Showing 48001 words to 51000 words out of 93195 words
Chapter 17 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt
Rukayya Allah yasa kuna lafiya"
Ta na Sauke goyon Hanifa da ke bayanta gefen Amma lokaci daya ta na Fadin"Zazzabin da muka sha ne da yara duk jikina ba Dadi. Babansu ma sai yau ya fara fita aiki. shi har da Basir ne ya tasar masa."
Ni da Amma muka had'a baki wajen fadin"Subhanallah." Na dauki Hanifa sai naga barci take yi na mikama Amma ina Fadin"Habi ai tace har Hanifa ta sha Zawon hakuri."
Adda Fati tace"Sosai ammh duk mun samu sauki su har sun tafi makaranta shima yau ya tafi na gaji da zaman gidan nace bari na biyosa ya saukeni agida kawai na duba ku."
Ledan da ta shigo da shi ta mikama Amma tana fadin"Sabulai ne da Manshafawa Amma. Ba kudi ne duk mun cinye a asibiti"
Amma tace"Bakomai Fati. Allah ya yi albarka ya azurta mijinki da kudin Halal ya shirya muku zuru'a."
Muka amsa da Ameen Ameen.
Kallona ta yi kafin tace"Hasiya wlh rashin wayarki na damuna kana son mgana da ku ammh sai ka kira makota."
Amma tace'Nima tsiyar da na ke mata ko da yaushe kenan. Kinsan ta da rashin son kashe kud'i ba Dalili."
Adda Fati tace"Kamar wata ma'aikaciyar gwammati ba. Komai ace sai an yi shi cikin Tsari."
Dariya kawai na yi bance komai ba.
Ina kusa da Amma ina kallon Hanifa da ke hannunta ta na barci.
Adda Fati ashe kallo na ta ke yi sai da na Dago muka had'a ido cikin ware mata ido nace"Na yi miki kyau ne wannan kallon fa Adda Fati"
Adda Fati tace"Kin kara fari ne sannan atamfar nan ta na yi miki kyau in kika sakata"
Na bi Atamfar jikina da kallo wata Bakar Atamfa ce Chiganvy baka da Fara ce tun ta akwatin aurena da Abubakar ne. Ba tun yau ba in dai na saka Atamfar ne sai mutane sun ce ta na yi mini kyau.
Dukkansu ni suka bi ni da kallo, ni kuma tuna Abubakar yasa yanayi na kawai ya sauya Amma ce ta ce"ki gayamata ta rage tunani baki ga ta na ta ramewa ba ne"
Adda tace"Amma Hasiya fa daman ka shi da rai ne. Tunanin rayuwa kuma Dole ne Amma. hasiya ki yi hakuri In sha Allahu Mijinki na Har Abada ya kusa zuwa. Wanda zaki Daura kayansa ki yi ta Daurawa har Abada."
Mirmishi kawai na yi ban yi mgana Ameen din ma wannan karon ban ce ba.
Hira Amma da Adda Fati suka cigaba da yi ni kuma sai na jingina da Bango na fada kogin Tunanin irin Rayuwar da muka shinfida da Abubakar. Sai ga shi cikin wattani uku komai ya zama Sai Tarihi. Tunanin da na lula yasa ko sallamar Ramatu ban ji ba sai da naji Challara kukan Noor sannan na san har ta iso. Na bita da kallo har ta zauna kusa da ni ta na gaida Amma Noor kuma na Hannun Adda Fati har ta fara kuka.
Cikin kasalan da ya Rufeni nace"Yaushe kika shigo.?
Tana mirmishi ta kalleni kafin tace"Lokacin da kika shiga kogin Tunani mana"
Sai kawai na yi mata mirmishi. Ta shi nayi na je na Debo musu ruwa. Na Dauki Dubu daya na fita tsakar gida ba yaran sai na leka waje Hamisu na gani yayan Salihi shi na ba ma wa nace ya siyomin lemun panta guda Biyu.
Ban dawo ba sai da na jirasa ya dawo sannan na Dawo Dakin. na ijiye mata a gabanta duka ta kalleni ta na fadn''Ji don Allah kamar wata bakuwa."
Ina Hararanta nace"Eh mana ke ai bakuwa ta ce mana ko Amma?
Amma tace"Ni ma Ramatu bakuwatace. Ammh kuma yar gida ce Tunda diyata ce"
Adda Fati tace"Kwarai kuwa. Hasiya karbi yarku mai kiyuya."
Ina Dariya na karbi Noor ina mata wasa. Fita na yi waje in da su Maman Salihi suke ganina da Noor yasa maman Boy ta karbeta tana Fadin"Yarinyar ta yi yawo fa".
Yake nayi kafin nace"In ba damuwa zamu zauna a dakin ki ni da Ramatu maman boy."
Cikim Fara'a tace"Haba Hasiya me zai hana? Na taba miki shamaki da Dakina ne?
Karaf Maman Salihi ta karbe da Fadin"Ballatana ni. Ko ya'yana ban muku shamaki da su ba, aike ko gaban anguwan nan ne ta aike su zasu je."
Mirmishi nayi kafin na karbi Noor ina Fadin"To nagode"
Na juya naji Kaltume da ke jajjagen kayan miya tace"Uhm ku dai bi a Hankali kada mu ji gobara ta fara bin Dakuna."
Ina mamakin meyasa Kaltume ta ke wasa da Kaddara ta? Ko don ita yarinyace domin ko haihuwa bata tabayi ba shekararta daya ne da wani abu a gidan bata wuce sa'ata ba ga rawan kai ga munafunci ga Gulma.
Ni dai shigewata daki nayi ban biye mata ba na iske Ramatu da Adda Fati na ta Hira. Zani na Dauka na goya Ramatu na Dauki mata lemonta nace tazo muje Dakin Maman Boy.
Ba musu ta taso ta na ce ma su Amma'"Adda bari mu je"
Suka amsa mana da Toh.
Dakin Maman Boy muka shige na saki Labule na san su da Dabi'an labe.
Daman mun shige mun bar su da mgana a bakinsu.
Zama muka yi a kujera d'aya ina ta kallon Ramatu ta yi kiba kamar ba ita ba Taga kallon ya yi yawa ta Zungureni ta na fad'in"Kallon fa kinga na sauya miki ne?
Kai Tsaye nace"Kin yi kiba Ramatu kin yi fari sosai ma sha Allah."
Ramatu tace"Alhamdulillah. Ammh kinsan har da Jego ko?
Ina Hararanta nace"Wani jegon? Mata kina neman wata biyar da Haihuwa kina kiran Jego kawai dai yayana ya iya kiwo ga Noor ma ta yi bulbul ta yi yawo."
Ramatu tace"Gaskiya kam baza'a raina ma yayanki ba. Yana ji damu sannan ya na kula damu yace na gaisheki ma sosai."
Ina mirmishin jin dadi nace mata ina amsawa. Nan muka shiga Hira har da Shewa sallah kadai ya tadamu girki ma Adda tace na bari zata girka.
Me zata Dafa? Nace muna da Sauran Taliya ta Dafa mana Amma na son ta da wake ta manja.
Tace to kafin ma ta Dora Biyu tayi sai ga Habiba ita ta karbi girkin. Cikin lokaci ta gama sai da muka ci muka natsa Noor ma Habiba ta karbeta mayya yara ne ina ta mata Fad'an ina zata kai yara har Biyu ga Hanifa ga Noor ta na Dariya tace"Kai Adda na iya fa renon yara kema ki bari ki Haihu ni zan renan miki ya'yan ki."
Mirmishi kawai na yi kafin nace"Habi ni ai bazan haihu ba ballatana ma ki renin ya'ya na ammh dai ga na su Adda da su Ramatu sun isheki Reno."
Ba Ramatu kadai ba Hatta Habiba sai da ta tsaya ta na kallona.
Ramatu ne tace taje kawai ta na Fita ta juya kaina ta na min Fad'a cikin Masifanta tace"Haba Hasiya. Shikenan sai ki cire rai da Rahmar Allah? Wa ya fada miki bazaki yi aure ba? Sannan wa ya fad'a miki ke ma bazaki Haihu ba?
Kai Tsaye nace"Komai a bayyane ya ke Ramatu kada ki yi kokarin Lullube abunda bazai taba lullubuwa Saboda ina taki ba. na sani kin sani, Ba bu wani Namijin da zai so ya aure ni ya auri Bala'i masifa da shiga uku da kudinsa ba Ramatu, ba bu wannan Namijin"
Kai Tsaye Ramatu tace"Akwai shi. akwai shi Hasiya."
Cikin Idanuwana da suka cika da kwallah na kalleta kafin nace"Akwai shi fa kika ce? To in akwai shi yana ina?
Shuru ta yi cikin wani yanayi kafin tace"Ya nan a inda Allah ya ijiyesa Hasiya. Kila kusa dake ko kuma nesa da Duniyarki. Ammh tabbas nasan akwai wannan Namijin. Namiji irin Salisu sannan wanda ya fi Abubakar Jarumta da Tausayi namijin da yasan Babu mai yi sai Allah ya kuma san Kaddara ce ke bibiyan Rayuwarki ba Canfi ba"
Kalamanta suka sakani sai da na Murmusa kai tsaye nace"Kada mu yaudari kanmu Ramatu ba bu wannan Namijin. ko zai amince da ni Ahalinsa bazasu taba bari D'ansu ya auro Jaraba da kudinsa ba."
Ramatu tace"ni kuma ina ji ajikina Hasiya bazaki Dauwama ahaka ba. Namijin da na Fada miki koma waye zai zo. Zai zo in sha Allahu"
Cikin Sauri nace"Zai zo? Yaushe..?
Ramatu ta kalleni cikin Rauni kafin tace"Bansani ba Hasiya.. ammh nasan Allah zai kawo sa."
Ina jin kalamanta sai nima nawa kalaman bakin suka kare cigaba da bani baki tayi ta na ta faman Lallashina.
Shine ma na sake har na gayamata mafarkin da nayi na Salisu. Kai Tsaye tace"Kada ki damu Salisu bazai taba Zargin ki ba ai yasan abubuwan da suka Faru ya tabbata ke ma kina kokarin kokuwa da Kaddaran ki ne."
Sai na gyad'a mata kai alamun gamsuwa shiyasa ta cigaba da Fad'in"Saboda haka ki kwantar da Hankalin ki Salisu zai warke kamar wani abu bai taba samunsa ba."
Da Sauri nace"In sha Allah.."
Muna nan muna mgana sai da aka kira la'asar muka koma Dakin Amma muka yi sallah mun idar kenan sai ga Kiran Adda Rukayya ta wayar Adda Fati bayan sun yi mgana aka bama Amma suka gaisa suka yi mganan da za su yi sannan suka yi sallama.
Sai alokacin Adda Fati ke fad'amana Ranat asabar Adda Rukayya zasu tare a Sabon gidan da Mijinta ya gida anan Gaskiya. Sannan tare da Birthday din Cikar Amna shekara Shidda Shine ta ke fad'ama Adda Fati tace ta fad'amana jin ma tana gidan sai tace ta bama Amma ta yi mata mganar Habiba tazo Ranar Jumma'a ta tayata parking.
Dukkanmu mun yi mata Murna. Adda Fati tace"Ramatu ki fad'ama Inna Talatu Ranar sati sai mu je mata Murna."
Ramatu tace"Zan fad'a mata Hasiya ki shirya muje.."
Zan yi mgana kenan in ce bazan je ba Amma ta yi saurin cewa"Zaki je mana Hasiya. Yanzu ma sai da tace na fad'a miki tana jiran ki."
Na sha mamakin wai Adda Rukkaya na jira na, matar da Tsoron fad'an mijinta ta ke yi sama da ni yar'uwanta.
Ganin yadda na yi ne yasa Adda Fati da Ramatu suka rika Tausana da kada na Damu yar'uwata ce Rukayya ban isa na sauya ma wannan alakar tamu suma ba jinina ce.
Da kalaman bakinsu yasa nace na amince zan ce batare da Tunanin wani irin Tozarci ke jirana in na shiga cikin sha'anin da ban saba shiga ba.
Sai Yamma Adda Fati ta tafi, Ramatu ta riga ta tafiya tunda ita gida zata koma.
Naji dadin zuwan Ramatu ko banza ta Debemin kewa tare da Shawarwarinta masu amfani.
****
Tahir bai dawo ba sai Ranar Jumma'a Da Safe ya je wajen aiki ko da ya dawo ya iske shi.
Ya san muhimmamcin sallama a musulunci an kuma ce in kai kaje to kayi ma wanda ka iske sallama. Shiyasa ya yi masa sallama ya kuma ba shi Hannu suka yi musabaaha. Yadda Tahir bai sakar masa Fuska ba shima haka ya yi masa gim da ransa.
Abu d'aya ya Kudurta ko kwashe kayansa Tahir ya yi zai sauya wajen zama bazai taba ce masa don me ba? Saboda sanda ya zo suka zauna Tare ba shi ya Kirasa ba Ra'ayinsa ne yanzu ma in yace zai sauya wajen zama bazai taba zama Takura ga Ra'ayin Tahir ba. Shi dai hakkin zaman tare ya Cire sannan ba zai fasa gayama Tahir gaskiya ba.
Duk da yasan shakuwa da Amintar da ke Tsakaninsu bazai saka su yi nesa da juna ba. Dole daya zai nemi daya kuma ya na Tabbacin ko kwashe kayansa Tahir ya yi ya na da tabbacin sai ya Dawo Domin bai saba da kowa ba sama da shi shiyasa bai damu ba ya shiga Harkan gabansa.
Yau da Danwakensa yaje wajen aiki ya ci a chan bai dawo da Saura ba Duka ya cinye. Ya ji kimar mai Danwaken nan ta karu a idonsa Matar mai mutumci ne tasan Daraja Costumominta tunda har ta iya lura da ya yi kwanaki bai zo siyan Danwake ba har ga Allah abun ya yi mishi dadi a ranshi.
Wata zuciyar ta fad'a masa ka sani ko itama ta na da manyan ya'ya dole ta damu da ya'yan wasu. Kawai Tunaninsa ya fi ba shi mai Danwaken nan Dattijuwa ce uwa kuma Rayuwa da yanayin da ake ciki ballatana ga ire iren anguwan nan sai a hankali zaka ga kowa na sana'a domin Dogara da kansa.
Kuma a tunanin Sadiq a irin su Sana'an Danwake, Kuli abinci haka na Dattijai ne yara kuma sai dai in su awara, Dankali da Sauransu. Bai taba kawo ma kansa matashiyace ke Danwaken da ke siya ya na jin Dadinsa ba.
Tahir da kansa tun a daran ya gaji da cin mganinsa ya sauko ya na masa mgana bai kuma tambayeshi ba ya fad'a masa kano yaje gidan Jb.
Sadiq bai yi mamaki ba daman ya na kallon Wani Turkish Drama ne a laptop dinsa ya Tsaida yana Sauraransa Tahir din.
Cikin Tattausan lazafi yace"Fatan ya na lafiya..?
Tahir ya sauke wayar Hannunsa ya na Fadin"Uhm kai kasan me? naga abunda ka ke gayamin Jb fa ya lalace mata haka ya ke kawowa gidan ana shaye shaye ana lalacewa."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Ba sabon abu ba ne."
Tahir yace"Ni ai ban zata haka ya lalace ba. Wlh da gudu na had'o kayana na dawo nima ya fara kokarin Tusamin lalacewarsa har da cewa zai kawomin yan mata Biyun da zasu rika tayani kwana kafin na dawo."
Sadiq ya gyada kai ya na kallon Tahir kafin yace"Me yasa baka karbi' tayinsa ba.?
Tahir ya harareshi kafin yace"Ni dan iska ne Sadiq? Haba haba dai."
Sadiq ya ce"Ok ashe yanzu ka Fahimci mganata. Da nace ba matsayin ku d'aya da Jb ba."
Tahir yace"Na Fahimta. Sorry Abokina Sharrin Shedan ne."
Sadiq yace"Is ok.."
Daga haka ya cigaba da kallon Tahir kuma ya Dauki wayarsa ya na Fadin"Usman Mb na gaisheka."
Kai Tsaye Sadiq yace"Mun yi chart da shi dazu ina wajen aiki."
Tahir yace"Oh nima jiya muka yi mgana da shi."
Daga haka Sadiq bai kara mgana ba, ya cigaba da kallonsa Tahir kuma ya cigaba da latsa wayarsa.
Washegari asabar da gyaran Daki Sadiq ya tashi da kuma wankin kayansa. Tahir na kofar dakin kan jakar ruwan da suka siya ya na kallon Sadiq ya tube dagashi sai 3Quater wando da Karamar riga ya na wankin kayansa.
Cikin takaici yace"gaskiya ka na cutar da Magajin gidan nan da ake kiran ka. Wanki fa ka ke yi da kanka."
Sadiq kamar bazai yi mgana ba sai chan yace"Eh mana ai ban fi karfin wanki da kaina ba. Ko daman chan lalacewa ne ace mutum ya zauna yace komai sai an yi masa, kuma nagaya maka mai wankin nan baya min wanki mai kyau. Sannan ga batar da kaya wanduna na nawa ya ce bai gani ba? Har fa wannan wandon farar shaddar tawa ya bace kuma zencen kenan."
Tahir yace"To ba sai ka yi masa kashedi ba..?
Sadiq ya yi tsaki kafin yace"Sai dai in a cikin kunnensa zan zuba kashedin sannan sai ya ji."
Tahir ya kwashe da Dariya kafin yace"Tsiyana da kai fushi. ni kam bazan iya ba. Ga ruguna na had'e da boxers dina na kawo ka wankemin?
Sadiq ya dago ya na nuna ma Tahir kwatan dake gabansu lokaci d'aya yana fadin"Kawo Tahir. Kwata ta kwashi nata rabon."
Tahir ya dage baki kafin yace"Mugunta phone store Abubakar Sadiq Sulaiman Shinkafi."
Sadiq yace"ba ka ga mugunta ba sai kaga fararen rigunanka acikin kwata."
Dariya suka saka gabadaya. Tahir na zaune har Sadiq ya gama wankinsa ya shanya suna da Igiya nan bakin barandansu saura kuma kananun kaya a daki ya baza saman akwatinsu tunda igiyan bata da girma.
kuma ba shi kadai ya yi wanki ba Tahir dai bai yi ba son jiki shi dai ya fi gane ma ya kai wanki a kawomasa a goge acikin Leda shi kuma Sadiq yace ya gaji da Hannunsa ba mai kara saka shi ciwon baki.
*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*
*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabooks:JamilaUmarjanafty*
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086
*12*
Haka kurum na ji na kwana da zumud'in tafiyar mu tarewar Adda Rukayya.
Abunda bai cika Damuna ba kenan wato shiga Mutane, shiyasa ko D'anwake ranar asabar d'in ban yi ba nace ma Amma zamu huta.
Amma tace daman ai ni ce ba na son jikina ya Huta ammh tuni tace na rika Hutawa ko sau d'aya a sati.
Tun safe na yi wanka na shirya Tunda Habiba tun jiya ta tafi, sai da na tsaya na yi ma Amma abinci na gyara daki wanka ne kada'i ba tayi ba tace min jikinta sai a hankali bazata iya wankan nan ba kila sai zuwa gobe.
Sai na Rabu da ita kawai daman mun yi da Ramatu zan biya mata mu wuce tare.
Inna talatu kuma tare zasu tafi da Adda Fati da zata biyo ta nan gidan su wuce. ina gidan kafin na wuce Suka iso gabad'ayansu da na so ma mu tafi tare sai nace ma Ramatu mu had'u achan kawai sai kuma na sauya Ra'ayi jin su Maman Salihi sun buga tsalle sun ce zasu je ma Adda Murna.
Ban san a ina ma suka ji labarin ba Kawai sai na ce musu sai sun zo.
Kayana na saka wanda Ramatu ta yi mana ranar sunan Noor. Sai na yi amfani da Farin Hijabina sabo ne lokacin Bikina da Salisu na d'inkashi.
Na saka takalmina mai saukakken Tudu tunda ina da tsawo ba na jin Dadin saka takalma masu Tudu.
Sai ga shi na yi yar kwalliyata har da Shafa hoda da kwalliya tare da man lebe Amma da su Adda suna ta fad'in na yi kyau da na kalli madubi sai da na yi dariyan kaina Fuskarta yar Sirit ce