Showing 42001 words to 45000 words out of 93195 words

Chapter 15 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11466

ta auri Abubakar mahaifin Sulaimanu, Innani Tun tana matashiyarta irin matan nan ne masifaffu tijararru an yi mata irin auran gida tun da fari ta rika guje guje auren ya lalace bai je ko'ina ba.
Iyayen Innani masu kudi ne, ko a baya Tunda suna Noma sannan suna da Tarin Dabobbi.
Innani itace Matar Abubakar ta biyu ko da akayi auran su taje ta iske shi da uwargidansa kuma uwar ya'yansa Barira. Wacce ta yi ta hauka sanda za'a auro mata Innani tunda a lokacin Mallam Abubakar ya nuna matukar kaunar Innani a Zahiri kuma ya ke nunawa da ya sanya tsananin kishinta a zuciyar Barira.
sannan sanda zata zo iyayenta sun yi mata kayan gata na alfarma tunda ita kadai suka haifa ga shi kuma sun kwana biyu a duniya. Shiyasa dukkan gata suka tattara suka ba ma Innani komai ta ke so ta na samu har da ma wanda ba ta so duka iyayenta na cika mata shi.
Shigowarta gidan Abubakar ya sauya komai saboda ta na son shi tunda ya na lallabata ya na kuma ji da ita. Sannan kuma ya na ji da Masifarta kuma ya na yi mata abubuwan da ta ke so. Sai sanadin haka ya kara hura wutar kiyayya da Tsakanin kishi a gidan Abubakar, komai Barira ta ga Innani da shi sai tace mijinsu ne ya siya musu sannan ta na zargin shi da Nuna bambamci a tsskaninsu.
Har kuma ta jawo ya'yanta cikin kishin ba su dauki Innani a matsayin uwa ba, sai itama kuma ta ce kowa ya yi ta kansa.
Haihuwanta ta farko Namiji ta Haifa aka samu Sulaimanu, bayan shi ta jima bata haihuwa ba,Sai daga baya ta samu mace mai suna Hauwa Kulu. Kuma har alokacin Barira da ya'yanta ba saa raba'ar Innani da ya'yanta duk ko yadda Abubakar ya so ya had'a kan zuru'arsa bai samu ba har ya bar gidan Duniya.
Ya tafi ya bar Barira da ya'ya Biyar,Sammani ne babba Gaddafi ,Sai Hassu sai Husai sai karamar su Zuwaira.


Kuma ya mutu bai bar komai ba sai gidan da suke ciki ita kuma Innani sai ta koma gaban iyayenta da zama ta cigaba da renon ya'yanta a kan nata Tunanin na kada su taimaki wanda bai taimake su ba, kamar yadda Barira ta janye ya'yanta daga Ya'yan Innani ita Innani haka tayi na bakinta tace kowa ya yi ta kansa.
Haka Rayuwa ta mika Innani ta rasa iyayenta komai na su ya dawo hannunta da shi ta zama yar kasuwa mai saida Hatsi, lokaci d'aya kuma ta na kula da su Sulaiman.
Sulaiman ya yi karatun zamani har matakin Diploma a garin zamfara Hauwa kulu kuma iyakarta Jss Innani ta yi mata aure da Shitu shima dan asalin garin Shinkafi ne,ammh wajen shekaru goma da auran su ba ta haihu ba,sai ya kara aure ya haihu sai aka fara Tunanin Hauwa kulu ce bata Haihuwa mgana tayi Tambari a gari Innani ko gida gida take bi ta na Tsine ma duk wanda yace yarta bata Haihuwa.
Sulaiman kuma bazai ce ga Silar Arzikinsa ba, sai dai yasan ya fara da bin wani dan'uwan Innani da ke sana'ar Siyar da kayan wuta a garin Zamfara, Daganan shima sai ya kafa nashi sana'ar ya na saida komai na kayan wuta Daga baya da yayi karfi har na'ura mai kwakwalwa ya ke sarowa ya na Saidawa.
itace sana'an da ya fara samu da shi, Sannan da ita ya yi auransa na Farko da Salamatu yar garin Gummi ce yayarta ke auran Dan'uwan Innani anan suka Had'u. Tsakanin Salamatu da Sulaiman auran Soyayya ce tsantsan da kuma amincewar Innani tunda ta ga Salamatu Allah ya Dora mata kaunarta acikin ranta saboda Ladabinta da Biyayyarta.
A garin zamfara suka fara zama a gidan Haya da ya kama lokacin. Innani kuma ta na Shinkafi ta na gudamar da sana'arta ta saide saide hatsi, da farko wani Alhaji ne ya fara haskamai saro na'urori daga kasar waje saboda an fi samun masu inganci da taimakon Innani ya fara zuwa kasar China saro computoci kuma yaji dadin zuwa sosai Tunda ya samu riba matuka gaya.
Daganan kuma sai ya ga waje bayan China har India ya ke shiga domin Saro kayayyakin wuta. Da shawaran abokan sana'arsa suka haskamai ya fara sana'ar saida Danyan gold kuma ya shiga da kafar Dama cikin Lokaci kad'an ya samu kudin da zai rufa ma kansa asiri tare da innani da kanwarsa.


Lokacin da ya yi ginan gidansa na Gusai sai ya koma tare da Amarya Suwaiba Hajiya Mama kenan, dalilin Ya na neman Haihuwan d'a Namiji ido Rufe,Tunda Hajiya Umma Tunda aka yi auran su ya'ya mata ta dinga Haihuwa kuma haihuwan nata akai akai take yin shi, Duk da Innani na son Umma bai hana saka Sulaiman ya kara aure ba tunda babban Burinta Sulaimanu ya samu Magajin da zai gaje shi watarana
Suwaiba asalin yar Birni ce agarin gusai aka haifeta kuma anan ta Girma ganin Alhaji Sulaiman na da abun hannunsa yasa mganar auren ma bata Dauki tsawon Lokaci ba akayi komai aka gama sai dai ba ta zo da Farinjini ba ganin Farko da Innani ta yi mata ta tabe baki tace bata da D'a saboda ta na ta kallon Mutane a yatsine tun kuma daga Lokacin har gobe Innani ba ta wani yin Mama sai dai bata Zafafa ba, ammh ko ya'yanta suka yi wani abun sai tace"Ya'yan suwaiba dai jarabbabu ne."
Itama sai al'amarin bai sauya zani ba, Itama ta na zuwa ta fara zazzage haihuwan ya'ya mata ba ta fara da Magajin kamar yadda Burin Innani ya ke ita da Alhaji Sulaiman ba.


Tashin Hankalin Innani kada yau sulaiman ya fad'i ya Mutu su Sammani su gaje abunda ya ke da shi ba shi da Magajin da zai gaje shi.
Sai Hankalin Innani ya tashi sannan ta tusa ma Sulaiman tunanin cewa in bai haifi Namiji ba kamar bai haihu ba ne ya'ya mata ba su da wani amfanin da za su yi masa namijin da zai Haifa shine asalin Magajin gida. Sannan da karancin ilimin addini a barayin Innani shima Alhaji Sulaiman da sauki ammh duk da haka ya na matukar kaunar Innani har da dalilin yasa baya iya saba mganarta sannan har yau har gobe da cewarta ya ke amfani sai dai in mganar Magajin gida ne zai Ture nata.
Da Farko da Alhaji Sulaiman ya gina ma Innani shashenta kin komawa ta yi tace saboda Hauwa bata son ta baro ta ita kad'ai sai yan uba ta shiga uiu Shiyasa ta yi zamanta a shinkafi sai dai ko da wani lokaci ta na Hanyar gusai kawo ma su Umma Rubutu da jike jiken magunguna saboda dai su haifi Namiji Sulaimanu ya samu magaji.
Umma da na iliminta wani lokacin sai ta kalli Innani ta na fadin"Innani Haihuwa ta Allah ce. Ko ya baka d'a Namiji ko ya baka mace duka Tsarinsa ne bawa bai isa ya kauce ma Kaddaransa ba wasu ma na neman Haihuwan ba su samu ba mu kuma mun fa samu ba sai mu gode masa ba?
A lokacin Innani hararan Umma ta ke yi kamar idanuwanta zasu fado kafin tace"Kaji min wani tsirfa da jaraba yo har mu zaki gayama Allah Salamatu? Tun kafin a haifeki na ke sallah Saboda haka baki isa ki gayamin komai ba"


Dole Umma ke kama bakinta duk Abunda Innani ta bata sha take yi, ita ko Mama sai ta yi gaddama da ya ke ta yi karatun aikin jinya bata cika shan jike jiken magungunar gargajiya ba.
Sai In tace bazata sha ba Innani ta fara bala'i ta na tsine tsine har cewa mata ta taba yi ko ta sha ko kuma ta kara gaba bazata zauna a gidan Danta ba ta sha mganin da zai kawo mata jikanta Namiji ba.
Mama Da Umma da mijinsu kamar makunnin wuta ne, Innani ce ke rike da Makunnin ta na Sarrafa shi, ya ce duk wacce bazata bi mganar Innani ba to zata kara gaba tunda shima Umarninta ya ke bi, a kauyen kuwa da ke zagaye da Shinkafi ba inda kafar Innani bai taka ba wajen neman taimako ba, duk in da taje mganarta kenan"Sulaimanu ba shi da magaji ga shi ya na cikin yan Uba wad'anda ba sa kaunarsa."
Tunda su ya'yan Barira sun saki ganin mahaifiyar ta su Barira Allah ya yi mata rasuwa. Ganin haka sai Innani ta ke mganar saboda sun ga Allah ya Daukakan Sulaiman ne shiyasa suke bibiyansa yanzu. Su kuma duk rayuwa ta koma sai a hankali suna Biyo dan'uwansu domin zumumci kuma da Taimako ammh Innani ta Tsare gaba ta tsare baya. Ko zuwa suka yi Innani zata tattare ta saka ya ba su kudi kad'an da ko na maida su gida bazai isa ba sannan ta hana su kwana acewarta shima Sulaiman ba kudin garesa ba Rufin asirin Allah ne.
Za'a iya cewa wani abun na Abba ya Tadda Hali ammh kuma da zugan Innani da irin Tarbiyanta.
Hauwa kadai ta ke bari Abba na tallafa mata itama haka take tsine ma shitu tunda yanzu matansa biyu kuma dukkansu suna ta Haihuwansu Hauwa ce aka bari cikin gorin dangin miji da kishiyoyi sannan Innani ta so ta raba auran Hauwa tace sai Shitu shima ya ce sai Hauwa daga karshe Innani ta fita batunta ta koma neman ma matan Sulaiman mganin Haihuwan Magajin gida.
Lokacin da Magajin gida ya zo Duniya komai na Rayuwa Alhaji Sulaiman ya gama mallaka ya yi karfi a sana'ar gwalagwalai sannan tare da Shigo da kayan wuta, da su kamfutoci a lokacin kuma ya'yan shi goma sha d'aya duka Mata ne innani ba inda bata shiga ba, ammh har alokacin Kum fayakum.
Umma ke da Shidda, Mama kuma na da Hud'u.
Surayya ce itace Babba, sai Suba'atu,Sadiya,Sa'adatu,Saddiqa,Sajida,Sai dakin Mama kuma Sa'ima ce babba sai sakeena,Saliha,da Shahida.
Kaf din su sunayensu da Harafin S ya fara kamar yadda na iyayensu ya fara Shiyasa ko a makaranta in za'a kira sunansu da SS Shinkafi a ke kiransu.
Kuma a zuwa Lokacin Innani ta Dawo Gidan d'anta da zama saboda ta ce ta rika lura da wasu abubuwan tunda har yanzu Allah bai kawo magajin gidan ba, Sai dai har alokacin bata Saduda ba Duk in da taji ana ba da taimako sai kafarta taje bata Hakura ba.


Umma ta samu cikin da tunda ta same shi ta ke wahala ba'a taba sanin ta na da Junnu ba sai alokacin suka tashi zabuban sai dai aka yi ta mgani Innani ce ta tsaya kan Umma alokacin ta rika kula da ita, sai dai ta sha Uban jike jike da Ruwan Rubutu a shashenta akayi renin cikin Sadiq wanda ko Innani bata sakama Ranta magajin gida ke tafe ba Ciwon Umma ya Dauke wannan Tunanin daga kanta.
Sadiq ya zo duniya cikin wani irin Hali da tsaka mai wuya Umma ta Haifeshi ba ta san wanda ke kanta ba, bata kuma san abunta ta haifa ba Kamar mahaukaciya haka ta koma ta na mganganu marasa ma'ana da kokarin tashi ta fita da gudu kamar wacce ta zare Abba ya so a yi na asibiti Innani ta hana Sannan Dangin Umma daga Gummi sun kasa mgana saboda ganin Kulawar Innani akan Umma sai suka kauda idanuwansa.
Tun da Sadiq ya fad'o duniya Daman Innani ta karbi haihuwarsa tace an samu Abubakar Sadiq,Magajin gida yazo tun kuma daga Lokacin Innani ta karbi Ragamar kula da Sadiq a hannunta tare da Umma Gabadaya.
Da abun ya ki yi ne tace za su koma Shinkafi da zama saboda nema ma Umma magani.


Abba ba shi da mafita saboda Umarnin Innani ne, haka ta koma Shinkafi da zama tare da Umma da Sadiq tana kula da Umma gefe daya ta na kula da Magajin gida. Shiyasa Sadiq yace Innani na da Muhimmanci a Rayuwarsa yana da wata takwas ta cireshi a nono saboda daman sai da Dubara Umma ke iya ba shi Nonon Tunda har Lokacin sai a hankali.
Shiyasa Sadiq ya gini da ciye ciyen abincin gargajiya tunda duk shi Innani ta rika Dura masa.
Ya taso ya gansa a Shinkafi ne tare da Umma da Innani, sai dai Abba da Sauran yan'uwansa na zuwa dubashi a kai akai ko da suke a shinkafi ba bu gatan da Sadiq bai gani ba Abba da Inanni kamar zasu lashe shi Saboda so da kauna in kana son su soka to ka so magajin gida sai suma su soka.
Umma sai da ta kusa shekara Biyar cikin wannan Halin sannan ta warke da taimakon magungunar musulumci,da addu'o'in malamai lokacin da ta warke ita kuma Sai Hauwa ta fara ciwo daga zazzabi ta fara sai rama kuma Sai Innani bata koma Gusai ba sai Umma ce ta koma Gidan Mijinta aka kuma bar ma Innani Sadiq a hannunta.
Shekara takwas ya kwashe a shinkafi sannan ya dawo gusai wajen iyayensa da zama tare da Innani wacce ta kasance itace komai na shi. Tun yana karaminsa ya ke da katon bangare shi kadai kuma ya mallaki komai da yan gata ke mallaka.
Sai dai shi ra'ayinsa ba shi kan Sauran Ra'ayin wadanda ke zagaye da shi.
Ra'ayinsa Dabam ne da na kowa sannan Rayuwarsa mai Sauki ce ba kamar yadda akayi Tunanin Magajin gida zai kasance ba.


Sultana Diyar Hauwa ce wacce ta Haifeta ko ganinta ba ta yi ba Allah ya yi mata rasuwa,Umma na ganinta ta ji ta na sonta ta Dauketa Innani ta Daurre mata Gindi Dole Shitu ya bar musu Sultana yasan Tijaran Innani bai isa ya musa ba. Dalilin da zamanta ya Dawo gidan su da Sadiq kenan Hannun Umma.
Sadiq tun yana karaminsa mutum ne mai sanyin Hali Tausayi da jinkai, ga Abba da mako da son abun duniya shi da Innani ammh kuma shi ba su iya masa gaddama. Tun yana da sha wani abu a duniya yasan ya taimaki wadanda ba su da shi, ko a hanya yaga mutum na neman taimako zai ce ka Biyosa sai gida sai dai Abba yaji sallama kuma ba shi da ikon cewa a'a kai tsaye Sadiq zai ce Abba a taimaka masa don Allah.
Sannan shi Yaro me da ke son zama cikin mutane ko da bazai Rabesu ba, ammh yana son zama cikin Anguwan da ke da cikowar Mutane shi dai ya kasance ya na ganin Mutane kowa na Harkan gabanshi.
Mutum ne da ke son Rayuwa daidai misali bai cika son Dora Rayuwarsa kan Babban mizanin da kowa ya Dauke shi ba. Ya san shi dan gata ne gaba da baya. Ba Iya Innani ba kaf Dangi kowa shi ya ke so burin shi ya farantamasa rai. Tausayinsa ya siya masa soyayyan Mutane tun kafin ya zama Saurayi su Baba Sammani suka rike shi kamar shine Abba Tunda in ka fad'amasa matsalanka to kaje gida ka kwanta ka gaddara ma matsalarka ta kare.
Ya na son Mutane da son yan'uwa mafi girman abunda ke ranshi Shine Tausayi Sadiq ba ya so yaga Mutane na cikin wani Hali ya kasa taimakawa baya so yaga wani cikin halin Babu ko Damuwa in dai yana da Halin taimakawa shiyasa in kaga Abba ya yi kyauta to Sadiq shi ne in yace ba'a iya Saba mganarsa Innani ta kan ce yi masa komai ya ke so tunda komai da ka mallaka na shi ne magajin gida.
A shinkafi ya fara Fimari dinsa sannan yazo gusai ya karisa secondary school dinsa wata makaranta ya yi mai hade da boko da arabi saboda son addininsa.
Yana da naci kan abunda ya ke so ya koya,yan'uwansa ba su so ya yi karatu ma a Nageria ba, sai dai kuma Uban gayyar baya Ra'ayin haka.
Sannan ga Mallam Taju da ya ke Daukan karatu a wajensa.
A makaranta suna hadda sannan in ya Dawo gida yana yi wajen Mallam Taju shiyasa cikin Lokaci ya samu ilmin da ko iyayensu ba su taba Tunanin yana da shi ba.
Kafin ya gama Secondary School ya Sauke Qur'ani sauran littafai ya Durfafa kowa ya san shi yana da Saukakkiyar Rayuwa. A kallo daya in kayi masa bazaka ce yana da wani gata ba saboda yana Daidaita Rayuwarsa daidai da ta kowa. An sha Fama da shi akan ya je waje ya yi karatun Likitanci ammh Sadiq fur yace baya Ra'ayi shi Quantity Surveying zai karanta masu kula da harkan Shimfid'a tituna kuma kowa yasan Ra'ayin shi ne gaba da na kowa hatta da Abba da Innani.


Suna ji suna gani ya tattara kayansu ya tafi zariya, in da ya samu Admission a ABU ZARIA zai karanta Ra'ayinsa.
Abba ya so ya kama masa gida ya zauna yace baya so a Hostel zai zauna cikin Dalibai yan'uwansa.
Wannan shine Mafarin Haduwarsa da Tahir kenan.
Tahir ya zo daga Daura ne d'an talakawa maraya da taimakon yayyensa da Kakarsa ya samu makarantar, Daki daya suke mafarin Zamansu kuma abokai duk cikin Dakin Sadiq ya fahimci Tahir ya fi su maida kai ga karatu, Su hudu ne Shi da Tahir sai Jabir sai Usman Muhammad Balarabe Mb kenan.
To har gwara Usman akan Jb da shima yaron mai kudi ne babanshi dan siyasa ne, kuma daga kano yake daga ganinsa zakasan ba karatu ya zo yi ba illah Shagala.
Da Farko Sadiq da Tahir fad'a suke yi kan gyaran Daki Tunda Sadiq baya son yaga Shirgi a Daki yana son Tsafta daga baya kuma sai suka zama abokai duk da ba Course daya suke karanta ba.
Cikin Lokaci kadan suka Fahimci Hallayan juna. Suna shekara ta uku Jb ya bar Dakinsu ya koma ya kama daki a wajen makaranta yana cigaba da watsewarsa.
Sadiq ya yi suna Abu zaria saboda Tausayinsa da taimakonsa Abba ya sha Biyama Dalibai kudin makaranta bai san iyaka ba. Sai dai Sadiq ya kirashi yace"Abba akwai wani a makarantarmu bai biya kudin makaranta ba gashi za'a fara Jarabawa. Abba zamu taimaka masa."
Abba ba shi da mgana illah yace"Za'a taimaka musu Magaji gida zamu taimaka musu in sha Allahu"
Tahir ko da Usman shekaran ta kusa da ta karshe duk Sadiq yasa Abba ya Biya musu kudin makaranta. Shi Usman dan gangare ne, yana da kokari sosai phamarcy ya karanta da suka gama ya samu Scoolarship zuwa kasar Ughanda domin cigaba da karatunsa.


Rabuwarsu kenan, Jb kuma daman Sadiq ya yanke alaqan sa da Jb Tahir ne ya kasa Rabuwa da shi.
Sadiq akan kirashi da sunan Alarammah Saboda Addininsa sannan masanin Qur'ani ne da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login