Showing 33001 words to 36000 words out of 93195 words
Chapter 12 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt
kara yi ma Hajja bayani. Ta washe baki kamar ta gane tana fadin"Yauwa na gane yanzu. Saddiqu ya wajen iyayen naka da sauran yan'uwanka? Ina kakarka?
Sadiq yace"Duk suna gaishe ku Hajja."
Daga nan suka bude hira tsakaninsu, Hajja da karfinta ba kamar Innani ba, Domin a shekarunta kasa da na Innani ne, ba ta wuce 70 haka shiyasa da karfi a jikinta sannan jiki ya saba da Wahala tuntuni ba kamar Inanni ba, duk dai itama ta yi zaman kauye ammh bata cikin Wahala.
Ruwa kawai su ka sha sai Furar da ta Dama musu saboda jumma'a ne yasa suka yi alwala zuwa masallacin jumma'a suka yi sallah. Sai wajen uku suka dawo gidan chan suka had'e da yayyen Tahir suka gaggaisa suka kuma Dungumo zuwa Dakin Hajja a tare da aka gama cika shi da abinci kala kala na tarbansu.
Sadiq ya saba zuwa gidan su Tahir tun suna makaranta ya saba da duka Ahalin Tahir kamar yadda shima ya saba da na shi Dangi. Kowa a gidan su Tahir yasan waye Sadiq kamar yadda Sunan Tahir ya yi tambari a gidan su Sadiq, tare suka had'u suka ci abinci Shi dai Sadiq Dambun Zogale ya ci Tahir kuma ya ci Taliya da Miya da Nama,Sadiq Naman kadai yaci saboda Nama na daga cikin abunda ya fi so duk Duniya.
Sallar La'asar ya tada su suka tafi masallaci bayan sun fito kuma ba su dawo gidan ba, sun had'e da abokan Tahir tun na kuruciya suka zauna akofar gidan su Tahir suna ta Hira sai da aka kira sallar mangariba sannan suka tafi masallaci ba dai su suka dawo gidan ba sai bayan Sallar Isha'i.
Suna shigowa suka iske kanwar Tahir mai bi masa Zulaihat tazo har da Girki ta yo musu.
Tana ganinsu ta washe baki tana Fadin"Yaya Dahiru sai yanzu? Tun dazu nazo Hajja tace kun je masallaci'
Tahir ya ware mata ido kafin yace"Ke.. ina wasa da ke ne? Ba na gayamiki ki daina kirana wani Dahiru ba Sunana Tahir"
Hajja na saman Darduma ta na lazimi tace"Kaji tsirfan banza, da Dahiru ubanka ya yanka maka Rago. Shi muka sani kuma Shi zamu cigaba da kiran ka"
Sadiq ya yi mirmishi yana Rufe baki ganin Tahir ya yi wani Fuska yana Huci Jikin Zulaihat ya yi sanyi sai ta Juya tana kallon Sadiq kafin tace"Yaya Sadiq sannun ku da zuwa"
Ya amsa mata cikin sakewa yana Tambayanta ya gida da yaran.
Tahir da kansa ya gaji ya saki Fuska, ballatana da ya Zulaihat tace alele ta yi ta kawo musu sai ya warware suna ta fira ballatana da yayyensa suka shigo suma aka had'e ana ta Hira ko da ba ma su kudi ba ne ammh akwai kaunar junansu da kyakyawan zumunci a Tsakaninsu.
Sannan da shakuwa da kaumar junansu musamman Tahir da suke ganin shine karamin su Tunda Zulaihat ta yi aure ta gina na ta iyalan.
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
Sai karfe sha daya suka watse su ma sallama suka yi ma Hajjo suka dauki kayansu zuwa Dakin Tahir na cikin Shashen Hajja daman nan suke sauka Daki ne irin na yan kauye dai. Tsaf an gyarashi Inda Sadiq ke da Tabbacin Hajja ta gyarashi ammh Tahir ai son jikinsa da kazanta bazai barshi ya tafi ya barki Dakin a gyare ba.
Sakamakon sun gaji kuma ba su samu Hutu ba yasa ba su bata Lokaci ba suka bi lafiyan Katifar Tahir wata yar yaloliya da ita. Ba su farka ba sai asuba Da asuban ma Sadiq ne ya tashi Tahir kamar yadda suka saba ko achan baya.
Bayan sun dawo sallar asuba suka koma barci ba su tashi ba sai goman Safe shima Hajja ce tazo dubasu tana Fadin barcin su ba na lafiya ba ne su tashi hakanan, ita ta saka musu ruwan zafi dukkansu suka yi wanka suka sauya kaya sannan suka shiga Dakinta suka karya. Sun iske kayan karyawan su kala kala daga Dakunan matan yayyen Tahir har Zulaihat ta yo musu kunin gyada da Fanke shi Sadiq ya ci Tahir kuma Tea ya sha da Buredi.
Sannan suka kwanta Dakin Hajja suna ta Hira. Tahir kan gadon karfen Hajja ya yi Dare dare yana charting shi kuma Sadiq na zaune samar Darduma a tsakar daki yana taya Hajja bare gyada suna ta hira in ka shigo ka gansu sai ka yi Tunanin shine jikan nata Tahir ne bakon.
Sai da abokin Tahir Jamilu yazo ya jasu suka fita zuwa gidansa ya yi aure Tahir din na Zaria. Chan suka je amarya ta yi musu abinci sai a hankali Tunda karamar yarinya ce Tahir sai shakiyanci ya ke yi ma abokinsa wai ya auri kwaila. Sadiq na kare ma Jamilu Tahir ya kallesa yace"Dole ka kare masa mana. Tunda duk tafiyar ku daya ce" Sadiq yace"Eh mun ji din".
Ya na da sakin jiki sosai Tun farkonsa Daman mai son mutane ne kuma ba shi da Bakunta ballatana amincin da ke Tsakaninsa da Tahir ya wuce duk yadda Mutane ke Tunani a kansu.
Ranar yini suka yi ziyarce ziyarcen gidajen yan'uwan Tahir har gidan Zulaihat sun je ta yi ta rawan jiki da su Sadiq yace Danwake zata yi masa. Shi kuma Tahir yace ta Dafa masa kwai. Sadiq ya zunguresa ya na fadin"Wai ajiyan kwan ka bata da zaka ce ta dafa maka?
Tahir yace"Kai ajiyan Garin Danwaken ka bata da kace tayi maka"?
Da ya ke ta na jinsu sai ta yi Dariya kafin tace"Kowa zan yi masa abunda ya ke so" haka ko akayi kowa ra'ayinsa ta yi masa Mijinta ne kuma yace duk abunda suke so ta yi musu Daga karshe Tahir nata Fad'an meyasa ta yayyaka ma Sadiq kwai a cikin danwakensa Tunda yace shi baya cin kawai Sadiq yayi masa bakam yana cin Danwakensa yana Santi.
Sai Dare Hajja ta gansu sai fad'a take yi tana fadin"ina kuka shiga ne yau? Tun dazu na gama Tuwon. Yan'uwanka sai zuwa neman ku su ke yi bakwa nan"
Sadiq ne ya ke fad'amata inda suke je yau tace sun kyauta sun yi ziyara. Ba su ci tuwon ba sun koshi sai dai Sadiq yace ta yi masa Dumame da Safe. Sai adaran Sadiq ke fad'ama Hajja da Safe Gusai zasu je. Ta fara fadan ba su gayamata da wuri ba nan da nan ta mike ta fara had'a abunda ta ke da shi Wanda zata bama Sadiq ya kai ma iyayensa.
Tun safe suka shirya kafin Takwas sun karya ,sun kuma shirya tsab Hajja ta bama Sadiq leda cike da su kuka,kubewa garin kuni,zogale danya da wacce ta bushe kayan kamshi sai aya mai kyau ta ce a kai ma Innani.
Yayyen Tahir har tasha suka rakasu suka ba su 10k. Sadiq dai bai isa ya ce komai ba tunda ko ya yi mgana ba za su saurareshi ba.
Da zasu tafi Kasim wanda shine Babba ya Dafa kafad'ar Sadiq yana Fadin"Ku kula Sadiq. Allah ya tsare ku mungode Allah ya bar zumumci"
Sai da Motarsu ta tashi sannan suka koma gida.
Da wuri suka isa Gusai, Sadiq sai yaji wani irin iska farinciki na shiga jikinsa da gaske ne ba gida kamar gidan ku. Ba kuma gari kamar garin ku, daga nan suka samu abun hawa zuwa Tudun wadan Gusai.
Lokacin da Sadiq ya Buga makeken get din gidansu Mallam Tajudeen ya Bude get din ya gansa sai ya washe baki cikin Tsananin Farimciki yace"Ma sha Allah. magajin gida barka da sauka. Mallam Attahiru maraban ku da zuwa.."
Sadiq ya yi mirmishi ya na Dafa kafad'an Mallam Tajudden kafin yace"Mallam mun same ku lafiya?
Daidai Lokacin da ya ke kokarin karban Jakar hannunsa sai ya hanasa ya noke yana fad'in"A'a kai fa malamina ne me yasa zan bari ka karban min kaya?
Mallam Tajudden ya yi dariya kafin yace"Ammh ni a karkashin mahaifinka na ke. Biyayyata a gareka Dole ce"
Sadiq bai ce komai ba ya mikamasa Akwatin ya karba da Sauri ya sake Bude musu kofar suka shiga Tahir na Binsa a baya Lokaci daya yana fad'in"Mallam Taju Tahir fa sunana ba Attahir ba."
Da Sauri Sadiq yace"Ko Dahiru zai ce?
Tahir ya tokare shi da takalminsa ta baya yana Fadin"Uban Dahirun"
A tare suka saka Dariya shi ko Malam Tajudden da gudu ya shege shashen Innani Saboda yasan itace ta Farkon da ya kamata tasan magajin gida ya dawo.
Suna tafe a haraban Gidan Sadiq na kallon Motocin da ke fake a Haraban gidan cikin Tsananin kewa ya ce"Abba na gida kasan yau weekend ko zai fita sai yammah."
Tahir ya bi motocin da kallo. Shi fa har mamaki yake in yaga Sadiq a wani wajen na wata irin rayuwa.
Sai ya Tuna mahaifinsa da gidansu da Duka Danginsa sai ya rika mamaki gata iya gata ba wanda Sadiq bai mallaka ba Motar hawa ko wace iri ya ke so zai hauta ammh in ka ganshi a yana yawo da kafarsa a layi sai ka rantse bai taba ganin Mota ba.
Muryan Sadiq dai ta katsesa sanda ya ke fad'in"Kaga fa Tahir akwai baki a gidan nan. Wacan kamar Motar Yaya Sa'im"
Tahir dai sai dai ya kallah baya mgana suna tafe suna bangazan kafad'an juna kuma suna tafiyan wahainiya. Tahir ya juya baya ya kara kare ma girman gidan kallo da girman Shashe shashe na gidan da irin kayan alatun da ke cikin gidan sai ya koma ya bi Sadiq da kallo da ke tafiya zuwa Shashen Innani.
Kawai sai ya girgiza kai ya kara d'an gudu ya cimmasa lokaci daya yana Fad'in"kamar ba daga gidan nan ka fito ba"
Sadiq sai ya murmusa kafin yace"Mutane da yawa haka suke dauka"
Tahir ya kallesa kafin yace"Dama ni ne kai Sadiq"
Da Sauri Sadiq yace"Tahir ka zama mai godema Allah da Ni'imarsa sai ya kara maka."
Tahir ya yi mirmishi kawai bai yi mgana ba.
Sun kusa isa kofar Shashen Innani kenan sukaji mganarta fad'i take yi"Kai Mallam Saju ba'a san malamai makada Annabawa da karya ba. Ka Rantse Kwarankwatsa Magajin gida ne ka gani"
Sadiq ya kalli Tahir shima ya kalleshi suka fashe da Dariya.
Da sauri sauri suka nufi Shashenta suna shiga suka isketa Tafe da Sandarta ga gilashinta a Fuska Mallam Tajudden na gefenta.
Daga bayanta kuma Siyama ce da Sultana sai yaran Sa'ima su Abadallah.
Daman suna Shashen nata ne Tun Safe da Abba da Umma tare da Mama suka shiga gaisheta bayan Taba Hira sai suka tafi Shashen Abba suka barta da Sultana Daman yar gidanta ne ko Innani bata ga kowa ba bata cika Damuwa ba. Tafi damuwa da in bata ga Sulsana ba acewarta ba.
Sa'ima ce tazo tafiya da yaranta da tazo gaishe da Innani suka zo tare da Siyama shikenan ta bar su nan ta koma Shashen uwarta.
Ko da Mallam Tajuddeen ya shigo da akwatin Sadiq yana ma Innani albishir ga Magajin gidan ne sai Masifa take yi da faman tambayan ba Sa'imar ta zo ba? Ta kwashi ya'yanta ta tafi mana sun gaji da su. Siyama yarinya ce sa'ar Sultana sun riga sun san Halinta ba su bi ta kanta ba.
Innani duk son ta da bako to in yazo gidan Sulaimanu kada ya wuce kwana uku komai mutumcinku da taga ka share kafa zata fara sakin Manganganun an zo an dora ma Sulaimanu nauyi Allah na Tuba shima Rufin asirin Allah ne ba shi da shi.
Ko da kuwa jikokinsa ne tace ai suna da Gidan Ubansu su zauna chan mansa.
Innani ba ta yarda da Mallam Tajuddeen ba shiyasa ta mike kamar ta kifa tana ya rantse dai da gaske Magajin gida ya gani.
Ko a yanzu din ma bata lura da shi a gabanta ba, sai Faman fadi ta ke Mallam Saju ya rantse kada yazo karya ya ke mata.
Sultana ta bayan Innani ta ke lekowa tana kallon Yaya Sadiq shi kuma Hankalinsa na wajen Innani yana ta mata mirmishi Siyama ta Buga Ihu ta nufesa tana Fadin"Wlh Innani da gaske Yaya Sadiq.."
Ta fad'a jikinsa cikin Tsananin murna Su Abdallah ma suka nufesa suna fadin"Uncle.."
Rikesu ya yi gabadayansu yana Dariya Innani sai ta rikice ta fara fadin"Ke don uwarki Siyama Ina magajin gidan"
Sadiq ya saki su siyama ya karisa ya rike Sandar innani ya saka Hannu ya ciro glass din idonta ya goge mata sannan ya maida mata Lokaci daya yana Fadin"Ga ni nan fa Tun dazu a gabanki Innani ko dai har yanzu Idanuwan naki da sauran gyara bakya gani Innani"
Ai jin muryan Magajin gida ya Rikita Innani ta rikesa gam cikin Lalube tana Fadin"Allahu Akbar Abubakar Saddiqu dai a gabana."Sai ta fashe da kuka tana fadin"Yau dai ga magajin Sulaiman ya dawo. Dole na damu kwana nawa bamu yi mgana ta wayar zamanin nan ba. Sulaimanu fa kai kadai garesa magajinsa Dole na shiga Damuwa in ban jika ba"
Rumgumeta ya yi yana Fadin"Innani ina nan lafiya. Ai na gaya miki Hidimar kasa na ke yi achan Zariya ko..?
Innani tace"Eh haka kuma kace to yanzu daga chan Zariyan ka ke?
Kai tsaye ya juya yana kallon Tahir wanda ya Dauki Afiya. Ya nuna mata Tahir kafin yace"Daga Daura muke. Tare da Tahir muke"
Innani ta yi shuru ta na bin Tahir da kallo kafin ta yamutsa fusaka tace"Waye kuma wani Sahir?
Sadiq na Dariya yace"Attahiru abokina Innani"
Ai sai ta washe baki tana Fadin"A'a dan kwalba uba kace Attahiru naga ya yi wani fari ne kuma shine don sheganta bai zo ya rumgumeni mun yi masa Oyoyo ba."
Sadiq ya kalli Tahir ya na Dariya Shima Dariyan ya ke ya Sauke Afiya ya Nufi Innami ya Rumgumeta yana Fadin"Allah ya bar mana Ran Innaninmu"
Ta make kansa tana Fadin"Kaji dadin Tsokana ta ko"
Dariya ya saka idanuwansa na kallon Sultana da ke bayan innani kanta na kasa ta na wasa da gefen Hijabinta.
Da karfi yace"Sultana daman kina nan? Ya makaranta"
Sai alokacin Sadiq ya ganta kallo Daya ya yi mata bai yi mamakin Tana wajen bai sani ba. Yarinyar ba ta da Hayaniya ko kadan. Yana mamakin yadda ta so ta zo daya ma da Innani.
Sai a lokacin ta gaishe shi ya amsa cikin Sakewa kadahan kadahan.
Ta kuma gaida Tahir ya amsa yana Tsokarta da Matarmu..
Tana jin haka ta ruga da gudu tana jin kunya Sadiq ya Take kafar Tahir yana Hararansa da ido shi ko ya yi kamar bai gani ba.
Innani ta tattara su sai Shashenta bayan ta ce ma Siyama"Maza je ki gayama iyayen ki ga Magajin gida nan da Attahiru a kawo musu abinci.
Ta juya ta na kallonsu suna zama a kujerun falonta domin Dakin Innani ko amarya ta sameshi to sai Hamdala.
Sadiq ta kalla kafin tace"Magajin gida me zaka ci ne a kawo muku? Kai ne baka fadi kuna hanya ba da Tun Safe na hana kowa zaman lafiya a gidan nan"
Sadiq yace"Innani sai anjuma ko zamu iya cin wani abu. Sai da muka karya sannan Hajja ta bari muka kamo Hanya"
Innani ta washe baki tace"Shiyasa na ke kaunar kakar Attahiru. Ta na kular min da kai kamar yadda na ke kula da kai, To ya kuka baro su? Attahiru ya wajen yan'uwa ka na chan Dauran?
Tahir ya bata amsa da suna gaisheta lokaci daya da Tura mata ledan gabansa yana Fad'in"Hajja tace a kawo muku Innani. Ayar ciki tace taki ce"
Innani ta ja ledan ta kara gyara zaman gilashin idanuwamta Lokaci daya tana Fadin"Kai naji dadi kamar tasan ina son wasa hakora na kwanakinan"
Sadiq ya kalleta yana mamakinta matar da kullum cikin cin nama take da kayan dadi ammh tana Fad'in kwana Biyu bata wasa hakora ba.
To ina ma taga hakoran? Ta na washe bakin yaga na Robanta das a bakinta suka kalli juna da Tahir suka saka Dariya.
Sultana kunya yasa ta kasa zuwa Falon Abba ta fad'a musu dawowan Yaya Sadiq sai Siyama ce taje ta Fad'a.
Umma ta mike da Sauri ta na Fadin"Auta na yazo ganin gida kenan"
Haka ma Abba ya mike har jikinsa na Rawa Fadi ya ke yi"Mun yi mgana da shi jiya kuma bai ce min zai zo ganin mu ba. Ke Suwaiba a shirya ma Magajin gida abun karyawa."
Siyama ta yi saurin cewa"Abba shi da Ya Tahir ne"
Abba na bin bayan Umma yace"To daman duk in da kika ga Magajin gidan zaki ga Attahiru a wajen.. ki yi kokari Suwaiba kafin Innani ta fara fadan an barsu da yunwa."
Mama ta ce"To Alhaji ammh mu je nima mu gaisa da su. Siyama zata yi ma Salima mgana zata ji da abun karyawan na su"
Abba yace"A'a ba na son korafin Innani kinsan Halinta kije kawai ki yi abunda na saka ki"
Mama bata da mafita illa juyawa zuwa Shashenta tana Danne abunda ke ranta.
Tana shiga ta ga Sa'ima da Salima suna Hira afalo ganin yanayinta yasa suka hada baki wajen fadin"Mama lafiya? Sai ta saki Fuska kafin tace"Magajin gida ya zo. Kuje shashen Innani ku gaisa da shi kafin kakarku ta fara tsinan ku."
Salima ta mike da Sauri tana Fadin"Bros ya zo?
Kafin mama ta kara mgana ta fice a guje Sa'ima ta mike ta na gyara Lullubinta tace"Mama bari na je mu gaisa da kanina na yi kewarsa sosai."
Mama ta murmisa tana fadin"Ki turomin Siyama ta taimakamin wajen hada musu abun kari"
Sa'ima ta amsa ta na Ficewa.
Tunda Mama ke da girki sannan Ranar asabar da Lahadi yan aikin su basa zuwa tunda yaran nan na gida kuma a Tsarinsu a karshen sati duk mai girki ita zata yi da kanta saboda Alhaji na gida.
Ko da Sa'ima ta isa Shashen Innani ta iske Abba rike da Hannun Sadiq kamar wani zai kwace sa gefensa Umma kuma ce ya d'ora kansa saman kafadanta ya narke kamar yaro. Gabansa kuma su siyama ne da Salima sai su Afiya kowa sai mgana ya ke yi Salima fadi ta ke yi"Yaya Sadiq tun wata daya da ya wuce na yi chart dinka a wsop baka duba ni ba"
Ta fad'a cikin shagwaba Siyama kuma fadi take yi"Yaya Sadiq mu ma a siya mana waya ni da Sultana"
Sai dai aka fadi Sultana ya Daga kai yana kallonta tana gefen Innani ta Rakube kanta kasa kamar wata marainiya.
Tahir ya kallah da ke kallonsa gira ya daga masa shi kuma ya balla masa Harara.
Innani sai msifa ta ke yi"Haba don Allah ku bar min jika ya Huta daga Dawowarsa kun fara damunsa da Korafe korafe."
Sa'ima ta yi mirmishi sannan ta yi sallama Falon Innani Tunda ba wanda yasan da Tsayuwarta..
Tana shigowa Sadiq ya mike yana Fadin"Ya Sa'im"
Kai tsaye ya mike ya Nufeta suka Rumgume juna cikin Farin ciki ta shafa kan