Showing 90001 words to 93000 words out of 93195 words

Chapter 31 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11478

Adda Fati zuwa ita da ya'yanta duka haka itama Adda Fati har da mijinta Inna Talatu ce ta zo daga baya sai Ramatu ma ta rigata zuwa.
Kowa kagani jikinsa duk ya yi sanyi na ganin tafiyar fa da gaske ne.
Ni na had'a gawayi na saka mana Ruwan zafi Amma ta fara yin wanka sannan ni nayi daga baya.
Na saka wani leshi na cikin kayan Abubakar ne mai Riga da zani, Amma kuma ta saka wata atamfarta da Adda Fati ta Dinka mata, ta kuma koma ta zauna ta cigaba da jan cashabanta duk hiran da su Adda ke yi bata saka musu baki ba.
Tuni har yan gidanmu sun aikama Makota cewa yau zamu tashi sai shigowa su ke suna mana sallama.
Ba wanda ya damu da yanayin Amma kowa ya na zaton cewa Saboda sabo me yasa jikinta duk ya yi sanyi ba ta walwala.


******


Ya gama Had'a duka Tunaninsa da Hangensa mafita d'aya ce kuma ita ya Tsaida har acikin ransa yasan Allah yaga kyakyawan Niyyarsa na Alheri da taimako kuma ya na da yakinin bazai barsa ya tabe ba.
Bai yi wani yunkuri ba sai da suka dawo sallar azahar shi da Tahir saboda saboda zazzabin da ya yi yasa shi bai je wajen aiki ba Tahir ma bai Fita ba.
Suna dawowa sallah daman akwai wuta ya saka ruwan wanka a Kittle sai da ya yi zafi sannan ya juyo ya yi wanka Tahir na kwance ya na ta Chart a wayarsa.
Sai da ya fito yaga ba shi da Niyyar tashi sannan ya ce masa bazai yi wanka ba ne?
Tahir ya dago ya na kallonsa kafin yace"Sai anjuma zan yi."
Sadiq ya kallesa kafin yace"Ka tashi ka yi zaka rakani wani waje ne."
Tahir yace"Ina.?
Sadiq sai ya yi masa banza bai yi mgana ba Tahir ya mike ya na mika kafin yace"Ka samu kanka kenan za'a fita?
Da Eh Sadiq ya amsa masa daidai Lokacin ya na bude akwatinsa.
Tahir shi kuma sai ya juyo ruwan da Sadiq ya saka masa shima ya fita zuwa wanka.


Ya yo wanka kenan ya shigo Dakin ya iske Sadiq ya ci gayunsa cikin wata shadda mai ruwan madara sabuwa ce ya na Tunanin ma bai taba sakata ba.
Abun mamakin har da Hula dara mai yanayin aikin jikin kayan sannan ya sanya takalmi budadde na Fatar damisa sannan ya na tashin kamshin Turare.
Yana cikin karya Hulan kansa Tahir yace"Daurin aure zamu je ne?
Kai Tsaye Sadiq yace"Kamar ka sani."
Tahir yace"Ikon Allah Daurin aure ranar Laraba ko dai Bazawara ce.?
Kai Tsaye Sadiq yace"Eh.!"
Tahir ya tsaya ya na kallonsa kafin yace"Eh fa kenan bazawara ce? To kai ya aka yi ka santa?
Sadiq yace"Zan sani mana."
Tahir na goge jikinsa da Towel yace"Nagane kila abokin aiki ka ne ko?
Sadiq ya daga masa kai Lokaci d'aya ya na Dora wani brown din Agogo na Fata mai kyau da yarari lokaci d'aya ya na ce ma Tahir"Ka yi sauri.."
Tahir yace masa Toh yanzu zai shirya.
Jin haka yasa Sadiq yace bari yaje ya ciro kudi ya dawo fita ya yi ya ganganra bakin Titi wajen masu POS ya ciro kudi ya Tura cikin Aljihun wandonsa.


Ya jima Tsaye a wajen ya na sauke Numfashi kamar mai ciwon Asthma.
Wata zuciyar tace"Anya Sadiq abunda zaka aikata daidai ne? Baka ganin cin Amanar yardan iyayenka ne?
To ammh ya zai yi? Tausayi ne ya cikamasa Kirjin da ya kasa tankwafar da wannan Rokon sai dai yana da nashi lTsarin da Sharadin har ya yi wannan abun ya gama shi babu wanda zai sani daga cikin wani Ahalinsa sai Tahir shi kuma yasan in ba shi yace ya yi mgana ba Tahir bazai taba cema kowa komai ba.


Da haka ya gangara ya koma ya na zuwa ya ga Tahir har ya fito shima cikin Shigan manyan kaya. Kofar su suka kule sannan suka fara Tafiya
Tahir ya dauka bakin Titi suka nufa ammah sai yaga sun nufi cikin anguwa.
Kai Tsaye yace"Ya na ga haka? Ba abun hawa zamu hau ba?
Sadiq na cin mgani yace"A'a."
Tahir ya kallesa bai samu zarafin mgana ba yaga Sadiq ya ciro wani bakin glass mai Duhuwa ya kwafa a Fuskarsa saboda batar da k'wayan idanuwansa da zasu bayyana asirin yanayin da ya ke ciki.
Tahir ya saki baki kafin yace"Wannan bakin Gilashin fa?
Sadiq ya yi kamar bai ji sa ba ya cigaba da Tafiya, shi dai Tahir yaga an zo wajen Taron jama'a bai gani ba sai da yaga sun tsaya a kofar wani Rubabben gida Dagargajajje.
Cikin mamaki ya kara kallon Sadiq kafin yace"Ina ne nan?
Kai Tsaye Sadiq yace"In da zamu zo mana."
Tahir ya bude baki kafin yace"Nan ne wajen daurin auren?
Sadiq ya gyad'aa masa kai lokaci d'aya ya na kwalama Salihi kira da ya gansu suna wasa a kofar gida ganin shi yasa har da Datti suka Rugo da gudu Sanin ya na ba da kudi.
Suna Rige rigen gaisheshi ya amsa ba Sakewa kai tsaye yace"Ku shiga ciki ku fad'ama Maman Hasiya Abubakar na mgana a waje."
Yaran suka kwashi gudu zuwa cikin gida Tahir ko mamaki ya sandarar da shi jin sunan da ya ambata kara bin gidan ya yi da kallo kafin ya Dawo da kallon kan Sadiq da baya ganin kwayar idanuwanshi saboda gilashin da ya saka.
Cikin mamakinsa Tahir yace"Nan ne gidan su Hasiyan kenan?
Sadiq ya gyad'a masa kai Tahir ya yi kwafa kafin yace"Tsakani ga Allah mu da zamu Daurin aure me ya kawo mu nan?
Sadiq ya yi shuru kafin yace"Nan ne wajen Daurin aure"
Tahir yace"Nan ne wajen Daurin auran? Ya fad'a cikin Sigan Tambaya again kuma Sadiq ya gyad'a masa kai.
Mamaki dai ko takaici zan ce ya kusa kashe Tahir a tsaye.


Cikin karin mamaki ya kara cewa"To waye zai yi aure?
Sadiq na kallon kasa muryansa ta yi kasa kafin yace
"NI.."
A Firgice Tahir ya Dago ya na kallonsa Daidai Lokacin da Amma ta fito ba ko Hijabi sai zaninta da tayi lullubi da shi Domin ta na zaune ne daman tana zaman jiran Tsammani sai ga su Salihi da sako.
Duk muna zaune adakin Amma Sakon yazo abunda ya bamu mamaki tashin Amma da Sauri da fitan ta batare da ta jira cewar komai ba yasa ta fita ta barmu baki sake cikin zullumi da Tunanin lafiya.
Ni kuma Tunda naji sunan wanda aka ambata gabbaina suka saki a tare. Abunda bai saba gani ba ne na gani yau ya saba indai yazo sai dai yace a kirani ammh yau Amma yace a kira kai Tsaye kenan tabbas akwai wani abu a kasa wanda ban sani ba.
Achan waje kuwa Amma na fita Taga Sadiq ba ta ko tsaya lura da Tahir ba ta karisa gabanshi ta na fad"in"Daman na sani. Ina da kyakyawan tabbacin zaka Dawo Abubakar"
Ta fad'a Lokaci d'aya ta na mirmishi.
Dagowa ya yi ya na kallonta sai dai Rauni da kukan UWA shi ne suka Dawo da shi sai kuma Tausayinsu gabadaya.
Cikin wani irin yanayi yace"Nazo da abunda kika bukata Amma meye abu na gaba?
Amma ta daga hannuwanta sama tace"Alhamdulillah. Alhamdulillah.! Allah na gode maka"
Sai kawai ta fashe da kuka ta na neman zubewa a kasa da Sauri Sadiq ya riketa kafin ta kai kasa kada ta tara masa Mutane.


Cikin kukan ta ke fad'in"Nagode Allah ya yi maka albarka. Yadda kaji kaima kaima Allah ya jikan ka, Allah ya haskaka Rayuwarka da Alheri Allah ya baka abunda kake nema Duniya da Lahira Allah ya tsareka a duk in da ka ke Allah ya sanya albarka acikin Niyyar ka ta Alheri."
Amma ta ke fad'a ta na kuka ga hawaye Shabe shabe Sadiq yasa Hannu ya share mata hawaye ya na fadin"Bakomai Amma."
Amma ta rike Hannuwansa ta jimke ta na fadin"Yadda ka share ma wannan UWAR hawayenta Allah ya share maka naka. Yadda ka sanyaya ma wannan Uwar zuciya kai ma Allah ya sanyaya maka taka zuciyar, Yadda ka duba lamarin wannan Uwar kai ma Ina Rokon Allah ya cigaba da Duba Lamarinka har Abada."
Sadiq na ta amsawa da Ameen Tahir ko ga shi nan Tsaye ya na ji kuma ya na gani ammh ya rasa gane ina aka dosa.
Amma ta na share hawayenta ta juya ta na fadin"Ina zuwa."
Cikin gida ta koma da Sauri duk muma Daki ta daga labule ta na kiran Sunan Adda Fati, ta mike ta na Fadin"Na zo ne Amma?
Kai ta gyada mata da Sauri ta mike ta fita ni da Ramatu muka kalli juna bamu da amsar da tambayar da ke zuciyarmu.
Suna Fita Gefe Amma taja Adda Fati tace ta yi maza ta kira mata Babammu Tanko ta na so ta yi mgana da shi.
Ba musu Adda fati ta latso lambarsa ta kirasa daman wayar na Hannunta sai da ta kira kusan sau uku sannan ya Dauka daman ita ta na da lambobin su ta na kiran su ta na gaishe su ko da su sun yada mu suna da Hakki muma mu bi mu yi zumumci da su.
Bayan sun gaisa tace masa Amma ke son mgana da shi nan da nan ya bata rai duk da ya jima rabon da yaji ta nemesa yasan kila wani abu take Bukata sai dai zencen ya sha Bambam ta na karban wayar ta yi ma Adda mgana da Hannu alamun ta bata waje.
A gurguje suka gaisa har ya fara Tsumewa ya zata ko wani taimako ta ke nema sai yaji ta fara rattaba masa wani jawabin da yasa ya d'an Saki Fuska cikin Sauri yace"Ina gida za su iya karisowa Aisha."
Daga haka Amma ta yi masa godiya suka yi sallama.
Abun mamaki Amma ta shigo Dakin nan bakinta a washe Adda Fati ta mikama wayarta Lokaci daya ta na Fadin"Fati ta shi ki shirya akwai baki a waje gidan Babanku Tanko zaki raka su yanzu."
Ni da Adda Rukayya muka had'a baki wajen fad'in"Gidan Baba Tanko kuma?
Cikin Alamun Sigar Tambaya. Amma ta gyada kai fuskarta na bayyanar da Annuri Adda Fati ba musu ta mike ta na Saka Hijabinta Hanifa na Hannuna ta yi barci sai tace na riketa bari ta Dawo Ta na fita Inna Talatu ta kalli Amma ta na fadin"Lafiya dai ko?
Amma na mirmishi tace"Sai Alheri in sha Allahu."
Adda Rukayya tace"Amma ko an fasa Tafiyar ne?
Amma ta kalleta kafin tace"A'a ban fasa ba sai dai kila tafiyar ne zata sauya daga ni da Hasiya zuwa ni kad'ai."
A tare muka kalleta ni dai sai da gabana ya amsa Ramatu ta washe baki kafin tace"Yauwa Amma ki bar mana Hasiya tare damu"
Amma na mirmishi tace"In sha Allahu Ramatu."
Amma fa ta bama kowa mamaki kudi tace na bata naira Dubu biyu na Dauko na bata ita kuma ta aiki Habiba shago ta siyo mata Cimgam da Minti.
Inna talatu ne sai da ta maganta cikin mamaki tace"Tashin ne har da rabon su Minti?
Amma tace"Wannan na Dabam ne Talatu."
Ni dai zaune na ke rike da Hanifa ammh ba na cikin Hayyacina.
Ina jin Ramatu na fad'in"Kawata nan Amma zata bar min ke"
Ta fad'a cikin Farimciki da Annushuwa kallonta kawai na yi ammh ni nasan a raina ba abunda take tunanina ba ne.
Abun mamaki me yasa Amma tace a raka su Assadiq wajen Baba Tanko?


*******


Ita kanta Adda Fati ta yi mamakin ganin Sadiq sai dai ba ta samu zarafin jin ba'asi ba gaisawa kawai suka yi tace su je Amma tace ta yi musu jagora zuwa gidan Babansu Tanko.
Sadiq sai da ya riko hannun Tahir da ya tsaya ya kasa bin su saboda ya na neman karin bayani.
Adaidaita suka samu suka hau har Babban Dodo. Ita ta fara shiga cikin gidan zuwa wani Lokaci sai ga Baba Tankon ya fito da kanshi.
Sadiq bai tsaya ma kallonsa ba yadai san Datiijo ne Hannu ya ba su suka yi musabaha kafin ya jazasu zuwa cikin Falon gidansa da ke da kofa ta waje.
Suna shiga ya fita ya barsu Tahir ya juyo ya na kallon Sadiq kafin yace"Zaka yi min bayanin meke faruwa ne ko zaka cigaba da barina cikin Duhu.?
Sadiq Kai tsaye yace"An kusa zuwa gabar da zaka san komai."
Shuru suka Cigaba da zama sai chan kuma sai ga shi ya dawo da wasu mutane kamar goma haka.


Shima Sadiq zuwan su wajen Tahir na jinsa ya na waya ya na kuma kwatancen inda su ke
Ba jimawa sai ga wasu samari suma bazasu wuce sa'aninsu ba.
Sadiq ya gabatar da su da cewa abokan aikinsa ne sai Tahir ya Fahimci daga inda ya ke Hidimar kasar sa ne to ammh me ya kawo su nan wajen?
Yaji ana kora jawabin bai tsaya Saurara duka ba ya dai fahimci kamar Aure za'a Daura? Ammh abun mamakin Daurin auran wa?
Ya na cikin wannan Tunanin yaji ana Fadin"Ina Sadakin na ku?
Sadiq ya karkato aljihu ya fiddo kudi ya mika nan da nan aka kirga Dubu Talatin cif.
Baba Tanko ya mika ma Saminu da ke gefensa Lokaci daya ya kallesu ya na Fad'in "Waye zai auri Hasiyan a cikin ku?
Tahir yaji kamar kunnensa ya Toshe ya na shirin mgana Sadiq yace"Ni ne."
Baba Tanko ya kallesa daga sama har kasa kafin yace"To ka dai san komai da ya shafi yarinyar ko?
Sadiq ya gyad'a masa kai batare da ya yi mgana ba.
Baba Tanko yace"Kai ko saurayi a haka kuma zaka zira jikin ka?
Ko baka duba asaran Dukiya ba ka Duba ta lafiyan ka."
Sadiq ya dago ya na kallon Baba Tanko na wani Lokaci kafin yace"Ni ai ba ni da arzikin ma ballatana na duba hakan. Mganar lafiya kuma Allah shi ke da ciwo kuma waraka daga wajensa ta ke."
Baba Tanko ya kalli Baba Saminu shima ya kallesa suka had'a ido.
Kafin Baba Tanko ya yi gyaram murya yace"Shikenan daman shawara ce. Waliyin ka ya matso kusa tare da Shaidun ka."
Sadiq ya nuna Tahir ya na fad'in"Shi ne Waliyina. ya nuna sauran ya na karishe fad'in"Su ne Shaidu na."
Baba Tanko ya kalli Tahir kafin yace"Shikenan daman Uwar ta su ta gayamin kai maraya ne ko?
Sadiq ya kara gyad'a masa kansa.
Tahir magana ya ke so ya yi ammh Sadiq ya hana shi yana ji ya na gani aka fara gudanar da Sigan Daurin aure.


Sadiq ya masa Rad'a a kunnensa da fadin"Kayi abunda ya dace. Zan yi maka karin bayani in muka fita."
Tahir ya na ji ya na gani ya karb'an ma Sadiq auran Hasiya akan Sadaki naira Dubu Talatin auren da ya samu Shaidu sama da Ashirin saboda kafin a Daura auran wasu mutanen sun karu ciki har da Isuhu Yaron Adda.
Domin bayan Fitan su Sadiq ya koma da mai motar domin kwashe kaya Amma tace maza Habiba ta rakasa chan shima.
Adda Rukayya ce ta kasa Hakuri ta kalli Amma ta na fadin"Amma wai me ke faruwa achan gidan Baba Tankon ne?
Amma ta juya ta na fadin


"Auran HASIYA za'a daura"


Ba ita kadai ba hatta mu sai da muka girgiza gabadaya muka juyo muna kallonta bakina ya fara rawan da na gaza Furta komai.
Inna Talatu ne tace"Da wa kuma? Sannan ba mu da labari?
Amma tace"Abun ne yazo a lokaci kurare."
Yadda na sandare a zaune haka su Adda Rukayya suka sandare sun kasa mgana Amma ko sai kasa Minti ta ke yi da Cimgam hankalinta kwance.
Muna nan zaune muna kallo kallo Ramatu ta kalleni yafi sau goma ta kasa mgana.
Sai kawai ga wayar Adda Fati a wayar Adda Rukayya ta na Dauka sai ta saka a Amsa kuwwa cikin mamaki tace"Rukayya Auran Hasiya fa aka Daura yanzu nan"
Adda Rukayya taja Numfashi kafin tace"Uhmm da wa?
Adda Fati tace"Da wanda in nayi miki bayani bazaki gane shi ba. Wani SADIQ ne, Wanda ya taba kai Amma asibiti kwanaki da Ciwonta ya tashi."
Gabana ya fad'i ras!
"ASSADIQ.."
naji zuciyata ta bani, Wani Dum naji acikin kaina ina jin suma mganganu ammh kuma bana fahimtar abunda suke fad'a.
Naji dai sanda Amma tace a fara fita da kaya ita kuma ta fita tsakar gida ta na Rabon minti lokaci d'aya ta na fad'in"Na daurin Auran Hasiya ta ne, yanzu aka Daura mata aure a gidan babansu na Dirimi."
Ni ko ina zaune rike da Hanifa na kasa tashi sai da naji Ramatu ta jijjigani ta na fad"in"Hasiya me na ke ji haka?
Na bita da kallo da idanuwana da suka Juye kamar yar maye.
Sai kuma na koma ina bin Dakin namu da kallo da yara ke ta shiga suna fita da kaya.
Yanayin da na ke ciki yasa na kasa ma yin wani kakkwaran motsi.


******


Kamar yadda Ramatu ta jijjigani haka Tahir ya Jijjiga Sadiq bayan sun fito daga Falon da aka Daura aure.
Cikin Fitan Hayyaci yace"Sadiq me na ke ji haka ne? Na kasa Fahimtar komai ka yi min bayani."
Sadiq ya kasa mgana sai da komai ya tabbata kuma ya fara jin wani irin Nadama da Tsoro.
Aure fa ya yi batare da sanin Abba da Umma ba. ba tare da sanin wasu daga cikin Ahalinsa ba.
Anya bai yi kuskure ba? Tabbas bai yi Tunanin faruwar haka ba sai yanzu ya zai yi da ita? Wannan shi ake kira Halin Tsaka mai wuya.


Sadiq ya Runtse ido ya bude shiyasa yasa ka bakin glass saboda kalan idanuwansa sun sauya daga fari zuwa Jajaye.
Tahir ne ya kara masa wani jijjiga mai yawa ya na kara fad'in"Sadiq aure ka yi? Aure ka yi batare da sanin Yan'uwan ka ba?
Kasan me ka aikata kuwa Sadiq?
Sadiq ya kwace jikinsa da Sauri ya na Fadin"Na sani..na sani Tahir Aure na yi. Aure na yi batare da sanin kowa ba"
Ya fad'a cikin karaji, Tahir ma cikin karajin yace"meyasa ka yi haka?
Kasan ko me ka aikata? Kasan wani irin girman zunubi ka aikata?
Sadiq ka na cikin hayyacinka kuwa?
Sadiq ya ji kansa ya sara ya Dafe kanshi lokaci d'aya ya na fad'in"Na sani Tahir na auri Hasiya saboda ina jin Tausayinta. Sai dai ban aureta domin na yi zaman aure da ita ba. Zan SAKE TA da zarar na inganta Rayuwarta ta yi tafiyarta ni kuma salin alim ba wanda ya sani zan koma gida na auri zabin iyayena."
Ya na mgana ne Ammh Tahir ya saki baki kawai ya na kallonsa ya fara Tunanin kamar Sadiq ya zare ko ya Haukace.
Daman shi ya sani wani abu zai faru mutanenan ba su bar Sadiq haka ba.
Ganin al'amarin ya yi kamar almara kamar a mafarki.
Sadiq ya yi aure? Kuma ba Sultana ya aura ba wata zabiyar yarinya mai mummuna kaddara a cikin Rayuwarta.
Yana tunanin Sadiq ba kanshi daya ba gaskiya to ko ya na sane ya aikata haka bakin Alkalami ya riga da ya Bushe.
ba bu wanda ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login