Showing 33001 words to 36000 words out of 85238 words
Chapter 12 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
ba gaba daya yaji zaman ya gundureshi amma ya kasa tashi ya tafi dan yana tunanin zata fito ganin har karfe tara da wani abu yasa ya tashi yayi ma iyayen nashi sallama, koda A Majeed yaje Gida baiga Zainab ba hakan bai wani dameshi ba dan inda sabo ya saba duk da abun yana bata mishi rai sosai, bedroom dinshi ya shiga kai tsaye toilet ya shiga wanka yayi ya fito da wani karamin towel yana goge kanshi kaman kullum zama yayi yana gyara gashin kanshi sai kamshi daya kara gauraye dakin Zainab ce ta shigo cikin night gown wanda komai na jikinta ana gani, abun ya bashi mamaki na ganinta a wannan lokacin dan baiyi zaton tana gidan ba kuma abun mamaki yau itace a dakinshi cikin wannan yanayi bai gama tsinkewa ba sai da yaji hannunta cikin jikinshi tana shafa shi tako ina, nan A Majeed ya fara mayar mata da martani dan dama kwana biyun nan dauriya kawai yake ranan yayi mamakin yanda zainab ta saki jiki dashi sosai, cikin jin dadi bacci ya daukeshi, koda ya farka bai ganta a dakin ba, dan murmushi yayi tare dajin dadi harga Allah yana son Zainab sai dai halayanta da baya so har take shirin fice Mai a rai gaba daya, ta gefen Zainab kuwa koda ta koma daki tsaki tayi tare da fadin shegiyan mata maita bani ne yau har nake nemanshi dakai na, gidan wata kawarta taje wata mai maganin mata wacce take Kawo ma kawar tata tazo inda ta basu tace suyi testing Zainab kaman ba zata shaba dakyar ta dan lasa kadan jin dadin maganin mai kama da zuma yasa ta amsa taita sha tun a gidan ta shiga wani hali ba shiri ta dawo Gida, dan tsaki tayi tare da fadin dan ba kara kar aje a maidani tsohuwar karfi da yaji ina cin ganiyan kuruciya Na, koda Gari ya waye A Majeed dakin zainab din ya nufa amma bata ciki ranshi yaji ya baci tare da fadin ina taje da safen nan, wayanshi yaji yayi kara kaman shigowan sako, kaman bazai duba ba ya dauko wayan ya duba sakon daka Zainab dinne *na tafi China jirgin mu 8 zai daga naga kana bacci na wuce saina dawo* wani irin iska ya furzar mai cike da takaici zama yayi tare da fadin wai mai Zainab take nufi Dashi ne haka? Sai kace ba matar aure ba in za tayi tafiya bata gaya min,Dan ajiyan zuciya yayi tare da fadin zanyi maganin abun daukan daya daka key din motarshi yayi ya bar gidan direct gidan mum ya nufa jin motsin mutum a kitchen yasa ya nufi kitchen din dan yasan indai Dad na Gida Mum ke mishi abinci, ganin wacce ke kitchen din yasa shi sakan wani murmushi tare da tsayawa a kofar kitchen din yana kallon yanda take aiki cikin natsuwa, Kare mata kallo yake tayi wacce take dauke da doguwan riga ya dan kama ta saman, kasan kuma a bude yake, ta daura dan kwalin kayan gaba daya ji yake kaman yaje yayi hugging dinta amma babu dama, jin kaman ana kallonta gashi kuma tana jin kamshin turaren shi tun dazu, yasa ta waigo sukai ido biyu wani murmushi ya sakar mata, saurin kawar da kanta tayi tare da waigawa taci gaba dayin aikinta, jin kamshin turaren shi kaman a kusa da ita yasa ta dan waiga ganinshi tayi kusa da ita, har suna iya jin numfashin juna, kokarin kaucewa takeyi dan tabar kitchen din gaba daya amma ya tare hanya domin a gabanta yake, cikin muryanshi Wanda kaman baya son yin magana ya kira sunanta tare da fadin plz ki saurare ni, mai yasa kike irin wannan fushin akai na, kina nunawa kaman baki sanni ba, inaso kiyi hakuri akan duk abunda na miki a bay...... Jin kukanta yasa hankalinshi ya tashi ba tare daya karasa abunda yake son fadi ba, cikin damuwa yasa hannunshi da niyan ya share mata tayi saurin kawar da kanta gefe ganin kaman kukan nata karuwa yakeyi gashi har cikin ranshi yake jin kukan na bai san lokacin daya janyota jikinshi ba tare da lumshe idonshi, da karfi tasa ta tureshi amma ko gezau baiyi ba domin ya riketa dakyu, cin zafin da yayi a hannunshi yasa ya saketa da sauri ta fita da gudu cizonshi tayi a hannun bude wajan yayi ya gani ya tashi yayi ja ga shaidan hakorinta nan a wajan, idonshi daya kada yayi ja ya furzar da wani irin iska mai zafi, fita yayi daka gidan gaba daya kai tsaye gidanshi ya koma gaba daya ranshi a jagule.
Itako indo tana shiga daki ta fada gado tana ci gaba da kuka, wai mai hakan ke nufi mai yake shirin faruwa ne, lallai na yarda namiji bashi da Kunya ko kadan yau itace A Majeed har yake kokarin taba jikinta bayan wasu Lokaci da suka wuce yake nuna kyamanshi akanta a fili ba tare da tuna yanda za taji ba a ranta, wani irin tsananshi taji yana karuwan mata a rai fiye da, dah, ganin zata office yasa ta fada toilet tayi wanka idon nan nata ya dan tashi, powder kawai ta shafa tare da feshe jikinta da turare, ta fito falo cikin riga da zani na Atamfa sai rigan likita akai da wani karamin gyale ta yafe kanta dashi tayi kyau sosai, Mum bata falo dan haka ta wuce office ba tare da tayi breakfast ba, driver ya kaita ya ajiyeta, kai tsaye Office dinta ta shiga ta fara duba mutane takai wajan shabiyu tana ganin mutane sannan ta fito dan ta nemi abinci kusa da asibitin akwai wani wajan snack da coffee, ta ajiye farar rigan Dr din a office ta nufa wajan inda taga yawanci mutanen wajan laraba da turawa sunfi yawa kuma duk yawanci coffee din suke sha, zama tayi akan kujera da babu kowa, nan ta fara duba abunda takeso shawarma tasa a Kawo Mata da chapman, fara ci tayi a hankali kaman bata son ci, yazeed wanda tun shigowanta wajan ya kafeta da ido tashi yayi ya zauna wajan da take tare dayi mata sallama amsawa tayi, sannan yace kiyi hakuri na zauna ba tare da neman izininki ba,dan murmushi tayi tare da tashiwa tace babu damuwa na gama, yace ya zaki tafi daka zama na, plz ki zauna duk maganan da yake mata da turanci yake yinshi, tace sorry ina sauri dai2 lokacin mai amsan kudin yazo tazo zata bayar ya riga ya biya kallonshi tayi a karo na biyu tace nagode tana fadin haka tabar wajan binta yayi da kallo tare da fadin sai yanzu na sami matar aure domin duk irin quality din da yake nema wajan Mace ya gansu a tare da ita wacce ko sunanta bai sani bah...
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
130to135
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Dan lumshe ido yayi tare da tashi wanda kamshin turarenta duk ya cika shi, motarshi ya shiga benz yaja yayi Gida, waye yazeed? Yazeed dane daya tilo wajan iyayenshi bawai ina nufin shi daya Suka haifa ba yana da yaya Mace wacce tana London ita da mijinta, sai shi da iyayenshi suke masifar So kasan cewanshi karami kuma namiji shine yake gabansu kullum babanshi Alhaji Ibrahim dan asalin sokoto ne, yana sana'an mai yana da gidajen mai da dama, yana da kudi sosai amma a abuja suke zaune, tun tuni suke fama da dan nasu yayi aure amma yaki yi Mum dinshi hjy Bilkisu har Yaran kawayenta take kawo mai amma yaki zaba, ganin haka yasa ta zuba mai ido, yana da burin auren Mace mai aji wacce tasan kanta, koh da yazeed yaje Gida tunanin indo yaita yi wanda abun yazo mai a bakon abu, dan murmushi yayi domin yasan bai taba ganin abu yana So ba bai samu ba, yazeed ba fari bane Ba kuma baki bane, chocolate colour kenan yana da kyau dai2 misali, koda indo ta koma Office kira ta samu daka Office din director inda za suyi meeting bayan Sun shiga nan aka fada mata ranakun da zata dinga zuwa Monday da talata, ran Monday da safe talata kuma da yamma hakan ya mata dadi ga kuma albashi mai tsoka, bayan an fito daka meeting dinne ta kira driver yazo ya dauketa bai dade ba yazo, Suka wuce Gida.
Tunda A Majeed ya shiga bedroom dinshi bai fito ba domin yanda yake jin jikinshi wani iri ga kamshin turaren indo daya dameshi yasa shi cikin wani yanayi dakyar ya tashi ya fada toilet yayi wanka amma still kamshin na nan sai juyi yakeyi tare da kallon inda ta cijeshi yana dan shafawa a hankali, yanda yake ji a zuciyanshi yafi zafin cizon sau dubu, domin babu komai sai son indo dake addabanshi, zazzabi ne ya rufeshi wanda yasa ya kasa fitowa waje koh sallah a daki yake yi dan bazai iya zuwa masallaci ba, haka ya kwana baiko leko ba, yana ciki yana fama da zazzabi sosai,
Indo da mum suna zaune a falon kasa, abdul ya shigo da sallama, duka Suka amsa da Fara'a, abdul ya gaida Mum cikin kulawa ta amsa da abdul har yanzu dai kana ta fama, dan murmushi yayi tare da zama, Mum taci gaba da fadin ni inaga daka hakura da yarinyar wlh ka auri wata nan gaba in Allah yasa matarka ce sai ayi, indo ce tace Mum niko nafi son ya auri yarinyar wlh saboda irin halin da take ciki, Mum tace hakane aysha taimako ne amma Abu yau wajan shekara biyar ana fama, indo ta danyi shuru can ta nisa tace niko Mum dan Allah inaso inje inga yarinyar, Mum kallonta tayi tare da fadin babu damuwa zan fadama Dad sai kusa rana, Abdul yaji dadin hakan sosai, masu aikin gidan ne suka Kawo ma Abdul Abun taba baki, ya kalli indo yace ya Office din? Indo tace Alhmdlh, wayan Mum ne yayi kara dauka tayi ban san mai ake fada mata ba naji tace gani nan zuwa, kallon abdul tayi tace wai A Majeed ne tun jiya daya shiga Gida bai fito ba, gashi matarshi bata nan shine driver dinshi ya kira, abdul yace bari inje in gani, mum tace muje tare, Bin abdul tayi akabar indo a gida wacce tunda taji hakan jikinta ya mata wani iri, daki ta koma ta kwanta tana jin wani iri.
Koda su Mum sukaje gidan a dakinshi suka sameshi ya lullube duk da AC din dakin a kashe yake amma yana ta rawan sanyi cikin tashin hankali Mum ta kira No Dr dinsu wanda yace mata gashi nan amma baya kusa zai dan kai nan da 30mnt,kwatancen gidan A majeed tamai sannan ta kashe, abdul fita yayi yabar Mum ita daya cikin tashin hankali tama rasa abunyi jin muryanshi tayi yana fadin aysha I love You come back to me I will treat you like a queen, shuru tayi tana mamaki, daukan wayanta tayi ta kara kiran Dr din yace yana hanya karta damu, Mum tace koh su Kawo shi hspt ne, yace ta bari ya kusa zuwa ba'a dade ba sai ga Dr din da abdul nan aka fara dubashi inda Dr ya mishi allura tare da bashi Magani, yace ma Mum a bashi abinci yaci, amma mai ruwa, mum da sauri ta hado mishi Tea cikin kitchen din da yayi kura dan Zainab ta Kori masu mata aiki sai dai wani lokacin ta kira azo a Mata shara duk saboda gudun kar a kara nanata abunda akayi da indo, mum rikoshi tayi tana bashi tea din jikinshi yadan fara rage zafi dan alluran da aka mai,mum ta bashi Magani yasha nan dr yama Mum sallama tace ya tsaya su tayata kama A Majeed din a sashi mota domin gidanta za'a kaishi hakan koh akayi aka kamashi suka nufi gidan mum din, sama akayi Dashi kusa da dakinta inda aka kwantar Dashi akan gadon dakin, idonshi a lumshe daka gani yana fama da ciwan sosai, Mum ruwa ta dibo tasa towel a ciki tana matsewa tana dan shafamai a jiki, lokaci daya zafin jikin ya sauka bacci ya daukeshi, Mum wani irin tausayin dan nata take ji, amma idan ta tuna abunda yayi sai taji ranta na baci, domin ya nuna mata baya son gatan da tamai, kun san d'a da uwa😢, dakin indo ta nufa wacce take zaune amma hannunta biyu akan fuskanta daka gani tunani takeyi domin har Mum ta shigo bata ji motsinta ba har saida ta kira sunanta, tayi firgit tare da tashi tana kakaro murmushi tana fadin sannu da dawowa Mum, mum amsawa tayi tare da zama akan gadon dakin ganin haka yasa indo ta zauna a kusa da ita, Mum tace aysha lafiya kuwa? Dam taji kirjinta ya buga kodai A Majeed ya fadama Mum ta cije shine, jin Mum tayi tana fadin aysha wannan irin tunani haka har in shigo baki san na shigo ba, dan Allah ki fadamin abunda ke damunki, ajiyan zuciya tayi tare da fadin babu komai Mum kawai dai ina tuna halin rayuwa ne, da yanda abubuwa sukan canza, Mum tayi dan murmushi tare da fadin hakane Allah babu yanda baya lamarin sa, sai yasa akeso bawa ya kasance mai godiya a duk halin daya sami kanshi, Allah yakan jaraba bawa ta hanyoyi da dama idan yayi hakuri ya dangana sai kiga Allah ya Kawo mai sauyi cikin sauki, indo wacce hawaye ya zubo mata a fuska tace hakane Mum sai yasa a kullum nake kara godema Allah daya hadani daku a rayuwa na, Mum janyota tayi jikinta tana fadin ki daina hawaye Allah ya fimu sanin dalilin haduwan mu duk da abunda ya hadamu ya raba mu amma Allah bai sa mun rabu ba har yau muna tare wanda zan so mu..... Dan shuru Mum tayi ba tare data karasa abunda take son fadi ba, indo jin tayi shuru ta dago ta Kalli Mum wacce idonta yake hawaye cikin tashin hankali indo take tambayan Mum lafiya kuwa? Mum rike ma indo hannu tayi tana dan murmushi ga hawaye kuma na zuba, tace aysha Allah yasa min sonki tun kafin in ganki tun lokacin dana ji labarin ki nake burin in taimaka miki, naso ace in kasance dake har abada domin nasan in A Majeed yana tare dake har abada muna tare sai mutuwa,dan shuru Mum tayi Kafin tace nasan nan bada dadewa za kiyi aure ki tafi gidan wani May be ma ya hanaki zumunci Dani, wani hawaye ya zubo ma indo mai zafi tare da fadin Mum har abada ke mahaifiya tace duk Mai sona dole ya soki,mum rungume indo tayi tare da fadin Allah ya miki albarka ya baki yara masu miki biyayya inga jikoki na, indo rufe fuska tayi ba tare data amsa ba, amma a zuciyarta ta amsa, mum tayi murmushi tare da fadin bari inje in duba A Majeed inga ko ya tashi, indo da mamaki take kallonta, Mum kaman tasan abunda take tunani tace nasa an kawo shi nan dan in kula Dashi, Indo cikin murya wacce ya dashe tace ya jikin nashi Mum tace da sauki, bayan fitan Mum ne indo tayi ta tunani akan maganganun Mum, tabbas abunda ta fahimta Mum har gobe tana sonta da dan nata, kai indo ta girgiza tare da fadin ba haka Mum ke nufi ba kawai tana son in yafe mai abunda yayi min ne da wannan tunanin indo tafi yarda dan haka ta tashi itama ta fita, motsi taji a kusa da dakin Mum din dan haka ta shiga Mum ce a ciki tare da A Majeed wanda yake kwance idonshi a lumshe kaman mai bacci amma idonshi biyu, kanshi ke mishi ciwo sosai ga zazzabin yaki sauka, Mum tace aysha inaga asibiti zamu gskya, jin an kira sunan wacce yake burin gani yasa ya bude ido a hankali, dai2 lokacin ta matso kusa da gadon idanshi a kanta yana mata murmushi, dakewa tayi domin irin kallon da yake mata yasa take jin wani iri, murya na rawa tace mai ya jiki?amsawa yayi da fadin kaina kaman zai fashe tanan gefen tare da nuna mata yana maganan ne dakyar, tashi tayi ta fita tare da cema Mum bari in duba shi, jim kadan sai gata da abun gwada VP, wayan mum ne yayi kara ta dauka tare da barin dakin, a hankali ta zauna gefen gadon tare da fadin Kawo hannunka,wannan ne karo na farko data mishi magana tunda ta dawo kasar, kaman dama jira yake ya mika mata jallabiya ne a jikinshi mai gajeran hannu ta daura abun a hannun lumshe ido yayi ga kamshin turarenta na dukan shi, idanta ya sauka a inda ta cijeshi domin taga shaidan hakori wani iri taji a ranta, jin muryanshi tayi yana fadin haka kike ma mutane a hspt kina taba su.......
Taku maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
135to140
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Mamaki maganan ya bata dan haka bata kulashi ba sai fara danna abun takeyi tana dubawa, jin tayi shuru yasa ya bude idonshi daya canza