Showing 78001 words to 81000 words out of 93195 words
Chapter 27 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt
kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.
*18*
Kamar wasa sai ga karamar magana ta zama babba, Adda ta dage tare da ni da Amma zata koma kafarta kafarmu tun ina ganin lamarin wasa har na sare na Saduda da cewa tafiya ta zama Dole.
Tuni har Amma ta sanar ma da matan gidanmu saboda rayuwa. An yi zaman Amana tun zamanin zaman mu acikin gidan nan ko cacar baki bata taba yi da kowa ba.
Mu ma haka babu ruwan mu tun ballatana ma da ba su cika Rab'ar mu ba, mu ma sai mu ka kama kan mu da Maraicin mu.
Adda Fati da Adda Rukayya matuka sun shiga damuwa. Adda Rukayya ta fi bani mamaki ita da ni ke ganinta ba ta damu da mu ba, sai ga shi ta nuna jimaminta sosai. Daman tun faruwar abunda ya faru a gidanta ta yi sanyi yanzu lafiya lau mu ke da ita sai dai duk da haka babu shakuwa Tsakanina da ita kamar yadda muka Shaku da Adda Fati.
Dukkansu ba su da mafita ne Gwara ma Mijin Adda Fati zai iya rike mu ni da Amma. Ammh mijin Adda Rukayya ba shi mutumci ko Habiban Adda ta ce zata rike wlh bazai rike ba. Mutumin da bai san kowa ba sai kan shi itama don ya na sonta ne shiyasa ya ke yi mata abunda ta ke so.
A baya ne na so na koma wajen Adda da abubuwa suka rikicemin ammh a yanzu kuma sai naji ba na son barin nan d'in. Amma ma ta gama iya nazarinta ta san ba mafita sai ta bar ma Allah duka zabinsa.
Adda Fati ta kira Ramatu ta sanar da ita ta kuma ce ta sanar da Inna Talatu. Washegari sai ga su sun zo Hankula ta she, Inna talatu ta ce"Yanzu shikenan kuma Amma zaki bar mu?
Kafin ma Amma ta ba ta amsa Adda ta karb'e da cewa"Ba ta bar ku ba. zumunci ai Allah ya riga ya had'a. In bukatar hakan ya ta so zamu zo. Kuma in wani sha'ani ya taso ko auran Hasiya duk za ku zo in sha Allahu."
Daganan Inna talatu tasan Adda ta riga ta yanke hukunci ba mai tada wannan mganar. daman ta dad'e ta na so ta Dauke Amma d'in ta koma wajenta.
Ni kuma Ramatu sai nanata tafiyarmu ta ke yi ta na fad'in"Yanzu Hasiya in kika tafi ya zan yi? Kinsan fa ba ni da wata kawa wacce ta wuce ki."
Cikin sanyin murya nace"Zamu rika waya Ramatu kada ki damu ba bu abunda zai sauya."
Ramatu ta yi tagumi ta na kallo na ina yi ma Noor rawa ta na bangala Dariya.
Cikin muryan kamar za ta yi kuka tace"Hasiya sai na ke ganin kamar rayuwar zata yi miki wahala. nan aka haifeki kuma anan kika ta shi chan kuma bakon waje ne a wajen ki. Akwai chanjin Rayuwar da kafin ki saba sai kin sha wuya."
Mirmishi na yi kafin nace"Zan saba Ramatu. a yanzu dai banga irin rayuwar da Hasiya bazata iya zama acikin ta ba."
Ramatu tace"Ni da zaki amince da na yi ma Nura mgana tunda ina da Daki sai ki zauna tare da mu."
Ido na waro ina kallonta kafin nace"Ramatu anya ki na da Hankali kuwa.?
Ramatu tace"Ras na ke Hasiya. Allah da gaske na ke in kin amince na yi masa mgana sai ki saka baki mu lallashi Adda da Amma"
Dariya na yi kafin yace"A'a ba da ni za'ayi wannan aika aikar ba. Bazai yu yu ba Ramatu ai ba mutuwa zan yi ba, Wajen zama kawai zan sauya kuma zumuncin mu na nan har Abadan"
Ramatu sai ta kasa magana sai kallona ta ke yi cikin Rauni. Da alamun so ta ke yi ta yi kuka ni kuma sai naki kallonta na cigaba da yi ma Noor wasa ina fad'in"Kinga Noor ta kara wayau sosai."
Ramatu ba ta ce komai illah tagumin da ta zabga ta na kallo na.
Noor ce ta fara kuka na tashi na goyata na fara zagaye dakin Maman Boy da ita ina jijjigata.
Sai ji na yi Ramatu tace"Shikenan sana'ar Danwake ya tsaya?
Juyowa na yi ina fad'n"Ya jima da Tsayawa tun kafin zuwan Adda rabo na da yi."
Ramatu ta sauke ajiyar zuciya ganin yadda ta damu yasa na karisa na zauna gefenta ina Dafa kafad'arta Lokaci d'aya ina fad'in"Ki daina damuwa ba mutuwa fa zan yi ba."
Ramatu ta kalleni kafin tace"Ko ba mutuwa zaki yi ba. Zaki yi nesa da ni ko?
Sai na kasa mgana zuciyata sai naji ta matse ni kaina ba na son yin nesa da su musamman wani da zuciyata ta saba da shi.
Cikin fitan hayyaci nace"Ni kaina ba na so na yi nesa da shi Ramatu."
Ban san me na fad'a ba sai ji nayi Ramatu tace"Shi wa?
Kallonta na yi ina tunanin me na fad'a.
Ganin haka yasa Ramatu tace"Shi waye baki son ki yi nesa da shi?
Ajiyar zuciya na sauke Ramatu ce wacce ba abunda na ke boye mata ita D'in Sirrina ce kamar yadda na ke Sirrinta.
Cikin sanyin muryata da ta kara yin kasa nace
" ASSADDIQ..."
Ramatu ta bud'e ido ta na fad'in"Assadiq kuma? Na ina?
Mikewa na yi jin Noor ta fara kuka ina jijjigata nace"ina wanda kwanaki ya taimaka ya kai Amma asibiti?
Ramatu ta yi shuru kafin ta ce da sauri"Na gane shi wannan Saurayi baki dogo ko?
Wanda ya rakamu dakin da ku ke ciki lokacin da aka kwantar da Amma?
Kai na gyad'a mata batare da na yi mgana.
Ramatu ko mikewa ta yi jiki na rawa ta iso kusa da ni ta na fad'in"Gayamin naji. Ya ce ya na son ki ne?
Ta fad'a lokaci d'aya ta na Dafa kafad'ata. Sai ta ba ni dariya da sai da na Dara cikin Dariyan nace"Wani irin so kuma Ramatu?
Ramatu ta harareni kafin tace"To in ba soyayya ba me yasa baki son nesa da shi? Kuma ma ban da abun ki Hasiya ai garin masoyi ba ya nisa."
Mirmishi na yi kafin nace"Ba fa soyayya mu ke yi ba. Tun bayan taimakon da ya yi mana sai muka saba yana zuwa gidanan sosai wajen Ammah. To cikin sati nan da ya fita ya zo ya yi mana sallama zai tafi kauyen su shine abun ya ke damuna zamu tafi bai sani ba Ramatu."
Ramatu ta kuramin ido cikin mamaki kafin tace"Sai ki kirasa a waya ku yi sallama"
Kai Tsaye nace"Ba ni da lambarsa."
Ramatu ta yi shuru ba ta yi mgana ba.
Ni ma na yi shuru na wani lokaci kafin nace"Ko Amma ta damu tace da ta san da tafiyar da ta yi masa sallama."
Ramatu tace"Ba a nan garin nan ya ke ba?
Kai tsaye nace"Eh shinkafi ko yace sunan garin su."
Ramatu tace"Bazamfare ne kenan"
Ban amsa mata ba ta cigaba da fad'in"Damuwarki akanshi ta ba ni mamaki kad'an Hasiya."
Kallonta na yi kafin na yi mgana ta yi saurin Tareni da cewa"Daga gani kina jinsa kusa da zuciyar ki ko?
Kamar wata gaula haka na gyad'a mata kai ina fad'in"Ban san meyasa ba. Ina yawan tuna shi sannan ina jinsa sosai a cikin wani lungu acikin zuciyata."
Ramatu yar dariya ta yi kafin taje ta zauna ta na fadin"Fata na Allah yasa shima ya na jinki a cikin zuciyarsa kamar yadda ke ma kike jinsa."
Sai alokacin na Fahimci inda ta Dosa da Sauri nace"Ke ba fa wannan ba. Kawai taimakon da ya yi min ne yasa na kasa manta alherinsa."
Ramatu tace"Nima na sani."
Daga haka bata kara mgana ba ta bar ni ina Tunanin mganarta.
Ramatu wai ta na Tunanin Ina son ASSADIQ Ne?
Tuna haka yasa sai da gabana ya fad'i Haramun ne na so wani acikin Rayuwata in dai zan yi duba da Halin da ni ke ciki to aure ko soyayya ta Haramta a gareni ni Hasiya.
Kawai girman Alherinsa na ke Tunawa tare da kirkinsa natsuwarsa da taimakonsa zuwa garemu yasa zuciyata ta bashi waje na musamman.
Ammh ni kaina nasan Assadiq ya fi karfina ko a kafad'an gwada tsara bazan iya tsayawa da shi ba.
Saboda na kauda Tunanin haka acikin Zuciyar Ramatu yasa na kalleta ina Fad'in"Kin samu Labarin Salisu kuwa? Ya jikinsa?
Ramatu tace"mun yi mgana da Musbahu kwanaki yace da sauki ya na tafiya da Sanduna guda biyu."
Kai na gyad'a a hankali kafin nace"Allah ya kara masa lafiya."
Ta amsa da Ameen. Daganan muka yi shuru kowa na ta sake sake, ita daga baya Mijinta ya kirata sai na fita na ba su waje suna mgana ta waya.
Sai Dare Ramatu da Inna Talatu suka tafi da Niyar sai jibi in zamu wuce za su zo sallama.
Gabadaya mun gama had'a kayan mu. Adda tace komai kada mu bari Isuhu zai dawo gobe ya samo mana motar da zata kwashe kayan duk da ba su da wasu yawa.
Habiba kuma aranar ta had'a kayanta Adda Fati da tazo suka tafi Tare sai Murna ta ke yi. Ammh da niyar gobe in zamu tafi za su zo mu yi sallama da Safe.
Matan gidanmu da makota sai jajanta Tafiyar Amma suke yi. Sabo shi a ke yi ma kuka daman duk sai suka ji ba Dad'i muma haka.
Mun kwana da shirinmu sai ga shi Allah mai sauya lokaci Da safen Isuhu ya kira Adda a waya yace matarsa na kan gwiwa zata haihu tun daran jiya ya kawota asibiti shuru har lokacin bata Haihuwa ba. Kuma ba kowa a wajenta ba yar garin ba ce yar kwanar farakwai ne da ke nan kaduna.
Jin haka yasa sai Hankalin Adda ya tashi ta yi shirin tafiya mu kuma tace zata je ta gani in an sauka Lafiya Isuhu zai dawo ya tafi damu.
Har acikin raina ban dauka wani Shafin kaddara rayuwa zata kara Bud'emin ba.
Sai ga shi ko da yan Sallama su ka zo Adda ta kusa isa gida ma.
Mu kuma muna nan bamu tafi ba sai dai kawai su ka sha yinin su tare damu Ramatu na ta murna harda addu'an Allah yasa Adda ta fasa tafiya ta hakura ta barmu anan.
Amma kuma acikin ranta addu'a ta ke yi Allah ya sa wannan tsaikon da aka samu Mafitan da ta roki Allah ne ya fara sama mata ta yi ta addu'an Mafita a wajen Ubangiji ga Hasiya ba ta son ta tafi da ita ammh in har Hasiya ta samu inda zata zauna na Har Abada zata koma gaban Adda ta zauna cikin salama har mai kasancewa ta kasance tare da ita. Ba zata rika kwana cikin Fargaba da Damuwa ba.
Habiba dai tunda Adda Fati ta riga ta tafi da ita bata dawo ba sai ya rage daga ni sai Amma. Tunda nasaka tafiyar a raina sai na cire sana'ar Danwake a raina tun ballatana da Assadiq ba ya nan sai sana'ar ta fita raina. Sai dai ana ta zuwa neman Danwaken sai nace ma Maman boy ko zata fara yin Danwaken ne kada ma su siya su gudu.
Nan da nan ko tace zata had'a jari ta fara, ni na zauna na nuna mata Tsarin komai sannan na bata shawaran ba sai ta tara jarin ba. Ta fara da kad'an a sannu sannu dai zata ga jarin nata ya taru.
A rana sau d'aya na ke girki tunda dagani sai Ammah wani lokacin ma ba na yin girkin sai da Daddare da Safe ko Tea ko kuni mu ke sha sai Dare mu ke kara neman abinci. Tun tafiyar Adda ba mu yi waya ba tunda ba ni da waya sai da Adda Fati ta kira wayar maman boy mu ka yi mgana tace Adda ta ce a fad'a mana matar Jauro ta sauka mu duba Isuhu cikin Satin zai zo mu tafi tare.
Tunda naji haka sai muka zama cikin shiri daman kuma ba mu wargaze duka shirin kayammu ba tunda ba fasawa muka yi ba.
A daran muna zaune da Amma ina yanke mata farcenta tace"Hasiya ni ko kwana nawa Abubakar yace zai yi achan garin su?
Kai Tsaye nace"Ban sani ba Amma. Nasan dai yace zai kwana biyu kafin ya dawo."
Muka yi shuru dukkanmu ina ajiyar Zuciyar Amma sai kuma chan tace"Na so a ce yaron nan ya dawo ko godiyar irim Dawainiyar da ya yi damu na samu na yi masa. bazai ji dadi ba duk ranar da ya zo ya iske ba ma nan"
Shuru na yi ban yi mgana ba saboda abunda ke raina ne Amma ta fad'a.
Da safe mai gidanmu yazo Daman Amma ta aika a fad'a masa zamu tashi akwai ragowan kudin mu tunda bamu cike Shekara ba.
Da ya nemi ya bamu ragowan kudin sai Amma tace ya barshi kawai mutumcin sa a gareta ya fiye mata komai alokacin duk in da muka je neman haya a hanamu a ke yi saboda Hasiya ammh shi ya ba su wajen zama tagode sosai Allah ya jikan magabata.
Suka rabu cikin amimci ta na masa addu'a shima ya na yi mata Fatan alheri.
Na riga na Sadakar tafiya ba fashi sai na saki raina kawai Acikin raina na ke jin shima Assadiq ya na daga cikin Mutumen da na ke had'uwa da su a rayuwata ammh kuma na d'an Lokaci ne zasu fita daga Rayuwata batare na so ba sai dai nayi addu'an a duk inda ya ke Allah ya biyasa sannan ina Fatan Allah ya had'amu a Darussalam.
Ina da tabbacin a wajen Adda bazamu sha wahala ba tunda ta baro Rugga da jimawa domin isuhu ya gina gida acikin gari ya Daukota suka dawo.
Sannan daman ya'yanta duk maza ne tafi Amma yawan haihu. Matan nata guda Biyu ne Halima(Tumba) sai Fatima( Baddo') da itace Auta yanzu a gabanta. Shiyasa na cire damuwa Assadiq a cikin raina ammh na kasa daina jinsa a chan kasan zuciyata.
******
GUSAU.
Da gaske Sadiq ya ke yi da yace Hutu zai je gida ya yi. Saboda tunda ya zo ko kofar gida bai fita ba iyakarsa cikin Shashensa ko Shashen Innani ko Bakin get wajen Mallam Taju in za su yi karatu ko yan'uwansa da suka Damu da ya kai musu ziyara bai je gidan kowa ba.
Ko bangaren Umma daman bai cika zama ba saboda su Sultana in ya na son mgana da ita ne ya kan shiga. Shashen Mama kuwa sai dai in ya shiga su gaisa.
Daman bangaren Innani ne wajen zamansa kowa ya sani ba shi da in da yafi nan. Har acikin ransa ya na kaunar Tsohuwar nan duk ko da Tarin Rikice Rikcenta.
Sai ko Shashen Abba in wani lissafin kud'i ya had'a su. Ko wata mgana da ya shafi Dukiyar Abba tunda komai Sadiq na da masaniya a kan su.
Duka kaddarorin Abba da Filayensa tsabar kudad'ensa., Akwai ma wasu kaddarorin da Alhaji Sulaiman da Sunan Sadiq ya siye shi daga shi sai Sadiq sai Lauyansa Barrister Tafida suka sani.
Ko Pin dinsa na akwatunan bankinsa duka Shekarar da aka haifi Sadiq ne mabud'in su. Yau ma tun safe Barrister Tafidan ya zo suna Shashen Abba suna lissafin kudade da zakkar da za'a cire wannan Shekarar.
Abba na gefe komai da Sadiq a ke yi Tunda shine Dan boko.
Wani Alfahari ke mukurkusan Abba in yaga yadda Sadiq ke sauya yare ya na Turance Barristet sannan ga Lissafi a kansa da kuma iya Sarrafa Na'ura.
Haba duk wanda ke gidan SS SHINKAFI bai iya sarrafa Na'ura ba ai yaji kunya tunda kowa tasowa ya yi ya gansu agidan tunda kasuwancin Abba ne na tun Tale tale ne.
Lissfin ya Dauke su har Yamma tunda Sadiq yasa Abba ya ware wasu kudad'e saboda yan'uwansa da ke kauye tare da yan'uwan Umma da Mama.
Bangaran abincin gida daman na Shekara suke ajiye sai wata Shekaran kuma ta zagayo.
Sai bangaran sauya motocin gida Umma da Mama suna da Motocin su sannan yara ma na da shi ta zuwa makaranta Abba kuma baya sauya Mota sai Sadiq yace ya kamata a sauya su. Sadiq kuma har yanzu ba shi da ko keke yace ba yanzu ya ke Ra'ayin Mota ba tunda shi ba mazauni ba ne.
In fita zai yi ya fi bin Abba wajen harkokinsa ko ya Tukasa ko kuma Direba ya tukasa. In kuma zai shiga gari ne sai ya hau ta Umma wani lokacin d'ayar ta Abba ya ke hawa Benz dinsa baka da bai cika Fita da shi ba.
Sannan yasa an ware ma ma'aikata na su albashin sai Hidiman makaranta su Siyama. Daganan sai aka cire Riban Shekaran sai kuma zakkar da suka fita Daman Abba yasan wad'anda ake ba ma Zakkar mabukata ne da takalawa yan'uwansa daman Sadiaq na so kason Dabam ya ke cire musu Abba bai isa ya ce Uffan ba.
In magajin gida yace haka za'ayi Abba jiki na rawa zai ce ayi haka d'in magajin gida.
Sai ana gabda mangariba suka gama Barrister Tafida ya tafi shi kuma yace bari ya koma Shashensa ya yi wanka saboda zuwa masallaci.
Abba ma yace wankan shima zai yi yinin ranar duk anan suka yi shi abinci ma sai dai aka shigo musu da shi.
Sadiq shashensa ya koma ya yi wanka ya saka Jallabiya bata kai masa kasa ba sosai sai ya saka wando baki. Tare da Abba suka tafi masallaci ba su dawo ba sai da aka yi isha'i.
A masallacin ma ana ta neman taimako gyaran speeker masallaci Sadiq ya ce ma Abba za su ba da na su Taimakon.
Abba yace ya ba da nawa yaga ya kamata yace Dubu ashirin za su ba da, Sadiq yasa Abba ya yi mgana da Liman suka ba da acct lamba za'a Tura musu sai godiya su ke yi daman in dai Sadiq na gari yaji ana neman tainmkon masallaci sai in da karfinsa ya kare.
Suna dawowa kai Tsaye Shashen Innani suka nufa suka isketa ta na sallah sai da ta idar suka gaisa.
Ta kalli Sadiq ta na fad'in"Magajin gida duk yau ban gan ka ba tun Safiyar Allah da ka shigo mun gaisa in jin dai lafiya ko?
Kai Tsaye yace"Lafiya ta kalau aiki muka yi da Abba."
Sai ta washe baki ta na fad'in"Au ho to Allah ya yi albarka."
Abba ne ya zauna yana karanta ma Innani abunda suka cire na kudade.
Ta na jin ance an cire ma Mama da yan'uwanta ta tabe baki kafin tace"Daman kwadayyayu ne ba domin Allah Suwaiba