Showing 87001 words to 90000 words out of 93195 words

Chapter 30 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11472

na yi gum suna ganina zaune ne ammh gabadaya Tunanina da Hankaluna suna dakin Amma ina Hasaso wani irin mgana ne Amma zata gayama Assadiq ya sa sai da tace na basu waje?
Wata zuciya tace ya wuce Labarin ki"
Daman nasan ai Tsatsuniyar gizo bata wuce ta kogi.
Har aka kira sallar mangariba Assadiq bai fito ba.
Ganin duk sun watse sun shige dakanunsu yasa na ari butar maman Boy na yi alwala na yi sallar mangariba adakinta.
Ina cikin azkar naji na kasa natsuwa a Daddafe na gama na mike na fita.
Ganin ba takalminsa kofar dakin Amma yasa nasan ya tafi.
Da sauri na fad'a dakin Amma sai na yi Turus ganinta ta na sallar mangariba.
gefenta na koma na zauna gabana naji ya na Di' di'
Bakina kuma ya kasa Furta komai.


*******


Tunda ya baro gidansu Hasiya ya fara ganin Duhu Duhu. Kansa ko da ya ke sara masa daman tun yana gaban Amma ya fara sara masa.
Ko da ya iso dakinsu jikinsa ne ya saki kwata kwata kwakwalwarsa ta daina amfani ballatana ta kaisa ga wani Tunani na Dabam.
Yaraf ya fad'a kan katifa ko takalminsa bai cire ba.
Tahir na Dakin Ammah ko kallo bai ishesa ba ballatana ya fahimci halin da ya shigo, ya na jinsa ya fita ya je ya yi alwala yazo ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci ammh shi duk yadda ya so ya yunkura ya mike domin ya fita ya Dauro alwala ya tafi masallaci ya kasa.
Gabbansa yaji kamar an sauke masa su ko'ina na jikinsa ya saki kamar ba shi da lakka ajikinsa.
Kansa na sara masa ammh kuma kwakwalwarsa ta tsaya cak din da ya kasa Dora wani sabon Tunanin tun bayan fitowarsa daga gidan su Hasiya.
Halin da ya ke ciki shi ake kira TSAKA MAI WUYA halin da ya kasa sarrafa Tunaninsa ma gabadaya.
Tahir sai da tara ta wuce ya shigo Dakin yana jin tashin muryansa a waje yana hira da yan makaranta da suke zaune tare.
Har kuma alokacin bai iya ko motsi da kafarsa ba. Yana jin Tahir har takasa ya yi ammh bai iya tashi ba.
Shi kuma Tahir haushin Sadiq yake ji shiyasa ya yi kamar bai gansa ba.
Da farko ya zata gajiya ce ta kwantar da shi sai da yaga bai je sallar mangariba sannan aka yi isha'i ma bai je ba sai yasan ba lafiya.
Lafiyar Sadiq kalau baya fashin sallah
Ko da ba shi da lafiya ne sai dai ciwon da ya kasa tashi shine zai hanasa zuwa masallaci.
Sannan ya shigo yagansa yarda ya barshi da gangan ya takashi Saboda ya yi mgana ya Fahimci Halin da yake ciki ya ji shuru daganan yasan ba lafiya
Kusa da Sadiq ya matsa ya na Taba kafarsa lokaci daya ya na kiran sunansa


"Sadiq Sadiq. Kai Sadiq"


Har Tahir ya fara tsorata ganin bai yi motsi ba sai kuma yaga ya juyo idanuwansa suna rufe bai bude su ba sannan bai yi mgana ba.
Da sauri ya kara kiran sunansa ya na fad'in"Kana jina?
Sai alokacin Sadiq ya bude idanuwansa da suka koma gauta saboda ja.
Cikin Tsoro Tahir yace"Baka da Lafiya ne?
Sai Sadiq ya samu kansa da Dagamai kai Lokaci d'aya ya na fadin"Ba ni da lafiya Tahir. Ba ni da lafiya."
Cikin wata irin murya da ta kara Tsorata Tahir da Sauri yacr"Me ke damunka Zazzabi?
Ya fad'a lokaci daya ya na Tattaba jikin Sadiq.
Shi kuma sai ya kara mulmulawa saman kafita cikin nishi yace"Rufamin abun rufa sanyi nake ji."
Jiki na rawa Tahir ya mike ya Dauko Bargon Sadiq ya lulluba masa ya na fadin"Maleria ce inaga. Ka dan huta zuwa anjuma sai ka tashi ka sha magani bari na fita na karbo maka a wannan chemist din"


Bai jira cewar Sadiq din ba ya mike bayan ya zare ma Sadiq din takalmin kafarsa ya maida ma'ajiyar takalman sannn ya dauki kudi a jakarsa ya fita Lokaci d'aya ya na jawo ma Sadiq kofar dakin
Sadiq ya dago ya na bin kofar da kallo kansa ya Dafe da hannu bibbiyu lokaci d'aya ya na fadin"Dama ace. Dama ace. Daman tun farko na fad'i gaakiyata da duk ban shiga wannan halin na Tsaka mai wuya ba."
Ya karishe fad'a kamar ya fashe da kuka.
A lokacin tunani da Hankalinsa ne ya ke jin ya rasa gabadaya.






FAA'ALUL LIMA YURID
LAIN YUSIBA NA
ILLAMA KATABALLUHU LANA.


Kuyi hakuri an samu kuskure a shafi na sha bakwai wajen Rubutawa, keyboard d'ina ke sauyamin Haruffan rubutuna.
Da masu ganin Gusai suna tunanin wani gari ne, suma su kula Gusau ne ba Gusai ba.
Nagode.








*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


*FATAN ALHERI DA SAKON GODIYA ZUWA GARE KU*


*AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH)*
*MARYAM JUMARE*
*NANA HALIMA(MASOYIYA)*
*HAFSAH HAFNAN(SAHIBATU)*


_*Nagode muku bisa yadda kuka yi ta Hidima da wannan littafin, HasiyarAssadiq tace ta gani kuma ta yaba, Innani kuma tace dukkan ku Allah ya yi muku albarka Amin*_




*20*


Sai bayan Fitar Tahir yaji wani mugun zazzabi ya kara rufeshi.
Nan da nan ya fara rawan Sanyi Hakoransa na had'uwa waje d'aya.
Kansa kuwa kamar zai Tsage gida Biyu Tsabagegen yadda ya ke sara masa, jijiyon kansa sun mike gabadaya Rad'au a saman kansa saboda Halin da ya ke ciki.
Idanuwansa biyu Tahir ya dawo da magangunan da ya siyo masa.
ba domi Tahir ya taimaka ya tada shi zaune ba ji ya yi kamar bazai iya ma tashi ya zauna da kansa ba.


Tea mai kauri Tahir ya had'a masa yace bazai sha ba , shi kuma ya lallabeshi kan ya samu ya sha saboda ya samu sha mgani.
Dalilin haka yasa ya sha kad'an ammh ji ya yi ba dad'i kamar ya na shan mad'aci saboda bakinsa da ya zama wani takaf kamar wanda ya yi shekaru cikin jinya.
Tahir ya ballo masa magungunan Paracetamol ne sai maganin maleria d'in nan mai warin kudin cizo. Shi ba ya son magani ya fi shiri da Allura ammh Bala'in Tahir yasa sai da ya sha magungunan gabadaya sannan ya kyalesa ya koma ya kwanta Lokaci d'aya ya na kara taba goshinsa jin har lokacin da zafi.
Ya dad'e barci bai daukesa ba ya na jin Tahir bi ni bini sai ya lekosa ya na masa sannu tun ya na daga masa kai in yajisa har wani wahallalen barci ya Daukesa mai cike da Tararradi da zullumi.
Bai san haka ya yi barci sosai ba sai da ya farka cikin ikon Allah yaji zazzabin jikinsa ya sauka sai dai sarawan kan kad'an. lokacin da ya yunkura ya mike sai yaji ba jirin Tunda ga shi har ya iya mikewa da kansa batare da taimakon kowa ba.
Tahir ya kallah da ya kwanta a kasa wayarsa na saman cikinsa kila wajen Dannan wayar ne barci ya Daukesa bai sani ba.


Yasan ba shi da laulayin yawan ciwo sai ya jima bai yi ciwo ba, in ko ya yi Ciwo sai dai ko ciwon kai in ya yi Tsanani ne zazzabi shi Allah ya Tsare shi da ciwukan zamani irin su Ulcer ko Typiod.
Jin ya samu karfin jiki yasa ya dibi Ruwa a buta bayan ya Dauki karamar wayarsa ya kunna Fitila.
Ruwa ya zuba a karamar buta sannan ya yi addu'a ya bude kofa ya fita daidai lokacin da karfe uku na dare ta cika a wayarsa. Ba shi da tsoro daman Tahir ne ke tsoron Fitan Dare ba Sadiq ba shi da ko a gida ko karfe nawa ne zai iya fitowa Haraban gidan su in yaji wani motsi to anan ma shi ke raka Tahir in lalura ya tashe shi cikin Dare.
Kai Tsaye makewayi ya haska ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito a tsugunna a kan damdamali ya yi alwala sannan ya koma Daki har Lokacin Tahir na ta barcin bai ma san ya tashi ba.
Darduma ya shimfida bayan ya cire kayan jikinsa ya saka wata farar Jallabiya ta mutanen Saudiya. Yasan akwai sallar mangariba da isha'i da ke kansa ba shi su ya fara yi kafin ya mike ya yi salla raka'a Biyu ya jima acikin Sujjuda ya na ta addu'a sannan ya Dago ya yi tahiya ya sallame nan ma d'in ya jima ya na kirga da hannunsa kafin ya daga hannunsa sama ya na addu'a na tsawon wani lokaci sannan ya shafa.
Bai koma kan katifar ba sai ya kishigid'a saman darduma ya na jin Kwakwalwarsa ta na shiga wasu Tunane Tunanen da a dazu kwata kwata ta tsaya cak. Iya hangen nasa ya gama Hango masa aikata Rokon Amma daidai ya ke da rasa goyon bayan wasu daga cikin Ahalinsa.
In yace kuma ya shawarce su ya bata komai domin ba bu wanda zai rama masa baya acikin wannan Halin da ya ke ciki.
A cikin zuciyarsa ya cika da Tausayinsu kuma ya na so ya taimaka musu ammh bukatar Amma ta yi tsauri ta kuma saka masa wani irin Dabaibayi ne mai wuyan fita. Ga shi ya riga ya furta tun farko shi maraya ne babu yadda za'ayi kuma daga baya ya sauya mgana.
Tunanin mafita kwakwalwarsa ta Zurfafa aciki ammh sai dai har barci ya kwashe shi bai samu wata mafita mai kyau ba duk Mafitan da ya hango sai yaga bazata bulle da shi ba.
Acikin barcin nan da ya koma sai ya yi mafarki ko nace kamar Allah ne ya nuna masa sakamakon zabin da ya mika garesa.


Ganinsa ya yi a wani Daji ba gida gaba ba gida a baya. Shi kad'i ya na ta faman bulayi ya rasa hanyar da zata fitar da shi Kamar daga sama yaji an kwala masa kira ya na juya sai ya ganta wata Doguwar mace ammh kuma ta saka mayafinta ta yane Fuskarta ba ya iya ganin kamaninta sai dai kwayan idanuwanta.
abun mamaki kuma da Tsohon ciki a jikinta.
Ya na ganinta sai ya yi Saurin karisa gareta ya riko hannunta suka fara tafiya tare. Ba zato kawai sai ga Sultana ta sha gabansu ba ta tsaya ba ita ta saka karfinta ta raba Hannunsu waje daya ma'ana ta raba tsakaninsu ita ta shiga Tsakiyarsu ta jimke hannunsa ta ja shi suka cigaba da Tafiya.


Waiwaye ya ke yi ya na kallonta ta na kuka ta na nuna masa bata da kowa da ita da abunda ke cikinta sai shi kada ya tafi ya barta. A cikin mafarkin yaga sanda ya kwace hannunsa acikin na Sultana ya ruga a wajenta ya riketa gam! Sultana na ganin haka sai ranta ya baci ta kara Dawowa zata rab'asu sai ba ta yi nasara ba, shi baisan ko daga ina ba ne? Yaga dai gabadaya yan'uwansa sun yi layi a gabansa da taimakon su suka raba hannayensu suka saka masa a na sultana shi kuma sai ya had'a da hannun wacce bai ga Fuskarta ba ya rike tare da na Sultana.
Umma ce ta bayyana gabansa ta kwace hannun Sultana ta fara tafiya da shi sai sauran yan'uwansa suka mara mata baya.
Yaga har da Abba shima bai bi bayansa ba ta karshen itace Innani ita ta jima a tsaye ta na kallonsu sannan ta juya ta bi bayan su Abba suka bace masa daga Daji nan da ba kowa daga shi sai wannan yarinyar da bai ga fuskarta ba.
Gudu ya ke yi ya na ta kiran sunan Abba da Umma ammh ko me kama da su bai gani ba Sai yaji wata murya da ya na jinta yasan ya santa ta kira shi da karfi.


"ASSADIQ.."


Yana juyowa sai idanuwansa ya gane masa itace. Abunda ta yane fuskarta da shi ya yaye da kansa ta bayyana a gabansa ta na masa mirmishi. Har gabansa ta kariso ta dauki hannuwansa guda d'aya ta Dora saman cikinta sai yaji motsi kamar abunda ke cikinta ne ya motsa a fizge yaji kalaman ta" Ni da abunda ke cikina ba zamu taba barinka ba. Zamu zauna tare da kai sannan zamu tayaka dawo da sauran Ahalin ka."
Hasken Fatar ta ya haske masa ido da yasa ya farka a firgice gabadaya jikinsa ya jike da Zufa.
Cikin Fitan Hayyaci ya Furta


"HASIYA."


tabbas Hasiya ya gani da Tsohon ciki? Me wannan mafarkin ya ke nuna masa.
Wannan mafarkin ya na nuna masa Zahirin abunda zai faru matukar ya aminta da bukatar Amma zai rasa Sultana sannan zai rasa duka Ahalinsa gabadaya.
Sannan ya nuna masa amsa Bukatar Amma zai iya zama alheri garesa ammh kuma kafin cimma haka akwai tarin kalubale sannan zai iya jefa rayuwarsa cikin Tsaka mai wuya da Halin k'ak'ani k'ak'ani.
Ajiyar zuciya ya sauke lokaci d'aya ya na Share zufan Goshinsa. Wayarsa da ke gefe ya laluba ya kunna sai yaga biyar da minti goma na asuba shiyasa yaji ana kiran salla a wasu masallatan.
Kansa ya koma ya dafe a fili ya sake Furta"Hasiya."
Wanda kamar acikin barci Tahir yaji sunansa ya mike a razane ya na fadin"sai naji kamar kana ambatan sunanta?
Ya fad'a ya na haske Sadiq din da fitila a saman gado sai kuma ya tsince shi shima a kasa kusa da shi.
Cikin alamun barci a idon Tahir yace"Sunan Zabiyar yarinyar nan naji kana ambata. Na shiga uku Allah yasa ba itace ta ka maka ka ke kwance ba Lafiya ba."
Cikin mamaki Sadiq yace"Ita wacece ta ka mani?
Tahir ya mike ya na mutseke ido kafin yace"Ita Hasiyar da naji ka na kira ko ba sunan wannan zabiyar yarinyar kenan ba.?


Karamin Tsaki Sadiq ya ja kafin ya yunkura ya mike Lokaci daya ya na Fad'in"Man ni naji sauki fa."
Tahir ya dafa sa lokaci d'aya ya na Tattaba goshinsa da wuyansa lokaci d'aya ya na fad'in"Eh naji jikin ka ba Zafi sosai kila taga bazaka ciwun mata ba ne yasa ta sake ka"
Sadiq ya kyalkyalce da Dariya lokaci d'aya ya na Dafe kansa saboda Saramai masa da ya yi.
Tahir ya kallah kafin yace"Tahir.. Tahir.."
Ya ke fad'a ya na kallonsa Tahir yace"Wlh da yanzu zan nemota duk inda ta ke ta tsallaka ka muguwa kawai."
Ya na wucewa wajen kayansa ya ce ma Tahir"Ba fa mayya bace Tahir. Kowa da irin tashi kaddaran"
Tahir ya karkace baki yace"Maita fa gaskiya ne."
Kai Tsaye Sadiq yace"bamu san maita a addininmu ba. Mu kambun baka kad'ai muka sani maita kuma da ka ke mgana duk Aljanu ne su ke yin abun su da aikin Tsaface tsaface irin nasu"


Daganan bai kara mgana ba ya Dauki Buta da Sauran ruwa ya bude kofa ya fice ya bar Tahir na mgana bai tsaya jinsa ba yasan ko kwana ya yi ya na mgana Tahir bazai aminta da mganarsa ba ya riga ya gama aminta da duk abunda aka Fad'a masa.
Shi kuma cikin bayanan Amma ya Fahimci Rayuwar Hasiya ba komai cikinta sai Kaddara da ke Dawainiya da ita haka Allah ya tsara mata komai in zai Faru da mutum daman akwai Sanadi.
Kuma ita sai ta kasance itace Sanadin na su kaddaran shiyasa ta ke Fuskatar kyama da Tsagwamma.


********


Na gama zura ma Amma ido ko zata min mganar abunda ta tattauna da Assadiq ammh kuma har muka yi shirin kwanciya ba ta ce min komai ba.
Sai da na yi mata shirin kwanciya sannan na zauna a gefen kafafunta ina Shafa mata man zafi a kafafunta tunda tace sun rike mata.
Ina cikin Shafa mata ina ta so na yi mata mgana ammh na kasa sai na yi kamar na yi mata mgana sai kuma na kasa.
Dakyar na yi karfin halin kiran sunanta"Amma.."
Ta amsa da cewa Umh. Kallonta na yi cikin wani yanayi kafin nace"Amma me kika fad'a ma Assadiq? a kaina ne?
Amma ta yi shuru ta na kallona kafin tace"Me yasa ki ke son sani?
Kai Tsaye nace"Ina Son sani ne kawai Amma."
Mirmishi ta yi kafin ta Dafa kafad'ata ta na Fad'in"Kada ki damu. In abunda na rokesa ya ji rokona ya amshi Bukata ta zaki ji komai zuwa da Safe. In kuma bai amimce da Rokona ba har Abada bazaki taba sanin me muka Tattauna ba."
Cikin mamaki na kalleta kafin nace"Amma."
Kai ta gyad'amin tare da mirmishi da ya Kashe min baki.
A sanyaye na gama shafa mata man zafinta sannan na gyara mata kwanciya.
Hannuna ta rike ta na fad'in"Khairan in sha Allahu Hasiya."
Jinjina mata kai na yi batare da mganarta ta shiga jikina ba.
Mamaki na ke yi wata mgana ce wannan da Amma ta kasa Fad'amin?
Da farko na dauka Labarin abubuwan da suke faruwa da ni ne sai daga baya kuma na Fahimci wata mgana ne ta Dabam.


Barci na a ranar rabi da rabi ne duk sanda na farka sai na hangi Amma saman Darduma ta na sallah. Na fad'a daman ba ni da kokarin sallar Dare shiyasa har akayi asuba ban iya tashi ba har sai da Amma ta tasheni sannan na iya tashi ina kallonta ina jinjina abunda zai hanata barcin na tsawon Dare duk da nasanta ta na daga cikin mata masu kokarin Ibada ammh bata kaiwa har dare ya fara ya kare bata yi barci ba Sai zargina ya tabbata da cewa tabbas akwai wani abu da ke faruwa wanda bansani ba.
Jikina a sake na tashi da shi, Amma kuma ta lura ammh kuma ba ta min mgana ba sai dai na lura da wani abu tunda garin Allah ya waye Amma ke duban hanya kamar ta na jiran wani ko wata. da ta ji sallama sai ta leko har na nagaji nace mata wa ta ke nema tace min bakomai.
Cikin ikon Allah mun gama karyawa kenan sai ga Hamma Isuhu ya diro ba makawa tafiya ta tabbata a ranar kenan Tunda yace tare da wani mai Motar da zai daukan mana kaya suka Taho dagachan ya Dauko Itace ne zai shiga cikin gari ya sauke sannan sai yazo ya kwashemu mu da kayanmu.
Jin haka yasa Amma tace na kira su Adda na fad'a musu su zo mu yi sallama.
Da wayar Maman Boy na kira su, nace Adda Fati ta kira Inna Talatu da Ramatu ta sanar da su. Daganan sai na fara wanke yan kanukan da muka bata da Safe daman kayammu suna kammale waje d'aya.
Isuhu ko na ciki suna Hira da Amma na wani Lokaci kafin yace Amma bari ya shiga cikin gari ya dawo lokacin mun gama fitar da komai zai kira mai Motar in ya gama sai su dawo tare.
Na kasa Fahintar yanayin fuskar Amma a lokacin. Ta na dai zaune ta na jan Cashaba ni ce na ke kazar kazar ina had'a mana sauran kayan sawan mu da kayan amfanin da na fito da su.
Su Adda ba su tsaigaita nan da nan sai ga su sun taho cikin Damuwa da jimami.
Adda Rukayya ma ta riga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login