Showing 54001 words to 57000 words out of 93195 words

Chapter 19 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11466

ke yi yana Fadin"Inna yanzu haka Mutane suka zama Jahilai.?
Miye haka don girman Allah."
Inna Talatu ta girgiza kai ta ma kasa mgana kafata ba ko takalmi ana ta kai wa ke ta kaya.
Dagani sai Ramatu muka shiga cikin Adaidata muka tafi Inna Talatu tace yanzu suma zasu tafi chan gida. Abunda ba su sani ba Tuni su Maman salihu sun zame jiki sun koma gida sun kai Amma Labarin duk abunda ya Faru.
Suma muna wucewa ba su koma gidan ba suka wuce sun ma mamta da wasu mutanen gidanmu tashin Hankalin da suke ciki ya ishe su. Suna Hanya Inna Talatu na Tunanin me zasu Fad'a Amma in ta tambaye su ni?
Adda Fati tace"Mu ce kawai ta na gidan Ramatu zata kwana biyu"
Inna Talatu ta girgiza kai kawai tana Uhm.! Kai jama'a.
Ni ko muna tafiya ina ta kuka , kuka da Karfi kamar zan Tsaga Adaidaitan Nura na gaba sai juyowa ya ke yi yana Fadin"ki lallasheta ke kuma mana.."
Ramatu na matsan kwallah tace"Ba ni da sauran kalamai Nura a gaban idona aka Tozarta Hasiya kan kaddaran da ba ita ke da iko a kan shi ba."
Nura yace"Ni kaina abun ya Tab'ani wlh wai ya abun ya faru ne.?
Cikin Damuwa ta fara ba shi labari.
Ya saka Salati yana fad'in"Kamar wasu Jahilai."
Mai adaidaitan da muke ciki yace"ai yanzu mutane sai Allah ba su da yarda da Allah komai ya faru da Mutum sai kaji ana Fadin jifa ne. Wannan Dabi'ar ta canfe canfe wlh ana Fama da ita yanzu nima akwai wata yar'uwata da tayi aure mijinta ya Talauce ya yi ta shiga bala'i itama a karshe an ce Farar kafa gareta ya sakota wajen shekara tara kenan duk wanda yazo neman auranta da ya samu wannan Labarin baya Tsayawaa. Sun kasa gane mutum bai isa ya san gaibu ba. Allah ke da arziki da Talauci."
Nura yace"Rashin yarda da Kaddara ne. Shi kuma rashin yarda da Kaddara Daidai ya ke da rashin yarda da Ubangiji. Mutum bai isa ya yi ma Mutum abunda Allah bai yi masa ba."
Mai adaidaita yace"Sosai ka ga anan wajen Tauhidi ya raunana. Sannan kuma a musulunci babu maita babu kuma Canfi ammh Mutanen wannam zamanin basa ganewa komai ya Faru da Mutum sai kiji ance ba Daga Allah ba ne akwai sanadi."
Nura ya gyad'a kai kafin yace"Abunda ke Faruwa kenan. Kuma malamai na iya bakin kokarin su mutane basa ji kwata kwata."
Mai adaidaita yace"Yanzu ai ko mutuwa ba ta zame ma Mutane wa'azi ba. kaga kuwa tunda Mutuwa ba ta zame mana wa'azi ba wlh tallahi ba bu abunda zai zama aya kuma agaremu."
Ina jin su suna ta mganganunsu su da suka gane haka kenan su ke kuma Fad'in haka. Muryata bud'e na ke kuka kukan bakincikin yadda aka yi min Tsirara gaban Mutane.
Ganin zamu tsaya gidan Ramatu yasa cikin kuka nace"Ku kaini gida. Don Allah ku kaini gida."
Ramatu tace"Amma Hasiya"
Cikin kuka nace"gida zan je Ramatu..na ce miki gida zan tafi."
Na fad'a cikin karaji da kuka Nura ne yace mu tafi gidan gabadaya.
Ni dai tunda na ganmu a kofar gidanmu ban tsaya jiran Ramatu ba na Diro daga adaidaita. Ko ganin gabana ba na yi kafata ta yi tsami ina dingishi. Fuskata ta sumtuma ga jini duk ya bata gaban hijabin da na saka ba Takalmi haka na Fad'a cikin gidan cikin kuka da Muryan karaji na ke kwalama Amma kira.
Wacce daman tun sanda su Maman Salihi suka zo da Labarin Amma ta kasa zama adaki tana Tsakar gida tana Safa da marwa labari kuma ya shiga kunnen matan gidanmu suna Tsaye cirko cirko.
Ina shigowa na zube gaban Amma ina wani irin kuka.
Amma jikinta ya fara rawa ta durkushe itama a gabana ta na Fad'in"Hasbunallahi wani'imal wakeel Hasiya yanzu abunda suka yi miki kenan.?
Itama sai kuka, daidai lokacin da Ramatu da Nura suka shigo.
Ni ko fad'i na ke yi"Amma menene laifina? Wani abu na aikata da na chanchanci shiga cikin wannan matsanancin tsaka mai wuyan?
Amma na tsiyayan Hawaye tace"Ba ki da wani laifi Hasiya. Ba ki da laifi har a wajen Ubangiji."
Cikin kuka na ce"Amma da gaske to ni Mayya ce?
Da Sauri Amma tace"Wlh ke ba mayya bace, kaf zuru'armu ba mu da maita haka zuru'ar mahaifin ku. Ba ki gada ba sannan baki siya ba Hasiya."
Ina rike hannun Amma nace"To miyesa haka ke faruwa da ni? Farko Abubakar daga baya Salisu Amma.?
Me yasa.? Me ke faruwa da Rayuwata ne..?
Na karishe fad'a ina jin Numfashina na cijewa ya na sama da kasa kamar zai yanke. Cikin kuka Amma ta rikeni ta na fad'in"Bansani ba Hasiya. Abu daya na sani ke mutum ce kamar kowa. Baki da bakin fenti a tare da ke, Komai da ke faruwa Hukuncin Allah ne da mutum bai isa ya ja da shi ba."
Amma na mgana ina jin amai na tasomin na fara tari ina rike kirjina Lokaci d'aya ina fadin"Amma kirjina, Mutwa zan yi ko?
Dama na Mutu na Huta."
Sai amai na fara kelaya shi a jikin Amma ina wani irin rawan jiki kamar zan mutu.


Na fita daga hayyacina da bansan su waye ke kaina ba naji dai hayaniya. Ramatu ta wankemin jiki bayan na gama Aman suka kai ni daki.
Daga lokacin kwance kawai na ke ina Numfarfashi kamar wacce numfashinta zai bar gangar jikinta.
Har dawowan Su Adda Fati ban sani ba.
jikina ya yi zafi ashe sai da Nura ya kira wani abokinsa mai Chemist yazo ya yi min alluran ulcer sannan ya sakamin Drip na samu barci.
Duk nan suka kwana Ramatu ce kad'ai ta tafi gida sai wayan gari na yi na ganni kwance an gama min karin ruwa.
Tun kuma wayewan garin na ke kuka lallashi da ban baki ba wanda Adda Fati da inna talatu ba su yi min ba sun yi har sun gaji sun kyaleni.
Amma ko bata mgana, ita kanta in da zata kwanta sai ta fi Hasiya jin jiki saboda yanayin da ta ke ji ajikinta.
Zuciyarta na zafi da rad'ad'i in ta tuna yadda Rayuwata ke cikin TSAKA MAI WUYA.!






*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*






*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*




https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj


Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari.


Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah.


Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus


*13*


Duk lallashin da suke yi min Ina jin su ammh kuma ba na daukan duka magangansu, domin nasan irin kalaman na su na kuma jima ina jin irin su, ammh har yau har gobe babu al'amarin da ya sauya.
Gayamin suke na daina damuwa komai da ya faru daga Allah ne.
Ni ban isa na tsara kaddaran mutane a Hannuna ba, to a irin yanayin da na ke ciki na gaji da jin irin kalamansu Tunda ba za su taba sama mun mafita ba.
Duk maganganun da suke yi ban bude baki na nace Tak ba. Kuka kawai na ke yi na had'a kai da gwiwa ina rafzan kuka. Ko ruwa ban bari ya shiga bakina ba duk ko da magiyan da suke yi min da na ci wani abu ko zan samu karfin jikina.
Haba rayuwar nan duk ta isheni in har mganar mutane ba gaskiya ba ne meyasa abubuwa suke faruwa da ni daki daki haka?
Farko Babanmu na biyu an ce ciwon Amma ni ce Sanadinsa halin da muke ciki duka Laifin na kaina, Sabo da ni Dangin mahaifin mu suka Gujemu kowama ya gujemu Abubakar ya aureni ya sakeni Salisu ma haka. Duk kuma ace haka kurum abubuwa ke faruwa dani kamar ni kad'ai ce Y'a a wannan Duniyan?
Tabbas akwai kamshin gaskiya. na fara Tunanin tunda na zama Annoba ga al'umma to banga amfanin Rayuwata ba ko na Mutu, ko kuma na yi nesa da Rayuwar da ni ke ciki. Ina ji Adda Rukayya ta kira Adda Fati sun yi mgana sannan an ba ma Amma ta na ta bata Hakuri.
Adda Fati ta dafani ta na Fad'in"Rukayya na gaishe ki. Tace a yi miki sannu gobe kila ta shigo ita da Habiba."
Ban so na yi mgana ba Saboda ba na jin yin mgana da kowa ammh a wannan gabar ina bukatar wani karin bayani, idanuwana jajir na dago ina kallon Adda Fati fuskata duk ta kumbura saboda kuka da duka cikin Dashewar murya nace"Adda Fati ban gane wani abu ba? Me yasa Adda Rukayya ta damu saboda dangin Mijinta sun Tozartani."
Adda Fati tace"Kada ki manta Rukayya jininki ne Hasiya. Duk in da aka kai aka kawo ba ta da kamarki kamar yadda ke ma baki da kamarta."
Na yi mirmishi ina jin yadda bakina ya Bushe da makogwaro na. Ban ce komai ba na maida kaina cikin gwiwoyina na suke.


Inna Talatu ne tace"Ita Halin Rukayya Wauta ne da rashiin wayau. Ammh ba ka budema miji sirrin yan'uwanka ka rika bata su a idon sa saboda gudun watarana ga shi yanzu sun yi abu kuma ya zo ya na Damunta."
Sai alokacin Amma ta saka baki jikin Raunin zuciya da na jiki tace"Kuma shi wannan dan'uwa da ka ke Tunanin wani ya fisa. To duk duniya shi ne naka akwai kuma bangaren da Dole naka ne zai iya kare maka shi. Baren bazai iya ba. Ina Fatan wannan abun ya yi sanadin dawo da Rukayya cikin Hayyacinta."
Adda Fati ta amsa da Ameen kafin tace"Kuma fa Amma ita zata iya yima Hasiya. ammh in wani ya ci zarafinta sai abun ya fi yi mata zafi kamar yadda ya faru. Wani kuma Tozarcin da suka yi har da zugan Kanwar Abubakar din nan tare da maganganun dangin mu muma."
Adda Fati ta sauke ajiyar rai kafin ta cigaba da fad'in"Tunda da bakinsu suke fad'in ga abunda suke fad'i a kan Hasiya. Har suna fad'in suma Dalilin haka suka gujemu, Kuma da gaske ne sun gujemu ba mai neman mu ko sha'aninsu wani Lokacin bama sani suna yin shi. Yanzu Baaba ta lagos sai ta zo garin nan sau biyar dakyar zata zo gidan sau d'aya to wai har gwara ita akan su Baba Tanko shi Baba Jibril karshe da shi da iyalansa ma ba su san inda muke Rayuwa ba. Sai Baba Saminu shi kuma daman tsegumi ke kawosa ya zo ya fad'i mganganu ya kara gaba gabadyansu ba mai Mu'amala mai kyau damu."
Amma ta jinjina kai kwarmin idanuwanta sun cika da ruwa cikin wani yanayi tace"Uhm. Ni kaina sun ba ni mamaki kuma lokacin da Alhaji ke Raye wlh ya yi musu komai ya samu na yan'uwan shi ne da iyalansa, ammh yanzu in da zai dawo Duniya yaga Halin da suka barmu a ciki na Tabbata zai yi bakinciki mai yawa."
Inna Talatu tace"Ai Allah ne ya kawo mu zamanin Zumuncin zamani. Daga kai sai kauri, in kana da shi ayi da kai in baka da shi kuma kai da banza duk Daya."
Amma na sharan hawaye da Gefen zaninta Lokaci daya ta na fad'in"Akwai Allah. Watarana sai Labari komai zai zo ya wuce Rayuwa zata fita daga cikin Tsaka mai wuya, komai kuma zai yi daidai in sha Allahu."


Duk ina jinsu ammh ban tankan su ba na riga na samar ma kaina mafita da ni ke ganin shine daidai da Rayuwata da rayuwar kowa sai dai na zabi na yi shuru da bakina ba na son ma wani ya Lallasheni ballatana ya bani baki. Adda Fati ita tayi aikace aikace ta yi abinci ni kam ko a bakina sun yi sun yi nace na ce na koshi ina nan kwance ina kukan zucci da na Sarari jiya an yi min Tozarcin da bazan taba mantawa da shi ba Tsirara a kayi min ana dukana da Zargin maita da kananun Shekaruna na ashirin da Biyar Shekaruna na Duniya, na Dand'ani Dacin Sakin aure har sau biyu bayan Tarin Tozarcin da ke bibiye da Rayuwata.
Adda Fati da Inna Talatu sai da Yammah suka tafi, Adda ta yi ta ba ni Hakuri kan ta tafi, inna Talatu kuma roko na ta ke yi kan naci abinci toh kawai na ce musu ba domin na amince da duka mganganunsu ba.
Zama a iren gidajen haya irin Gidan mu mtsala ne duk abunda ya faru in dai sun sani sai mutanen gari sun gama ji ballatana ni da Labarina ya yi Tambari a gari.
Magana har ta yad'u a gari makotana nata shigowa yi ma Amma jaje da ganin Halin da na ke ciki, abun sai ya kara tabani batare da Tunanin komai ba su Adda na tafiya na mike ina ganin jiri ammh ban damu ba na fara Had'a kayana cikin akwatina babba tun ta auran Abubakar ne, Tunda ya barmin komai da akwatin da duka kayan gidan Gabadaya.
Amma na kallo na ta kasa mgana sai da taga shirin nawa ya fi karfin hankali sannan tace"Hasiya lafiya.? Me yasa kike had'a kaya.?
Kai Tsaye nace"Amma wajen Adda zan koma bazan iya juran zama na anan ba."
Da Sauri Amma tace"Hasiya ba na kashe wannan mganar ba? Ba inda zaki koma nan zaki zauna tare da ni."
Kai Tsaye nace"ni kuma ba zan zauna ba Amma ko ki barni na koma wajen Adda ko kuma na shiga Duniya."


"Hasiya..!"


Tsawa Amma ta dakamin da yasa na Fashe da kuka ina Fad'in"To miye amfanin Rayuwata tun bazan sama ma kaina sukuni da mutanen da ke Zagaye da Duniyata ba? Amma ki Fad'amin meye amfaninna? Ai gwara na Mutu ko kuma na yi nesa da ku gabadaya hankalin ku ya kwanta nima nawa ya kwanta.."
Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Juyowa na yi ina kallon Amma Lokaci D'aya ina nuna saitin zuciyata na cigaba da fad'in"Anan daidai wajen na ke jin kuna Amma. Jiya fa Tsirara a ka yi min ana kira na da sunan Maita. Amma ki fad'amin akwai Tozarcin da yafi wannan ne? Ki fad'amin ta yadda zan iya yaki da Tsaka mai wuyar da ni ke ciki? In ban yi tunanin kashe kaina ba, ban yi kuma yi tunanin shiga Duniya ba. To Amma ki bar ni na koma wajen Adda zan fi samun kwanciyar Hankali."
Kuka na ke yi har sai da na Durkushe Amma ta kasa tasowa itama jiri ta ke gani in ta mike cikin karfin Hali tace"Hasiya na ce miki ba zaki koma ko'ina ba ko? Tare zamu zauna Mutuwa ce ko aure kad'ai zasu Rabamu."
Cikin Ihu nace"Ni kuma in na cigaba da zama anan mutuwa zan yi Amma don girman Allah ki bar ni na tafi."
Amma na kuka ina kuka kafin tace"Sai dai ko mu tafi Gabadaya ammh bazan barki cikin wannan rayuwar ta tsaka mai wuya ke kad'ai ba."
Jin haka yasa na kasa mgana na koma na dora kaina kan akwatin da na cika da kaya ina ta kuka Halin da nike ciki yasa ko Danwake ban tuna da shi ba. ina ji da Safe ana ta zuwa Nema su maman Boy suna fad'in babu mai Danwaken ba ta da lafiya.
Bayan mangriba sai ga Ramatu da Nura sun zo Dubani ita tazo min da Su maltina da Madara sai kayan Marmari da magungunan jiya da Aka Rubuta suka siyomin.
Zuwan Ramatu yasa Amma tace duk yau ban ci wani abu ba Ramatu ta fara lallashina da Fad'in"Haba Hasiya kin san kina da lalura me yasa zaki zauna da yunwa.?
Hannunta na Dauka zuwa Saitin zuciyata ina fad'in"Daidai nan ne ke min ciwo Ramatu. Wlh na zabi mutuwata da wannan Rayuwar."
Da Sauri ta Rufemin baki ta na Fad'in"Ki daina fad'in haka Hasiya. Allah na sane da ke kuma shi ya zaba miki wannan Rayuwar. Fad'in haka kuma Daidai ya ke da nuna masa baki yarda da kaddaransa ba."
Kuka ya kwace min na kwanta akan Cinyarta na fashe da kuka ina Fadin"Kaddaran ne tamin nauyin Dauka Ramatu ya zan yi? Ki fad'amin ya zan yi? Wlh ina so na mutu mutuwa zan yi."
Na ke fad'a ina wani irin Gunjin kuka Ramatu ma sai kukan Nura ne ya ke ta lallashin mu ya karishe da kallon Ramatu ya na fad'in"Ke kuma miye haka? In kina kuka wazai lallashe ta.?
Jin haka yasa ta daina kuka,ni kuma kukan da Amma ke yi yasa na tsaigata nawa Ramatu ta had'amin maltina da Madara na sha ta kuma saka sai da na sha Kayan marmari,sannan ta bani magunguna na sha.
Amma ta kalli Ramatu ta na fadin"Ramatu ki kara lallasamin kawarki. Ta kafe Wajen Adda ta ke son komawa"
Ramatu ta kalleni ina Runtse ido kafin tace"Hasiya Amma ba ta son tafiyarki. Kuma in kika duba duk in da kike je ba zaki samu sukuni ba in dai ba kina tare da Amma ba ne. Don Allah ki yi hakuri watarana sai Labari."
Kai kawai na gyada mata bawai don na aminta da mganarta ba.
Ai nasan Hanya Amma sai dai ta tashi taga na tafi bazan zauna ina Kara Rusa mata Rayuwa ba. Ga ciwo ga kuma jikin girma.
Haka Ramatu da Nura suka tafi akan gobe zasu dawo. Bayan sun tafi Amma ta zauna ta na ta min nasiha ina sharan kwallah itama ta na sharan kwallah acikin raina ina Tunanin ita Rayuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login