Showing 30001 words to 33000 words out of 93195 words

Chapter 11 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11455

Tsine tsine a bakinta.".
Tahir ya fashe da Shegiyar Dariyansa yana Fadin"Allah Sarki Inanni gaskiya ina missing nata. Yaushe zaka gida na bika nima?
Sadiq yace"mu bari weekend, Jiya Abba ke fad'amin Innani na Shinkafi chan ya barota wajen sha'anin Diyar Baba Saminu da akayi, So kuma ba na son zuwa ba ta gida. Abba yace dakyar suka lallasheta da ta ce sai tazo ta ganni ina nan ba uwa ba uba Allah yasa ina Hannu nagari"
Tahir ya kara kwashewa da Dariya kafin yace"Allah ya ja da ran magajin gida da girman kujeran ka.." ya fad'a har yana daga masa babban yatsansa alamun jinjina.
Sadiq ya make hannun yana Fadin"Ka bari Tahir."
Shi ko sai fadi' ya ke"Takawarka Lafiya Autan Umma dan gatan Abba. shalelen Innani. Angon SULTANA"
wata uwar Harara Sadiq ya sakar masa kafin yace"Tahir sunan Sultana ya fita a bakin ka? Inanni bata kyautamin ba"
Ya fad'a yana yamutsa Fuska Tahir ya Dafa kafad'arsa yana Fad'in"Mutumina kaji dadin ka. Kai dan gata ne irin wannan zukekiyar Yarinyar duk ka kai kadai? Ya ke fad'a yana Dariya Lokaci daya yana kashe masa ido d'aya.
Ture hannunsa Sadiq ya yi yana fadin"Tahir Allah ya shirye ka."
Tahir yace"Ni dama Hajjo nima ta kamamin wata achan Daura yar Fara haka Danya Sharaf mallam"
Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Ai tasan halin yan kayanta ne. In ko ta kama maka zaka iya kunya tat
Tahir."
Cikin Magiya da Fuskar Tausayi Tahir yace"Wlh a'a. Kaga da mun gama Hidiman kasar nan muka kama aiki sai kawai kaji mun angwance Rana Daya da yan Shillan mu Abokina."
Dukkansu Dariya suka saka har suna Tafawa kafin Sadiq yace"A'a in muka angwance Rana d'aya wa zai rakani Dakin Sultana?
Tahir ya bushe da Dariya ya Daki kafadar Sadiq da karfi yana Fadin"Shige abokina ashe kana son yarinyar nan sai ka rika wani basar da ita?
Sadiq na mirmishi yace"Tahir ba komai ke bukatar bayyanawa ba. Sultana Zabin Umma ce. Sannan Burin Innani ne, ni kuma kaga matan nan biyu suna da Muhimmamci a Rayuwata da ko wuta suka ce na shiga wlh zan shiga. Sun gama min komai a Rayuwata. Sultana a gaba na Umma ta Reneta yarinya ce karama fa Tahir sai na zauna ina Biye mata? Ni ma yaron ka ke so na koma?
Tahir ya ce da Sauri"ko ba ka koma yaro ba akallah dai ka Damu da ita kamar yadda ta damu da kai."
Sadiq ya mike tsaye yana gyara zaman 3Quater da ke jikinsa lokaci d'aya yana Fad'in"Tahir har yanzu da Sauran Lokaci. Baka gane abunda na ke gayamaka ne? Shekarata Talatin wannan Shekaran Sultana ba ta wuce sha Shidda ba Jss3 fa take. Ba ta ko gama socondary ba, Sannan ni ma ina son Dora Masters dina bayan mun gama Servise din mu, ina da abubuwan yi a gababa ma su tarin yawan da ba na so wani abu ya Daukemin Hankali itama ba na so na zama Silan samun matsala a bangaran karatunta shiyasa kaga ina mata haka kuma mganar kira muna gaisawa, daga gaisuwa da tambayan makaramta bata iya fa mgana da ni,wani Lokacin ma in ta kirani da wayar Umma ina Dauka sai dai ta ce bari ta kaima Umma. Ka kyale yariyanan Kuruciya ne da Wauta ke Dawainiya da ita fa"


Tahir na yar Dariya yace"Kuruciya da Wauta ko dai Soyayya? Wlh Sultana ta na sonka Sadiq"
Sadiq yaja tsaki kafin yace"So? Tahir kai ma shekarunka ba su yi maka amfani ba. Ina yarinya kamar sultana ta san wani So?
Tahir yace"Wad'anda ma basu kaita ba susan So mallam. Ni ka manta yarinya yar Jss2 ta turomin wasikar tana so na? Sai kace me kuma?
Sadiq yace"Abun ya na faruwa ne da yanayin In da mutum ya taso. Rayuwar Sultana ba daya ya ke da matan wajejjan nan ba Tahir. Kawai dai kace ta san ni zan aureta haka iyayenmu suka tsara to na yarda akwai wannan Shaukin na sanin haka Tun da karuciyarta ammh ba zencen so ba Tahir"
Tahir zai yi mgana Sadiq ya kallesa yana Fadin"Tahir.."
Sai ya yi shuru yana jinjina kai kafin yace"Shikenan zamu maimaita mganar nan watarana in da rai da Rabo abokina."
Sadiq ya sauka Daga kan katifar yana Fadin"Ranar jumma'a zamu tafi Daura mu kwana Asabar, Ranar Lahadi mu je zamfara sai mu dawo talata da safe."
Tahir ya mike ya Daka tsalle akan katifa yana fadin"Ehhyeee..Gida gida Dad'i"
Sadiq ya girgiza kai bai yi mgana ba Buta ya dauka ya zuba ruwa yana Fadin"La'asar ta kusa Tahir"
Tahir ya duba agogon wayarsa kafin yace"Da sauran lokaci."
Sadiq ya shafa cikinsa kafin yace"Cikina ya lalace yau ina ta shiga bayi a kamfani"
Tahir ya kwashe da Dariya kafin yace"Ba dole ba. Danwake da wake fa kake ci? Ga yaji. Ai cikin ka ma na baka lafiya a irin yame yamem da ka ke masa ya ci ace kashin ka ya Daina karfi ya koma zawo ma"
Sadiq ya yamutsa fuska kafin yace"Da gaske fa Tahir. In na fito wannan na biyar fa kenan"
Tahir ya zaro ido kafin yace"Ka sha mgani?
Sadiq ya fita da Sauri yana Fadin"Duba in muna da sauran filajin in kuma babu Tahir ka fita ka siyomin. Wlh cikina sai kartawa ya ke yi"
Y na fad'a ya zura a guje ya shige makewayin su na waje Allah yasa ba kowa a baranda sauran masu Dakunan ba su dawo daga cikin makaranta ba.
Tahir na dariya ya saka Rigarsa Fara T.Shirt ya Dauki 500 cikin Jakarsa da ya Dawo da ita daga makaranta ya fita.
Chemist din ba nisa shiyasa ya jawo kofar sai dai ya isa gaban Makewayin da Sadiq ke ciki ya Daga Murya yana Fadin"Na fita ban kulle kofar ba. Ka kula da motsi"
Sadiq na ciki sai ji ya yi ya ce"Uhmmm... Tsuwww..!
Zawo na fita Tahir ya Fashe da Shegiyar Dariyarsa ya tsallaka Baranda yana fadin"Eh lalle dole in nemo maka mgani. kada cikin Dare ka zame min kaya na shiga uku"


********


*Dogon gida*.
Alhamis_8:30am.


Habiba na ke sakawa Danwake a roba, tana tsaye a kaina ta na Fad'in"Adda kada ki sa min da yawa. Ki ijiyemin na anjuma don Allah"
Kai na jinjina kafin nace"ke kam da Danwake Habi"
Dariya ta yi bata yi mgana ba na gama saka mata mai da yaji na mika mata ta karb'a. Sauri ta ke yi ta makara Daki ta shige da gudu.
Ni kuma ta barni ina kiciniyar kwashe wanda na saka a wuta ga mutane suna jira na cikin gida da waje.

Abun ne yanzu na wannan rayuwar sai godiyar Allah. Farko an fara da cire tallafin man Fetur ne, takala ya shiga wani Hali na Babu da k'anik'ani. Sannan sai man fetur ya rika tashi ya na Hauhawa, sai kuma ababen rayuwa da yau da kullum su ka rika tashi suna Hauhawan Farashi komai yanzu ya zama dan zani.
Masu kudin ma suna ji ajika ballatana mu talakawan da ba tallafi sai mun tallafama kanmu da ire iren sano'i'on cikin gida.
Shiyasa komai ya yi tsada har Danwaken yanzu na 400, bai iya kosar da Mutum sai dai aci kawai a gode Allah.
Godiyar da na ke yi ma Allah da Sana'ar ba ta kwace a hannun mu, duk da ciki muke wasu Hidimdimun ammh kuma da Sauki acikin lamarin ba ma abinci, mu ci danwake da Safe ko mu ci wake,Da yammah mu ci shinkafar da muke siyarwa. Amma kuma daman yar koko ce da Farau Farau. Ko ayi mata Faten Tsaki da Shuwaka, sai bangaran ci da shan mu ya samu sauki bangaran Sabulun wanka da na wanki sai kuma in Adda Fati ta yi nukasanin kawowa ammh ta Dauke mana wannan bangaran.
Duk da ina gajiya ammh ba na nunawa ko a fuska aiki na ke yi kan jikina kan karfina ni ce saka Danwake, juyawa kwashewa. Zuzzuba ma Mutane tare da sallamansu Layi a ke yi min abun sai godiya kawai.
Sakamakon ya kasance Safiya sai ki ga babu chanji a Hannuna in aka zo siya nakan ce aje a dawo lokacin na tara yan canji.


Ina cikin Kwashe Danwake Datti yaron Maman Salihi ne ya iso gabana da kyakyawan Kular da tun kwana goma da suka gabata ake zuwa siyan Danwake da ita. Ya na zuwa tun kafin ya yi mgana na ce"Na Dari takwas ko?
Waken Dari hud'u Danwaken D'ari Hud'u sannan manja za'a saka"
naa Haddace lissafin koma waye mai siyan Danwaken nan yana da ka'ida da Tsari ne.
Dariya Datti ya yi lokaci d'aya yana mikamin Dubu daya lokaci d'aya da Fadi'n " ya ce ayi sauri"


Kai na jinjina kawai batare da na yi mgana ba. Bansan meyasa na ji na Damu da ma ko waye mai siyan Danwake a kyakyawan kular nan ba. Ko saboda kirkin da ya ke min ne bansani ba?


Tun ranar farko da ya fara siya ba chanji nace ma yaron da ya aiko ba chanji sai anjuma. Sai ya ce bakomai zai dawo gobe, washegarin da ya dawo na bashi chanjinsa bai karba ba. kuma Tun daga ranar dubu daya yake zuwa da shi cinikin 800 ya ke yi min 200 kuma chanjinsa baya taba Karb'a. Ko na aika da shi zai dawo da d'an aiken ne, kuma yaran gidan mu na son zama akofar gida da Safe haka saboda in ya aike ka ka fito sai ya baka Kudi. Ba ma su ba ni kaina ina jin dadin haka har acikin raina sannan sau biyu ina Tambayan Datti Yaro ne ko Babba ke aiko shi?
Kai tsaye yace"Babba ne fa Tab"
Sai da na yi Dariya ranar da ya Fad'amin haka.
Jin yace ya na sauri ne yasa na ke hanzarin gama kwashewa na Fara sallaman shi, bansan fitowar Amma ba sai jin mganarta na yi a gefe na. "kawo na rika taimaka miki da zubawa"
Na juyo da sauri ina fadin"Amma.."
Bata samun zarafin mgana ba Habiba ta fito da shirin ta na tafiya makaranta, Ta na Fadin"Adda kudin tara zan tafi"
Amma ce ta kwance hab'an zaninta ta Dauko mata naira Hamsin ta ba ta ta karb'a ta na fadin"Sai na dawo"
Ni da Amma muka had'a baki muka yi mata Fatan dawowa lafiya.
Robobin na mutane na tura ma Amma gabanta lokaci daya ina gayamata adadin yadda zata saka musu ni kuma na jawo kular nan mai kyau mai hawa uku yar doguwa da ita.
kullum aka zo da ita sai na Dagata na kallah tana Burgeni ban taba ganin kula mai kyan ta ba.
Ashe Amma na lura da ni har na gama kallo na saka Danwaken na bi kuma Tsarinsa,Wake Dabam, Danwake Dabam sannan yaji dabam da mai.
Ina gamawa na mikama Datti da ke Tsaye yana jirana kafin na yi mgana yace
'"ya ce in ba chanji a bar shi kawai.."


Mirmishi na yi na mika masa ya fice da gudu har ina lekensa Amma ta kalleni ta kara kallona batayi mgana ba sai da muka sallami mutanen da ke kanmu sannan ta kalleni tana Fad'in"Hala Danwaken waye?
Cikin ko in kula nace"Bansani ba Amma. mee barin chanjin nan nasa ne ban taba ganinsa ba"
Amma ta yi shuru kafin tace"To koma waye Allah ya yi masa albarka."
na amsa da Ameen Ameem.


Amma bata barni ba sai da muka gama Duka. Sannan ta barni ina Had'a kayan ita kuma ta tafi raban Fad'a Tsakanin Maman boy da Kaltume.
Ire iren rigimrigimun gidanmu ba sa Damuna wlh na riga na saba.
To abunda ya ke kamar Ibada ayi da Safe ayi da rana ayi da Daddare.
Dambe ko tun zamanin baya an sha cin uban Dambe ballatana Dogon gida yana da karfin suna na Dabi'ar Fad'ace Fad'ace.
Fad'an dai Kaltume ce bata da gaskiya Kuma tsakani ga Allah halinta ne na Munafunci yi ma Mutane Labe in suna waya ko in sun yi baki. Shine ta yi ma Maman boy labe tayi wayarta da mijinta ta zo tana yad'ama su Maman Salihi wai mijin Maman boy neman mata ya ke yi. Taji maman boy nata fad'a a waya. Mgana ta famtsama agida har Maman boy taji shine ta Tada Rigima.


Kaltume sai Rantsuwa ta ke yi ba ita ta Fad'a ba. Maman Salihi ma na Rantsuwan ita ta fad'a mata sauran na maida yadda akayi, Ina jin Amma na ta ba da hakuri Maman boy taja Daramam sai ta yi ma kaltume jina jina,abun takaici mijin kaltume fa na gidan bai riga ya fita ba ake wannan jidalin sai Dura manyan asharai suke yi ba dad'in ji, zagi Irin na ma su b'ata Tarbiyan in yaro yaji su. Shiyasa yaran su ba su da Tarbiya sai kaji munanan zagi a bakinsu ga rashin kunya.
In ana irin haka Daki na ke shigewa yau ma haka nayi ina gama wanke wanke na kwashe komai na kai Daki Sauran Rushin kuma na saka mana Ruwan wanka.
Ya zamu yi? Ba mu da wata mafita ammh gidan Haya ai ba gidan zama ba ne wlh.
Ina fata da addu'an duk wad'anda ke gidajen Haya Allah ya Hore musu su yi na kansu.
Mu kuma irin mu da muka d'and'ana rayuwar gidan kai kaddara ta kawo mu in da muke yanzu sai nayi mana Fatan ganin karshen lamarin.






*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*








*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*




*08*


Ranar Jumma'a tun safe suka shirya tafiyarsu a son samun Sadiq ma tun 6:30am na safe su bi motar Katsina. Ammh nukun nukun Tahir yasa sai dai suka wuce takwas na Safe a zariya.
Kamar shima bai son Halin Tahir ba, da yace su had'a kayansu waje d'aya ya yarda da batunsa.
Sai da ya gama zama ya shirya musu kayansu na tafiya a karamar akwatinsa. Da duk abunda zasu bukata na tafiyan kwana Hud'u, Ammh Tahir da iskancin sai bayan an gama shiryan kayan ya ke fito da Tsirfe tsirfe daga yace ya manta ba'a saka masa kaza ba, sai ya ce ba kaza zai je da shi ba Sadiq yaji kamar ya cire kayansa ya sauya jaka. Sai dai makaran da suka yi yasa ya yi Hakuri Tunda ya san Halin Tahir ya had'a kaya da shi.


Motar katsina suka samu Direct sai sun je ne zasu Hau na cikin garin Daura. A motar KST irin mu cin mutane sha takwas din nan ne, Tahir gaban Mota ya shiga. Shi kuma Sadiq baya son matsuwa sai ya shiga kujerun baya na daga su sai Direba.
Sun Dauki Hanya aka fara Hirarraki na cikin motar haya na abubuwan da ke faruwa a kasarmu.
Tsadar Rayuwa da yadda komai ya sauya sai kuma aka gangaro kan yan sace sace da ake fama da shi na Mutane a hanyoyin mu na tafiye tafiye.
Sadiq na jinsu bai saka baki ba. Saboda shi bai cika saka baki a irin wad'anan hirarrakin ba. Ammh Abun mamaki Tahir har yana zakewa ana Hiran yan kidanafin ya Dage yana ta zagin su yana Fad'in cewa ai yan iska ne sai sun ce a basu kudin fansa an gama Biyansu kuma sai su kashe rai. Duk a motar Tahir ya fi kowa Zakewa muryansa tafi ta kowa amsa kuwwa acikin Motar.
Har yana wani Tada jijiyan wuya Sadiq na ta so ya Juyo su had'a ido ya yi masa gargad'i ta cikin idanuwansa ammh ina Hira ta Rufe masa ido. Yasan mafita daya ce itace wayar Tahir yasan ba ta subucewa daga Hannunsa.
Da Sauri ya tura masa da sako kamar haka "Tahir.. Tahir wlh ka kiyayi kanka ka na Daga murya in akwai su acikin motan nan fa?
Ganin Sakon Sadiq yasa Tahir ya Dawo cikin Hayyacinsa. Sai ga bakinsa ya yi gum wani na gefensa har ya na tabosa irin acigaba da Labarinan ammh ina Sai Tahir ma ya fara barcin karya ganin Dannan wayar tasa ma bazai fisheshi ba.
Kuma ya na kama bakinsa sai Hirar ta Sauya daga baya ma kowa ya cigaba da Harkan gabansa Daman Tahir ne uban yan Zakewa.
A haka har suka isa katsina sha d'aya na Safe daganan suka sake samun motar Daura.
Sai daya saura na rana suka iso Daura. Gidan su Tahir babban gida ne, na ginin kasa Inda yayyensa da matansa ke ciki da Sauran iyayansu da kawunansa. Tahir maraya ne ba uwa ba Uba hannun Kakarsa ya taso Hajja.
Suna sauka da kayansu yaran yayyyen Tahir suka kyalla ido suka gansu suka zura cikin gida da Gudu suna murna Fad'i suke yi"Ga Baba Dahiru chan yazo. Hajjo ga Baba Dahiru."
Kafin su ce me wasu yaran sun yayyayemesu har sun dauki akwatinsu zuwa cikin gida. Sai dai suka bisu a baya suna shiga gidan Shashen Hajja na daga ciki ne sai sun wuce shashen matan gidan.
Suna shiga sai tashin oyoyo Dahiru ke tashi sai dai kaji ana oyoyo Baba Dahiru mutanen Zaria.
Sadiq Dariya ta kusa Shakesa yana kannewa da ganin yadda Fuskar Tahir ke yi in akace masa Baba Dahiru. Sai da suka gaggaisa da su sannan suka karisa Shashen Hajja. Allah Sarki tunda taji zuwansu ta kasa zama ta na Tsaye kofar dakinta tana Duban Hanya Tunda an shigo da kayansu dakinta.
Suna shigowa ta washe bakinta cikin Tsananin Murna ta ke fad'in"Maraba da bakin Zazzau. Ah'a har da Saddiqu a she? Maraba lale da Saddiqu"
Sadiq ya yi mirnishi ya karisa har gaban Hajja shi da Tahir ya rankwafa zai gaisheta ta saka Hannu ta rikosa tana Fadin"Haba Saddiqu mike mike..Ku shigo ciki maraba"
Tahir ta kallah kafin tace"Dahiru maraban ku da zuwa'
Tahir ya hura hanci kafin yace"Hajja wani irin Dahiru don Allah? Sunana Tahir..Sunana Tahir Hajja Ahto"
Hajja ta make kansa tana Fad'in"Tafi d'an nema Dahiru muka sani mu dai ba wani Attahir ba"
Me Sadiq zai yi in ba Dariya ba ya juyo yana kallon Tahir kafin yace"Dahiru shiga gaba mu je"
Tahir ya balla masa Harara shi kuma yana Dariya ya bi bayan Hajja zuwa cikin Dakinta.
Allah Sarki yar tsohuwar nan ta kasa zama saboda su kawo musu wannan kawo musu wannan Farinciki ya kasa barin Fuskata sai faman tambayansu take ya karatun ya'yan nan?
Tahir na jin Haushin Daman sunan da ta daina kiransa da shi yace"Hajja sau nawa zan fad'a miki mun gama karatu Hidimar kasa muke yi yanzu..?
Hajja ta ce'Yo ina ce duk karatun ne ko?
Tahir bai kara mgana ba Sadiq ya bari da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login