Showing 66001 words to 69000 words out of 93195 words

Chapter 23 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11463

kira Adda na fad'a mata?
Amma tace''A'a kada ki tada mata Hankali kyaleta kawai."
Daman nasan haka Amma zata ce, ko ciwo ta ke yi bata son a kira mata Adda kada wai a tada mata Hankali.
Adda Fati da Adda Rukayya tare suka tafi sai aka bar min Habiba tare da ni.
Ba matsalan abinci Adda Fati ta zo min da Fanten doya da allayahu.
Har na cire rai da zuwansa sai ga shi da Daddare bayan isha'i sun zo da abokinsa mara sakewa da Mutane sai akaci sa'a Amma na farke ba ta koma barcinta na fama.


Sanda suka shigo ina bayi sai Habiba kadai suka iske kallon rashin sani Sadiq ya yi mata. Ita ma haka ta yi masa sai dai ya ga kamarta da Amma da Adda Fati su suna da jan fata ba irin Fari na garesu ba.
Habiba ta gaishesu suka amsa suna tambaya ya mai jiki?
Habiba tace ta samu sauki gata nan ma ba ta koma barcin ba.
Tahir dai na daga baya Sadiq ne ya karisa gaban gadon Amma.
Sanye ya ke da kananun kaya Riga da wando. Rigar mai kalan Ruwan kasa da layi layi ta na da Dogon Hannu. Wandon kuma mai ruwan kasa ne kafarsa cikin Rufaffen takalmi.
Amma tunda ta gansa jikinta ya bata Bawan nan ne Allah da ya kawota asibiti.
Daman tun dazu ta ke ma Hasiya mgana sai tace mata bai zo ba.
Yana gaisheta ta amsa cikin Sakewa lokaci d'aya tace"Abubakar ne?
Cikin mamaki ya ce"Eh ni ne Mama."
Amma ta muskuta ta na son mikewa da Sauri ya kamata ya na kara mata Filo ta baya.
Amma ta kallesa haka kurum taji Saurayin ya shiga ranta.
Cikin Mirmishi da muryan ciwo tace"Nagode Allah ya yi maka albarka."
Ya amsa da Ameen sai lokacin Tahir ya kariso ya na mata sannu ta amsa masa shima cikin sakewa.
Sadiq yace"Abokina ne."
Amma ta jinjina kai kafin tace"Allah Sarki nagode sosai Hasiya ta ba ni labarin irin taimakon da kayi mana. Allah ya ba ka lada. Allah ya biya ka da gidan Aljannah"
Da Ameen Ameen ya ke ta amsawa.
Tahir ko na gefe ya na bin ko'ina da kallo fuskar nan dihim.
Ya rasa dalilin Sadiq na matsa masa sai ya rakosa asibitin nan. Ka taimaki mutane to ba sai ka rabu da su ba ina laifi? Ammh lamarin Sadiq sai Allah kawai da ya Hallicesa game da maida lalura da Damuwan Mutane na shi.
Amma ta kalli Habiba ta na fad'in"Habi Hasiyan ba ta fito ba ne?
Habiba tace"Ba ta fito ba Amma."
Sai Amma ta kallesu ta na Fad'in"Hasiyan ta shiga makewayi ne."
Sadiq ne ya gyad'a mata kai, Suna Tsaye dai daga gefe ledan da Sadiq ya shigo da ita a hannun ya mikama Habiba ta karb'a ta na fadin"Angode."
Sai ta duba abunda ke ciki Taga Tsire ne mai yawa da Sauri tace"Amma nama ne."
Ta fad'a cikin jin dadi. Daman Habi da son Nama kamar wata kura. Amma ta yi mirmishi kafin tace"Allah ya ba da Lada. Allah ya yi shi albarka"
Dukkansu ba su amsa ba Tahir sai danna wayarsa ya ke yi shi kuma Sadiq ya harde hannayensa saman Kirjinsa.


Kai tsaye na fito daga makewayin. Tabbas na ji mganganu ammh ban Dauka shi ba ne. Na zata nurses ne ko Likita sai da na fito dagani sai Doguwar rigar jikina da Dankwali.
Kuma ta facing dinsa na fito daidai ya Dago nima na Dago mu ka had'a ido.
Wlh sai na ji kunya. na dukar da kaina kafafunawa na rawa na fara takowa cikin Dakin.
Amma ta tareni da Fadi'n "Sun zo tun dazu Hasiya."
Tahir a ransa ya maimaita Sunan Hasiya a ranshi.
Tabe baki ya yi yace daman ai daga ganinsu kauyawa ne.
Kuma ta dace da sunan nata Hasiya.
Ban samu natsuwa ba sai da na Rarumi Hijabina na zura sannan na gaishesu Abubakar ne kad'ai ya amsa cikin Sakewa Tahir daga lafiya shikenan bai kara ba.
Habiba ta nuna min Naman da suka zo da shi,godiya na yi masa bai amsa ni ba illah cewa da ya yi"Kuka ya kare ko? Tunda naga jikin Maama ya yi Sauki ko?
Ban ce komai ba sai dai na Rufe Fuskata da Tafin hannayena.
Amma ce ta amsashi da cewa"Hasiya ai sarkin kuka ce. Ita dai in dai ta ganni ina ciwo bata kara sukuni sai ta ganni na warke tukunnah."
Sadiq yace"Allah sarki. To ta kwantar da Hankalinta kin samu lafiya."
Amma tace"Ah Alhamdulillah. Jikina ne kawai ba karfi."
Sadiq yace"Shima a hankali zaki ji ki warware."
Amma tace"In sha Allahu."


Shuru na wani lokaci ba wanda ya yi mgana Tahir na kuncin ya gaji da Tsayuwa Sadiq kuma na Tunanin Jikin Hasiya da yanayinta ya boye Shekarunta. In dai ya canka daidai Yarinyar nan kanwarta ce kenan ta girmi Sultana sai dai kila sa'ar Salima.
Amma ce ta katse masa da Tunani da Fad'in"A nan garin ku ke ne?
Sadiq yace"A'a Mama karatu mu ke yi anan d'in."
Amma tace"Allah Sarki Allah ya taimaka."
Sadiq ya amsa mata.


AMMA bata gaji ba ta kara kallonsu ta na Fad'in"To a wani gari ku ke ne?
Tahir ya kallesa shima ya kallesa ganin Haka yasa Amma tace"ku yi hakuri ina son sani ne saboda taimakon da ka yi mana."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Ni d'an kauyen Shinkafi ne da ke zamfara. Abokina kuma mutumin Daura ne."
Tahir ya kura masa ido ya na mamakin meyasa Sadiq ke son boye kansa.
Bai gama mamaki ba yaji Amma na tambayan akwai iyaye ko babu?
Bude ido ya yi da hanci ya na kallon Sadiq sanda yaji ya na fad'in"Ba bu Mama a kauyen mu na taso hannun Dangin mahaifina"
Amma cikin Tausayawa tace"Allah sarki.Allah ya jikansu da Rahma kada ka damu ni ka Dauke ni a matsayin uwa kaji ko?
Sadiq ya jinjina kai ya na fadin"Nagode Mama."
Tahir mamaki bai barsa ya yi mgana ba.


Yana jin Amma na ta yi ma Sadiq tambayoyi yana amsa mata da cewa sun gama karatu suna Hidimar kasa ne a zariya d'in. Suna cikin mganar ne Likita ya shigo ya duba Amma ya na fad'ama Sadiq bayan sun gaisa cewa Amma zata kai sati anan suna Bukatar ta kara Hutawa ya ce bakomai.
Bai jima ba ya fita bayan ya yi ma Amma yan Tambayoyi. Bayan fitan likita ba su jima ba suka yi mana Sallama suka fita Amma na ta saka albarka da addu'o'i.
Har waje na rakasu Tahir haraban Asibitin ys fita ya na jiran Sadiq da Tarin mamakin da ke ransa.
Nima dai godiyar na sake masa bai amsa ba kai tsaye yace"Kannen ki nawa ne?
Cikin mamaki nace"Ni?
Sai ya gyad'amin kai cikin natsuwa nace"kanwata d'aya ce Habiba wacce kuka gani. Mu hud'u Amma ta Haifa Adda Rukayya baka ganta ba sai Adda Fati wacce ka gani jiya sai ni sai Habiba."
Kai ya jinjina kafin yace"Ashe ba yarinya bace. Da kallon yar ficika na ke yi miki."
Maganarsa sai ta sakani Dariya kafata ya bi da kallo. Nima sai na bi in da ya ke kallo sanye na ke flat shoe baki na Habiba ne ma ya yi min yawa Tunda Habiba ta fi ni cikar tsokar kafa.
Kai tsaye yace"Wannan takalmin ba naki ba ne ko??
Ina yar dariya nace"eh na Habiba ne. Ammh ya aka yi ka gane ba nawa ba ne?
Yana mirmishi yace"Saboda kafarki ba ta boye takalmin ki."
Dariya na yi har hakora suka bayyana waje. Shima sai naga ya yi dariyan sai na shagala da kallonsa ganin yadda ya yi kyau kamar wata Daran goma sha Hud'u.
Cewa ya yi na koma ciki bari ya tafi muka yi sallama sai da na juya yaga wucewa sannan shima ya tafi.
Ko da yaje Tahir ya cika saura kadan ya fashe ya na cewa"mu je.'
Tahir ya balla masa Harara ya na Fad'in"Wai son zabiyar yarinyar nan ka ke yi ne Sadiq?
Cikin mamaki Sadiq yace"Sunanta Hasiya ba Zabiya ba."
Tahir ya yi dariya kafin yace"Wai Hasiya. Juz imanging fa, Sadiq ka fara son wannan yarinyar ne?


Sadiq ya yi gaba ya na fadin"Wani irin so kuma? Tahir ka rika saka Tunani in zaka yi mgana pls"
Tahir ya bi bayanshi ya na fadi'n"To na rasa gane maka. Yadda ka rasa sukuni Saboda Mutanen nan da yadda ka ke washe ma yarinyar nan baki Sadiq Sannan har da karyan su Umma da Abba sun rasu fa! Duk saboda menene ka ke aikata haka?
Kamar bazai yi mgana ba sai dai ya juya ya na kallon Tahir suka Tsaya a bakin asibiti suna kallon juna kafin yace"Tahir kasan taimako dabi'ata ce ba su ne na farko ba. kuma baza su zama na karshe ba. Baka ga su na bukatar neman taimako ba ne?sannan da ka ke mganar so? Son wa? Wannan yarinyar ne zan so? Bata cikin Tsarin matan da ni ke so Tahir."
Tahir yace"Na ji ba sonta ka ke yi ba. Taimako ne. To kashe su Umma da kayi da ran su ba da karyan asalin da ka yi musu fa?
Sadiq yace"Ba karya na yi ba ni asalina dan Shinkafi ne tunda nan ne Tushena. Su Umma kuma ban san Dalili ba kai ma kasan ba kowa ya ke sanin hakikanin waye ni ba."
Daga haka ya wuce Tahir ya rike kugu ya na bin bayansa da kallo cikin mamaki. Haka kurun ya ke ji aransa Wani abu zai faru wanda ba Daidai ne ba shi fa mutanen ba su yi masa ba. Wasu kamar yan gudun Hijira ita kuma yarinya farinta ne baya so kamar wata Zabiya.
Bayansa ya bi ammh ba su kara tada mganar ba. Mashin suka samu zuwa gida kuma har suka kwanta Tahir bai kara yi ma Sadiq mgana ba sai dai ya na kallonsa ya na nazarinsa.
Yana fatan Allah yasa ba garin taimako Sadiq zai jajbo ma kansa Wahala ba.


Washegari kafin Sadiq ya tafi wajen aiki yaji yana jin cin Danwake kamar yadda aka saba da kansa yaje da karamar kularsa. Da datti ya ci karo tun kafin ya kirasa yazo da Sauri ya na Fad'in"Danwake zaka siya?
Ya gyada masa kai da Sauri Datti yace"Ba'a yi mai Danwaken mamanta ba ta da lafiya. Suna asibiti har yanzu ba su dawo ba."
Shuru ya yi ya na nazari kafin ya yi mirmishi ya Dafa kan Datti naira Dari ya zaro daga Aljihunsa ya bashi ya tafi ya na tsallen Murna.
Bai damu ba har ya juya zai tafi sai mganar yaron ta kara Dawo masa sai ya tsaya bayan ya juyo ya na kare ma gidan kallo kamar gidan kamar kuma ba nan ba ne.!
Domin kore mamaki ya ga Salihi na gara taya zai shiga gidan sai ya kwala masa kira sannan ya fitosa da Hannunsa. Saninsa ya na ba da kudi yasa Salihi ya zo da Sauri bakinsa washe yace"Ba'a Danwake yau."
Da Sauri yace"Na sani. Y
ya sunan mai yin danwaken?
Salihi yace"Adda Hasiya."
Sadiq ya maimaita"Hasiya."
Salihi yace"Eh mamanta ba ta da lafiya suna asibitin in ji mamanmu."
Sadiq ya cika da mamaki sai dai bai bari Salihi ya tafi haka ba shima darin ya ba shi ya tafi ya na ta murna.
Sadiq na tafiya a hanya ya na Mirmishi har da Dariya shi kad'ai.
"Hasiya mai danwake."
Tabdijam.
Daga alamunsu daman ba su da Hali Talakawa ne. Ammh ina mahaifin su? Me ya asalin su? Duk wad'anan amasoshin ba shi da mai amsa masa shi.
Ammh har ya koma dakin su yana Dariyan sunan Hasiya da ya maida mata da Hasiya mai Danwake.


*******


Sai da Amma tayi sati Cur sannan aka sallameta Lokacin ta samu sauki sosai ta na zuwa bayi da kanta. Sannan ta sallolinta a Tsaye ta samu karfin jiki.
Ba bu abunda zan ce ma Abubakar sai Godiya. Domin komai na laluran asibitin nan shi ya yi mana shi hatta kudin gado da sauran magungunan da aka sake rubutama Amma shi ya siya.
Sannan ya samo mana adaidaita ta Dauke damu da kayanmu har gida shi kuma yabi bayanmu a kan Babur.
Da farko ya ki shiga ciki sai da na matsa sannan ya shiga har daki ya Duka ya kara gaida Amma.
Amma ta rike hannuwansa ta na fadin"D'an nan ina ka samu kudade da ka yi ta mana wannan Hidimar?.
Kai tsaye yace"Amma ba na gaya miki ina Hidimar kasa ba? To ai gwammati na ba mu wasu kudi duk karshen wata."
Ina zai gayamusu Abba ne komai na shi tunda ya riga yace ba shi da iyaye shi maraya ne.
Amma ta shiga kwarara add'au tana ma iyayensa da suka rasu addu'a da samun salama.
Har sai da ta yi hawaye ganin haka yasa ya ce"Amma bakomai. Ki daina kuka."
Dole Amma ta yi shuru ta na ta saka masa albarka.


Da zai tafi ni na rakasa ina ganin Matan gidanmu kallo kamar zasu fad'i.
Sai da muka fito ya kalleni ya na Fad'in"Gidan ku kuna da yawa haka ne?
Kai tsaye nace"Gidan haya ne .mata goma sha uku ne aciki, Dogon gida kenan."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Dogon gida kad'ai ake kiransa?
Na gyada masa kai ina fad'in"Eh."
Kai Tsaye ya na kallo na yace"ba'a cewa gidan su Hasiya mai Danwake."


Zaro ido na yi ina kallonsa shi kuma yana Dariya yace"Amma ta ji sauki a cigaba da yi ma na Danwaken mu"
Cikin mamaki nace"Ya aka yi kasan ina Danwake?
Kai Tsaye yace"Ina siya ne."
Cikin kura masa ido nace"Ka na siya?
Kai ya gyad'amin ya na mirmishi.
Kamar an tunamin na nuna sa ya na Fad'in"Kai ne daman me zuwa da kula da Dubu daya har ka ke barin min chanji."
Bai amsani ba sai da ya yi mirmishi da yasa na gane shi ne. Kallonsa na ke yi nima cikin jin dad'in kafin nace"ka ci sunan ka. Masu suna Abubakar Sadiq ma su tausayi ne da yakana ma su jinkai ne da Taimako."
Na fad'a kai na Tsaye ina kallonsa Idanuwana suna faman cika da kwallah da tuna wani bangare na Rayuwata.
Shi kuma sai ya tsaya ya na mamakin mganata cikin sigar tambaya yace"Kin san wani mai irin sunana ne?
Kai na gyad'a masa ina fadin"Sosai ma kuwa. Shima kamar ka ya ke ga Kirki ga Tausayi Fara'a sanin ya kamata yakana jin kai da Dattako. Duka ya na da shi shima."
Na fad'a hawaye sun cikamin kwarmin idanuwana ina son Abubakar ammh kaddara ta rabani da shi.


Kai tsaye yace"Saurayin ki ne?
Sai lokacin na dawo Tunanina da Sauri nace"A'a.."
Na kauda fuskata ganin yasa bai tsawaita mganar ba. Ya yi min sallama zai tafi nima kuma daman na kosa na koma gida an fara wucewa ana kallon mu.
Kuma nasan mamakin ganina da wani ake yi wasu har suna yi ma Abubakar kallon Tausayi.
Sun zata Saurayina ne.
Ko da na koma gida sai kuzarina ya Ragu bayi na shiga na ci kuka na kamar bazan daina. Ina kewar Abubakar kewa mai yawa sai dai ina yi masa Fatan alheri a duk inda ya samu kansa.
Tunda har Sadiq na son Danwake yasa na gayama Amma zan cigaba Saboda shi. Amma tace ko shi kad'ai sai a rika yi masa ya na zuwa ya karb'a ya Chanchanta.
Washegari kad'an na yi namu na gida da na shi ina ta Allah Allah yazo to bai dawo ba sai bayan kwana Biyu ya zo Duba Amma.
Amma da kanta ta fad'a masa na yi masa Danwake shekaranjiya bai zo ba.
Cikin natsuwarsa yace"wani uzuri ne ya hanani zuwa Amma."


Ni kuma da na fita rakashi da yi masa godiyan ruwa da maltina da kayan marmarin da ya kawo ma Amma sai yace kada na kara wahalar da kaina.
Na cigaba sa sana'ata in yana so zai aiko a siya mishi.
Lura da na yi bayason gaddama yasa na amsa masa da Toh.
Habiba na Tura kasuwa ta yi mana Cefane tunda da Adda Rukkaya ta zo gida kara Duba Amma dubu biyar ta bani Adda Fati kuma ta kawo mana kayan abimci. to da su na had'a aka siyo kayan Danwake.
Amma na da kwana biyar da Dawowa gida na cigaba da sana'armu ta Danwake ranar farko da ya aiko sai nace a maida masa da kudinsa. Ya ki karba yace a dawomin da shi sai na saka Hijabi na fita da kaina nace masa don Allah ya bar kudinsa.
Kai tsaye yace"Hasiya duk sanda zan aiko siyan danwake ki karbi kudi nace."
Yadda ya yi mganar ne yasa ban isa na yi gaddama ba a muryansa ya na da wani abun da in ya ce abu baka iya masa gaddama.
Ya rage yawan shigowa Duba Amma bai wuce a sati sau daya ba.
Sai dai in ya aiko siyan Danwake sai yace"a gaida masa Hasiya mai Danwake"
In ko bai aiko ba ranar haka zan wuni cewa ma Amma''Yau fa bai zo ba Amma ko lafiya?
Sai Amma tace ya na lafiya kila wani abu ne ya tsaidasa.
Ina jinsa a raina kamar wani yayana Ban ko iya kiran sunansa sai dai nace shi.
Habiba ko Hamma ta ke kiransa Sosai muka saba da shi.
Matan gidanmu har sun fara Tsegumi tunda Kaltume har tareni tayi da tambayan shine Sabon Surukin na su?.
Kai Tsaye nace mata"A'a wannan Dan'uwan mu ne"
Daganan na kashe bakin munafukai ammh nasan ana nan ana lura da ni ana jiran aji wata mgana ne a tare shi da Labarina.
Bai taba tambayanta komai game dani ba, sai dai ya taba cewa"ina baban ku? Nace masa ya rasu da Dadewa."
Sai yace"ina dangin mahaifin na ku?
Sai nace masa suna nan. Daganan bai kara min wata tambaya ba, sai dai suna Hira da Amma har sunan gidanmu ta fad'a masa na Anguwan Kona.
Sannan in suna Hira ta kan fad'a masa ita bafullatanan Gadan mallam mamman ce, aure ya kawota zariya.
Sannan mu mun dauka da gaske Abubakar maraya ne ba shi da kowa.
Ina jin dadi in nagansa ya zo ina jinsa kusa da zuciyata.
Ban san me yasa na Damu da shi Fiye da kaina ba.
Bansan wata irin kaddara ce ke shinshina a tare da Mutumin da ban Dade'da sanin sa ba.
Kaddarace mai girma Hasiya.
Girman kaddaran da zata iya sanadiyar shigan ku Tsaka mai wuya.


.*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*


Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login