Showing 72001 words to 75000 words out of 93195 words

Chapter 25 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11462

wasa karamar mgana ta zama Babba Domin washegari Innani Sashen Umma ta yini ta rika sata ta na kiran mata su Surayya da kanta ta ke musu mgana ta na fad'in su fara shiri auran Kaninsu da kanwarsu bad'i kowacce haka taji mganar Daga sama ba sanarwa.
Sai bayan Innani ta koma Shashenta suke ta kara kiranta suna Tambayan ba'asi ta na kora musu jawabi.
Surayya tace"Umma gaskiya abun bai yi ba me sultana ta sani na aure yanzu? Sadiq ma nasan ba shi da Ra'ayin aure yanzu."
Umma tace"To ya muka iya. Kun san dai Halin kakar ku."
Surayya tace"Umma kin gayama Sadiq?
Umma tace"A'a na kasa gayamasa ko yau mun yi waya da Safe. Tsoro na ke ji Innani ko Abban ku susan ni na Fad'a masa."
Surayya tace"Ummi ni zan kirasa na fad'a masa gwara ya dakatar da abun kafin ya yi nisa."
Umma tace"To Allah yasa kada sunan ki ya fito."
Surraya tace"ban damu ba Umma. Bikin Kaninmu so mu ke a yi shi one in Gusai in sha Allahu."
Surayya ita ta kira Sadiq ta gayamasa Halin da ake ciki.


Bai yi wani mamaki ba sai dai ya tausayama Innani da ta ke masa shisshigi a rayuwarsa.
Mgana ta waya bazai yuyu ba yasa ranar asabar ya ce ma Tahir zai je Gusai Tafiyan Ujila ya taso masa.
Tahir ya tambayesa kwana nawa zai yi? Yace daya gobe lahadi zai dawo.
Tahir ya yi masa fatan dawowa lafiya.
Domin kwanaki nan fad'a su ke yi akan mutanen da Sadiq yaga ya daukesu da Muhimmanci Fiye da Sauran mutanen da yasan ya na taimako.
In yau bai je gidan ba to gobe sai yaje bayan kullum ya na hanyar zuwa siyan Danwake da ya ke da tabbacin in ma wani tsafin ne ta nan aka saka masa.
Tunda har ka taimake su kuma matar nan ta samu lafiya ka rabu da su mana ammh ya lura Sadiq na so ya saka kanshi a abunda zai zo ya na danasani daga baya.
Shi fa tsoronsa kada Sadiq ya fara son zabiyar yarinyar nan. Tunda yaji Sadiaq din na fadin"kamar kanwarsa ya ke ganinta sannan suna ba shi Tausayi."
Tunda suna son su jaawosa a jiki ne komai ma zasu iya yi. Haka kurum ya ke jin baya son wannan alaqar ta Sadiq da Sabbin mutanen da garin Tausayinsa ya jajibo ma kansa.
Har Sadiq ya tafi shi kad'ai ya rika Tunanin hanyar da zai raba wannan Alaqar da ta fara kulluwa.
Ammh kuma ya kasa samun mafita in dai ta mgana ce har ya yi ya gaji Sadiq bai sauraresa ba.


******


Ba wanda yasan da zuwan magajin gida sai da aka ganshi kawai.
Kuma zuwan daman na Innani ne wanka kawai ya yi ya sauya kaya ko Shashen Umma bai shiga ba ya yi ma Falon Innani Tsinke da ta Rud'e da jin zuwansa
Yana shigowa ta fara


"Maraba maraba da Magajin gida."


Fuskar nan ba Fara'a Siyama da Sultana ne tare da Innani lokacin ma mganar auran ta ke karanta musu. sannan kuma wai ta na koyama Sultana Dubarun zama da miji Siyama na gefe ta na shan Dariya.
Fuskarsa ba Fara'a suna gaishe shi bai amsa ba yace"Ku ba ni waje zan yi mgana da Kakar ku."
Jin sunan da ya kira Innani yasa suka san ba lafiya da sauri suka fice.
Suna Fita Siyama ta kalli Sultana ta na Fadin"Sultana ko Ya Sadiq zai ce ba za'ayi auran ku yanzu ba ne?
Sultana a sanyaye ta ce"Bansani ba. Ammh da hakan ta faru da zan so haka."
Siyama tace"Me yasa kika ce haka?
Kai Tsaye Sultana tace"Na fi so sai na gama makaranta Siyama. na kara wayau tukunna"
Siyama ta jinjina kai kafin tace"Eh kuma fa hakane gwara da wayan ka an fi sanin Darajan ka."


Suna tafe suna Hira har shashen Umma taga gansu ne ta ce suka bar Innani ita kadai Siyama tace suna mgaana da Ya Sadiq ne.
Umma ta yi mirmishi a ranta ta na jin Dadi tasan Dole kanwar naki Innani ta bar mganan auren nan.
Ilai kuwa Sadiq achan Falon Innani Wuta ya bud'e mata.
Kamar bai taba saninta ba sai ta fara kuka ta na fadin"Ni daman in ga ya'yan ku ne kafin na mutu."
Sadiq yace"Duk ya'yan su big sis da ki ke da shi baki godema Allah ba.! In kuma nazo Allah bai bani haihuwan ba fa ya zaki yi.?
Da Sauri Innani tace"Allah ba amin ba. Da ikon Allah sai ka tara zuru'a"
Tsaki ya yi kafin yace"To tunda kinsan Allah me yasa kike yi ma Allah Shisshigi? Aure da mutuwa da Haihuwa al'amarinsa ne na kuma sha miki gargadin cewa in kina so ki Mutu cikin salama ki kiyayi shiga Hurumin Allah."
Innani tace"Na bari alqur'an bazan kara shiga ba."
Kai Tsaye yace"Kin shiga mana. Ina ruwan ki da mganar aurena. Ke zaki zauna da matar in kika aura min ita yanzu? Ko ce miki akayi na gama karatun kenan? Ina gama bautar kasata zan dora masters dina. Mganar aure kuma na Soketa sai ranar da na Shirya Innani."


Innani ta yi shuru bata yi mgana ba.
Ganin haka yasa ya taso daga in da yake zuwa gabanta ya zauna ya rike Hannayenta ya na fadin"Innani ki kwantar da Hankali in sha Allahu ke zaki rakani Dakin Sultana ranar angwancina."
Jin haka yasa Innani ta washe baki ta na fadin"Allah ya nuna min wannan ranar. Allah yasa ina raye ban mutu ba."
Hawayenta ya ke share mata da Hannunsa Lokaci d'aya ya na fadin"In sha Allahu bazaki mutu yanzu ba Innani sai kin Dauki ya'ata ko d'a na ni da Sultana."
Sai Innani ta Rumgumesa ta na fad'in"Idon makiya a tsiyaye a kan jikana. Yadda kace haka za'ayin magajin gida"
Shima Rumgumeta ya yi ya na fadin"Yauwa Kakata mai kyau."
Shikenan mgana ta mutu murus. Kwana daya ya yi washegari lahadi ya Dawo zariya.


Innani haka ta tara su Abba akaro na Biyu tace mganar aure bata sai magajin gida ya yi masta dinsa.
Haka yaran ma duk ta kirasu ta na fad'a musu sai magajin gida ya samu masta za'ayi auransa da Sulsana.
Kowa yaji sai ya Dara, Duk wanda yace aikin waye haka da Innani ta Sauya mgana."
Umma na dariya ta kan ce"Aikin waye kuwa ban da na magajin gida magajin kowa."
To in ba magajin gida ba, Waye ya isa ya sauya wannan mganar ai sai shi kad'ai ne wanda mganarsa ke saman ta Innani da ta Abba shi kan shi.


*****


Ya dawo a gajiye dalilin da yasa bai leka gidan su Hasiya ba kenan.
Sai washegari litini bayan ya dawo daga in da ya ke hidimar kasar sa. Ya na jin Amma a ransa in ya ganta Umma ya ke gani Hasiya da Habiba kuwa tamkar Siyama da Salima ya ke kallonsu. Ya kuma san zasu damu da rashin ganinsa tunda bai fad'a musu zai yi tafiya ba.
Sanin Tahir baya son ya ji zai je gidan nan sai ya fara maganganu yasa bai fad'a masa ga in da za shi ba, ce masa kawai ya yi zai je ya dawo
Takaici suka saka Tahir ya kasa mgana Sadiq ya fita ba Dadewa sai ga wani Mutum ya zo ya na masa sallama a kofar dakinsa.


Ya ma zata abokan zaman su ne Tunda in suna bukatar wani abu suna yi musu mgana. Tun ballatana sun san Halin Sadiq abun sa na mutane ne.
Ya na fitowa sai ya ga bakuwar Fuska da bai taba gani ba mutumin zai kai shekara arba'in dattijon matashi ne.
Hannu ya basa suka yi musabaha, cikin mamaki Tahir yace"Lafiya? Kamar ban gane ka ba?
Mirmishi ya yi masa kafin yace"Baka sanni ba shiyasa baka gane ni ba.?
Tahir yace"Oh to ko wani ka ke nema?
Da sauri yace"Ai naga wanda na ke nema dazu ya fita ko?
Tahir yace"Sadiq?
Cikin alamun tambaya kai ya gyad'a masa kafin yace"Abubakar Sadiq sunansa kenan shima."
Tahir duk bai gane ba yasa ya kankance idanuwana kafin yace"mallam wai lafiya?
Kai tsaye yace"Taimako ne yasa na zo gareka. na fahimci kai ne abokinsa da ku ke zama tare. To in dai har kana son abokin ka ya cigaba da Rayuwa ya kamata ka dakatar da shi da Rab'ar in da yarinyar nan ta ke."
Tahir ya saki hancinsa ya na shakan Iska kafin yace"Wata yarinya kenan.?
Kai Tsaye yace"Hasiya mai Danwake wata Fara farinta mai haske haka Siririya."
Tahir yace"Oh na ganeta lafiya? Da wani abu ne?
Mutumin yace"Sosai ko da matsala dan Samari ganin ko ba yan garin nan ba ne kada a cutar da ku ba ku sani ba. Kada ka bari abokin ka ya auri wannan yarinya ta na da bakin jini da bakin kashi mai kashe rai da asaran Dukiya."
Tahir ya ware ido kafin yace"Bawan Allah ban ga ne ba? Wa ya fad'a maka Sadiq auran wannan yarinyar zai yi? Taimakon su kawai ya yi shikenan ba wata mgana."
Shima kai tsayen yace"Duk da haka dai ya yi nesa da ita gudun matsala abu ne ya faru ba sau d'aya ba sau biyu ba kowa a anguwan nan yasan da labarinta gwara ka ba shi shawaran ya kiyaye domin tsira da Lafiyarsa."


Tahir ya gaji da jin mganar da ya kasa ganewa kai tsaye yace"Mallam ka tafi kai tsaye kan mganar ka. Ba na son wannan zagaye zagayen naka."
Jin haka yasa ya shiga warware ma Tahir komai da ya Dangancin Hasiya.
Har da mutuwar babanta ma itace cutar mahaifinta karayan arzikin su. Gujen su da Ahalin babansu suka yi. Auran ta da Abubakar da abunda ya faru da kuma na Salisu ya karishe da Fadin"yarinyar ba'a san mayya ba ce ko wani abu. Ammh tabbas duk wanda ya Rabe'ta akwai asaran rai ko Dukiya in ba'a Mutu ba za'a wahala sannan a rasa komai irin su zama da su bala'i ne da Masifa."
Har Mutumin nan ya tafi Tahir na Tsaye rike da kugu baki bude mamaki ya Rufe shi.
Lalle biri ya yi kama da Mutum yarinyar nan shiyasa farinta ya yi masa wani iri ashe ashe bakar daga ce Gobara daga kogi mganinta sai Allah.
Bari Sadiq ya dawo in yaji haka don Dolensa sai rabu da huld'ar da duk abunda ya shafi wannan yarinyar.




*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*








*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj




*17*


Shi ko Sadiq gidan su Hasiya ya je. Daman ya saba in dai yaje a waje ya kan tsaya ya aika yara sai Hasiya ko Habiba su fito su shiga da shi ciki.
Saboda akwai mata a gidan sannan a tsarin addini shi balaggage ne babu tsari ya rika shiga gidan matan aure kai tsaye batare da izini ba.
Duk da matan gidan na su Hasiya kallo garesu ba wani abu ba ne, kamar ba matan aure ba. Shi dai har ya shiga ya fito kansa na kasa ba shi da dogon kallo a rayuwarsa koda da wanda ya sani ne, ko da akwai sabo a tsakaninsu.


Yau ma d'in Habiba ce ta fito ta shiga da shi ciki har dakin Amma ya na shigowa da Hasiya ya ci karo ta na ganinsa ta sakar masa mirmishinta shima sai ya maida mata martani cikin zolayar da ya fara mata kwanaki nan yace"Hasiya mai Danwake."
Baki ta tura kafin na juya ina kallon Amma lokaci d'aya ina fad'in"Amma kin gan shi ko? Wai Hasiya mai Danwake ya ke kirana."
Amma na zaune ta na mirmishi na ganin Abubakar d'in, Allah ya sani haka kurum ta ji Allah ya Do'ra mata kaunar wannan bawan Allah, har cikin ranta komai na shi ya yi mata.
Cikin Annurin da kan bayyana saman Fuskarta in har ta ga Abubakar tace"Ke ma ba sai ki rama ba. Da ya kira ki Hasiya mai Danwake sai ke ma ki ce masa Habu mai siyan Danwake."
Gabadayan su suka fashe da Dariya Habiba na rufe bakinta tace"Amma Hamman ne Habu mai siyan Danwake.?
Da ya ke Hamma ta ke kiransa. da Ladabin Fulani yaya kenan.
Abubakar ya yi dariya har sai da Fararan Hakoransa suka bayyana awaje Hasiya ce tace,"Shikenan ko Amma ta kawo shawara."
Sai da ya zauna gaban Amma sannan yace"Hasiya mai danwake ya fi dad'in fad'a ko a baki Amma"
Amma ta yi dariya ba ta ce komai ba gaisawa su ka yi a mutunce kamar yadda suka saba.
Habiba ta kawo masa ruwa a jug. Hasiya kuma ta kallesa ta na fad'in" a kawo abinci..?
Kai ya girgiza Lokaci d'aya ya na Fad'in" na sha fura a wajen aiki. Cikina ya cika Sosai."
Amma tace"ko aikin ne ya hana ka zuwa kwana biyu Abubakar?
Ya na sosa kansa yace"A'a Amma kauye na je. kuma tafiyar ta gaggawace shiyasa ban Sanar da ku ba."
Amma tace"Ayya. Ka same su lafiya ko?
Ya ce"Eh duk sun ce suna gaishe ku Amma"
Amma ta amsa cikin sakewa. Kafin su cigaba da Hira kan rayuwa da sauran su.


Rabin Hiran duk na Amma ne shi na shi eh a'a ne sai ko in ta yi masa wata Tambayar.
Habiba islamiya ta shirya ta tafi ni kuma sai na fita waje na Hura gawayi na Dorama Amma ruwan wanka tunda ba ta yi ba.
Daman ban cika zama adakin ba in ya na nan saboda gudun zargin mutane.
Yan gidanmu sun ta bin kwakwafin ko saurayina ne to ganin ya na shiga har Daki kuma su jima su na mgana da Amma sai suka aminta da cewa da gasken dai kila d'aan uwan mu ne.
Kila kuma cikin Dangin Babanmu da suka watsar da mu ne.
A cikin raina na ke jin Abubakar a chan kasan raina na saka shi cikin Layin masu kaunar mu. Ina shiga Damuwa in bai zo ba, Saboda shi ma ina Fargaban kada watarana a rabamu da shi ina jin Tsoron faruwan hakan shiyasa in bai zo ba na rika shiga Damuwa kenan ina faman ce ma Amma" yau fa bai zo ba"
Amma kan tausheni da cewa"Zai zo Hasiya. A jikina na ke jin yaron nan ba irin sauran ba ne. Zai zo in sha Allahu."


Yau ma sun jima suna Hira da Ammah sai da yammah ta yi ana gabda kiran mangariba sannan ya yi ma Amma sallama ya tafi. Bayan ya ba ta dubu uku Amma ta ki karb'a ta na Fad'in"Kai da ka ke d'an makaranta Abubakar kuma ka ke Hidima damu? Ai sai abun ya yi maka yawa."
Haka ta ke fad'i duk sanda ya yi mata wani karamin kyauta.
Shi kuma kai tsaye ya ke cewa"Amma kin manta na fad'a miki ina Hidimar kasa ne? Suna biyan mu duk wata kuma Dubu uku ai ba Hidima bace."
Amma ta amsa lokaci d'aya ta na Fad'in"Allah ya yi albarka. Allah ya jikan iyayen ka, Allah ya haskaka makwancin su Allah yasa suna cikin Dausayin Aljannah. Nagode sosai Allah ya tsare ka duniya da Lahira."
Shi dai na shi amsawa da Ameen ne cikin jin dadi.
Ko da ya fito da niyyar tafiya samuna ya yi ina ta fama da fifitan gawayi ya ki kamawa saboda nayi rashin sa'a ya na da Sanyi a jikinsa.


Ban san ya zo kusa da ni ba sai da naji ya na fad'in"Wutar ta ki kamawa ne?
Da sauri na juyo ina kallonsa.
Ya na tsaye a gefena sanye da riga da wando masu ruwan toka rigar ta na da Layi layi sannan tare da dogon hannu na Fahimci ya na son saka riguna masu Dogon hannu.
Sannan Dabi'arsa ne ya na tsaye ya tura Hannayensa cikin Aljihun wandonsa.
Yau ma haka d'in ya yi sai naga ya yi min kyau. Haka daman masu suna Abubakar su ke da gayu da kyau tare da Tsari?
Shagalar da na yi ina kallonsa yasa har ya Durkusa a gabana ban sani ba sai ji kawai na yi ya na fad'in"Kawo na tayaki fifita wutar."
Da sauri na dawo Hayyacina da Sauri na tashi ina kallon bayana ganin matan gidanmu a tsakar gida an zuba mana ta mujiya musamman ma Kaltume.
Da sauri nace"Don Allah ka bar shi. Kayan ka za su yi hayaki?
Ya na kallona yace"kin tabbata zaki iya hura wutar?
Da sauri na gyad'a masa. Shiyasa ya mike ya na fadin"Bari na tafi"
Ban san bakina ya kubce ba sai da na jini ina fad'in"Tun yanzu?
Agogon Fatan da ke hannunsa ya kai ma Duba kafin yace"Mangariba ta kusa ne"
Jinjina kai na yi kafin na yi mgana ya rigani da fad"in"Zo mana Hasiya."
Ba musu na amsa masa.
Daki na koma na dauki Hijabina ina ce ma Amma Abubakar na kirana a waje ta amsamin ta hanyar d'aga kanta sama.


Ina fitowata matan gidanmu suka sakarmin na mujiya
Har na fice suna kallona na kuma san ina fita za'a dasa yi dani.
A kofar gidan na ganshi ya jingina da garu ya na kallon hanya.
Ina fitowa ya tashi daga jingina da ya yi da garu ya na kallona.
Kallo ba Dabi'an sa ba ne ammh sai ya samu kansa da karemin kallo, Fuskata ta kara masa Fayau saboda jan Hijabi ne ajikina in ba sanin fatata ka yi ba sai kayi Tunanin ba ni da jini ne saboda yadda Fata ta dashe fari sol ba alamun ja ja a jikina.
Ni kuma sai na Tsargu da yanayin kallon na shi. Barin ma da mutane ke ta wucewa suna kallon mu har da ma su waiwayowa suna cin Tuntube saboda Gulma.


Shi kuma kallona ya ke yi ammh kuma Tunaninsa ya tafi ga Tunanin sunan da Tahir ke kirana wato Zabiya kuma sai yaga gaskiyan shi kad'an ne ya ragemin ban zama Zabiyar ba.
Ko Amma fara ce Ammh ba kalan fari na ba ne Habiba ma haka kalan haskenta mai ja ne ba irin na wa ba ya na da tabbacin duk da bai ga sauran yan'uwana duka ba kalan Fatata ta fita Dabam da na su.
Gyara murya na yi dalilin da ya sa ya sauke kallonsa a kaina lokaci d'aya ya na fad'in"Hasiya mai d'anwake "
Ya fad'a cikin Zolaya. ni ma kai tsaye Nace"Habu mai siyan Danwake ba."
Dariya ya yi ya na girgiza kai kafin yace"Sunan ki Asiya ne ba Hasiya ba.'
Kai tsaye nace"Na fad'a maka ni sunana Hasiya ba Asiya ba ce."
Kai ya jinjina kafin yace"Daman an ce bafullatani da kafiyar tsiya."
Baki na tabe kafin nace"Da Amma ka ke ni bazazzagiya ce tunda Babanmu mu haifaffan garin zariya ne."
Shima kai tsayen yace"Ammh kin yarda ke Ruwa biyu ce Hausa Fulani. Wani ma in ba kin fad'a masa ba kin fi kama da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login