya moving gaba daya Dr din sun sadakar ta rasu lokaci daya kuma oxygen din ya fara tafiya alaman Tana da rai tayi doguwan suma ne, nan sukayi kanta ana dubata tayi wajan 30 mnt Tana numfashi a lokacin an kimtsa yaran sannan Dr din da kanta tasa nurse suka tayata kamata akai toilet da ita dakanta Dr din ta mata wanka har lokacin idanta a lumshe yake bata bude ba da duka alamu bata cikin hayyacinta har Dr din ta gama gyara mata jiki Sannan tasa mata wata doguwar riga daka cikin kayanta da suka zo Dashi tare da pad, Dr din ta fita da sauri A Majeed ya matsa kusa da ita yana tambaya tace congratulations ur wife give birth to triple yace yan uku, Dr tace yes a hankali yace itafa hope babu abunda ya sameta? Dr tayi shuru ba tare da tace komai ba yace Dr ta mutu ta mutu koh Dr tace bata mutu ba amma har yanzu bata farfado ba jikinta yayi weak Allah yasa ta haiyu da kanta ba'a kai dayi mata aikin ba yanzu sai mu jira kadan muga yanda abun zai kasance, da sauri yace Dr zan Iya ganinta tace eh amma ka bari a kaita dakin hutu nurses ne suka fito da yaran Mum da Dad suka amsa Zainab ta amshi daya itama A Majeed kam ko kallon yaran baiyi ba danshi burinshi yaga matarshi kawai yaran kyawawa kaman babansu sak gasu farare tas dasu duka kamansu daya sai dai macen ta fisu haske sosai, Zainab wani irin hawaye ne ya zubo mata wannan ne rana ta farko da taji Sha'awar haiyuwa domin yaran sun burgeta dana sanin shan maganin hana daukan ciki duk taji ya kamata lallai itama Tana bukatan haiyuwa duk da lokacin da tasan indo nada ciki ta daina shan maganin amma har yanzu batai ciki ba dole taje hspt a dubata dan itama Tana da bukatan haiyuwa a yanzu, fito da indo akayi akan gadon marasa lafiya ana turata hankalinsu duka ya koma kan gadon A Majeed Da sauri ya nufi gadon tare da rike mata hannu yana hawaye kaman karamin yaro har dakin da za'a kaita suka shiga hannunshi na manne da nata yana hawaye tare da fadin get up aysha tashi kiga yaranki plz kowa dake wajan yaji tausayinshi musamman yusuf da yake ganin gudan kanwar tashi a kwance bata motsi iya tashin hankali shima ya shiga Mum ce ta dafa ma A Majeed baya tare da fadin son kayi hakuri insha Allah zata tashi rungume Mum yayi yana kuka Mum nata bashi baki lokaci daya indo ta bude ido Tana ganin wani irin dishi2 a hankali ta Gama bude idan ta ganta a kwance mutanan dakin ta fara kallo lokaci daya kuma abunda ya faru ya dawo mata ido ta kuma lumshewa sannan ta bude karaf ya sauka akan na A Majeed Da sauri ya kira sunanta da aysha murmushi ta sakar mai da sauri yace mum ta tashi Alhmdlh nan Yusuf ya fita ya kira Dr ta dubata tace komai normal dama ta tsorata ne sosai tun farko shiya ja mata suman da tayi yanzu dole ta kwana dan muga yanayin jikin, sai a sannan A Majeed ya kalli yaran tare da amsar wanda ke hannun mum ya mika ma indo tare da fadin kinga dani suke kama dariya tayi kowa ya fara mata sannu tare da barka fita Su Mum sukayi aka barta ita da mijinta zainab kam Gida ta wuce nan A Majeed ya fara fadin aysha dama nasan ba zaki mutu ki barni ba dariya tayi tare da fadin hakane nima bazan so in tafi in barka ba kodan yarana ma zanso in rayu dan kar suyi rayuwa irin nawa, matseta yayi da karfi a jikinshi yana fadin I love You baby macen ce ta tsala ihu da sauri ya Saki indo ya dauketa yana jijjigata Mum ce ta shigo ta amshi yarinyar tare da bama indo ita tace yunwa take ji, indo kunyan amsan yarinyar tayi mum tace amsheta mana aysha babu yanda ta Iya dole ta amsa tare da fadin Mum ina kayana? Mom ta janyo mata akwati ta Dan tashi kadan ta dauko hijab tasa sannan ta Fara bama yarinyar nono Mum dariya tayi tare da barin dakin ganin Mum ta fita yasa A Majeed komawa kusa da matar tashi yana ma sauran yaran wasa, inna Maryam ce ta shigo dakin ita da mum hannunsu dauke da basket bayansu mai aikin Mum ce dauke da flask da kayan tea indo tace inna Maryam saukan yaushe? Tace yanzu nan indo ta gaidata inna maryam ta amsa tare dayi ma indo barka, inna Maryam ta hadama indo Tea mai kauri tare da zuba mata farfesun naman rago amsan yarinyar tayi ta ajiyeta sannan taba indo Tea din da naman amsa tayi ta Fara ci duka naman ta cinye inna Maryam tace bari a karo miki tace a'a ya isa, A Majeed yaso ya kwana wajan matarshi Mum ta korashi inna Maryam ce ta kwana da ita Yusuf suma suka shigo suka kara yi mata barka tare da sallama suka wuce washe Gari wajan karfe 7 A Majeed yazo asibitin nan inna Maryam take ta tsokananshi wai yayi sammako shidai babu abunda yake yi sai dariya wai yau shine yake da yara har uku, ikon Allah, mum itama tazo asibitin tare da abinci nan aka zuba ma indo shima zama yayi suna ci tare Mum fita tayi dan taga dan nata wani sabon fitsara ya koyo, Abdul Da matarshi suma sun zo asibitin Sun dade kafin suka tafi A Majeed babu abunda yake sai daukar yaran hoto sai wajan karfe 5 Dr ta sallamesu dan taga jikin da sauki, gidan Mum suka nufa direct, A Majeed sai kashe kudi yake tayi akan yaran Zainab bata kara zuwa ba tunda tabar asibiti dan tace sai ran suna zata ta gefen Mum ma sai kashe ma yaran kudi take tayi......... Yau akayi sunan yaran inda aka kashe naira kaman babu gobe namijin yaci sunan dad muhd suna kiranshi da irfan dayan kuma Aminu sunan mahaifin indo suna kiranshi arfan macen kuma sunan Mum fatima suna kiranta da zarah Zainab itama tama yaran kaya na kece raina duk da tana jin kishi amma Allah yasa mata son yaran sosai a ranta, haka akaci suna aka watse kowa nasan barka, saida indo tayi arba'in sannan ta koma gidanta Mum tasa an hada mata ita sosai yanzu da masu aiki uku aka hadata dasu, koda ta koma Gida taga dakin da aka ware ma yaran an kashe kudi sosai komai ansa na wasan yara kala2 ga gadajensu nan guda uku kowa da nashi ji tayi an rikota ta baya ihu tasa a hankali ya furta kin cika tsoro Baby dariya tayi tare da turo baki kuma yace mai nene kuma? Tace nayi missing dinka yace really toh muje a amshe ni ido ta zaro tare da fadin ba irin Wannan missing din ba yace toh ni nayi wata nawa banji dumin jikinki ba dariya tasa tare dayin dakinta da gudu shima binta yayi a dakin yaga yaran ko wanne adan gadonshi mai keke yana tura Su, yace Baby nikam mai zan miki kiji dadi a rayuwa? Dan shuru tayi can tace inaso inje garinmu domin inga inna tani da Baba Musa, shuru yayi kafin yace banda wannan mai kuma kike so dariya tayi tare da fadin soyayyan miji na, yace ai kin samu tun tuni yace plz tell me mai kike so? Tace kaman yanda nace inason zuwa garinmu da kuma soyayyarka, yace shikenan ki bari yara suyi kwari sai muje kinji kai ta daga alaman toh nan aka shiga duniyar da yara basa zuwa sai sun girma😝 ranan dukansu Sun san sunyi missing din junansu sosai watan indo biyu da haiyuwa ta fara aiki a hspt dinta lokaci kadan tayi suna sosai danta kware a aikinta abban Yusuf ya sami lafiya sosai babu inda baya zuwa gashi Yusuf ya rike Mai amana na dukiyarshi dan lokacin da yake ciwo Yusuf yake ta juya dukiyar gashi an sami riba sosai ganin haka yasa yace Yusuf yaci gaba da juya kudin sannan ya dinga raba riban uku biyu na Yusuf daya nashi Yusuf rasa bakin godiya yayi dan murna a lokacin zaliha Tana dauke da ciki itama na wata 7 Yusuf ya kara kudi sosai ya kara kyau da girma.
*Bayan shekara daya*
Indo ce cikin wani tsaddan leshi anyi mishi dinkin doguwan riga tayi kyau sosai yaranta suka nufota suna dariya su ukun duk wanda ya gansu zai ce sun wuce shekara daya dan sunyi girma sosai da wayau, rungumeta sukayi suna dariya ita dariyan tayi tare da fadin karku fadar dani dai2 lokacin A Majeed ya fito yana fadin muje yaran daddy yau zaku kauye koh? Kai suka daga duk da basu san mai yake nufi ba, fita sukayi indo Tana fadin ni garinmu ba kauye bane murmushi yayi sunyi ma Zainab sallama wacce har yanzu burinta bai wuce ace A Majeed ya Saki indo ba, fita sukayi cikin wata katuwar jeep driver ke tuki suna baya shida yaranshi da matarshi da yake kalan jeep din nanne mai baya biyu, wayanshi ne yayi ringing Yusuf ya gani dauka yayi tare da fadin mun fito yanzu kuna ina,ban san Mai yace mishi ba naji yace ga munan zuwa, Sun hade da Yusuf da matarshi da yaranshi biyu abba da Hauwa, suma a tasu motar tafiya sukeyi kaman zasu tashi Sama har suka karasa garin taraba yaran duka sunyi bacci indo tunda suka zo garin gabanta ke fadi amma ganin Sun wuce yasa ta kalleshi tare da fadin ina zamu yace jalingo gobe zamu dawo taraba yamma yayi yanzu ya kamata mu huta bata kara cewa komai ba har suka karasa gidansu na jalingo gidan da aka fara kawo ta nan suka sauka Yusuf dai yace hotel zasu sauka dan bazai kwana gidan kanwarshi ba duk da A Majeed bai soba haka suka tafi kafin su shiga gidan saida yasai musu abinci bayan ya dauki yaran ya kaisu falo masallaci ya nufa dan anata kiran sallah magrib, ita kam indo abubuwan daya faru a gidan ne yake ta dawo mata sai dariya take tayi da yake Tana fashin sallah a haka ya dawo ya sameta Tana dariya kallonta yayi tare da fadin maman uku lafiya kuwa turo baki tayi tare da fadin baban uku driya yayi sosai tare da fadin kina tuna baya ne koh? Lokacin da kike tsoran tv dariya tayi mai karfi tare da tashi takai mai dukan wasa a kirji wajan ya rike tare da fadin ashhh Baby akwai zafi fah, tace toh bakai bane kake tsokana na, yace toh na daina kar a hanani abun dadi ido ta rufe da hannu Tana dariya, yace wai yaushe zaki gama wannan abunne nifa gskya a matse nake tace yaranka dai na wajan dariya yayi tare da fadin bari ma in tashe su suci abinci sai su kwanta tashin su ya farayi bayan Sun tashi shida kanshi ya basu abinci sannan ya kaisu daki ya musu wanka tare da sa musu kayan bacci suka kwanta fitowa yayi daka ganin alama shima wankan yayi yace ma'am kema muje in miki wankan tace nagode bana bukata yace kinma isa dariya tayi tare da fadin kazo muci abinci yunwa nake ji yace ohkey nan suka Fara ci har suka koshi suka nufi daki Dan su kwanta su huta.
Washe gari bayan Sun tashi sunyi breakfast wajan karfe 9 Yusuf yazo suka nufi taraba, kauyansu suka shiga yana nan yanda yake babu wani canji har yanzu dai basu da wuta sai dai wasu gidan an danyi gyare2 ta wajan gidan mai gari suka wuce nan ta hango SULAIMAN cikin wasu matasa duk ya rame kaman bashi ba wani irin hawaye taji yana son zubar mata amma ta dake dan tasan yanzu gogan nata zai fara tambaya idan kuma yaji akan abunda take kwallan tasan zaiyi fushi dai2 kofar gidansu Yusuf ya tsaya dan haka driver dinsu shima ya tsaya gidansu yana nan yanda yake sai kwanon daya cire akasa kalan abun itacen nan gidan ya tsufa sosai, indo ce ta fito Yusuf yace ta shiga taga gidan, gabanta na fadi ta nufi gidan babu kowa saida tayi sallama sannan wata ta fito cikin wasu kaya kaman tsumma saida ta kalleta dakyau sannan ta gane abu ce ita koh abu kallon indo takeyi baki sake tana mamakin kyanta tare da fadin anya mutum ce kuwa Baba Musa ne ya fito ganin abu bata dawo ba shima bakin ya Saki cikin wata shadda duk ta kode gashi tasha faci duk da hakan akwai wajan daya yage, hannunshi daya yana makale a kirji daka gani wani gefen jikinshi ya shanye ne yace hjy wa kike nema ne? Tace Baba musu indo ce cikin kuka yace karya kike yi indo ba haka take ba tace wlh nice baba shima kukan ya Saki yana fadin na gode Allah da bai dauki rayuwa na ba iya tsawon wannan lokacin yau gashi na ganki zan roki gafararki duk da akwai aiki a gabana ban san inda zan sami Yusuf ba, cikin kuka tace Baba tare muke Dashi da sauri yace kice ya shigo mana nan ya shiga daki ya dauko tabarma duk tayi datti ita kam abu mutuwar tsaye tayi dan ta kasa ko motsi, Yusuf tare da A Majeed suka shigo da yara da zaliha A Majeed babu komai a ranshi sai tausayin matarshi dama a irin nan tayi rayuwa, indo batai zaton mijin nata zai zauna akan tabarman ba amma sai taga ya zauna, Abu ce ta fashe da kuka Tana fadin dan Allah indo ki gafarta min nayi miki laifi babba a rayuwa duk kuma shairin tani ne da xugani da takeyi dan Allah ki yafe min nima gashi tun a duniya na fara ganin abunda na shuka, indo tace karki damu Abu na yafe miki ina inna tani? Abu tace Tana ciki nan abu ta shiga ta dauko tani dake daki Tana jinsu Tana kuka ana kawo ta duka suka toshe hanci ta rame ta Side babu kyan gani ga ciwo wajan nononta daka gani cancer ne dan wajan yayi kaman donut yayi rawun, tani ta Fara fadin yusuf indo sai kuma ta kara sakin kuka tare da fadin dan Allah ku gafarta min kunga yanda Allah yayi dani koh, duk da abunda ya faru baisa na hakura ba haka naita bin malamai dan mijinki ya koroki ya auri abu wata rana naje wani daji na fadi na soke nonona tun daka lokacin ya fara ciwo harya fara ruwa nasha Magani har na gaji tun ina iya tafiya har na kasa gashi ance sai nayi na asibiti wai daji ne gashi babu kudi mun so mu saida gidan nan mai Gari ya hana wai naku ne duk da a lokacin muna ganin munma yusuf shairi yabar gidan ai gidan ya zama namu Ashe ba haka bane gashi duk yanda naso Sulaiman ya Saki abu lokacin yaki dan nayi mishi mugun sihiri kafin ya yarda ya auri Abu ya rabu dake danginshi tunda suka san asiri aka mai ya auri Abu suka tsaneta sosai shiko kullum santa yake yi kaman ranshi ina ta zugata taita hadashi fada da yan uwanshi harta uwarshi baya Raga mata akan Abu ganin abun nata na yawa yasa suka tashi tsaye wajan addu'a har kadarin mu ya karye kuka ta Saki sosai kafin taci gaba da fadin ranan naga tashin hankali domin aljani aka tura mai yasa ya auri Abu rannan ya fita ya fadi aka dawo dashi Gida yana ta sambatu nan aka gane iska ne aka kira liman ya fara karatu nan aljani yayi magana tare da fadin karku konani dan Allah nima aiko ni akayi nan ya fada musu wanda ya aiko shi nan ya fita koda sulaiman ya farfado aka fada mishi abun daya faru wanda yayi kuka ya farayi tare da fadin yaushe na auri wannan mara tarbiyan ni ban ma san nayi auren ba tashi yayi cikin fushi ya nufi dakin Abu.......
Taku maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/