Showing 3001 words to 6000 words out of 93195 words
Chapter 2 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt
tarwatsa duka farincikinmu har ma da auran Gabadaya.
Wanka Ramatu ta matsamin na sake yi na sauya kaya zuwa wata Shadda milk, ita ta dinkama ni da ita da sunan in ta haihu mu saka ammh da auran nan ya taso sai tace mu yi amfani da shi. Ban yi kwalliya ba na dai shafa Hoda na saka man baki. zuwa Lokacin hayaniyar gidan ta ragu, Kayana na sawa Ramatu ta had'amin su a wata karamar akwatina tun na aurena da Abubakar ne.
Dakin Amma a ka kaini bata tawaita nasihan ta ba, Albarka ta sakamin kamar yadda ta saba. kuka nake yi kukan da har ya fito ana jin Sautin shi Ina ji Gambo na sake fadin"Kuka kuma Hasiya? Ke da ba auran Farko ba?
Ina cikin Babban mayafin da Ramatu ta sakani sawa, na ke kallonta tunda Shara shara ne ana ganin na waje,ban sa waye ya bata amsa ba tunda akwai muryoyi da yawa a dakin
Har da Gabadaya matan gidanmu suna Dakin.
Daga karshe naji Muryan Ramatu na Fadin"Ko ba auran Farko ba ne ai aure dai sunan shi Aure"
Ni dai ina hawaye muka baro Dakin Amma zuwa Dakin Maman Boy, Adda Fati ta shigo tana fad'in"Ramatu ina ga dai sai bayan mangriba angayen zasu zo ko? Domin naji ana ta kiran sallah"
Ramatu tace"To kila dai sai an yi sallar"
Adda Fati ta fice tana fad'in"Gaskiya dai mu ma bari mu yi sallar kafin su iso"
Tafad'a tana ficewa Daga Dakin sai alokacin Tunanin ina Adda Rukayya ya Fad'omin tun safe da na ganta sau d'aya ban kara ganinta ba.
Ko ya'yanta ban ga ko D'aya ba, sai yaron Adda Fati nagani kuma shima zuwa ya yi ya gaisheni.
Sai na kalli Ramatu da ke faman latsa wayarta ina fad'in"Ramatu wai ni ina Adda Rukayya ne? Ko ta koma gida ne?
Tsam naga tayi kamar tana nazari ni ko na kafeta da ido ina nazarinta, taasan na santa sarai bata isa tamin alaye ba.
Sai kawai nayi mirmishin takaici nasan amsar shurunta. Adda Rukayya ce fa ita ce jini na uwa d'aya uba D'aya ammh in ba'a fad'a maka ba sai kace bamu Had'a komai da ita ba.
Cikin karyewar murya nace"Ba sai kin ce min komai ba Ramatu na Fahimta. Allah ya sa mu dace"
Sai ta kasa amsamin, kallona take yi a sanyaye ni ko sai na kauda kaina.
Adda Rukayya ce fa ta kalleni ido cikin ido tace'"Gaskiya Hasiya ki daina zuwa gida na. In wani abu kuke da Bukata ki kirani kawai. Baban su Amna ma baya so yace tsoro yake ji. Baya son zuwan ki gidan shi"
Tunda ranar da ta fad'amin wannan mganar na san in da na sauke Matsayin Adda Rukayya a wajena.
Ko Amma ta na fad'a ta kuma sha Fad'amin cewa"Hasiya ku yi hakuri da Rukayya. Kaf cikin ya'yana tana da Bambamci ba D'aya take da ke ba, sannan ba D'aya take da Fati ba. Ku yi mata addu'an da Fatan Allah ya Daidaita rayuwarta. Rokona shine kada ku yanke zumumci da ita ko bayan kasa ta rufe idona"
Nasan ta zo ne ma da Safen gudun Fad'an Amma, ba sabo da ni ba. Gabadaya Hidiman auran nan Ramatu ne da mahaifiyarta sai Adda Fati kan lamarin ni ko sau d'aya ban ma sakata aciki ba.
Ni fa ko ciwon Amma ya tashi bana jiranta tun kiran ta da na tab'a mata kan kan jikin Amman ya tashi ta fara min Fad'a da cewa komai ya ke faruwa ni ce Sila tun haihuwata Rayuwan mutane da Dama ba su wuta ba ciki har da su da Amma ni ce silar Cutar Amma da bata da mgani.
Tun daga ranar na kiyaye mata, sai Amma ta sha ciwonta bata sani ba. Sai in taji daga baya ta fara kumfar bakin ba'a Dauketa bakin komai ba tunda Ba'a fada'a mata ba.
Har tutiya ta tab'a yi a asibiti Lokacin da aka kwantar da Amma. Ban kirata ba Adda Fati na kira ta zo muka taho asibitin sai bayan an ba ma Amma gado ta kirata ta Fad'amata.
Shine da tazo ta rika fad'an meyasa ban kirata na fad'a mata ba? Kuma a lokacin kai tsayen ta kalli Adda Fati tace"Naga kamar sun fi daukan ki wata Tsiya. Allah na tuba me kike da shi Ballatana shi Habibun?
Ni dai da kuka raina ni nake da shi,kuma nake rufa muku asiri ni da Mijina"
To me wad'anan kalaman ne kuma don in bata zo ba meyasa zan damu?
Ina ta kokarin nuna yanayina ba komai ganin haka yasa sai Dakin ya Dauki shuru daga ni har ita ba mai wani mgana kowa na saka wasu abubuwan acikin ransa.
Sallar mangariba ya Tada Ramatu ta fita tayo alwala tazo ta gabatar da sallaar tana cikin sallar ne kafin ta Idar, wayarta dake gefena ta Dauki neman Dauki. Ina dubawa naga Salisu ne sai da gabana ya Fad'i.
A kasalance na dauki wayar ganin ya sake kira bayan kiran D'azu ya katse. Na latsa koren alamun Dauka na kara kunne ina jin muryansa cikin Shauki da murna yana Fad'in"Ramatu ga mu nan zuwa. Kada ku ji mu shuru mun bari mu yi sallar mangariba ne"
Numfashina ne ya kwace min batare da na shirya ba, kuma da hakan ya fallasa ma da ni ce na Dauki wayar.
Cikin Shauki da Soyayya yace min"Hasiya..! Hasiya. Numfashin ki Kad'ai ya isa ya shaida min da ke kika Dauki wayar nan"
Sai na kara sakin Numfashin cikin Rashin Mafita tsoro nake ji kada wannan Shaukin da Muryan Salisun ta Rikid'e ta koma shaukin bakinciki da takaici. shiyasa na kasa mgana Dakyar na iya bude baki nace"Sai kun kariso. Allah ya tsare"
Daga haka na yanke wayar ina jin kamar ana Saremin gwiwoyina. Daidai Lokacin da Ramatu ta Idar da sallar ko kafin ma ta nemi ba'asi tace"Salisu ne ko?
Sun taso ne?
Dakai na amsa mata sai ta mike Dakyar ta fice tana fadin bari tayi ma su Adda Fati mgana.
Ni dai in da ta bar ni nan nake zaune wani Lokacin ina jin yayan mutane alamun ina cikin duniyarmu. Wani Lokacin kuma sai na tafi dogon zangon Tunanin da zan ji kamar komai ya tsayamin Dif! Bana jin yayar wannan duniyar tamu. Da mganar mu da Salisu an fi minti talatin kafin
naji Hayaniyar cikin gidanmu tafi ta kowani Lokaci karfi.
Tabbas ba Lafiya in dai hayaniyar gidanmu ta rika amsa kuwwa acikin Dakuna.
Gabana ya yanke ya Fad'i ras!. Kaina ya saramin a lokaci d'aya, mikewa nayi da sauri jikina da gabbaina sai da suka amsa saboda karfin da na saka wajen tashi.
Habiba ta fad'o dakin da sauri sai muka kusa cin karo da juna cikin Fitan hayyaci Tace"Salisu..Salisu ya yi hatsari.!
Kamar saukan Aradu haka naji kalamanta,Shuu! Naji kunnuwana sun yi kafin naji Habiba na jijjigani, kafafuwana sun yi sanyi kalau din da suka kasa Daukata,sai ji nayi na tafi luu numfashi na tare da ji na da ganina suka Dauke gabad'aya.
Ammh zuciyata harbawa ta ke yi da tunanin Ni HASIYA tabbas ina cikin TSAKA MAI WUYA..!
Ba suma nayi ba,ina cikin Hayyacina sai dai ji nayi kamar na samu cutar shanyewan duka jikina, Tunda ina jikin Habiba ne, ammh gabbaina ba inda yake iya motsi wani irin mutuwar jiki ce ta kamani kamar wacce likitoci suka yi ma alluran kashe jiki.
Naji mutane nata shigowa Dakin, a na ta maganganu a saman kaina ina jin Muryan Adda Fati tana Salati tare da Fadin"Mun shiga uku. Allah yasa ba abunda ya faru akan Abubakar ba ne zai maimaita kansa a kan Salisu ba"
Shine ma! Naji na amsata a raina ai ba bu wani bambamci balle da naji Muryan Ramatu cikin Damuwa tana Fadin"Yanzu abokinsa Musabahu ya kirani cikin damuwa yana fad'amin. Ashe suna kokarin tahowa nan Daukan mu sai ga waya Shagon Salisu ya kama da wuta ga kayan mutane aciki. Shine a rud'e ya hau mashin din kaninsa ya tafi,to ya ce min bai ko karisa ba Mota ta tureshi ya Fad'a ma wani mai adaidaita suka yi fadin anrigizo tare"
Sai salati ke tashi a dakin da Hayaniya. Muryan Inna talatu naji tana fad'in"Wani hali Salisun ke ciki?
Ramatu tace"Yace suna Emergency har yanzu likitoci na kanshi ammh shi Direban adaidaitan ance nan ta ke ya rasu"
Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un.
Su Adda fati ke ta faman maimaitawa.
Gidan Gabadaya ya Hargitse har da makota masu shigowa jin gulma da ganin yadda za'a kaya.
Muna nan ana ta maida zence ni dai tun bayan da Habiba ta jinginar da ni jikin garun Dakin Maman boy ban kara motsi ba, kuma ba Hawaye acikin Idanuwana. Ramatu ta zauna a gabana tana fad'in"Don Allah Hasiya kada ki damu Musbahun ya tabbatar min komai zai zo da sauki"
Kallonta kawai nake yi ina jin kamar karo na farko da Naji kalaman Ramatu ba su burgeni ba. Tunda karya take Fad'amin babu abunda zai yi daidai karya take min.
Na sani! Itama ai ta sani komai zai kwabemin ne kamar yadda ya kwabemin Lokacin aurena da Abubakar. Yana sona ina son shi ammh Kaddara da Tsaka mai wuyar da Rayuwata take ciki ta yanke aurena tsakanina da shi Har Abada.
Daga kofar D'akin Maman Boy ma muna jin kururuwa da Muryanta, tare da mganan wasu suna fad'in"Ku rike ta mana"
Ammh ina kururuwa take yi,kamar tsohuwar mahaukaciya, kamar an samin magad'isun mganin a jikina sai gani na mike kan kafafuwana, ko mutuwa nayi na dawo nasan muryan Sahura Matar Salisu, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha zuwa ta min kashedi kan mijinta.
Ramatu na kokarin rikeni na Fizge jikina na fice,ina ratsa matan gidanmu da suka yi Dafifi kofar Dakin Amma.
ba wuta ammh akwai hasken Farin wata ya haske tsukakken tsakar gidan namu Tarwai ana ganin komai.
A gabanta na tsaya ana rike da ita, ihu take tana kuka tare da kuruwan ina nake sai ta kashe ni.
Ba zato ba tsammani taji muryana a saman kanta ina Fad'in"Gani..Gani Sahura"
Na fad'a cikin wani yanayi a muryata,gabadaya sai kallo ya Dawo kaina har da Ramatu da ta biyo bayana.
Adda Fati a rude' ta riko ni tana Fadin"Ke Hasiya lafiyan ki kuwa?
Amma na da cikin Daki tunda Labarin ya shigo gidan taji zazzabi mai zafi ya Rufeta ammh kiran sunana da Fati tayi sai ya tafi da kaso mafi girma na cikin sauran kuzarinta sai ga shi ta kife saman katifar da ta ke zaune tana makyarkyatan Sanyi.
Adda Fati na kokarin janyeni Sahura ta kyalla ido ta ganni tayi kukan kura kwace rikon ta da kannenta mata suka yi mata,ta nufeni gadangadan tana zuwa ta shakemin wuya, shakar da har ina kakari da gaske take yi Halakani zatayi kuma Daman ta Dauki alwashi.
Idanuwanta Jajir kanta ba ko Dankwali gashin kanta ya mike tsaye kamar mahaukaciya sabon kamu Cikin kuka ta jijjigani tana Fad'in"Daman sai da na ce kada ya aureki. Ga mata nan kala kala Dole sai ke? Ina zaman zamana da mijina zaki kashemin shi. Na rantse da Ubangijina in Mijina ya mutu sai nayi ajalin ki Hasiya ni zan kashe ki da Hannuna"
Cikin ido na kalleta kafin nace"Nima zan so haka. Zan so ki kashe ni kamar yadda kika ce"
Na fad'a cikin muryata mai cike da yakinin nima mutuwar ce ta Dace da ni.
Kara makureni tayi tana ikirarin sai ta kasheni.
Naji hannaye da yawa suna kokarin bambare hannayenta daga saman wuyana da kuma masu janyeni daga gareta.
Ammh ni na kasa wani yunkuri na kwatan kaina.
Na riga na gama sadaukarwa Rayuwa ta bata da amfani in dai zan rika zame ma duk wani mai sona Tashin Hankali da Bakinciki.
gwara na Mutu kowa ma ya Huta.
*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*
*Janafty*
*Friday 11/08/2023*
*1:30pm*
*Post on 01/01/2024*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabooks:JamilaUmarjanafty*
*GAISUWA BAN GIRMA ZUWA GA IYAYEN D'AKINA.*
*HAJIYA HADIZA MAHE MUHAMMAD*
*HALIMA DALHA SHEHU(MAMA)*
*ANTY ZAINAB ABDULWAHAB*
*HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
*HAJIYA LUBABATU MUSA*
*ANTY FIRDAUSI KABIR*
*ANTY FADILA KABIR*
*ALHERIN ALLAH YA LULLUB'E RAYUWARKU GABADAYA AMIN*
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
+201123302418
*02*
Dakyar mutanen da ke zagaye damu suka samu nasaran raba hannayen Sahura da wuyana.
Ammh kafin su samu nasaran raba hannayen nata da Wuyana na jigata, domin shaka ne ta yi min da niyar da ke zuciyarta da kuma kalaman bakinta na sai ta kashe ni.
Ko bayan an samu ta sakeni karin kokarinta kuma ta kara rike wuyana. Da gaske take yi sai ta kasheni ni ko gabbaina sun yi sanyi da ba na iya ma wani motsi Adda Fati ne da Ramatu ke faman ja na.
Ammh na kasa kokarin Tallafa musu wajen kare kaina.
Kafin kace me? Gidanmu ya cika Damkam da mutanen anguwa har da Maza magidanta da Samari, ana ta faman maida zencen abunda ke faruwa.
Ko ba'a maida ba irin zage zagen da Mugun alkaba'in da Sahura ke jifana da shi kada'i ya isa mutane su gane abunda ke faruwa.
Sahura ta haukace ko na ce ta fita daga Hayyacinta ihu take yi tare da kwakwazo tana Fad'in duk mganar da tazo daga bakinta a kaina mara kyau da mugun Fata.
An yi an yi a fitar da ita daga gidanmu ammh abun ya ci tura kannenta bazasu iya ba. Sai da suka kira wasu daga chan gidan ba jimawa sai ga su ciki har da yan'uwan Salisun.
Wata mata kamar yayar mahaifiyar Sahuran ce sai da ta tsinke Sahura da kyakyawan maruka har guda Biyu. sannan ta dawo cikin hayyacinta ta koma ta zube a kasa tana sakin wani Gunjin kuka mai fitowa daga karkashin zuciya.
Buda'r bakin Matan cikin Fad'a tace" ashe baki da Hankali ban sani ba Sahura? Mijin ki na asibitin rai ko mutuwa ammh ke kina nan kina Hauka da Shirme?
In yau Salisu ya mutu babu wacce tayi asara sai ke, kin zama bazawara sannan ya'yanki sun zama marayu"
Kalamanta suka sanyayyar ma da kowa jiki ciki har da ni da nake tsaye cikin Halin Tsaka mai wuya.
Jikin Sahura sai ya yi sanyi ta koma ta na kuka Kasa kasa, Umarni taba ma sauran aka kamo Sahura daga zaune ta mike tana Sharbe kuka cikin Kaushin murya tace"Mu je gida Sahura. addu'a mijin ki ke bukata ba wannan hayaniyar ba, kina mganar zaki kasheta in kika Fad'a gaban yan Amin fa? Kika kashetan fa? Ke ma kina da Labarin kashe ki za'ayi?
Sai sahura ta kasa mgana sai Kuka, Wata kanwa ga Salisu ta na matsayin Diyar kanwar mahaifiyarsa ne Zaliha ta kyabe baki tana Fadin"To ba gwara ta kashe mugun iri ba. Ban da Abun Namiji me Salisu ya gani ajikin wannan abar da ya kasa sukuni sai ya aureta? Ta fad'a tana nuna ni sama da kasa kafin ta cigaba da fadin"Ba yadda yan'uwa ba su yi da Salisu kan ya hakura da yarinyar nan ba ammh yak'i Yarinyar da akace ko iyayanta kan Dole suke zaune da ita tun haihuwarta bala'i ke fad'a ma Ahalinta tayi auranta na Farko ta Tsiyace mijin da Ahalinsa gabadaya, ammh kasan da wannan abun kace kai ma sai ka aura ? Haba haba ai wlh ba haka nan ba ne wannan al'amarin da wata a kasa"
Karaf wata tace"Kila farar fatan ta ke Rud'an su. Ko lange langen jikin nata?
Ammh ni ban ga abun sha'awa a tare da wannan abar ba sai jaraban tsiya da Bala'i"
Sai kuma da suka Fad'an na kara bin kaina da kallo duk mganganun da suka Fad'a gaskiya suka fad'a. Ba ni da kyau na azo a gani sai farin fata ,ammh ko dirin nan na mata ba ni da shi siririya ce ni sosai kamar a hureni na Fad'i.
Sun yi ta Fad'an mganganu marasa Dad'i su Adda fati da matan gidanmu ke basu hakuri.
Shudewar awa d'aya sannan balataliyarsu ta bar gidanmu sai gidan ya yi tsit sai dai tashin yan kananun mganganu.
Ni dai juyawa nayi kafana na taku daya bayan d'aya cikin sanyi da wani irin yanke kauna zuwa Dakin Amma. Duk girman tashin hankalin da zan shiga Amma ce mace ta farko da kan Fad'omin araina a irin wannan yanayin.
Ina shiga Dakin Duhu ne ya fara mamaye ganina, ana cikin wannan halin waye zai tuna da kunna yar karamar Fitilar mai chaji din da Adda Fati ce ma ta siya mana ita. Sakamakon Dakin namu falle daya ne karami yasa ina shiga ko da Duhun dakin nasan mazaunin katifar Amma chan na nufa kai tsaye gabana na Fad'uwa.
Sai dai naji gwiyoyina sun yi sanyi ne sanda na isa gefen katifar na ji tashin nishin Amma da kuma rawan sanyi mai had'uwa da sautin karan Bugawar Hakora.
Cikin Daburcewa na Fara lalubanta da Hannayena Lokaci daya ina fadin"Amma..! Amma..!
Jin muryata yasa ta Dago daga kifewar da tayi a tsakanin Wuyanta zuwa cikinta, Da sauri itama ta fara mikomin hannunta guda Daya ta na so ta tab'ani cikin ikon Allah naji Hannunta cikin nawa,sai na kara Firgita jin Dumin hannunta Rau har ya Gauraye da Sanyin na wa Hannun
Bakina da Jiki na rawa da Tuni na manta da Halin da nake ciki na Fara fad'in"Amma jikin ne ya tashi?
Ta shi muje asibiti jikin ki ya Dauki Zafi"
Na ke fad'a cikin Fitan Hayyaci, na mike kenan da karfin gwiwata Amma ta yunkura ta mike zaune Lokaci D'aya tana riko hannuna, sai da na dagata na juyo ina kallonta ta cikin Duhun Dakin muryanta a shake tace"Dawo ki zauna Hasiya"
Musu ba Halina bane balle Musu da Amma sai na dawo gefenta na zauna ammh ban saki hannunta ba Zafin jikinta na shiga jikina ta Dalilin hannayenta da ke cikin nawa na Jimke.
Sai da ta ja gauron numfashi sannan ta kira sunana cikin karyayan Sauti na amsa mata da Sauri cikin Fargaban jin yadda take sauke numfashi, ina tsoron tashin hankali ammh na fi tsoron Tashin hankalin tashin Ciwon Amma da bai da mgani.
Tayi ta wahala ko mun je asibiti sai dai su bata allurai da Ruwa shikenan ya lafa mu dawo gida ammh ni kad'ai nasan a irin yanayin da Amma take kwana ta na tashi in ciwon ta ya tashi.
Shiyasa nake a firgice ko tari mai karfi naji tayi sai Hankali ya tashi matuka.
Cikin Tattausan lafazi ta fara fadi'n"Kiyi hakuri da Kaddaran ki Hasiya. Watarana zaki ji dad'i in sha Allahu"
Kallonta na ke yi ina laluban Fuskarta ta cikin Duhun Dakin,