Showing 72001 words to 75000 words out of 85238 words
Chapter 25 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
ina? A Majeed yace ina gidan Mum, yace ok gani nan zuwa, basu dade da gama wayan ba saiga abdul yazo nan suka fara tattaunawa inda yake fadamai gobe zasu bar kasar shida indo, Abdul yace Zainab ta yarda kuma? A Majeed yce itace ma tace yakamata muje tare da aysha din, Abdul yace kai Zainab tayi sauki ,A Majeed yace sosai kuwa ni har mamaki take bani wlh dariya suka sa su duka, bayan mum da indo an shiga daki Mum ta kalli indo tace aysha badai ya miki wani abu koh? Tace eh Mum baya min komai tana maganan ne cikin jin kunya ,mum dai tana zargin indo tana da ciki dan tayi mugun haske da kyau sai dai kuma bata tabbatar ba dan tasan amare suna irin wannan kyan musamman idan hankali a kwance yake yau idan akace aysha nada ciki ban san irin murnan da zanyi ba zanga jika na, A Majeed ne ya katse ma mum tunani daya budo kofar tare da fadin yanzu dai Mum ni baki da lokaci na dariya tayi tare da fadin toh yau kuma tanan aka bullo shima dariyan yayi tare da fadin Mum bari muzo mu wuce, Indo bata so ba dan basu wani dade ba, mum tace inkun dawo daka tafiyar nan saiku shirya kuje garin su aysha kaga danginta dan baka sansu ba yace hakane Mum, bayan sunyi sallama ne Mum taba indo su dambun nama dasu snack taso ta bata Magani amma Tana tsoro kar ace tana da ciki ya zube, bayan sun fito Abdul ya gaida Mum sannan suka gaisa da indo, inda take tsokananshi da angon watan gobe dariya yayi sannan suka fita su duka, A Majeed direct gidan Yusuf ya kaita taji dadi sosai tare da mamakin dama yasan gidan ne, kiran Yusuf yayi tare da fadin gamu a gate yace ku shigo mana bayan Sun shiga yusuf yasa aka musu tarba mai kyau indo tace yaya Yusuf ina Anty na? Yace Tana gidan abba bata san zaku zoba ma, tace ya jikin abba din yana shan Magani kuwa? Yace eh da sauki har ya fara dan jan kafa kinga sauki ya fara samuwa,tace Alhmdlh Yusuf ya kalli A Majeed yace a tayani yima dady godiya yasa an sako ma abbana kayanshi da costume suka kama, A Majeed yace Allah ya taimaka nan suka fara fira inda A Majeed yake Cema yusuf idan Sun dawo daka tafiya zasu garinsu yusuf yace Allah ya dawo daku lafiya nima inason inyi maka magana akan ya kamata aysha taje, yace tare ma zamu insha Allah sunyi fira sosai kafin suka koma Gida, a falo duka suka zauna A Majeed ya kalli aysha tare da fadin Baby wai miye labarinki ya akai kika san Mum? Dam taji gabanta ya fadi amma saita dake tace baka san koni wacece ba harka yarda ka aureni? Yace aysha plz tel me kin san yanda auren namu ya kasance tun farko inaso inji daka bakinki plz hawaye ya fara zubar mata......
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
230to235
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Janyota yayi jikinshi tare da rungumeta yace Baby plz tel me ina bukatan sanin labarinki, a hankali ta fara magana zan fada maka..... Labari ta fara bashi da irin wahalan da tasha da yanda ta hadu da abdul har zuwa sanda akayi aurensu, A Majeed shuru yayi cikin matsanacin tausayin matar tashi lallai tasha wuya sosai amma zai zame mata uwa uba zai zame mata gata wani irin sonta yaji yana kara shigarshi lokaci daya lallai Abdul aboki na kwarai ne dama aysha ce yarinyar da zuka zubar ma kayan tallah Ashe itace abdul yake so amma ya bar mishi ita, kara matseta yayi a jikinshi tare da fadin kibar kuka Baby lallai labarinki abun tausayi ne insha Allah duk wani wahala ko maraici ya Kare dan zan zame miki uwa da uba zan baki gatan daba kowa ke samu ba, a hankali ta furta kalman nagode cikin kuka, hannu yasa ya fara goge mata hawaye tare da fadin ya kamata ki bude association na taimaka ma marasa galihu da wanda ake zalinta, tace inason inyi hakan amma nasan bazaka barni ba, yace zan barki baby jin labarinki yasa na kara yarda da matata nasan bazakiyi abunda zai ban kunya ba na yarda dake nasan zaki karemin mutunci na a duk inda kike, tace nagode da mijina ya yarda dani, yace amma ki bari komai za'ayi sai mun dawo hannunshi yasa akan kirjinta yana fadin ya naga suna kara girma anya babu ajiya na a jikinki? Dariya tayi tace babu komai tare da tashi ta haura Sama shima binta yayi yana fadin muje in duba in gani, sukai ciki.
Washe gari wajan karfe biyu jirginsu ya daga zuwa London, bayan sun sauka a airport suka hau taxi duk da Dad dinshi yana da Gida a London yace a hotel zasu sauka, direct hotel aka kaisu,indo taji dadin yanayin kasar tare da ganin tsaruwan kasar, bayan sun sauka a dakin da suka kama mai kyau ga girma dakin kaman ciki da falo ne akwai wajan kujeru idan ka kara shiga wata kofa bedroom ne da toilet a ciki, indo akan kujeran dakin ta kwanta dan ta gaji kallonta yayi tare da fadin Baby lafiya kuwa? Tace na gaji da yawa dan murmushi yayi tare da cire mata takalmin kafanta ya ajiye a gefe yace come on muje kiyi wanka sai kici abinci sai mu huta gaba daya dariya tayi tare da fadin anjima zanyi bacci nakeji yanzu ni bana jin yunwa, kallonta yayi, ganin dagaske bata da niyan tashi yasa ya dauketa yayi toilet da ita dariya takeyi tare da fadin plz ka saukeni anjima zanyi bayan sun shiga toilet dinne tace ya fita tayi wankan yace shi zai mata tunda ta gaji babu yanda batayi ba amma haka nan ya cire mata komai tare da kokarin yi mata wankan amma zancen saiya canza salo dan ganin kirjinta wanda yake rudashi dan yana son orange sosai gashi aysha Tana dasu, shafawa ya farayi yana wasa dasu tare da murzasa ido ta Fara lumshewa cikin wani yanayi mai wuyan misaltuwa sucking din boob din ya farayi da karfi ta rikeshi tare da shafa mishi bayanshi da kanshi Tana sauke ajiyan zuciya tare da nishi....... Saida suka dawo hayyacinsu sannan sukai wanka tare da alwala suka fito sallah sukayi ta tashi ta duba jakanka,kallonshi tayi tare da fadin babu cream din dazan shafa, yace yanzu kizo muje mu siya sai muci abinci in mun fita, tace bacci nakeji fah kallonta yayi tare da fadin bazan bari ki kwanta ba har sai kinci abinci baki ta turo sannan ta tashi ta canza kayan jikinta tasa wata doguwar riga tare da boyfriend jacket ta yane fuskanta da Gyale, fita sukayi a kafa suna dan tafiya Tana makale a jikinshi har suka karasa wani super market gefe kuma akwai wajan cin abinci wajan cin abincin suka nufa bayan sun zauna yace mai zaki ci?tace burger nakeso yace ba snack ba abinci wannan sai a siya idan kinci abinci, tace ni shi zanci, babu yanda ya iya shi yasa aka kawo mata shidai yaci nashi abincin, bayan sun gama yasai mata su snack da yawa suka fita super market din suka shiga yana tura keken kayan Tana daukan abunda take bukata har suka gama ya biya suka dawo, suna shiga ciki ta kwanta sai bacci dariya yayi tare da girgiza kai falo ya koma yana kallo tunawa yayi bai kira Zainab ba dan haka ya dauko wayanshi yasa sim dinshi na London doka ma Zainab kira yayi bugu uku ta dauka tare da fadin dear I miss you so much, cikin jin dadi yace nima haka dear ya kike? Tace lfya qlau ya sister dina? Yace Tana lafiya nan sukai fira cikin kulawa daka karshe sukai sallama yana mai kara alfahari dajin dadi domin burinshi kullum yaga Zainab ta canza yanzu gashi ta canza din, Mum ya kira suka gaisa tace ina aysha din yace Mum Tana bacci tace OK inta tashi a gaida min da ita sannan sukai sallama.
Tunda suka zo London kullum indo bacci basu samu sunyi yawo ba kaman yanda taso gashi bata son cin wani abinci sosai sai dai abu daya bataso A Majeed yayi nisa da ita dan tace Tana son kamshin jikinshi duk da ta fahimci abunda ke damunta amma tayi shuru dan bataso ya sani yanzu, shiko abun na damunshi yawan baccin da takeyi ga zaban abinci yau tace wannan gobe wannan, yana zaune a falo ta fito cikin shiri tasa riga da wando tare da daura suwaita a kai mai tsawo, hannunta tasa a gashin kanshi Tana yamutsawa tare da fdin my one tashi muje yawo kasan bamu je ko ina ba, kallonta yayi tare da fadin yau babu baccin? Dan murmushi tayi tare da fadin yau banaji, tashi yayi suka fita ranan sunyi yawo sosai tare da siyayya da yawa sai dare suka dawo suna shiga tayi toilet tayi wanka tare da alwala doguwar riga tasa tayi sallah Tana idarwa ta kwanta a wajan ta fara bacci shigowa yayi ya gnta a kasa Tana bacci dariya yayi tare da fdin bby gskiya gobe dole in kaiki hspt wannan baccin yana cutana, daukanta yayi ya kwantar da ita akan gado tare da rufeta da blanket shima kwanciya yayi kusa da ita tare da janyota jikinshi ya rungumeta a haka bacci ya daukeshi shima.....washe Gari duk yanda yaso suje hspt taki yarda haka ya barta domin ta dage lafiyanta qalau haka taita daurewa suna fita yawo tare da siyayya satinsu biyu cif suka fara kokarin komawa Gida, ana gobe zasu koma suka kuma fita siyayya sosai.
Karfe biyar Suka sauka a Nigeria inda driver gidan Mum yazo daukansu direct gidan Mum suka nufa an shirya musu abinci kala2 Mum tayi mamakin ganin yanda indo ta koma ta kara haske kyau har dan jiki tayi gwanin Sha'awa jikin yayi bul2 Mum yanzu ta tabbatar da abunda take zargi sai dadi takeji tama rasa mai zata bata Mum tace aysha muje kuci abinci bayan sun nufi dinning indo tace ita ta koshi A Majeed ya kalleta tare da fadin wai mai yake damunki ne aysha kwana biyu kallon Mum yayi tare da fadin Mum ki mata magana muje hspt haka tun a can bata cin wani Abu sai snack ga bacci yanzu sosai, Mum tace aysha ya kamata kije a dubaki indo dai shuru tayi dan ita tasan maike damunta, jin Mum tayi Tana fadin bari in kira family Dr dinmu daukan wayanta tayi ta kira family Dr dinsu ita kadai take duba Mum haka Dad Shima yana da nashi, bata dade ba sukazo nan suka gaisa tare da fadin Dr aysha Ya aiki Tana kallon indo wanda kallo daya ta mata ta gane Tana da ciki, nan Mum ta mata bayani akan canjin da indo tayi Dr tayi dariya tare da fadin bari in duba ta Dr aysha muje ciki, tashi indo tayi suka shiga ciki, ta bukaci ta bata fitsari indo tace Dr basai kin gwada ba dan nasan ciki dinne Dr tayi dariya tare da fadin shine kika ki gaya ma mum, tace wlh kunya nakeji yanzu saiki fada mata, fita Dr tayi jim kadan sai ga A Majeed cikin farin ciki da murna a zaune ya ganta a dakinta na da rungumeta yana fadin aysha u r pregnant Alhmdlh Allah na godema ashe nima zanga dana ina sonki Baby ban taba jin labarin da yasa ni farin ciki irin haka ba tun bayan da kika furtamin kalman I love you surutai na soyayya ya dinga mata ji yake kaman ya goyata dan murna haka Mum ta shigo ta samesu ganin Mum yasa ta fara kokarin jan jikinta shima sakinta yayi indo ko kunya taji Mum ta fahimci hakan amma saita basar tare da fadin yanzu dai Dr tace zaki hspt kiyi scan kiga lafiyan jikinki dana Baby Mum tana maganan ne cikin farin ciki duk wanda yaganta yasan Tana murna A Majeed yace Mum bari mu wuce Gida saiki bamu masu aiki ko mutum biyu ne, Mum tace ok amma daka barta in an gyara gidan sai ta koma ko zuwa gobe, babu yanda ya iya dole ya yarda duk da ba hakan yaso ba wucewa yayi masu aiki kuma driver yakai su, A Majeed gidan Zainab ya nufa tayi murnan ganinshi duk da ranta na mata daci tare da kishin mijin nata a hankali ya furta dear baki da lafiya ne? Tace maika gani yace kin rame dariya tayi tare da fadin lafiya na qalau kawai nayi missing dinka ne, peck ya sakar mata a goshi tare da fadin nima nayi missing dinki my dear, ranan dai a gidanta ya kwana amma bini2 ya fita ya kira yaji lafiyan aysha, yace ma Zainab itama gobe zata tare a gidanta ta nuna jin dadinta sosai, washe Gari kaman yanda yace haka kam akayi Zainab bata dauki komai ba sai kayanta na sawa shima saida aka kira mai mota dan kayan suna da yawa, bayan Sun karasa ya nufi gefen Zainab din komai an gyara yayi kyau sosai komai ansa sabo kal, hugging dinshi tayi tare da fadin gidan yayi kyau sosai, nan aka fada duniyar love dama an dade ba'a hadu ba, a kullum yana mamakin yanda Zainab ta yarda take bashi jikinta, fita yayi tare da fadin zaije ya dawo gidan Mum ya nufa dan dauko Indo amma Mum tace ya barta ta kara kwana biyu dan sunje hspt dazu ance cikin wata daya ne da kwanaki Tana bukatan hutu dan cikin baiyi kwari ba abu kadan zai iya sawa ya zube, A Majeed babu yanda ya iya kodan lafiyan matarshi da Baby dinshi dole ya hakura yace Mum kwana nawa za tayi? Tace ban sani ba sosa kai yayi tare da fadin inaso ne dama in dauko mata kaya Mum tace Tana da kaya a nan, shuru yayi tare da fadin yauwa na siya kayan akwatin ta zuwa gobe koh jibi zasu iso kayan sai a kawo mata nan mum tace hakan yayi, kaman yanda yace an Kawo akwatin tare da kayan tsaraban da sukayi akwati guda 18 ya mata ko wanne cike yake makil da kaya gana tsaraban da sukayi mum tace bari a cire mata wanda zata bukata sai akai mata sauran Gida hakan akayi kuwa.
Yau satin indo biyu gidan Mum A Majeed kullum yana sintiri gidan shi duk ya kosa matarshi ta dawo Gida itama ta gefen indo din hakane dan Tana son ta jita jikin mijinta musamman kamshin jikinshi da take masifar so, yanzu ta rage yawan bacci sai dai kwadayi dason abu mai yaji, Tana zaune A Majeed ya shigo dakin da take tace yauwa my one rogo nakeso plz, yace rogo dan shuru yayi tare da tunanin miye shi dan bai san abun ba, tace eh yace a ina ake saidawa? Tace nima ban sani ba ni kawai shi nakeso, yace toh naji wani iri ne abun nan ta Fara fadin zaka ganshi fari kaman doya ana saidawa a kwano yace oh na ganeshi baby plz ban san ciye ciyen irin wannan abun kar yaja miki matsala, bata fuska tayi tare da fadin nima babu abunda zai min kawai ka siya min, kallonta yayi yanda take wani daurewa yace ok naji toh zan siyo sai a dafa miki a nan tace toh tare da sakin murmushi tashi yayi ya fita driver yaba kudi ya siyo mata bayan an kawo yasa aka dafa mata bayan ankai mata ta fara ci sosai kallonta yake tayi yanda take ci Tana jin dadi kaman wani nama amsan kwanon yyi tare da fadin ya isa haka tace plz ka bani wlh ban koshi ba, mum ce ta shigo Tana fadin lafiya yace Mum tun dazu take tacin abun nan kar ya mata wani abu, mum tayi murmushi tare da fadin kaga ka bata kayanta taci babu abunda zai mata badan yaso ba ya bata ta zabga yaji da garin kuli, yace mum kin gani koh dariya Mum tayi tace babu abunda zai mata kasan duk mai ciki akwai abunda take so bai dade ba ya wuce, Gida ya nufa Zainab ta tareshi tare da fadin wai ina aysha ne tunda nazo ban ganta ba, yace Tana gidan Mum bata jin dadi cikin kulawa tace waiyo maike damunta? Yace she is pregnant wani irin duhu ta gani tare dajin wani dum lokaci daya kuma ta Saki kuka tare da fadin shikenan na rasa ka har abada bazaka taba dawowa gareni ba har abada kallonta yayi tare da fadin Zainab Wannan wani irin magana ne haka? Tace Ciki fah kace Tana Dashi shikenan yanzu zanga canji a gidan nan tunda ni Allah bai ban ba kamota yayi tare da rungumeta yace kiyi hakuri Zainab haiyuwa na Allah ne kema karki fidda tsammani Allah bai manta dake ba insha Allah kema zaki sami ciki ki haiyu kaman kowa, nan yaita rarrashinta tare da fadin idan aysha ta haiyu zai bata rikon dan data haifa, jinshi kawai take amma zuciyarta babu komai sai takaici da bakin ciki tare dayin dana sani nashan maganin hana daukan ciki da takeyi dan a yanzu taji Tana sha'awan haiyuwa tunda akace Indo nada ciki, tashi tayi tare da nufa daki danta kwanta binta yayi yana kara bata hakuri akan zata samu itama insha Allah....... Watan indo daya cif ta dawo Gida ranan A Majeed ji yake kaman ya goyata dan murna Mum ta bata masu aiki har biyu wanda zasu dinga mata