Showing 6001 words to 9000 words out of 93195 words
Chapter 3 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt
tunani ya tafi nesa da mganar ta ina tunanin yaushe ne Ranar jin Dad'in?
Sai naji mganar Amma daga sama tana Fad'in"Kada ki sake ki saka Tunanin da mutane suke yi a kan ki. Kada ki kuskura ki yarda da su karya suke yi. Abunda suke Alakanta ki da shi Jahilci ne ba Farar Kafa a addini mu Kambun baka kada'i Annabin Rahma ya sanar damu, ko maita babu shi a addininmu saboda haka kada ki damu da duk abunda ke faruwa, Allah ne ya Saukar ma Abubakar duka kaddarorinsa. Sannan shi ya kara Dauro ma Salisu na shi Jarabawan, Ba ke ba ce Hasiya ke baki isa ki zama silar kaddara ko Jarabawan bayin Allah ba. Ba ke ba ce baki da wannan Hurumin komai da ke faruwa da sanin Allah kuma ikon shi ne"
Ta karishe Fad'a tana faman jan Numfashi Lokaci daya Jikinta na kara makarkyata. Na rude hankalina ya kara tashi sai kawai na fashe da kuka ina Fadin"Amma jikin ki na rawa ga shi Zazzabi ya rufeki ki bari mu je asibiti"
ko da ba na ganinta nasan mirmishin nan nata na karfin Hali tayi min kafin ta saki hannayena ta koma ta kwanta tana fadin"Bafa wani abu Hasiya.. dubamin dai panadol na sha Zazzabin zai sauka"
Kafin ta gama mgana ma na bazama Bangon yammah na Dakin saboda Tsabar yadda nasan kowacce kusurwa na Dakin yasa ko cikin Duhu nasan inda muhallin komai ya ke. Wata jaka ce tawa a rataye nan nake saka Tarkacen magungunan Amma in ciwon ta ya tashi kafin mu tafi asibiti.
A cikin Duhun na Dauko mganin, ammh ganin ba na gani yasa na lalubo fitilar na kunna haske ya gauraye Dakin. Da ita na samu na Haska na Debo ma Amma ruwa cikin wani karamin kofi na kuma ballo mata panadol guda Biyu, na tada ita na kuma bata tasha sannan ta koma ta kwanta tana Fad'in"Nagode Hasiya. Allah ya miki albarka Allah ya warware miki kaddarorin da suka Zagaye rayuwarki"
a cikin zuciyata na amsa da Amin ganin ta koma ta kwanta ta na sauke Numfashi yasa na mike a kasalance na karisa wajen ma'ajiyar kayan sawanmu na dauko mata zani cikin zannuwan ta na rufa mata daga kafafunta zuwa kugunta.
Sannan ni kuma na koma gefenta na jingina da Bango ina faman kokuwa da Numfashi na. Ammh kuka ko Hawaye gabadaya sun kafe a idanuwana.
Kirjina na ke wani irin suya,ga harkarina duk ya rike nasan kuma Ulcer ce ammh ba ni da kuzarin mikewa domin na taimaki kaina Ahalin da nake ciki ba na bukatar komai ma duniya komai ya ficemin a raina.
Ina jin tashin Hayaniyar su a tsakar gida, ana ta uban maida zence da Hayaniya kafin Daya bayan daya su fara shigowa dakin Amma, ina jAdda Fati da Ramatu na tambaya ta ko jikin Amma ne ya tashi?
Da kai kawai na iya amsa musu na kasa mgana sai bin mutane da kallo, abun mamaki duk sun ki tafiya har da yan gidan su Babanmu. Su da basa kaunar su Rabemu Daurin auran ma Alhaji Tanko da ya kasance Shakikan Mahaifin mu guda daya daya ragemana, da Adda fati taje har gida ta Fad'a masa mganar Salisu lokacin da yace zai turo.
Ammh Bude bakin sa sai cewa ya yi"Ai kawai Fati ku samu Limamin anguwan ku ya amshi mganar har Daurin auran ma. Wahala ce sai an zo har nan d'in"
Ba nisa fa, ina Samaru ina Dirimi chan gidansa yake ammh a bayyane ya ke kowa baya son Rabarmu saboda ni Hasiya.
Ko su Gambo da suka k'i tafiya saboda jin kwakwaf ne da samun abunda za'a koma ana ba da Labarinsa.
Duk maida zencen da Ramatu da Adda Fati suke a kunnena ammh na kasa wani motsi, sai da naji Ramatu na waya bayan ta gama.
Na kura mata ido ina neman karin bayani sai dai kafin na kai ga muskutawa ta fara fad'in"Musbahu ne"
Gabana sai da ya fad'i na Runtse idanuwana ina jin kaina na wani Gif Gif jira kawai naji Ramatu tace Salisu ya rasu.
Ammh sai ajiyar zuciya ta kwacemin sanda naji Ramatu na Fad'in"Ya ce likito su ce karaya ce guda biyu ya samu, kafa da cinyarsa ta Dama sai kuma yan Rauninka. Ammh ya tabbatarmin da Sauki"
Bansan ajiyar zuciya ta kwacemin ba sai da naji ta fito sarari sannan da kuma kallon da kowa ya bi ni da shi. Sai na samu kaina da Sadda kai na kasa ina jin yar salama da Natsuwa kad'an suna shigata.
Bazan iya sanin iya tsawon Lokacin da na Dauka ban yi barci ba. Abu d'aya na sani shine sai da gabadaya kowa ya yi barci ya barni Har Amma ta samu barci, ta kuma kara farkawa Zazzabin ya sauka tace na bata ruwa ta sha na Dauko mata.
Bayan ta sha ta koma ta kwanta tana ce min"Hasiya ki kwanta ki yi barci kin ji ko"
Da kai na amsa mata,ba domin ina jin barcin ba, Hatta Ramatu da Innarta nan suka kwana Dakin bazai Daukemu ba ita da Adda Fati Dakin Maman Boy suka kwana Tunda ita Mijinta Direba ne baya nan.
Nasan ba ni da kokarin Ibada bar ni da Khamsil Salawati da nake yi a kullum, ammh bangaran Dagema Sallar Dare da Sauran Ibadu ina da wannan Raunin Shiyasa har barci ya Daukeni gabanin asuba ban iya tashi na Raya wannan daren ko don rokon Sauki daga wajen Allah a kan Halin Tsaka mai wuyar da ta ke ciki.
Tare da Fatan samun waraka ga Salisu ni ba ma Aurena na ke ji ba.
Lafiyar Salisu ta fi damuna fiye da aurena da ni da shi.
*****
Washegari ma abubuwan da suka faru duka ba masu dad'i ba ne.
Daga iren mutanen da suka rika shigowa da sunan Jaje ana maida zence tare da nuna ni, da kuma watsewar da taron biki da Salisu ya yi ba wani armashi.
Ramatu ta koma gida Daman a Tukur-Tukur take aure Inna Talatu kuma Sabongari take da zama da Gida d'aya muka zauna da su kafin Yayan Ramatu ya yi gidan kanshi su koma chan Gabad'aya.
Su Gambo kuwa sai yammah suka koma, bayan sun gama ganin duk abunda ya faru,suka yi ma Amma sallama suka kara gaba.
To gwara su sun zo din ko da na ganin ido ne, A gidan su Babanmu su shida ne yan Daki daya Hudu sun rasu ciki har da Babanmu Alhaji Tanko shi ne babba sai Mahaifimmu, sai karamarsu Halima ita tana Birnin Ikko tana auran wani Babba ne a aikin Costume.
Suna da tarin ya'ya da Jikoki kaf garin Zaria da kewayanta ba wanda bai san gidan Alhaji Mammadi kona ba.
Ammh an wayi gari ba bu mai son Huld'a da mu saboda rashi da babu, Tare da Tsoron kada su rab'emu na shafa musu tsiyata kamar yadda suka sha fad'i a kaina.
A kwana uku da Faruwar abun da na Fita sai da na raina kaina. Da kuka na dawo gida haka ake nuna ni dandalin matasa har da Dattawa. Chemist naje siyan mganin Ulcer saboda ta tasan min a kwanakin nan.
ganin kuma Jikin Amma ya yi sauki yasa na Dauki Dubu Daya cikin Jarin Danwake da nake yi ne naje siyan mgani.
Har achan Chemist din a gaban idona wani ya nuna ni yana fadin"Wannan ce mai Farar kafa da ake mgana?
A aureta a auri bala'i ance mijinta na Farko mai kudi ne ammh yanzu ko keke bai da shi, yadda ma naji Biyar ma na bashi sha'awa yanzu"
Wani na gefenshi ya karb'e da fadin"To shi wanda aka daura musu aure cikin Satin nan fa? shagonsa ya kone ko tsinke ba'a fita da shi ba.
Ga karaya har biyu ga rauninka naji ma ana labarin Kano za'a kaisa ayi masa Dauri wajen miliyan Biyu ake nema kaga shima karshenta Sanadin Jinya ya rasa komai na shi"
Ina kallon cikin idanuwan matashin ya kalleni ya tsintar da yawu yana Fadin"Tab.. irin su ai bala'i ne ga al'umma. Allah ya yi mana Tsari da Dangin tsiya"
Mganin da ban karba ba kenan na Dawo gida da kuka.
Ina zuwa kuma na kara cin karo da wani abun takaicin Adda Rukayya na samu tazo ina shigowa Dakin Daidai tana ce ma Amma" Ni fa ba wanda ya kirani ballatana ya fad'amin abunda ke faruwa. Sai da Babansu Amna ya dawo ya ke fad'amin a gari yaji ana ta Fadin Labarin da yazo yana tambayanta nace ban sani ba. Amma tsakani ga Allah mganar mutane akan Hasiya ba Canfi ba ne gaskiya ki fa Duba Abunda ya faru da Abubakar ga wannan ma, to ko karayar arzikin Baba da Jinyarsa duk itace sila kema ga naki ciwon matsaloli sun ki su kare mana. Ni fa Matsalanta har neman Shafan zaman aurena ya ke so ya yi Tunda Har Baban su Amna ya ce shi ya fara jin tsoro, Mamanshi har mgana ta tab'amin nace mata kashin Tsiyar Hasiya kad'ai ke da ita ban damu ahto kada dalilinta aurena ya Mutu na shiga Uku"
Ta fad'a kai tsaye babu kuma alamun Tausasawa a muryanta.
Kamewa nayi a kofar dakin Amma na kasa karisawa ciki Amma na zaune kawai tana kallonta, dukkansu ba su san ina Kofar dakin ina Sauraransu ba.
Adda Rukayya ta gyara zama tana Fadin"Shine na kawo shawara Amma.
Me zai hana tunda dai nasan shima auran nan sunan shi Sakakke. Saboda ba iyayen da zasu bari D'ansu ya zauna da Hasiya mganar gaskiya kenan. Ki tarkata ki kaita Dangin ki chan gada wajen Adda ta zauna tunda chan ba wanda yasan abunda ke faruwa yafi nan da labari ya gama Zaga gari. A chan sai tafi samun kwanciyar Hankali ta samu mijinta tayi aure zai fi ye mata kwanciyar Hankali daga ita har mu Amma"
Amma kallonta kawai take yi idanuwanta har sun kawo ruwa.
Takaici da bakinciki sun saka ta kasa mgana.
Ni kuma sai naji kamar takaicin nawa ma ya Dauke gabadaya, hawayen da duka rage a cikin idanuwana na Share sannan na kariso cikin Dakin ina Danne yanayina.
Naso na shareta ne ammh kuma Son nuna mata naji mganganunta yasa na kalleta ina Fadin"Sannu Adda Rukayya?
Sai yau aka zo mana?
Sai ta kasa mgana Daga ita har Amma ni suka kurama ido suna nazarina yanayina sai kawai nayi mirmishin karfin Hali kafin nace'"Amma shawaran Adda Rukayya ta yi. Gwara na koma wajen Adda na zauna tabbas zai min kwanciyar Hankali da ku kanku Gabadaya. Ga Habiba nasan zata kula Dake Amma."
Na fada ina kwaso jarumta zuwa saman Fuskata.
Jin kalamai na yasa Adda Rukayya ta samu kwarin gwiwa gyara zama tana Fadin"Ahto nima haka nagani. Amma kada ki dauki mganar nan da wata Manufa mafita na samo ma Hasiya da mu kanmu"
Sai Amma ta kauda kai kafin tace"In kinga Hasiya ta bar garin nan to ki tabbatar ma kanki Rukayya kafata kafar Hasiya. sannan kafar Habiba.
Nasan Fati zata rika zuwa Dubamu sannan Adda bazata gujeni ba, sannan bazata kyamaci Hasiya ba, har Abada ita din mafaka ce gareni da Ahalina"
Mgana ce ta fad'a ba masu yawa ba ammh masu harshen damo ga mai Hankali.
Adda Rukayya dai sai jikinta ya yi sanyi kafin ta tabe baki tace"Amma ni fa ba bakuwar zafi ba ce. Ki yi hakuri in mgana ta ta b'ata miki rai"
Daga haka ta kakkabe jakarta ta fice daman abunda ya kawota kenan. Duk yadda Amma taso ta fahimci yanayina ban bata Damar haka ba Dakin na kakkabe na share Habiba na makaranta.
Bayan na gama na kwashi wankin Amma na fita da shi na Daureye mata, Ruwa ma almajirai na saka suka Dibomin ruwan tunda Bohol din na kofar gidan mu, Fita na kuma ba zai yuyu ba. saboda ko'ina yi da ni ake yi na zama abar kwantace da nunawa.
Kwana biyar tsakani Adda Fati da Ramatu suka dawo a bakinsu nake jin Salisu da gaske kano za'a kai shi Asibitin Dala ayi mishi Daurin asibiti.
Hankalina duk ya tashi Daman a kwanakinan yana raina kamar naje asibitin na dubashi ammh ina tsoro tare da Fargaban me zuwa na zai iya Haifarwa.
Ammh ban duba abunda zai iya zuwa ya dawo ba nayi ma Ramatu mganar zuwa asibiti na Duba Salisu. Itama ta jima bata ce min komai ba tana nazarin abunda zai faru, ammh bata min gaddama ba ta shawarci Adda Fati itama sai da ta jinjina kafin ta kalli Amma tana fadin"Amma kin ga ya dace Hasiya taje ta duba Salisu?
Amma tace"Sosai ya dace ai mijinta ne. kuma rashin zuwan ma wata mganar ne in zai samu ki shirya har da ke aje a duba shi"
Da wannan shawaran ta Amma yasa har Inna talatu da taji tace zataje itama muka Shirya Tafiyar.
bansan yadda mganar ta fita har matan gidanmu suka ji ba, sai suma suka Daka Tsallen zasu je,nasan dai bai wuce ganin abunda zai faru achan ammh ban magantu ba.
Ramatu ta yo lafiyayyen Ferfesun kifinta daga gida muka tafi da shi. Mota guda muka samu Bus,Tunda matan gidanmu su tara duk da zasu je, Son ganin Salisu da Halin da ya ke ciki ya Boye tsoron dake cikin Raina.
Na shirya cikin Atamfata wata ja riga da Sikat duk cikin kayan aurena da Abubakar ne tunda lokacin akwati shidda ya yi min Shake da kayan alfrma. Sai na saka Jan Hijabi har gwiwana, fuskata fayau daman gata karama sai Zullumi ya kara kankantar da ita.
Bayan La'asar muka tafi, tunda Lokacin Musbahu da Ramatu ta kira yace ana bari shiga. Mun shiga asibitin Chika Hud'u da minti Arba'in muna tafe tiri tiri har Emergency bayan mun yi tambayan shashen yan Hatsari aka nuna mana.
Duk jikina sai ya kara mutuwa sai ya kasance na koma baya ina bin tafiyar Ramatu tamkar nima tsohon cikin gareni.
Bansan wanda ya hangemu cikin yan gidan su Salisu ba ya je ya gayama sauran yan'uwan nasu dake chan wani gefe suna zaune.
Mu dai muna tsaye ne Ramatu na kokarin kiran Musabahu muka ji muryan wani kanin Salisu yana fadin"Wa kuke nema?
Gabana sai da ya amsa ganin su Ritutu, wasu ma ban san su ba. Nasan dai Salisu ba shi da mahaifiya ta rasu ammh suna da yawa a dakinsu. sannan mamanshi na da abokiyar zamanta itama da nata gayyar.
Inna Talatu ne ta sanar da shi munzo Duba Salisu ne, sai naga sun fara kallon kallo kafin su yi mgana sai ga Musbahu yana fadin"Hasiya ne da yan'uwanta daman sun min waya zasu zo duba Salisu da jiki"
Sunana kad'ai da aka ambata ya Rushe sauran Annurin su. Kafin ma mu yi wani motsi wata cikin matan nan mai Kiba ta bake kofar Emergency tana Fadin"A'a kuje kawai mun gode. Ammh bazaku shiga da gayyar tsiyarku ku karisa mana Dan'uwa ba"
Inna talatu da Adda Fati suka kalli juna kafin Inna talatu ta Tausasa murya tana Fadin"Asshaa baiwar Allah meya kawo wannan mganar? Daga Dubiya sai kuma zencen mu karisa shi? Ai bamu muka sakashi cikin wannan Halin ba ballatana kice zamu karisa shi"
Ta fad'a tana mai kwantar da kanta. Ba wacce ta tare kofar ba ce tayi mgana wata mai karamin jiki ne sai dai kallo farko zakayi mata kasan jinin Salisu ne domin suna kama sosai tace"ku ne silar shigar sa wannan Halin mana. Tunda silar auran yarku ce mai kashin Tsiya da bala'i. Ta nakasa mana Dan'uwa ga kuma asaran dukokiyon al'umma duk ta sanadin auranta me zamu ce da wannan auran?
Ta bakin kofar Emergency tace"Sai Allah ya tsine ma auran kawai zamu ce Ikilima"
Sai gabad'aya matan gidanmu suka saka salati na jimami har da masu gulma Ramatu taji jikinta ya yi sanyi ni take kallo ammh sai na samu kaina da jin kunyarta kaina na kasa ina kallon kasan asibitin cikin bushewar ido da na zuciya.
Adda Fati da Inna talatu tare da Musbahu ba yadda ba su yi su barmu mu shiga ba ammh Su ka ki, bayan kuma suna ta bin mu da mugayen mganganu, Har hankulan mutane ya fara dawowa kanmu.
Kallon Ramatu kawai nayi ina Fadin"Ramatu ku taho mu tafi kawai. Allah ya bashi lafiya"
Kasa min mgana ta yi, ta tsaya tana ce min"Hasiya wannan abun da nayo fa?
Sai da na kalli kwandon hannunta sannan nace"Ki ba wa Musbahu in kuma zai zama matsala mu koma da shi"
Ba ta yi musu ba taja Musbahu gefe ta mikamasa kwamdon hannunta bayan sun yi mgana, yana ta bata hakuri tace bakomai, su Adda fati tayi ma mgana yasa muka fito daga wajen da niyar Tafiya. Matan gidanmu suna baya suna ta Gulma daman abunda ya kawosu kenan.
A haraban asibitin muka had'u da Sahura da yan gidansu kallo kallo akayi tsakanimmu an rasa mai mgana, ganin tare take da wata yar Dattajuwan Mata Ramatu ke shaidamin Innar Salisu ce. Ina kallonta suka gaisa da Inna talatu da su Adda Fati cikin sakewa daga yanayinta yasa na Fahimci zatayi saukin kai ba kamar sauran ba.
Cikin Fara'arta tace"kun samu ganin Salisun?
Inna talatu tace"A'a ba'a barmu mun ganshi ba"
Cikin mamaki tace"ah kuma la'asar ai ta gota. Lafiya kuwa.?
Adda Fati Zatayi mgana Inna Talatu ta rike mata hannu tana fadin"Gudun Fitine kawai.
Ayi masa sannu Allah ya bashi lafiya"
Ni dai sai na samu kaina da Jawo hijabina ta sama ina Rufe fuskata.
Nima yanzu kunyar nuna Fuskata nake yi ga Mutane da gaske ni din Annaba ce ko kuma nace gobara Daga kogi mganinta sai Allah.
Inaga ta Fahimci mganar Inna Talatu yasa tayi ajiyan zuciya kafin tace"Rayuwar ne sai hakuri. Abubuwwn duk sun rikice ni na rasa ina zan kama. Ku yi hakuri don Allah gobe ma za'a wuce da Salisu kano ayi masa Daurin asibiti. Ku yi hakuri da duk abunda zai biyo baya don Allah"
Inna talatu tace"Bakomai Allah yasa ayi a sa'a"
Ta amsa da Ameen sannan muka wuce itama ta wuce, Tunda Sahura da gayyarta sun yi gaba suna harare harare da yada mganganu.
Har muka isa gida ban tofa komai ba duk da ana ta maida zence a cikin motar. Amma ma Adda fati ta zayyanemata komai ta sauke numfashi kafin tace"Allah ya kyauta"
Kowa jiki ba Dadi' haka Ramatu ta tafi tana kara bani baki nace mata bakomai Inna Talatu ne sai dare ta tafi gida Adda Fati kuma mijinta yazo Daukanta bayan ya shigo ya gaida Amma.
Har ya bata dubu daya.
Washegari wajen misalin karfe sha daya na Safe sai ga Musbahu abokin Salisu ya yi sallama da ni a