Showing 9001 words to 12000 words out of 85238 words
Chapter 4 - Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel By Maryam Obama.txt
basu maganin Suka nufi gidan su mum dake abuja domin tace ba zata gidansa ba, hakan akayi, driver ya aika yace ya siyo mai jallabiya guda biyu da zai sa, Kafin ya koma gida, wanka yayi sannan Mum ta kawo mai abincin da tasa aka siyo kafin tayi girki, kadan yaci sannan ya kwanta, bacci ne ya dauke shi, ganin haka Mum ta nufi kitchen ta duba kayan ciki, abunda babu ta bayar a kawo mata su, wanda suka zo tare kuma ta basu kudi tare da cewa suba driver ya siyo musu abunda suke so, Mum ta kammali komai ta nufi dakin dan nata, ji tayi yana waya yana fadin yanzu Baby kina ganin kin kyauta yau wajan 7 days ina kiranki baki packing, ban san mai take ce mishi ba,naji yana fadin kin san ina missing dinki sosai har hakuri na ya kare yau na dawo daka hspt, gskya Baby kina cutana da yawa, shuru yayi yana sauraranta Kafin yace ok plz come back 2moro, I love you too My angel, kashe wayan yayi Mum dake tsaye gaba daya takaici ya kamata wlh bazata sabu ba, idan shi baison ciwon kanshi ba, to ita tasan zafin haiyuwarsa, dakin ta karasa ta ganshi a zaune murmushi ya sakar mata ganin fuskan Mum din a daure yasa yasha jinin jikinshi tare da fadin Allah yasa ba maganan matarshi zata mishi bah,mum zama tayi a gefen gadon dakin tace ya jikin? Yace da sauki My Mum, dan murmushi tayi tare da fadin muje kaci abinci,yace No Mum bana jin yunwa sai anjima zanci, tace toh shikenan, tashi tayi ta fita, jim kadan sai gata ta dawo da wani bowl a hannunta naman Rago ne, bashi tayi tace gashi kaci amsa yayi ba tare da musawa ba, ya fara ci, fita ta kuma yi ta dauko mishi maganin shi da drinks, duka naman ya cinye tare dashan maganin, dan fira Suka fara can mum tace A Majeed kai yanzu haka kake so kaita zama koh? Shuru yayi domin yasan za'a rina, taci gaba da fadin yau matarka tana can kasan gobe tana can, baka da iko da ita, inkai baka son kanka karka manta ni ina sonka kuma kasan bazan dauka ba, tun tuni nake maka maganan karin aure kana nokewa toh wlh kaji na rantse wannan karan sai ka kara aure, inko kaga bakai auren nan ba toh wlh bana raye, yau shekara nawa dayin aurenka har yanzu shuru babu karuwa yau mata nacan gobe tana can, shidai shuru yayi dan yasan Mum tunda ta rantse dakyar ta canza zance, zufa yana keto mai tako ina, Mum tace na baka nan da wata daya ka Kawo min wacce kake so tashi tayi ta fita daka dakin fuuuu, A Majeed innallilahi wa Inna'ilaihira jiun kawai yake fada, yanzu da wani idon zai kalli zainab yace zai kara aure, bayan ya mata alkawarin bazai mata kishiya ba, kuma sun tsara yanda zasu tafi da Al'amarin su, kai gskya bazai yihuwa ba dole yama Mum bayani yanda zata fahimce shi, duk da yasan yana da karfin Sha'awa amma hakan ba matsala bane zai fara azumi, hmm tabdi lallai kana da aiki A majeed, bari dai nayi shuru🙊 inga yanda zata kaya .
Indo ta fito da dambu ta nufi tasha kaman jiya aka siye duka, tana zaune a wani benci a cikin tashan dan bata son komawa yanzu, kaman daka sama taji magana waigawa tayi taga Abdul, ita harga Allah ta manta yace mata zaizo, cikin sauri tace ina wuni yaya Abdul, yace lafiya qalau kanwata tun dazu nake ta jiranki a waje nayi wajan awa daya, naji shuru shine nace bari in shigo koh zan ganki, tace kayi hakuri wlh na manta ne,kuma tun dazu na siyar, yace toh yanzu ni zan koma abuja, gashi baki da waya, ni kuma kullum ina son jin muryan kanwata, murmushi tayi tace hakane sai dai idan ka dawo, yace kai gskya zan dan dade coz ina da aiki sosai yanzu dai na samo mana mafita, muje waje, tashi tayi ta bishi Suka fita waje, mota ya bude ya dauko wani leda, yace gashi waya ne, akwai sim a ciki, sai kisa caji, kai ta girgiza tace ka barshi ni bana bukatan waya, yace saboda me? Tace hakanan mu bamu da wuta ma a garin mu, shuru yayi cikin mamaki,babu yanda baiyi ba akan ta amshi wayan taki, haka ya mayar tare da bata kudi yace tunda taki amsa shima dai Kin amsa tayi sai da yayi mata da gaske Kafin ta amsa, sallama ya mata tare da fadin zai zo ranan juma'a koh sati, tace toh sannan ya wuce, tsallaka titi tayi sai ga dan jummai yasha gabanta, yana fadin indo ina washe baki tunda kin hanani kanki zan turo gidanku inna aureki ai babu wanda ya isa ya hanani inyi yanda naso koh, tace waye zai aureka Allah ya kiyaye, dariya yayi tare da fadin wlh saina aureki indo ke gobe2 zan turo gidanku sai inga ta tsiya........
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*DASHEN ALLAH......*
*(TOGETHER WE STAND NENVER DIVIDE FOR ALL)*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
45to50
*DEDICATED TO....*
*FAIZA DABO......Allah Ya raya Baby girl akan tafarkin addinin musulunci👏*
Indo bata kara cewa komai ba, tayi gaba abunta, binta yayi da kallo tare da lashe baki yana fadin inna aureki zan kwashi dadi, gida ta nufa tayi sallama Tani na zaune Akan tabarma duk ta cinye, tace sannu da gida inna? Bata amsa ba sai hannu data mika mata alaman ta bata kudin, mika mata tayi ta girga taga ya cika, Abu ce ta fito da tilin kayan wanki ta zubar a kasa tare da komawa ta dauko wasu, kayan da yawa sosai ta Kalli indo tace ga sunan kizo ki wanke Min ta wurga mata naira ishirin gashi ki siyo sabulu, indo babu yanda ta iya hakan ta dauka ta fita bata dade ba ta dawo, dakinta ta nufa zata shiga tani tace kee ina zaki kuma kizo ki kwashe kayan nan, indo tace inna hijjabina zan ajiye, Tan bata kuma cewa komai ba sai tsaki da taja ta shige daki, indo na shiga daki ta boye kudin da abdul ya bata cikin kayanta dake daure a leda, sannan ta fito ta fara wanki kayan da uban yawa ta dauki Lokaci sosai har wajan karfe goma saura tana waje tana wanki gashi ta gaji ga yunwa, haka ta gama wankin bayanta duk ya rike ga ruwan gidan ya kare, daukan roba tayi ta nufi gidan makotansu ta dibo kadan Kafin safiya yayi, bayan ta gama ta nufi dakin tani sallama tayi tace inna na gama tani tace toh naji mayya saiki tashi kije kisha ruwa ki kwanta domin sauran tuwan dana ajiye miki abu ta cinye,tashi tayi ta fita jiki a sanyaye dakinta ta nufa ta dauko kudin da abdul ya bata ta nufi dakin jamila tura kofar tayi a hankali dan kar ajita, jamila dake kwance ta tashi da sauri jin an bude mata kofa yar fitilan kwanta ta dauko ta haska taga indo ce, tace indo lafiya Kuwa? Indo tace lafiya inna jamila mika mata kudin indo tayi tace gashi ki ajiye min, jamila a ina kika sami wannan kudin indo tace inna jamila wannan mutumin ne ya bani wanda yaban kayan jiya, jamila ta dan bata fuska tare da fadin indo daka yau karki kara amsan abun wani saurayi domin ki tsira da mutuncin ki, indo tace wlh Inna jamila babu yanda banyi ba amma saida yaban, nan ta bata labarin yanda sukayi, jamila tace toh Allah ya saka mishi da alkhairi, yanzu dai bari inga nawa ne, kirgawa tayi taga dubu ishirin zare ido jamila tayi tace kai wannan uban kudi haka, yanzu mai zakiyi dasu, Indo tace inna makaranta nake son shiga wlh ina son nayi karatu in zama wata abu, jamila tace Allah sarki indo sai dai burinki kaman bamai yihuwa bane saboda Tani ba zata barki ba, indo jikinta yayi sanyi domin tasan haka dinne, jamila ta dauko mata shinkafa ta manja taji kayan miya sosai ta bata, nan indo ta fara ci sosai abincin ya mata dadi, tas ta cinye, jamila tace tunda kin gama tashi ki tafi daki kar Tani ta ganki, tace toh tare da tashi ta fita tana sambo kaman munafuka ta shiga dakinta.
Washe gari kaman kullum indo ta Gama aikinta, sai dai abu daya dake damunta rashin ganin Sulaiman kwana biyu, har taje tasha ta siyar da dambu ta dawo gida, ko zama ba tayi ba Tani tace ta daura tuwan dare, haka ta gama Tani ta dan yafa mata kadan kaman wani karamin yaro zaici, dauka tayi taci da babu ai gwara babu dadi, Mlm musa ne ya shigo yana ta sababi ai wannan zancan banza ne, akan wani dalili, Tani tace lafiya kuwa? Yace wlh ina zaune majalisa sai gashi mai gari ya aiko a kirani, ina zuwa wai dansa ne yaga y'ata yace yana so, wlh nasha koh Abu yake magana ashe wancan tsinannar yake nufi, Tani cikin sauri tace toh mai kace musu? Ai ce mishi nayi an mata miji, Tani tace oh yau naga iya shege amma wannan dan mai gari ko dan banza,koda yake ba'a banza ba ta kama masa kurwa, dan mayya ce ta gada wajan iyayenta....... Sallama sukaji mlm musa ya fita tare da amsawa bai dade ba sai gashi cikin Fara'a da jin dadi, yace toh gashi dai Dan jummai ya aiko neman auren indo na kuma bashi, Tani guda ta saki tare da fadin ai dama ita saida irin su dan jummai, Abu dake daki ta fito tana fadin Tani saurayi nane fah? Tani tace ke dallah mai za kiyi da dan jummai wannan matsiyacin aike sai mai mato irin na yaron mai gari, washe baki Abu tayi tare da fadin kai Tani sai yasa nake sonki, Tani tace mlm ai sai asa bikin da wuri koh, yace duk yanda kika tsara ai yayi, indo dake bakin kofa babu abunda take sai kuka, yanzu shikenan dan jummai zata Aura, kazami gashi dan iska yasha yima mata fyade a garin amma maman shi saita fita ta shiga ta rufe bakin iyayen yara jummai akwai shegen bin bokaye bata son laifin danta gashi bata da mutunci, kaf cikin kauyensu babu wanda baya sana'a sai shi, wanda zuciyarshi ta mutu, dakyar indo ta tashi ta shiga daki tana ta sharan kuka.
A Majeed, dakin Mum dinshi ya nufa, ya sameta tana danna laptop, zama yayi kusa da ita tare da fadin mum plz ki fahimce ni, bani da burin tara mata Zainab ta isheni rayuwa Mum plz karki bata min tsarin da nayi, just give me another punishment..... Dakata A Majeed karin auren ne horar wa,? Lallai kayi nisa sosai kaiga Romeo and Juliet koh? Shuru yayi baice komai ba, taci gaba da fadin bazaka gane abunda nake hango maka ba sai nan gaba, Allah bai azurtani da samun yara masu yawa ba, kai daya Allah Ya bani, na dauka zaka so kayi aure danka tara yara inga jikoki na da yawa amma kaida matarka baku da ra'ayin tara yara, inma kai kana dashi matarka bata dashi karka dauka bana son matarka ne, a'a wlh ban taba kinta ba sai dai halayenta da bana so kawai, jikinshi ne yayi sanyi yanda yaji tana magana, yace Mum kiyi hakuri zamu gyara insha Allah, kai ta girgiza tace A Majeed auren ne baka son karawa amma karka manta na rantse maka babu fashi , yace shikenan Mum ni bani da zabi ki bani duk wacce ta miki yana fadin haka ya tashi ya fita fuuu .........
*Naji korafi bana typing da yawa bana posting akan lokaci zan kara yawan rubutu.......*
*Amma sai na fara ganin comment da sharhi sosai zan kara yawan rubutu*
*Taku Maryam obam😘*
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
50to55
*DEDICATED TO....*
*MY ANGEL FAUXY MUM SAHMA❤*
Mum ta bishi da kallo yanda ya fita kaman iska na turashi ajiyan zuciya tayi, tare da fadin zan ko zaba maka, komai za kayi aure dai babu fashi, kiran number din Abdul ta shiga yi, ringing biyu ya dauka tare da gaida ta, bayan Mum ta amsa tace Abdul ina abuja kazo ina son ganin ka, yace toh Mum nima ina hanyar shigowa abuja dinne,tace OK Allah ya kawo ka lfya tare da kashe wayan. Shiko A Majeed Gidan ya bari gaba daya ya nufi gidanshi ranshi a bace yake sosai, dan mai yasa Mum zata wani sa ya kara aure, shi matarshi ta isheshi baya tunanin zai iya hadata da kowa sai dai kawai yace baya son halinta, kuma ai duk abunda takeyi akwai yarinta a ciki nan gaba zata gyara, yanzu taya ma zai Kalli Zainab yace mata zai kara aure, kai No bazai taba yiwuwa ba, inko Mum tayi min haka batai min adalci ba at all, dan gajeran tsaki yaja ya dauki phone dinshi ya kira Abdul, harya gama ringing bai dauka ba tsaki ya kuma ja tare da jefar da wayan.
Jummai ce zaune Tana surfa Bala'i akan danta bazai auri indo ba, yarinyar da tun tana karama yayanta ya lalata ta, shine mafa sanadiyan barinshi garin nan, dan jummai dake zaune yace haba jummai dan me zaki hanani aurenta ni wlh babu mai hanani, ya tashi ya fita yana surutai, kallon mijinta tayi tace sannu aika kyauta kaine a gaba wajan neman auren ma dan jummai wannan yar ko yayi maka kyau Allah ya bada Sa'a, bai ko kalleta ba balle ya amsa saima tashi yayi shima yabar gidan.
Tunda akasa maganan bikin indo da dan jummai, Tani ta shiga ta fita domin tace Abu saita riga indo aure koh kuma ayi rana daya, indo na daki tana kuka saiga yaro yayi sallama wai dan jummai na kiran indo, Tani tace kace Tana zuwa, Tani tayi shewa tare da wage baki tana kiran indo, fitowa tayi cikin hijab, Tani takai mata duka dan ubanki bazaki amsa ba, shegiya makira kawai, maza ki fita dan jummai na jira, bata ce komai ba ta fita, a waje ta sameshi, yana ganinta ya wage baki duk datti, yace indo In dodo, Indo ta dan jummai, har na kosa ayi bikin musha amarci ai ranan zanci dadi, indo toshe kunne tayi dan haushin maganan shi take ji, kwata2 babu tauna zance komai ya fado mishi fada yakeyi, ga warin jikinshi ma kawai ya ishe mutum, yace indo in dodo yanzu idan mukai aure tunda kin hanani ranan mai zaki min, bata kulashi ba sai hawayen dake zuba a idonta, bai damu da shurun nata ba yaci gaba da fadin a salulan garba mai gwanjo naga wani abu da turawa sukeyi, sai su hade bakinsu waje daya suna sha..... Da gudu indo ta shige gida, Tani na zaune taga ta shige daki da gudu, tashi tayi tabi bayanta, tace ke dan uwarki miye haka? Indo tace wlh inna dan iska ne dan Allah inna nifa bana sonshi, dariya Tani tayi tare da fadin aiko kina So ko bakya So wlh sai kin auri dan jummai shegiya gaki babbar yar iska kina bin maza a tasha suna miki juye makira, ko kin dauka ban san komai bane, shegiya har kina da bakin kiran wani dan iska munafuka mai bakin hali maza ki tashi ki fita yar iska kawai, tashi tayi tana kuka ta kuma fita ganin baya nan yasa taji dadi ta dawo gida tayi ta maka mata duka a baya tare da fadin matsiyaciya nan da sati biyu za'ayi bikin inga ta tsiya, daki ta shige tana kuka.
Yau mijin jamila ya dawo garin, murna wajan jamila ba'a magana domin wannan karan kafarta kafar mijinta, ranan jamila anata soye2 Tani ana ta hadiyan yawu tare da yima jamila sannu da aiki 🤣 jamila dai amsawa take amma tasan badan Allah take Mata ba, ranan dai Tani ta zauna anata jan jamila da fira harta gama girki ta zuba ma Tani, nan Tani aka amsa ana ta washe baki ta shige daki🤣 dama shi take jira, Tani da abu suna daki suna kwasar abinci saiga yaro yayi sallama wai ana kiran Abu yayar indo, Abu ta fito tace waye? Yaron yace yaron mai gari ne, da sauri Abu tace kace ina zuwa, daki ta koma ta shafa powder, Tani tana ta mata kirari tana dariya Abu tace kai Tani gskya akwai ki da fada da cikawa gashi har ya kawo kanshi, Tani tace saima kinga ya turo maganan aure, Abu fita tayi ta ganshi ya hade hannunshi biyu ya hade, murmushi take tayi kaman wata sauna, tace sannu yakake, yace lafiya ba tare da bata lokaci ba nidai sonki nakeyi kuma da aure dan haka mai kika ce? Abu tace babu komai na amince yanzu kawai ka turo, yace toh Alhmdlh zan fada a gida sai azo ayi komai cikin lokaci kadan, suna cikin fira saiga indo ta dawo daka tallah ido ta bisu Dashi ta shiga gida tana kuka, har Abu ta dawo gida tani tana ta guda sai kace an daura auren, tun daka lokacin kullum sai sulaiman yazo wajan Abu, indo tun tana jin abun na