Showing 75001 words to 78000 words out of 93195 words

Chapter 26 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11469

buzayen yamai."
Cikin mamaki nace"Ina ne kuma Yamai.?
Ya na Bude ido yace"Baki san yamai ba?
Na gyad'a masa kai. Kai tsaye yace"Ke bakauya ce a she ban sani ba."
Ina yar Dariya nace"Kuma bak'auya ta had'u da bak'auye ba."
Baki ya rike ya na fad'in"Hasiya ashe haka ki ka ji Hausa ban sani ba.?
Ban ce masa komai ba sai dai na Murmusa.


Shuru ya yi na wani lokaci kafin yace"Bari na zo na tafi. An fara kiran sallah."
Ina dagowa nace"Kwana biyu ba ka zo ba? Ba tare da ya ba ma mganar Muhimmamci ba yace"Eh na yi tafiya ne."
Iduwana na kallonsa nace"Garin ku ka je?
Wannan karon da kai ya amsamin kafin ya yi mgana da sauri na tare shi da cewa"Gobe za ka zo?
Cikin mamaki ya kalleni sai na ji kunya da nauyi da sauri na gyara maganata da fad'in"Amma ce ke damuwa in baka zo ba."
Mirmishimsa mai Tsada ya saki kafin yace"Ko ban zo ba. zan aiko a siyamin Danwake."
Cikin marairaicewa nace"Don Allah kada ka aiko da kud'i"
Kai tsaye yace"Nima don Allah ba na son gaddama."
Ganin yadda ya yi mganar yasa ban kara cewa komai ba.


Sallama mu ka yi ya wuce ni koma na koma cikin gida ina shiga Maman Boy ta washe baki ta na fad'in"Ai na jiki shuru nace Hira ta yi dad'i. naga rushun ya ruru sai na aza miki Ruwan."
Ban sakar mata Fuska ba nace Nagode. na shige dakin Amma ina kallonsu suna had'a ido da Maman Salihi za'ayi gulma.
Acikin raina nace"Tunanin abunda bazai taba faruwa ba ku ke yi."
Ko da Allah ya ce zai Farun Hasiya?


******


Bai koma Daki ba sai da ya tsaya masallaci ya yi sallar mangariba ana wa'azi da Fadakarwa kan mutuwa yasa ya zauna har aka kira Isha'i.
Sai da sallar isha'in sannan Tahir ya zo bayan an idar da salla suka koma Daki tare.
Bai masa mganar ba sai da suka yi shirin kwanciya. Tahir wayarsa na Hannunsa shi kuma Sadiq Laptop dinsa ya jawo bai ma kai ga kunna ta ba yaji Tahir na fad'in"Wai dazu ina ka je.?
Ba tare da ya kallesa ba yace"Gidan su Hasiya na je."


Tahir takaici ya sa ka shi ijiye wayarsa duk ko abunda zai sa Tahir sauke waya lalle muhimmancin al'amarin ya girmama.
Sadiq bai ma san ya na yi ba kokarin Sarrafa Na'urar hannunsa kawai ya ke yi Lokacin da yaji Tahir na Fad'in"Sadiq ko dai ka fara son Zabiyar yarinyar nan da gaske ne?
Ba tare da ya bama tambayan Tahir Muhimmanci ba yace"So kuma? Ka cika maimaita mgana D'aya ina ce mun rufe wannan mganar da kai ko Tahir?
Tahir ya katseshi da Fad'in"To in baka so nayi zargin haka ka rabu da su mana. Yan'uwan ka ne da dole sai ka rika zuwa in da su ke? Ina ce daga Taimako ba shikenan ba?
Sadiq ya yi shuru kamar bazai yi mgana ba sai kuma chan yace" Tahir na fad'a maka Tausayin su na ke ji. Kuma ni wajen mahaifiyar su na ke zuwa matar na so na wlh."
Tahir ya yi wata Dariyar renin wayau kafin yace"Ta na sonka? Eh dole ta soka Tunda ta na son kaima ta jefa rayuwarka cikin gagari ta sanadin yarta kamar yadda ta jefa Sauran."
Sadiq bai Fahimci in da Tahir ya dosa ba shiyasa ya ce"Naji ka bar ni. Rayuwata ce ba taka ba Tahir."
Tahir yace"Kasan me naji a kan wannan yarinyar da Ahalinta?
Sadiq kai tsaye yace"Sai ka fad'a."
Ya fad'a hankalinsa na kan Allon Na'urar da ya ke kallo.


Tahir yace"ka na fita wani Mutum ya zo can u just imaging yarinyar da ka ke ma kallon yarinya karama auranta fa Biyu bazawara ce."
Sadiq ya yi shuru kafin ya Dago ya na kallon Tahir cikin mamaki yace"Me ka ce? Bazawara ?
Tahir yace"Yes ofCourse Bizet ba. Abunda zai kara baka mamaki ma shine Bayan mganar auran nata yarinyar ta na da wani abu a tare da ita na Dabam kuma"
Sadiq ya yi saurin cewa"Kamar na me?


Nan Tahir ya shiga zayyanemasa har da kari ya karishe da fad'in"An ce duk arzikin mutum in ya rabeta sai ya talauce in ma bai rasa rai ba. Mijinta na farko da shi da iyayensa sai da suka rasa komai nasu, na Biyun kuma ya na chan ya na jinya.
To wai yarinyar da ace itace silar karyan arzikin Ubanta ta yi kuma sanadiyar mutuwarsa da ciwon uwarta da duka Halin da suke ciki itace Sila kasan wasu haka Allah ke yin su da Farar kafa ba bu albarka ko wani nasibi a tare da su."
Tahir ya tsagaita ya na kallon Sadiq ya na so ya Fahimci yadda ya karb'i mganar sai yaga hankalinsa na kan abunda ya ke kamar ma bai ji abunda ya ke fad'i ba.
Kai tsaye Tahir yace"Baka ce komai ba?
Sadiq kai tsaye yace"Me zan ce maka Tahir?
Cikin mamaki ya ce"Baka ji mganata ba ne?
Sadiq yace"Na ji mana. Me ka ke so ayi yanzu?
Tahir ya gyara zama ya na fad'in"Ka yi nesa da su don Allah Sadiq. Ka na da wad'anda in wani abu ya sameka za su shiga wani Hali."
Sadiq ya yi kamar bai ji Tahir ba sai da shi ya gaji da jiran jin ta bakinsa ya kwace laptop d'in ya na fadin"Sadiq mgana fa mai muhimman na ke yi maka ka yi min banza"
Sadiq ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce"Tahir me ka ke so nace.?
Tahir yace"Au me ma zaka ce ka ke tambaya ta Sadiq?
Lafiyar ka Dukiyarka ka tseratar da su mana."
Sadiq ya goya hannayensa a saman kirjinsa lokaci d'aya ya na fad'in"To naga ai ni ba mai dukiya ba ne ballatana ace zan talauce."
Ya fad'a lokaci daya ya na kyalkyacewa da Dariya.


Galala Tahir ya yi ya na kallon Sadiq ganin ya na dariya kamar wanda ya fad'i wani abun dariya.
Tahir ya shaka da yasa a fusace yace"Sadiq abun dariya ne wannan?
nace abun dariya ne wannan?
Sadiq ya tsagaita da Dariyan ya na Fad'in"Gaskiya abun dariya ne Tahir. Ta ya ya zaka yadda da wannan mganganun kamar almara?
Daman mutum ya isa ya yi ma wani mutum wani abu batare da Allah ne ya yi masa ba?
Ya tambayi Tahir Lokaci d'aya ya na kallonsa. Tahir yace"Ba wannan bane, Ka fara tunanin janye jikin ka daga wannan yarinyar Sadiq in dai ba sonta ka ke yi ba."
Sadiq yace"Wlh tallahi ba sonta na ke yi ba. Mganar kuma na janye jikina bai taso ba ban fara domin na daina ba Tahir."
Tahir yace"Sadiq ka na jin fa an ce ga abunda ke faruwa a rayuwar yarinyar nan. Daman ni tunda naganta ba ta min ba tsoron ganin Fuskarta ma na ke yi farin ta ya yi yawan da zai iya zama matsala."
Sadiq ya kara Bushewa da dariya kafin yace"ina ruwan ka da farinta. Fari ko baki wani hallita ne na ubangaji. Kada ka danganta haka da yanayin da Allah ya halliceta."
Tahir yace"Sauran mazajen da ta aura fa? Me zaka ce a hakan haka.?
Sadiq ya gyara zama kafin yace"Ni ban zan ce komai ba. Saboda ni musulmi ne na yi imani da Allah da Annabawansa tare da Sahabansa da Littafansa. Sannan na yi imani da Tauhidi da iklasi na kuma san akwai kyakyawan kaddara da Mummuna shiyasa bazan ce komai kan mganganunka ba Tahir, Basu da ma Tushe ballatana makama kai ma ban yi tsammanin jin irin wad'anan maganganun daga bakin ba Tahir."


Ya na gama fad'in haka ya karb'e laptop dinsa ya na fad'in"Ni ga Allah na Dogara nasan kuma shi ke aikata mai kyau ga bawa da akasin sa ba Mutum ba."
Tahir ya saki baki kawai ya na kallon Sadiq bai taba zaton zai iya Ture wannan mganar ba.
Sai yanzu da ya maida abun wasa yasan raba Sadiq da wannan yarinyar nan aiki ja ne.
Tahir bai hakura ba yace"Sadiq ba Rayuwarku d'aya ba. Ku na da tarin bambamce bambance don Allah ka bar su ana su Duniya kai ma ka koma taka Duniyan."
Sadiq ya amsa shi cikin Sakewa ya na Fad'in"musulmi dan'uwan musulmi ne Tahir. Kuma taimako ai ba laifi ba ne ni ban ga wata matsala ba aciki."
Cikin kumfar baki Tahir yace"To aure auren nata ka san da shi?
Ka daa garin Taurin kanka ka siya ma kanka wahala Sadiq."
Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Abunda ya shafe su sai nace sai na sani? Nima ai ba su san komai a kaina ba, Kaga Tahir plz ka kyaleni da wannan mganar bata da asali ballatana Tushe."
Sadiq ya fad'a ya na cigaba da Sarrafa Laptop dinsa Wani Turkish Drama ya ke kallo shi ya ke kokarin kunnawa, sanda Yaji Tahir na fad'in"Ammh kasan akwai farar kafa acikin mutane ko?
Kamar Sadiq bazai yi mgana sai kuma ya Ture Na'urar gabansa ya na kallon Tahir na wani Lokaci kafin yace"babu Farar kafa a cikin Mutane Tahir. Kuma babu Farar kafa a musulumci Duk canfi ne kuma Canfi karya ne addini baizo mana da shi ba kai ko Maita ma Annabi bai sanar damu ba kambun baka kad'ai Annabi ya sanar damu akwai shi a acikin musulunci."
Ya fad'a cikin Tarin natsuwarsa. Tahir ya yi kasake ya kasa mgana.
Sadiq ya cigaba da fad'in" Babu wanda yasan gaibu sai Allah Tahir.
Allah Fa'alim lima yarud_ shine mai aikata abunda ya ke so alokacin da ya so. babu Canfi ko farar kafa a musulumci, lamyasiduna_ Babu abunda zai same mu a wannan rayuwar Illama katabullahi lana_ sai Abunda Allah ya Rubuta zai faru same mu.
Wahuwa maulana_ kuma Allah shine majibancin dukkan lamuranmu.
Wa'allallahi falyatawakkalu mu'uminun_Ga Allah kad'ai ne mu mumumai ne zamu dogara."


Sadiq ya karishe fad'a ya na kallon Tahir kafin ya Dora da fad'in"Saboda haka ka kiyaye irin wad'anan mganganun. Ko wani kaji ya na yi ka fad'a masa Allah shine masanin gaibu ba Mutum ba."
Daga haka ya cigaba da abunda ya ke yi ya bar Tahir ya na kallonsa.
Ba domin wa'azin Sadiq ya wani Shigesa ba. Dole fa akwai ayar tambaya acikin Rayuwar yarinyar sai ace haka kawai komai ke faruwa kai ina da walakin Goro a miya. Dole sai ya yi kamar ya na yi Ko saboda abotan da ke Tsakaninsu da Sadiq ba zai taba bari ya saka Rayuwarsa acikin Tsaka mai wuya ba.


Tun daga ranar bai kara yi ma Sadiq mganar ba saboda yasan ko ya yi masa bazai Sauraresa ba.
Sai ma karin wasu ayoyon da za su biyo baya da tarin Hadisan da Sadiq zai rika gayamasa ya na fassara masa.
Kuma ya na gani Sadiq bai fasa zuwa gidan ba sannan bai fasa zuwa siyan wannan munafukin Danwaken da ya ke Tunanin koma wani Mugun abu ne ciki ta saka ma Sadiq din domin ta ja Ra'ayinsa a kanta.
Har so ya yi ya kira Umma ya fad'a mata sai kuma ya kasa. Ba sa taba irin haka da Sadiq ba duk da shima kamar dan gida ne bazai kyautu ya kai karar Sadiq gidan su ba.
Ya na cikin neman mafita ne Makarantar da ya ke Hidimar kasa su ka yi Hutu yace ma Sadiq zai tafi gida ko shima zai tafi Gusai? Bai tab'a zaton Sadiq din zai ce za shi ba. Ammh sai ya ce masa shima zai tafi gida ya yi sati biyu sannan ya dawo.
Tahir ya ji dad'i sosai tare da Fatan Allah yasa kafin Sadiq ya Dawo ya manta da zabiyar yarinyar.
Rana d'aya suka tafi kuma abunda Tahir bai sani ba Sadiq a daran ana gobe Tafiyarsu sai da yaje ya yi ma Amma sallama a kan zai je kauye zai jima kafin ya dawo.
Har Amma na fadin ko dai in ya tafi bazai dawo ba ne? Yace mata in sha Allahu zai dawo ai bai gama hidimar kasar ba.
Hasiya ta rakosa har waje in ba idanuwansa suka ga masa karya ba yaga damuwa da kewa acikin Idanuwantaa.
Ya na cikin motar zuwa Gusai ya ke tunawa da mganar ta cikin sanyi in da ta ke cewa"Ammh zaka dawo ko?
Kai ya gyad'a mata kafin yace"In sha Allahu SIYA."
Sai ta d'aga masa hannu alamun bye bye kafin tace"Allah ya kiyaye hanya. Ya kuma dawo da kai Lafiya ASSADIQ."


"ASSADIQ.."


Sunan ya daki zuciyarsa har sai yaji ya amsa acikin jikinsa. Lumshe ido ya yi ya na kallon siraran hannunta lokacin da ta ke d'aga masa hannu da Sanda ta juya siraran kafafuwanta ta koma cikin gida.
Sake Bude' idanuwansa ya yi yana jin wani iri aransa In da gaske ne auran Hasiya Biyu me ya faru da ita ta yi aure aure a kananun Shekarunta? Tabbas akwai wani abu shi kuma mutum ne da ba ya cika Takura ma Mutumin da ke tare da shi akan sanin wani abu na fanni Rayuwarsa.
Ammh zai so ya ji garin ya ya da kananun Shekarunta ta yi aure har Guda Biyu kuma ta na fitowa?
Ya tuna kwanaki har Amma ya taba ma tambayar Ko Hasiya Sikila ce?
Amma sai da tayi dariya kafin tace"Hala sirintar ta ka gani ko?
Haka na Haifeta lafiyanta kalau Abubakar."
Abun mamaki har ya kai Gusai duniyarsa da Tunaninsa akan Hasiya ne.
Acikin ransa Tausayinta ya ke ji tun kafin yaji me ya faru da ita. Tausayin yadda ta na karamar yarinya ta Fuskanci Kalmar Saki har sau biyu.
Da rana ya sauka agida.
Murna wajen iyalan gidan Alhaji Sulaiman ba'a mgana.
Kada su Innani ta ji labari ta kasa zama ta kasa tsayuwa Magajij gida ya dawo. Abba baya nan sanda ya dawo ya gaji shiyasa shashensa ya wuce ya yi wanka. Kafin yaci abinci Tahir ya kirasa yace shima ya sauka gida Tun dazu ba su jima suna mgana ba suka yi sallama.
Salima ta kawo masa abinci ya ci ya sha sannan ya kwanta ya na warware gajiya."


******


Tafiyar Sadiq da kwana Biyu Adda ta zo Dalilin ta kira Adda Fati ta na tambayan lafiyan Amma. Ita kuma ta gayamata Ciwon da Amma ta yi kwana Biyu tsakani sai gata tare da d'aya daga cikin ya'yanta Isuhu Jauro.


Ko alama Adda bata nuna ma Amma da mganar tafiya da ita tazo ba Jauro nan ya barta ya koma sai da ta kwana sannan ta zaunar da Amma da mu tare da Adda Fati da Adda Rukayya.
Domin Adda Fati na zuwa tace ta Kira mata Rukayya jin Adda ke kira yasa ta zo da sauri a tunanin ta ba lafiya.
Sai da taga kowa lafiya har Amma sannan ta kwantar da Hankalinta.
Maganar da Adda ke fad'i ne ta girgizamu ba Shawara ba ce wannan karon tace Umarni ne zata Dauki Amma su koma gida.
Adda Fati ta zaro ido kafin tace"Adda mu kuma fa? Mu kadai anan ba mu da kowa fa"
Adda tace"Ba ku kad'ai ba ne. Ku na da mazajen ku sannan nan ne Tushen ku ga kuma Dangin Uban ku duk suna garin nan, Aisha kuma aure ne daman ya kawota kuma wanda ya yi silan zuwanta ba shi Tuntuni ya dace na tafi da ita mu zauna tare saboda ku na kauda kai. Ammh yanzu komai ya zo karshe Da Aisha da Hasiya da Habiba duka zan iya rike su, na saka Tuni an gyara muku muhalli ci da sha bazai gagaremu ba in sha Allahu."
Ta fad'a kai tsaye ta na kallon mu.
Cikin mu sai aka rasa mai kara cewa wani abu tun bayan mganar Adda Fati.
Adda ta kalli Amma da ta dukar da kai kafin tace"Wannan karon ba karb'an uzuri. In Hasiya ki ke ji ki daina damuwa achan ma zata samu miji in sha Allahu."
Adda Rukayya tace"Ammh Adda rayuwar ce ba d'aya ba kina ganin akwai takurawa gareki kema ki na Fama da kanki.?
Da Sauri Adda Fati tace"Eh nima shi na ke Tunani."
Adda ta yi mirmishi kafin tace"Ni fa da Aisha muka taso tun bayan rasa iyayen mu. Kuna tunanin bazan iya rike ku ba ne? Kamar yadda na tara ku suma yarana haka na Tarasu kuma suka bani goyon bayan Tahowa da ku kuma in sha Allahu sun ce baza su gaza ba, Naga nan din da ta ke zaune ba wani mai kula da ita. Dangin babanku kuma sun yi butulci da Hankalina ke chan a tashe gwara na Dawo da ita a kusa da ni zai fi min kwanciyar Hankali. Ba shawartanku na ke yi ba Umarni ne.
Ke Hasiya ku fara shiri kin ji ko?
Cikin sanyin jiki nace"To Adda."
A baya na fi kowa Murna da komawar mu gadan mallam mamman.
Ammh abun mamaki yanzu sai naji kamar in na tafi zan bar wani abu mai Muhimmamci anan to menene shi wannan?
Wata zuciyar ta tunasar da ni shi.


"ASSADIQ."


shine na ke jin wani iri ya ya zai ji in ya dawo akace masa ga in da muka koma? Maimakon na yi murna sai naji na kasa yin farinciki ko kad'an.
Ammah kuma ba ta iya ma Adda Gaddama ba tace duk yadda tace haka za'ayi.
Su kan su su Adda jikinsu duk ya yi sanyi haka suka tafi.
Washegari mun tashi da had'a kaya duk da bamu gayama kowa ba sukola muka ta shi da shi Tun Safe ni da Habiba.
Sai da yammah sai ga Adda Fati da mijinta. na zata yazo gaida Adda ne sai bayan sun Fati Adda ta kalleni ta na fadin"Fati da mijinta sun roki a ba su Habiba ta zauna tare da su saboda karatun ta. to ganin yadda ta damu yasa na amince sai ke ki shirya tare da ke zamu tafi."
Gabana sai da ya fad'i na kasa ma mgana Habiba na jin haka ta fara tsallen Murna, daman karatunta ta ke ji in ta koma chan ammh jin haka sai ta fara murna.
Amma ba ta ce komai ba sai dai a kasan ranta ni ta ke Tausayi.
tun jiya da Adda ta yi mganar nan ta ke ta nema min mafita ammh bata samu ba.
Habiba ta samu nata mafita saura Hasiya. Ita da Rayuwarta ke cikin Tsaka mai wuya ta na bukatar Farinciki da jin dad'i.
Ta na bukatar wata rayuwar da ta fi wannan da ta ke ciki.




*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*






*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk


Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login