Showing 57001 words to 60000 words out of 93195 words

Chapter 20 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11477

meyasa ba ta cika ne sai da Kalubale.? Sai dai ni nawa kalubalen mai girma ne, mai tafiya cikin Tsaka mai wuya.
Na firgita ne Lokacin da Amma ta mike zata fita ta Dauro alwala jiri ya kwasheta saura kad'an ta fad'i sai da ta Dafa Bango ta na salati. Duk da nima ba jin dadin na ke yi ba. Sai dai Amma ce komai nawa gwara ni na Raunana da ita ta Raunana Haka na mike na rikota ina Fad'in"Amma. Me ya faru..?
Cikin Damke Hannuwana tace"Bansani ba, tun safe na ke ta fama da jiri ga ciwon kai"
Jikinta na taba na ji zafi sai gabana ya fad'i cikin wani yanayi nace"Amma Akwai zazzabi a jikin ki fa."
Tsoro daya kada ciwonta ya tashi zaunar da ita nayi, baho na samo da Ruwa a buta na yi mata alwala nace ta yi sallar a zaune Tunda ta na ganin jiri.
Mangariba da Isha'i ta had'a Lokaci daya Bayan ta idar na sakamata abinci taci na bata panadol ta sha ina Fadin"Amma ki kwanta ki Huta."
Kallona ta yi lokacin da na kwantar da ita ina lulluba mata zani a wajen kafafunta.
Hannuna ta rike guda d'aya lokaci d'aya ta na kallona cikin wani yanayi. Cikin sanyin murya nace"Amma menene..?
Cikin wani sauti tace"Don girman Allah kada ki je ko'ina Hasiya. Ina tsoron na kwanta barci ki aiwatar da Kudurin ki."
Sai Amma ta bani Tausayi da Sauri na jinjina mata kai Lokaci daya ina jimke hannunta kafin nace"in sha Allahu bazan je ko'ina ba Amma. Ina tare da ke."
Da Sauri tace"Kin Tabbata.?
Jinjina mata kai na yi ina Fadin"Na Tabbata Amma."
Sai taji dadi ta saki hannuna ta koma ta kwanta tana sauke ajiyan rai.
Ni kuma matsuwa sai ta kamani na Zuba ruwa a buta, na fita zuwa makewayi sanda na dawo har Amma ta samu barci sai nima na samu gefenta na kwantar da kaina Saman katifar jikina na kasan leda ina Tunanin makomar Rayuwata.


*******


*9:30pm*


Jiya bai ci Danwake ba yau ma ga shi bai ci ba, Jiya saboda wankin da ya yi ne yasa bai je ya siya ba. Yau kuma barci suka yi tayi dagashi har Tahir sai Sha daya na Safe suka tashi kuma yana da Tabbacin ko yaje Danwaken ya kare sai ya Hakura.
Gyada ya fita ya siya da rogo chan Babban Titi. Tahir kuma Taliya da wake ya Dafa mai kifi duk ya karnace musu Daki.
Shi kuma baya Shiri da kifi kwata kwata in har abinci da kifi ba ya ci Tun yana yaro haka ya ke.
Ko yaya ya ci abinci da kifi to ranar yini zai yi amai ba sukuni. Kuma ko karnin kifi yaji yanzu sai zuciyarsa ya tashi. Kuma Tahir yasan da haka ammh Saboda ya saka shi mgana yasa ya kirkiri dafa Taliya da kifi.
Gabadaya Dakin sai da ya Dauki karnin Tsabar wulakanci irin na Tahir akwai nama acikin Miyan da Umma ta yi masa ya zo da shi da ya yi masa mganar ya yi amfani da shi cewa ya yi shi fa yau ji ya ke yi in bai ci taliya da kifi kamar dan cikinsa zai Zube. Sanin Halin Tahir na wulakanci yasa ya fita batun shi.


Yinin Ranar a rashin sukuni ya yi shi da Daddare zuciyarsa ta rika ta shi cikin Masifa ya kalli Tahir da ya gama cin taliyarsa ga farantin nan a gabansa da abun maltinan da ya gama sha, shi kuma yana ta faman Danna wayarsa cikin Nishadi.
Kai Tsaye yace'Tahir kasan me wannan abun da ka yi ya jawo min?
Dakin nan gabadaya sai karnin kifi ya ke yi kuma kasan yadda na ke da Kifi ko?
Kai Tsaye Tahir yace"Sorry Abokina wlh yau da ban ci taliya da kifi ba, da kaga Hanjina ta waje."
Ran Sadiq ya baci yace"Na kasa cin komai yau a dakin nan Tahir karni na shiga min ciki cikina."
Tahir ya Dago ya na kallonsa kafin yace"Is That Serious..?
Saboda Takaici Sadiq bai kara mgana ba jin garin akwai sanyi sanyi yasa ya mike ya nemo Jaket din sa ya saka saman Rigar da ke jikinsa.
Ya shuru takalminsa ya fice ya na jin Tahir na fad'in"Ina zaka kuma..?
Ko Tankashi bai yi ba ya Fice karamar wayarsa ke jikinsa da ita ya yi amfani ya haska tunda ba wuta anguwan ta yi Duhu.


Ba domin siyan wani abu ya fito ba iskar gari ya ke so ya shaka Tunda Tahir ya sauya iskar Dakin gabadaya.
Tafe ya ke kawai ya na kallon zirga zirgan Mutane kamar rana sai kuma yaji ya samu natsuwa har bakin Titi yaje sannan kuma ya sake kwana ya Juyo yana cikin tafiya ne ya hangi dandalin Samari a wani Rumfa sai da karisa yaga mai Shayi ne matasa da magidanta an taru ana ta shan Shayi ana Hiran Siyasa da yadda kasa ta ke ciki na Hauhawan man Fetur kowa na fad'in Ra'ayinsa.
Sai kawai yaji abun ya Burgesa Sallama ya yi musu suka amsa kafin ya ba su hannu dukkansu suka yi musabaha. Shima ya samu gefen wani matashi ya zauna.
Mai Shayin da bai taba ganinsa a wajen ba ya kariso ya na Fadin"Yallabai me za'a yi maka? Shayi ka ke so ko kwai za'a soya maka ko kuma wainar kwai?
Sadiq ya dago ya na kallonsa matashi ne ba Wani babba ba shi fa a Tunaninsa Masu yin shayi sai magidanta sai daga baya ya Fahimci matasa suma sun mike da neman na kansu. Saboda yadda Kasar tamu ta koma aikin Gwammati sai wane da wane.
Aljihunsa ya laluba ya ciro wallet dinsa duka duka 2k ne a ciki sai ya Dago ya na kallon mai shayin kafin yace"Tea zaka had'amin."
Sale mai Shayi ya ce"An gama yallabai sikari da yawa ? Madara ko melo?
Sadiq yace"Madara. Sugar din ba da yawa ba."
Ya juya kawai ya wuce wajen tukunyar Shayinsa.
Su kuma sauran suna ta labarinsu, acikin Hiran na su ne yaji wasu duk sun yi karatu ammh ba bu aikin yi sai Buga Buga mai shayi na Had'a masa Tea ya Daga Murya yana Fad'in"Yallabai a had'o da Buredi.?
Sadiq bai san ma da shi ake mgana ba sai da na kusa da shi ya tabashi sannan ya amsa masa da kadan ba da yawa ba.
Cikin Lokaci ya hado masa Tea dinsa mai kauri ya kawo masa. Ruwan ya yi zafi da ya sa yaji dadinsa ya gasa masa ciki. shi kanshi da ya kalli kansa a Teburin mai shayi sai da ya Murmusa Sadiq mai abun mamaki suna da kayan Tea a gida ammh sai yaji kamar yafi samun jin dadi da sukuni shan shayi a cikin Mutane daman haka ake ji? Abun mamaki ya sha da yawa kadan ya Rage saboda ya na sha ne ya na jin Hiran matasan da ke wajen. Anan kuma ya ke jin ashe Sale mai Shayi Degree garesa a BUK ya yi karatu bai samu aiki ba ya fara sana'ar Shayi ya na Rufa ma kansa asiri da iyayensa.
Tambayan kudinsa ya yi aka gayamasa 600 sai ya ba shi Dubu Daya yace ya rike chanjin Sale na ta Godiya baisan ya Dauki Lokaci ba sai da ya Duba agogon wayarsa ya ga sha daya saura na Dare Dole ta sakashi ya mike ya yi ma matasan sallama ya wuce.
Tunda ya zo garin zariya bai taba wuce tara a waje ba. Ba shi da Dabi'ar yawo hatta Tahir da ke da Rawan kai baya yawo Tunda ba su san kowa a garin ba.


***


Bansan Lokacin da Barci ya kwasheni ba chan cikin barci naji Nishi da wani irin kakari.
Na mike a firgice jin Sautin daga wajen da Amma ke kwance ya ke fitowa da sauri na mike ina Fad'in"Amma. Amma.."
Na ke fad'a ina Yin kanta da Sauri na Dagota ammh ina Amma bata hayyacinta numfashinta na fita da Sauri Sauri jikinta ya Dauki Zafi sai makyarkyata ta ke yi kamar wacce aka Jona ma Shooking.
Bude Murya na yi ina Kiran sunanta Ammh ina Amma ba ta jina kamar ta yi nesa da Duniyarmu gabadaya. Jikinta ya saki Gabadaya ga Zufa na uban keto mata ta ko'ina.
Zufan da nagani da kuma nauyin da ta sakarmin yasa na Tsorata tunda na sha jin ance in mutum ya mutu ya na yin nauyi sannan ya na jikewa da Zufa ya yin Daukan rai sai na gigice.
Na fara girgiza Amma ina kiran sunanta cikin kuka da wani irin Tsoro ta ina zan iya daukan rasa Amma a wannan Lokacin?
Fadi' na ke yi"Amma don Allah kada ki mutu ki bar ni. Ka da ki tafi ki barni cikin wannan rayuwar ni kad'ai bazan iya ba. Wlh bazan iya ba."
Na ke fad'a ina kuka ammh sai naga kamar Amma ba ta Numfashi ji nayi zuciyata ta tsinke da Gudu na Saketa na fice ina haki nima kamar Shed'ata zata Dauke.
Dakin Maman Boy na tafi ina Bugawa Cikin kuka nake fad'in"Ku taimaka min Amma Amma kada ta mutu"
Duka Dakunan gidanan ba in da ban buga ba. Na tabbata in wasu ba su ji ba, wasu sun ji kuma lokacin dare bai Raba ba duk da ban kalli Lokaci ba ammh ba wanda ya fito ballatana ya taimakamin.
Ganin haka yasa na kwashi gudu na koma Daki na kara tarairayo Amma jikina na kara kunnena saitin zuciyarta ta ji dif kamar bata Numfashi, sai naji kamar wani abu ya Sare daga baya na. Tashi na yi ina Haki kafata ba takalmi zanin Amma na Raruma na yafa na fice daga Dakin da gidam ma gabadaya domin neman agajin nutane.


Kamar an yi ruwa an dauke ban ga kowa a waje ba shiyasa na Dauki Hanya ina tafiya gudu gudu tunanina na tafi Chemist din gaban gidanmu na nemo Taimako ba na ko ganin gabana jefa kafafuwana kawai na ke yi ina ji kamar zuciyata zata fashe.
Sai ji nayi na bangaji mutum da karfin da yasa ya yi baya nima na yi baya ina rawan jiki.
Sadiq da yaji ya sha bangaza kamar wasa ya ja baya cikin mamaki gabansa bai Fad'i ba sai dai ya yi kokarin kiran sunan Allah.
Ni ko yamayin da na ke ciki yasa ban ko Tsaya ba sa Hakuri ba na kama Hanya zan wuce da fitilar wayarsa yasa ya haske Fuskata daga sama har kasa ya ke bi na da kallo ganin kafafuwata ba Takalmi da kuma yanayin da ta ke ciki yasa da Sauri ya ce"Ke ke Baiwar Allah."
Jin ya kirani yasa na juyo ina kallonsa da idanuwana da suka Kumbura.
Cikin Wata irin murya naji yace"Lafiya kike tafiya ba takalmi?
Har zan wuce sai na Tuna Amma kawai sai na dawo gabansa na Duka ina Fad'in"Amma Amma ce. Don girman Allah bawan Allah ka taimakamin Amma ce ga ta chan. Kamar ta mutu bata Numfashi."
Na fad'a cikin gunjin kukan da yasa na Duka na Dafa kafafunsa ina Cigaba da Fadi'in"Bawan Allah ka taimakamin don Darajan Allah. Don Daraja da kaunar da ka ke yi ma iyayenka ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka. Ka taimaki mahaifiyata kada ta mutu."
Sadiq ya ja baya da Sauri cikin in ina ya ce"Kinga yi shuru yanzu ina mahaifiyar ta ki ta ke?
Ina jin haka na mike jikina na rawa nace"Ta na. Ta na gida."
Sai kawai yace"Mu je na gani."
Jin haka yasa na yi gaba da Sauri ina Tafiya ina Hardewa shi kuma ya bi bayana har acikin zuciyansa Lokacin da nake tafiyan nan ya Tsorata.
Wata zuciyar tace"To in Aljana ce fa Sadiq?
Tuna haka yasa ya rage tafiya har sai da na yi masa nisa sannan na juyo ina kallonsa ba na wani ganin Fuskarsa akwai Duhu daga nesa yace"Ina ne gidan?
Da hannu na nuna masa gidanmu ina Fad'in"Ga ga gidan chan."
Jim Sadiq ya yi kafin ya kad'a kai yace "Muje.."
A ransa yace Allah kaga Niyyata na Tausayi da taimako kada ka bari wannan yarinyar ta Cutar da ni in ta na da Niyyar haka.
Yadda da Allah da kuma addu'a yasa ya bi Bayan Hasiya har cikin gida saboda dare da kuma yanayin da Sadiq ya ke ciki yasa bai iya gane gidan da ya ke zuwa Siyan Danwake ba ne.
Bai ji hankalinsa ya natsu ba sai da Hasiya ta yi masa Jagora har cikin Dakin Yaga Amma kwance kamar ta Mutu.
Cikin kuka na Nuna masa Amma ina Fadin"Ka duba ta. Ta mutu ko?
Da Sauri ya isa gabanta ya rike hannunta na wani Lokaci kafin ya Dago ya na kallona cikin kuka nace"Ta mutu ko?
Da Sauri yace"A'a ta na numfashi sai dai muna bukatar kai ta asibiti da gaggawa."
Kawai sai na sulalle ina wani irin kuka bai Saurareni ba ya fice daga Dakin da sauri ni kuma sai na Dora Hannuna a saman kaina ina Fadin"Wayyo Allah na shiga ni Hasiya na lalace"
Na Dauka ya tafi ne shiyasa kawai na koma na zauna ina Rafzan kuka babu wanda zai taimake ni a wannan Halin da muka samu kan mu aciki.
Sai dai me sai ga shi Mutumin nan ya Dawo da Sauri ya na fadin"kama min ita ga adaidata chan na samo mu kaita aaibiti."
Ina jin haka na mike jikina na rawa na tayasa ya daga Umma sai ya Fahimci nima sai a Hankali Tunda jiri ya kwasheni na kusa Fad'i sai da ya Rikemin hannu da hannunsa Guda daya cikin Tausayawa ya ce"Ki na lafiya.?
Kai na gyad'a masa ina sharan Hawaye ganin bazan iya ba yasa ya ba ni wayarsa ya na fadin"Rike min ki gani" da Sauri na karb'a sai ga ni nayi ya ciccibi Amma da dukan Karfinsa yana fadin"Ki biyo ni a baya ki rika haskamin hanya."
Da Sauri ko na bi bayanshi wai sai da muka fita ne sai ga matan gidanmu suna Bude kofa suna Fitowa ganin an Dauko Amma kamar ba rai yasa su Maman Salihi ke fad'in"Wayyo jikin Amma ce ya tashi?
Ko kallonsu ban tsaya yi ba daman shi Tuni ya yi gaba. Da muka fita mai adaidaitan ya taimaka muka sakata a adaidaitan shi gaba ya shiga ni kuma na shiga baya na rike Amma.
Mun fara Tafiya mai adaidaitan yace"Wani asibiti zamu je yallabai?
Juyowa ya yi ya na fadin"Wani asibiti ku ke zuwa.?
Cikin kuka nace"Kowanne muna zuwa."
Tsayawa ya yi kawai ya na kallona ina kuka ba haske acikin adaidaitan shiyasa baya ganin Fuskarta.
Cikin natsuwa ya maida Hankalinsa wajen mai adaidatan Lokaci daya yana Fadin"Asibitin da ya fi kusa ka kaimu chan."
Kukan ne baya so ya na da Raunin zuciya bangaran Tausayi.
Wani asibitin kudi da ke samaru ya kaimu muna zuwa ya fita ya kira Nurses suka zo da abun Daukan marasa lafiya suka Dauki Amma suka yi ciki da ita.


Mu kuma muna waje muna jira yadda bai zauna ba nima ina Tsaye ina Tsiyayan hawaye.
Kaina na rufe shi da zanin da Lallube jikina baya ganin Fuskata Tunda muka kawo Amma aka shiga Emergeny da ita ba su fito ba sai daya da wani abu na Dare shima ta agogon asibitin na Fahimci haka.
Mutumin suka yi ma bayani sannan shi naga ya na ta shi ya fita ashe fita ya yi ya siyo mganguna da allurai a wani kwali suka amsa suka shiga ciki.
Ni ko ina Tsaye jiri na ke gani ammh na kasa zama sai da naji ina barazanar zubewa yasa na samu kujera na zauna ina kara Fashewa da kuka.
Bansan ya zo kusa da ni ba sai da naji Tattausan muryansa yana fad'in"Ki yi hakuri ki daina wannan kukan. mahaifiyarki na nan da Ranta bata Mutu ba."
Da Sauri na Dago Fuskata muka Had'a ido Hudu da shi.
Akwai haske a asibitin tunda akawai wuta da Farin kwai.
Tar fuskata ta haska shima haka tashi.
Kallona ya ke yi yana ganin Fari na da haske kamar wata zabiya ashe ma yarinya ce bai dauka haka ba.
Ni kuma ba ma shi na ke kallo ba Tunani na da ya ce Amma na da ranta ba ta Mutu ba.
Cikin Dashewar murya nace"Amma ba ta Mutu ba?
Kai ya gyadamin kafin yace"In sha Allahu."
Da Sauri nace"To ta na ina?
Kai Tsaye yace"Ta na ciki sun ce jininta ne ya yi kasa sai low sugar ammh sun samu nasaran ceto numfashinta."
Sai kawai na Rumgume hannuwana a kirjina ina fadin"Alhamdulillah.."
Hawaye na Diga bisa zanin jikina.
A jikina naji gir!
Har sai da na tsorata sai daga baya na Fahinci wayace na daga zanina na Dauko wayar bawan Allah nan ne.
Na mika masa lokacin shi kuma ya na kallon gefe na ya na Tsaye ya saka Hannayensa duka cikin Aljihun wandonsa.
Cikin wani yanayi na ce"Bawan Allah."
Kai Tsaye ya juyo sai na mika masa wayar ina Fad'in"Ga wayar ka ana kira."
Bai karb'a ba sai da yace"Sunana Abubakar Sadiq. Ba bawan Allah ba."


Da Sauri na kallesa jin sunan da ya ambata suna mai Daraja a wajena.
Shi kuma bai Kara kallona ba sai kawai ya juya ya d'an yi nesa da ni ya na amsa wayarsa.




*Wattpadian Family kuna da yawa masu karantawa, ammh kun rage comments da Vote*




*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332. mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*










*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk


Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.


*14*


Tahir ke kiransa ya na Dagawa yaji Muryan Tahir cikin Firgici yana fad'in"Sadiq ka na ina ne? Har daya saura na dare baka dawo ba?
Wlh na zata ka dawo gida barci ne ya kwasheni sai farkawa na yi naga baka dawo ba."
Sadiq ya shafa kansa da Hannunsa guda d'aya kafin yace"Eh ban dawo ba."
Cikin Tashin Hankali a muryan Tahir yace"Sadiq ba ka dawo ba? To ka na ina ne?
Kamar bazai yi mgana ba sai kuma dai yace"Ina asibiti ne."
A firgice Tahir yace"Asibiti? Innalillahi me ya faru da kai?
Tahir ya fad'a gabansa na fad'i saboda Matukar Razana ya razana da rashin Dawowar Sadiq abunda bai taba Faruwa ba ne.
firgicinsa kada wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login