Showing 39001 words to 42000 words out of 93195 words

Chapter 14 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11460

Dawowa."
Sadiq ya juyo kafin yace"Yauwa. Ka yi sallah?
Tahir yace"Wace sallar?
Kai Tsaye Sadiq yace"Isha'i.."
Sai Tahir ya zaro ido kafin yace"Wai kana nufin har an yi isha'i.?
Sadiq ya yi karamin tsaki kafin yace"Ana ta jiran ka Tahir kaji ana ta jiran ka. Ka na da rauni wajen ibada ammh wajen Shagalan duniya baka da wannan Raunin Tahir ka gyara ka gyara Rayuwarka."
Tahir ya yi dariya kafin yace"Ka na ba ni mamaki ko da yaushe sai ka na mganar na gyara Rayuwata?. Shin rayuwata ba ta akan hanya ne ko ya ya?
Sadiq haushi yasa bai kara mgana ba ya Juya ciki ya na ji Tahir na Fadin"Naji yanzu zan ta shi nayi shikenan".
Shi dai Shigewarsa ciki ya yi ya adana Littafinsa a muhallinsa. Wanka ya shiga bayan ya fito ne Tahir ya shigo ya shiga ya yi alwala sama sama ya yi sallar tasa kamar yadda ya Saba ya fita ya koma Falo kan waya kai kawai ya girgiza Tahir sai Allah kawai.
Riga da wando ya saka Fari da baki yana son ganin Abba Kafin ya kwanta akwai mganar da ya ke so su yi.
Falo ya fito kujeran da ke fuskantar Tahir ya jawo basket din gabansa.
Pepe kitchen din da akayi domin sa ya ci duk da Tahir ya ci ammh ko Rabi bai ci ba naman kawai ya ci ya kora da lemu ya yi hamdala. kayan da Tahir ya bata duk shi ya tattara ya ijiyeshi nan gefe yasan su siyama zasu zo su dauka.
Sai alokacin ya Dauki wayarsa ya na Dubawa. shi waya ya Dauketa kawai a kira ka kira Mutum ba shi da Juriyan Chart gwara ma karanta labaran abunda ke Faruwa. Ammh Tahir har mamaki ya ke ba shi baya gajiya Tahir na daga cikin mutanen da waya ta ke hanasu koomai ciki har da cikakkiyar Ibada ta shiga ransu da ta sanya suka Shagala.


"JB na gaishe ka.."


Tahir ya fad'a Hankalinsa na kan wayarsa. Sadiq ya Dago ya na kallon sa cikin mamaki yace"JB..?
Tahir yace"Yes yanzu ma haka da shi muke chart na fad'a masa muna Gusai. Shine ya ke mganar bamu tab'a kai masa ziyara kano ba."
Karamin Tsaki Sadiq ya yi kafin yace"Haka kawai sai mu bar abunda ke gabanmu mu kai masa ziyara Tahir?
Tahir ya kalli Sadiq kafin yace"Yes ofcourse. Abokin mu ne fa Sadiq. Ba bu illah domin mun kai masa ziyara ba bu laifi a hakan.."
Sadiq ya ce"Da laifi. Mutane irin JB a ga kana mu'amala da su kai ma kimar ka zata iya tabuwa."
Tahir da mamaki yasa ya bar Danna wayarsa ya Dago ya na kallon Sadiq da ya cigaba da fadin"Tunda na Fahimci Halayyarsa na janye daga gareesa kaima Kuma na maka mganar Ka janye masa ammh baka ji Tahir. Jb ba rayuwarku daya da shi ba kuna da Tarin bambamci."
Kai Tsaye Tahir yace"Ko zaka iya gayamin bambamcin?
Ya tambaya cikin wani yanayin. Ganin kamar Tahir din ya ba shi Hankalinsa ya sa ya sauke wayarsa hannunsa ya gyara zama ya na Fuskantar Tahir lokaci d'aya yana Fadin"Jb irin ya'yan musu kudin nan ne da gata ya bata su Tahir. Jb na neman mata shine shaye shaye duk ba wannan ba Kasani na sani JB baya sallah Tahir sannan har zarginsa ake yi da neman maza fa! To duk munsan wannan meyasa zamu rika Huld'a da shi Tahir?
Tahir ya kurama Sadiq ido kafin yace"Duk na san wannan bayan su fa?
Sadiq yace"Kuma ba irin rayuwarka Daya ba. tahir kai maraya ne ya kamata ka iya rike maraicinka ko Domin Hajja ka tuna da sauran yan'uwanka ka tayasu kula da kanka."
Sai kawai Tahir ya yi mirmishi kafin yace"Daman nasan zaka zo wajen nan. Wato JB yaron masu kudi ne ni kuma yaron Talakawa maraya da bai mallaki komai ba. Bai dace na yi abota da shi ba ko Sadiq?
Sadiq ya yi kasake ya na kallon Tahir ya bude baki zai yi mgana ya Daga masa lokaci daya yana fadin" Nagode da ka Tunasar da ni matsayina., Na fahumci Jb da irin ku ya dace ya yi abota ya'yan masu kudi dan gata kai ma nagama Fahimtar zama da kai ganganci ne. Nagode da duka alfarman da ka yi min."
Sadiq ya bude murya yana Fad'in


"Tahir.."


Shima A fusace ya ce"Abubakar Sadiq Sulaiman Shinkafi na san matsayina yanzu nace.."
Daga haka fuu ya shige ciki bayan ya Dauki wayarsa, Sadiq ya bisa da kallon mamaki ya na nazarin wani abun. Tare fa suka zauna da Jb a Abu Hostel ya san halinsa sosai wannan mganganun ma na Tahir ba nasa ba ne, Na Jb ne shi ya ke zugasa ya na Fad'a masa mganganu a kansa Tunda yasan in dai yana Tare da Tahir bazai taba barinsa ya ja Tahir ga halakar da ya ke ciki ba. Shima ransa a bace ya ke shiyasa bai bi Tahir din ciki ba nan ya bata Lokaci daa yaji yana jin barci sannan ya shiga ciki. Ya iske tahir ya kwanta a kasan cafet yana danna wayarsa ga akwatinsu nan ya kwashe kayansa ya zube su a kasa. bai ce masa komai domin shima a yanzu ya riga ya san wani matsayi ya sauke Tahir.
Da asuba shi ya tashi Tahir su je masallaci ammh sai ya Fahimci ba shi da Niyar zuwa sai ya tafi abunsa da suka Had'u da Abba a masallaci sai da ya tambayesa ya ce Tahir din ya makara ne. Haka da yaje gaida Umma da Mama tunda sun saba in dai tare suka zo to tare suke shigowa gaida su. Hatta Innani sai da tace"Ina Attahiru ne tun jiya ban gansa ba?
Sai ya ce yana barci Innani ta tabe baki batayi mgana ba. Nan ya bata lokaci sai da gari ya yi haske ya koma bangaransa ya iske Tahir ya yi wanka ya shirya har ya zuba kayansa acikin wata babbar leda wacce ya fita da kansa shago ya siyo.
Mamaki bai barshi ya yi masa mgana ba, sai ma ya fito falo ya bar masa Dakin Siyama da Sultana sun shigo da Basket din abun karyawansu kenan Tahir ya fito ya na wani cin mgani ganin su Siyama yasa ya saki Fuska suka gaisa. Sun fahimci duka abokan ba su da walwala Sadiq ma dakyar ya amsa gaisuwarsu suka sauke na Hannunsu suka Dauki na jiya da suka yi amfani da shi.
Suna Fita Siyama tace"Sultana me ya faru da yaya Sadiq ne?
Sultana ta girgiza kai alamun bata sanu ba ammh ita kanta taga alamun bacin rai a tare da su gabadayansu.
Tahir kallon Sadiq ya yi ya na Fadin"Zan ta fi. Nagode da alfarman ka."
Sadiq ko kala bai ce masa ba sai kawai ya mike sannan yace"Ka tsaya ka karya sai ka tafi. Domin ni bazan haka ka yi abunda ranka ke so ba Tahir"
Sai da ya harari kwandon abinci kafin yace"Nagode Sadiq na iya da maraicina kaji ko"
Daga haka ya fice daga Falon Sadiq ya Zura hannayensa A aljihun wandonsa ya bi bayan Tahir da kallo yana mirmishi ya na da kyakyawan Tabbacin ba Zariya Tahir zai koma ba Wajen Jb zai tafi.
Tahir bai tafi ba sai da ya shiga ya yi sallama da Umma da Innani Abba ne bai samu ba fitan gaggawa ta same shi.
Umma ta ganshi shi kadai tace"Ah ba Auta yace tare zaku tafi ba.?
Sai Tahir ya sosa kai yana Fadin"Umma kiran gaggawa ne ta sameni daga wajen aikina. Shi sai gobe zai taho"
Umma dai kamar zatayi mgana sai kuma ta fasa 10k ta bashi tace ya yi na Mota, in Sadiq zai dawo gobe zai taho musu da Miya da Sauran kayan abinci ya amsa ya na ta godiya. Har Mama yaje ma Sallama itama sai da tayi mamakin tafiyarsa ammh bata Damu Tunda daman wani lokacin Tahir na fara biyo Sadiq nan ko Hutu suka yi daganan sai Direba ya kaisa har Daura watarana tare da Sadiq watarana kuma shi kadai.
Innani ce ta basa 500, ta yi ta dai saka masa albarka bata damu ba jin ba da Sadiq zasu tafi ba daman bata son tafiyarsa.


Sadiq ko a fuska bai nuna ma iyayensa wani abu ya taba had'ashi da Tahir ba. Ba wannan ba ne na Farko an yi haka kusan sau uku kenan.
Tahir ya na da wawanci wani Lokaci zai nemesa lokacin da yasan shi Abotar gaskiya ya ke tsakaninsu ba ta Sharri ba.
Kafin Dare duk abunda zai tafi da shi Umma ta had'a masa, Miya mai yawa da taji Naman kaza,sai soyayyan Naman sa da yawa. Surayya ta yo masa pepe chicken da Cake,Sauran kuma daga mai Dunout sai mai samosa,Cincin Cookies Nama ba abunda basu had'a masa ba.
Mama kuma ta yi masa Cincin manya na ci da Tea mai yawa tare da Tuwon madara.
Daman shi yasan dan gata ne wasu abubuwan ma sai yana ma barinsu a gida, Saboda sun masa yawa kowa dai burinshi yaga ya kyautata masa.




Da daddare suna Shashen innani Siyama da Sultana suna Shashen Umma, Salima daman akwai son girma ta na shashen Mama.
Hiran mutanen Shinkafi a ke yi da mganar Mahaifin Sultana Umma tace ya kirata sun gaisa ya fi sau biyar cikin Satin nan kamar dai yana son Sultana taje wajensa ne tunda yana ta mganar sauran kannenta suna ta kewarta.
Innani ta yi karaf tace"Kaji wani tsirfa to ta yi masa uban me in taje chan! Ban da abun mutum ba ma kasamu an Dauke ma Laluranta ammh ka na wani lalacewa"
Abba ya yi mirmishi kafin yace"Innani ai ba'a sauya ma Tuwo suna Sultana yarmu ce ammh kuma Shitu ne Hallatattacen mahaifinta."
Innani ta tabe baki kafin tace"Shitun me? Maketancin Mugu Allah dai ya isa tsakanina da shi Sanadinsa Hauwata ta bar gidan duniya.".
Ta fara jan Hanci zata fara kuka Sadiq ya ce"Innani.."
Tana jin haka tace"Na yi shuru magajin gida nayi shuru."
Kai ya gyada kafin ya kalli Abba yana fadin"Abba a sha'anin Baba Sammani nawa ka ba shi Gummuwa?
Abba yace"Dubu talatin Innani ta ce na ba shi da Hamsin na yi Niyya. Innani tace ya yi yawa ko ba haka ba Innani.?
Innani ta yamutsa Fuska kafin yace"Yo ina laifi Allah na Tuba a wannan marar da muke ciki na Tsadawan Rayuwa da farko yace Hamsin nace a'a bayan Sammani akwai yan bani bani irin su Husai da Hassu su sai ya kacachala musu ahirin din ba shi kenan ba."
Sadiq ya kalleta ya kalli Abba takaici ya ishe shi Dole Baba Sammani ya kirashi ya na kukan ya ci basussuka Lokacin sha'anin ya taimaka masa.
Ta ina wanda zai aurar da ya' ba shi da shi ya na kallon ka a wanda zai masa komai kuma kace ka bashi Dubu Talatin.
Umma ya kalla kafin yace"Umma kinsan da haka kuma baki kirani kin Fad'amin ba.?
Umma tace"Bansani ba Auta. Ban samu zuwa bikin ba, da Maman yara suka tafi sai da ya dawo ya ke Fadamin nace gaskiya bai kyauta ba, kuma ita kanta Maman Aishar sai da ta kirani ta na min kuka suna Bukatar taimako"
Innani ta tareta da Sauri da cewa"Uban me tace ita Madihan? Au sun raina talatin din ne? Sulaimanu fa ba mai kudi ba ne shima din Rufin asirin Allah ne in ya biye ma mutanen nan wlh kaf sai sun talaautamin d'ana ya koma ya na bara kamar yadda suke bara"
Mama da Umma suka kalli juna kowacce ta kasa mgana. Abba yace"Wlh Innani kinsan Dan kauye in ya ganka a birni sai ya yi tunanin Duniya ka tara. Abunda suke zato ba su san ba haka ba ne nima din buga buga ce kawai."
Sadiq ya kasa mgana kawai ya zama dan kallo yana jin Innani ta zauna sai zuga Abba ta ke yi tana hanashi yin alheri daman shi ya jima da Sanin wasu halin Abba marasa kyau wajen Innani ya gajesu.


Bai damu da ita ba kai tsaye ya kalli Abba kafin yace"Gaskiyan mgana Abba kudin da ka bashi ya yi kad'an kada ka manta ba shi da hali nomar ma da suke yi kai ka ke tallafa musu shima na iya ci da iyali ne. Y'a fa ya aurar Abba ta ina dubu talatin zatayi masa? Ya kirani yana gayamin yacci bashi Saboda haka zamu biya masa duka ba shin da ya ci Abba."
Abba sai ya kasa mgana ya na ta zaran ido,Innani ta yi galala galala kafin tace"Yau na ji tsiya da wasila ta ina zai fara biyan bashin da bashi ya ci ba? Sulaimanu fa ba bawan su ba ne ai ya na da ya'ya su biya masa ba shin mana."
Ran Sadiq ya baci yace"Innani kada ki kara sakamin baki in ina mgana da Abba na."
Innani ta saki baki ammh kuma ta kasa mgana jin muryansa cikn kaushi yana Fad'in"Sai Baba Hassu ta kirani kan yaronta ya samu makarantar nan ta police acadamy wudil tana neman a tallafa masa Abba. Shima zamu taimaka mata."
Abba ya kasa mgana har yanzu Sadiq ya cigaba da fadin"Sannan Baba Husau ma ta kirani yarta zata yi jarabawan fita ba kudi tana son don Allah a tallafa mata.!"
Ganin Abba ya kasa mgana yasa ya ce"Abba dukkansu zamu taimaka musu.".
Da sauri Abba yace"Eh.. Eh zamu taimaka musu za'a taimaka musu."
Innani na jin haka ta fashe da kuka tana Fad'in"shikenan zasu talautamin Dukiyan yaro. Kai su Sammani dai ba su ji dadi ba Allah dai ya tsine musu albarka dukkansu. Tunda ba su da Godiyar Allah.".


Sadiq a fusace ya kalli Innani ya na fadin"Allah bazai taba tsine musu ba sai dai ke ce in baki gyara halin ki tun a duniya ba wlh ki ka je lahira tsinuwan Allah sai ta kamaki."
Sai Innani ta razana ta Dafe kirji tana Fadin"Na shiga uku ni Dije? Anya magajin gida ne wannan? ni ko me nayi da Allah zai la'ance ni"
Kai Tsaye yace"Kina hana alheri. Kin ba da taimakon wajen maida Abba haka. kinsan yana da halin taimakawa ammh sai ki rika hanashi meyasa haka Innani? Ka yi alheri a duniya ka tsince shi a lahira yau in Abba ya Mutu ni da ke da su Umma ko dukiyar da kike kareta bamu isa mu hana shi karban hukuncin Allah kan yadda ya tafiyar da Dukiyarsa ba. In za'a fitar da zakka ki rika masifan danki ba shi da kudun Rufin asirin Allah ne, in zai yi kyauta ki hanashi kice ba shi da shi haba Innani ki sani fa wannan abubuwan da na ke saka shi yana aikatawa Sune Zasu bibiyeshi acikin kabarinsa Ranar da ya Mutu. Ki sani wannan aikin Alherin shi zai zama gatanmu bayan ba bu Abba. Ki sani Akwai mutuwa zaki mutu, Abba zai Mutu Umma ma zata mutu mama ma haka nima zan mutu watarana duka bamu a wannan duniyan to gwara mu aikata alherin da zamu je kabari muna jin daman mun ninka aikin alherin da muka yi a duniya Saboda yadda Ni'imar Allah zata rika ziyartamu acikin kaburburan mu ki Sani wlh tallahi duk abunda ka aika na Alheri zaka girbeshi in na Sharri ne ma hakan. To ki gyara kada ki mutu cikin wannan Halin Tsinuwar da kike kira ma Mutane ta Sauka akan ki"


Ya karishe fad'a fusace Lokaci daya ya na mike ya kama hanyar barin Falon yana fadin"Zan kira su Abba. In na ji adadin kudad'en da za'a taimaka musu zan gayamaka."
A yadda ya ke mgana suka Fahimci ran Maza ya baci.


Jikinsu Abba duk ya yi sanyi sun kasa mgana Umma ta kalli Abba ta kalli Innani da ke sharan kwallah tana Fadib"Sulaimanu ka yi aikin Allah kaji ko ? Ka yi ta alheri da taimako ko na mutu, ba cikin tsinuwan Allah ba duk wannan shekaran ka kai su Samnani Hajji kai duk ma su dawo nan gidan da zama wlh bazan kara mgana ba."
Umma da Mama suka kalli juna suna Mirmishi Abba ne ya koma ya na ta lallashin Innani.. daman Umma tasan mai gayya mai aiki in yazo to kamar zanen kaddara ne komai da yace a yadda ya ke so haka zai faru.
Duk yadda ka ke nakasun ta wani bangaren to Allah na haskaka ta wani Bangaran
Washegari fuskar cunkushe ya tashi sallama ma tsakaninsa da Innani sama sama ne, Sai faman ba shi hakuri ta ke yi tana fadin"Ai nace dukkasubsu dawo nan da zama an zama daya. To menene ma Duniyan nan Allah na Tuba magajin gida? Sulaimanu fa da ka ke gani ya na da arzikin nan duk su zo mu ci arzikin tare"


Kamar zai yi dariya sai dai ya fasa ta bashi kuli mai siga da yawa da ta samo a Shinkafi da gyad'a soyayya daman shi ta ijiyemawa ya karb'a yana Fadin"Nagode innani Insha Allahu zaki mutu cikin salama kuma ba bu tsinuwar Allah a kan ki."
Innani najin haka ta washe baki tana Fadin"Yauwa har naji Hankalina ya kwanta. To nace ba ka samu kun kebe da Sulsana ba? Kaga ina so nan da Bad'i Sulaimanu ya aurar da ku.".
Kai tsaye yace"Innani.."
Ta amsa ya cigaba da fadin"Innani ba Ruwan ki da aurena da Sultana. Ko da kuka zabamin ita Ra'ayina ya sa na karbeta saboda haka yaushe zamu yi aure wannan na Ubangiji ne ki daina katsaladan a Sha'anin Allah kada ki Mutu kasa taki karban ki.".
Hankalin Innani ya tashi ta rika Fadin"N shige su alqur'an na bari. Wlh magajin gida bazan kara shiga ba."
Ya na mirmishi ya Rumgumeta yasan ya gama Firgitata Innani na Tsoron azaban Allah.
Direban Abba ya kaisa har zariya Tunda ya na da kaya. Har da lemuka duk daga gida Umma ta saka ya Dauko.
Ko da ya koma Daki duk ya yi kura. Da yake daga shi har Tahir suna da key a hannunsa.
Bayan ya gama shiga da kayan ya zage ya gyara daki tas ya tsaftaceshi. sannan ya yi wanka ya sauya kaya. Bai fita ko'ina ba yaci Nama ya kora da Ruwa ya koma ya kwanta yana barcin gajiya.


*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*






*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V


*10*


Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi haifaffan garin Shinkafi ne da ke Jahar Zamfara.
Asalin sunan Innani Dije ne kuma ta yi aure aure kamar uku kafin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login