Showing 51001 words to 54000 words out of 93195 words

Chapter 18 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11467

gaskiyan mgana komai na jikina karami ne ba Babba ba, hatta ko da kaina duk da tarin gashin da na ke da shi kana kallona zaka san ina da karamin kai. sai dai fuskar ta yi fasali Farar Hoda na saka daman ita nake shafawa,tunda ga yanayin Fatar Jikina ina da Haske sosai kamar wata zabiya.
Adda Fati na ta yi min d'an bikin na jirasu nace Wlh bazan tsaya jiran wannan gayyar tafiyar na su ba. Na ko yi tafiyata bayan na yi ma Amma sallama tace a dawo lafiya.
Na riga na yi yak'i da kaddarata shiyasa na yi Gundunbalan fita ba Abun rufe Fuskaa duk da ba wanda ya tareni da wata mgana ammh na sha nu ni da baki da Hannu ana zud'ena.
Adaidaita na samu zuwa pizzet daganan na samu na D'anmagaji tunda yanzu ta cikin Titin Tukur Tukur suke bi.


Karfe sha d'aya da wani abu na isa gidan Ramatu na iske Nura na gidan ashe ya dawo yana gari.
Na ganshi sai fama ya ke da Noor itama kuma Ramatu na ciki ta na Shiryawa. Shigowata na karb'eshi ina Fadin"Kawata muguwa ce. Shikenan sai ta barka da reno kai da ka dawo ka na Bukatar Hutu."
Yana dariya yace"Yauwa Hasiya ki yi mata Fad'a bata Tausayamin da na dawo kamar ta samu D'an reno"
Ramatu na daki ta daga Murya ta na Fad'in"In baka nan zan rena ammh fa in ka dawo kaima zaka Tab'a"
Kai ya girgiza kafin yace"Kin ji ta ko?
Ina sabata saman kafad'ata nace"Kyaleta da ni, zan yi maka mganinta."
Ramatu ta fito cikin Shirin Fita ta wurgamin zanin goyo tana Fad'in"Goya yarki mu tafi mun yi rana."
Ba musu ko na goyata Nura kuma ya shige ciki Ramatu ta bi bayansa sai chan suka fito tare.
Tunda yana nan shi ta bar ma gidan Ammh har bakin Titi ya rakomu muka samu abun hawa zuwa gaskiya Bayan Ramatu ta kira Adda Rukayya ta yi ma mai adaidaita kwatance wajen.
Cikin Lokaci ko sai gamu a sababbin anguwannin Gaskiya ne gida mai suna gida Baban su Amna ya gina Tunda babba ne a ma'aikatan MBAIS.
ko da muka isa mun iske gida cike da yan'uwa kamar ana wani Biki Adda Rukayya daga ita sai Habiba ne sai makotanta inda suka taso.
Gidan Babba ne shashen Adda Rukayya dakuna Hudu ne kowanne da Bayuka sannan ga Falo ga kitchen. shashen mai gidan ma babban waje ne sai kuma wani bangare da ba'a gama ba.
Tunda muka shigo na lura da yanayin yan'uwan Mijin sai faman nuna ni suke yi ana kus kus. Wanda ma bai sanni ba duk an gayamasa komai a kaina ban maida kai ba muka wuce cikin Dakin da Adda Rukayya take.
Abun mamaki ta yi maraba damu sosai ta saka wani leshi sabo ta ci kunshi da kitso kamar wata Amarya.
Kai tsaye ta kalleni tace"Hasiya sai yanzu.? Ba fa kowa sai ni kad'ai Allah yasa ma Habiba na nan"
Mirmishi kawai na yi ban ce mata komai ina ta kallon wajen gadajen duk Sabbi ne falon ne bakomai Kila ba'a kawo kayan ba ne. kafin ma mu tambayeta ta shiga gayamana masu kujrun ne ba su kawo ba sai an juma Gadaje kawai aka kawo sai kayan kitchen data siya tunda munzo muje mu tayata jera komai.
Hijabina na cire ban sauke Noor ba Duk da tayi barci yanzu ina Sauketa zata Farka. Habiba sai faman mopping din Tayels ta ke yi ta gama wankin bayi wai a hakama sun Rage ayyukan tunda tun jiya da Daddare duka dawo nan suka kwana.
Dangin mijinta kuwa suna tsakar gida ba abunda suke yi sai shewa da Hira.
Tare da Adda Rukayya da makotanta muka gyara mata kitchen d'inta wasu kayan duk Sabbi ta siya muna ji suna hira da makociyarta adashen dubu Dari Biyu ta shiga aka bata kwasan farko.
Kallona ta yi kafin tace"Hasiya na ware muku wasu kaya suna chan gidan. Har da wasu kayan amfani na cikin gida in Habiba zata dawo zata Taho muku da shi."
Kai na jinjina kafin nace"Mungode Adda Congrat Allah ya sanya alheri yasa an yi ma rai ne."
Ta amsa da Ameen cikin Fara'a kafin tace"Ina Adda Fati ne wai?
Kai tsaye nace"Suna tafe sai da ta biya ta gida ita da Inna Talatu da mutan gidanmu ne su Maman boy."
Adda Rukayya tace"Munafukai za'a zo ganin kwaf."
Ramatu tace"Su zo ai arziki ne sai su dagwala su kara gaba"
Adda Rukayya cikin Farinciki ta saka Shewa suka kashe da Ramatu ta na Fadin"Wlh kuwa su zo su sha kallo."
Nan suka cigaba da Hirar su da Ramatu tare da makotanta ni nawa kawai Mirmishi da eh ko a'a.
Babu wani sakin jiki ko shakuwa Tsakanina da Adda Rukayya yau ma na Fahimci tana cikin Tsananin Farinciki ne shiyasa.


Sai bayan azahar su Adda Fati suka iso lokacin har an kawo abinci daga Gidan su Baban Amna cikin gari.
Ba su da nisa da Babban gidanmu na marigayi Mammadi kona. Sun san mu kamar yadda mu ma muka san su.
Abincin ma kula Hud'u ne suka Dauki Biyu suka ba ma Adda guda Biyu.
Ni na zuzzuba mana muka ci muka sha Ruwa da lemu tunda Walima ce aka yi.
Amna da Aslam na ta tsallen Murna sun yi sabon gidan. Yaran sun fi sabawa da Dangin Ubansu shiyasa ma suna tare da su. Ni dai tunda na Fahimci yadda na zama mujiya da abun nunawa sai na kama kaina acikin Dakin Adda ko Fitowa ban karayi ba tunda muka gama gyaran kitchen.
Su Maman Salihi sai zaga gidan suke yi suna santi bayan sun gama ci sun sha abun mamaki har Kaltume da nasan gulmar da ta kawo ta ta fi wacce ta kawo su maman Salihi.
Sai Gabda La'asar Baban Amna ya kira yace ga masu kawo kujeru nan da wasu kayanbA gyara waje jin haka yasa muka mike muka kara gyara Falon da Sauran Dakunan. Kawo kayan yasa Danginsa suka shisshigo mazan su suka rika shigowa da kujeru ne sai katifi da cafet sai tv bango guda Biyu da sauran tarkace.
Sai Falon ya yamutse kowa na fad'in yadda Setin kujerun suka yi kyau da cika ido. Adda Rukayya sai faman washe baki take yi tana fadin"bangare na za'a fara gyarawa, na shi yace sai daga baya"
Shagala da ganin abun arziki yasa na fito nima na Tsaya cikin mutane ana santin ganin kayan da ni.
Noor ta tashi ta na Hannun Habiba. alokacin ba ni da Hijabi Domin Tunda na cire ban maida ba, sallah ban yi ba Tunda ina Hutu.
Kamar Daga sama naji an kira sunana da Karfi
"Hasiya.."
Sai na juyo sai da Gabana ya fad'i ganin Jummai kanwar Abubakar ce itace Autar su.
Kallonta na ke yi ina kokarin daidaita yanayina jin ban amsa ba yasa da ta shiga Tafa Hannu ta na Fad'in"Na shiga uku na lalace wa na ke gani haka kamar Hasiya Jaraba da Masifa da bala'i.?
Jin mganarta yasa sai Hayaniyar ta Tsaya kallo da Hankali ya Dawo kanta.
Ita ko kai tsaye ta shiga nuna ni ta na kuma kallon kanwar Baban Amna Tunda ta dalilimlnta tazo gidan. Ita jummai tana auran kanin mijin Kanwar Baban Amna ne su d'in Facalolin juna ne.
Cikin mamaki tace"Me ye had'in ku da wannan Jarabar?
Ta fad'a ta na nuni Kamwar Baban Amna mai suna Zainab tace"Wannan wai? Kanwar Ya Rukayya ce matar Yaya Adamu."
Ai sai jummai ta Rafka salati tana Fadin"Me ya kai ku jawota nan wajen? To Allah ya kyauta mu gama taron nan lafiya wani bala'in bai afka ma dan'uwan ku ko wannan gidan ba."
Duk na Tsure na kasa ko kwakwaran motsi kamar yadda su Ramatu suka yi.
Da yake Abubakar suna da Tarin zuru'a a gidansu nima ba duka na san su ba su Adda Rukayya ba su san Jummai ba sun fi sanin manyan.
Ramatu ce ta kalleni ta na Fad'in"Wacece wannan Hasiya?
Dakyar na Hadiye miyan baki na kafin nace"Jummai ce k'anwar Abubakar.".
Ramatu ta zaro ido Adda Fati na gefe tace"Subhanallah Allah yasa kada ta watse taron nan"
Ai bata gama Rufe baki ba Zainab kanwar Baban Amna tace"Mun santa sarai Jummai ni kaina da na ganta tazo sai da nayi mgana to ammh gudun ka yi mgana ace ka tada Fitina yasa ban ce komai ba."
Jummai ta ce"Kin ko yi kuskure. Wannan matar ba Mutum ba ce ina zargin Mayya ce."
Su Adda suka saka Salati Inna Talatu ta shiga Tsakiya ta na Fad'in"Ashas. Wani irin maita kuma baiwar Allah?
Kai Tsaye Jumma tace"in ba maita ba menene? In ta kama kurwan mutum sai ta Allah kawai. yaya Abubakar sai da zaman zariya ta gagareshi ya koma kano komai ya taba da sunan sana'a sai ya lalace ta gama lalata masa Rayuwarsa gabad'aya muma ta lalata mana Rayuwar mu tunda ta dalilinta Ubannu shima ya rasa komai na shi in ba Maita ba mene wannan? Ki sake mana kurwan d'an uwa don girman Allah Hasiya."
Tun kafin ta gama mgana na Fara Hawaye cikin murya ta nace"Wlh ni ba na maita. Dangin mu kuma ba Mayu."
Da sauri Zainab kanwar Baban Amna tace"Kina fa da Maita Hasiya. in ba maita ba menene? Ina ce a auran ki na Biyu ma abuunda ya faru kenan? An ce shima sai da aka rasa Dukiya sannan shima har tana neman ransa Tunda yana chan yana jinya da karaya uku ajikinsa ko'ina kika shiga Bala'i ne da Masifa zai faru to in ba Maita ba ne, sai ki fad'ama na uban me kike da shi..?
Kalmar maitan da suke jefana da shi yasa na Fashe da kuka.
Ramatu ta rikeni ta na Fadin"Wani irin maita kuma? Hasiya ba mayya ba ce in da mayyace da Tuni kun sani ai kunsan tushenta asali ma kusa kuke da su"
Nan fa mganganu ya rika tashi kannen Abubakar suna ta cewa a bakin ya'yan Baba Saminu suke jin Labarin su ma sun ce maitan gareni.
Adda Fati tace"Mu ba mu da Maita. Ba mu yi gadon shi ba. Da muna da shi da kunga Rukayya da shi."
Kai Tsaye Zainab tace"Ai an ce ana siya kuka sani ko itama siyan tayi."
Adda Rukayya da ta kasa mgana Tun dazu sai yanzu ta dakama Zainab Tsawa kafin tace"Ya isheki Zainab. Kina wuce gona da iri ya kuma isheki jifar yar'uwata da kalmar Maita."
Zainab ta Saki gud'a kafin tace"Ku na kokarin Boye abunda bazai Boyu ba Yaya Rukayya. To in ba maita ba ce ku fad'a mana ko menene muna son ji."
Adda Rukayyah sai ta kasa mgana Ramatu ce tace"kaddaran Allah ce. Hasiya ba Allah ba ce ba ta da masanin gaibu. Kuma wannan mganar da kuke yi kamar kuna Jayayya da Kaddaran Allah kuma Daidai ya ke da Baku yarda da Allah ba."
Maganganun Ramatu yasa suka yi Shuru Jummai ta tab'e baki kafin tace"Wlh kada ku yarda da mganar su. Gwara ta tafi tun kafin mugun abunda ta tsara ya saukar mana."
Jin maganganunta yasa kannensa suka fara cecekucen sai na bar gidan kada na jawo musu wata asarar.
Kuka na ke yi da Bakina da zuciyata. Adda Rukayya ta ba ni mamaki yadda ta shiga ta na masifan sun zo sun tozarta ta tunda suka Tozartani.
Tabbas jini jini ne, Dan'uwanka zai iya maka abu ammh shi bazai iya Daukan wani ya yi maka ba.
Mgana taki karewa suna ta Tafka bala'i kan sai na bar gidan har suna Hakilon za su fita da ni ita kuma Adda Rukayya tace ba zan tafi ba ba su isa ba. Ganin abun na neman ya yi yawa yasa nace ma Adda Rukayya bari na tafi kawai.
Idanuwanta jajir tace"Ba fa zaki tafi ba. Ko da suke tunanin nan gidan Dan'uwansu ne. Ni ma su yi Tunanin Ni matarsa ce ina da iko da komai na shi."
Inna Talatu ta ga Hayaniyar ta yi yawa ga maza masu kawo kaya yasa ta ce ma Adda ta bari na tafi kawai ta kalli Ramatu ta na fad'in"Ramatu ku je gidan ki da ita."
Ramatu ta gyad'a mata kai sai ta Rikemin hannu na koma Dakin Adda ina sharan kwallah na saka Hijabina
Da takalmina Habiba sai kuka ta ke yi ta na fad'in"Adda Hasiya ki yi hakuri."
Ban iya mata mgana ba. Ramatu ta karbi Noor ta goya muka fito ammh duk da Haka Rigimar bata kare ba.
Kamar wasa zamu fita muka bangaji juna da bakin da suka shigo ni ban san yadda abun ya faru ba sai gani na yi d'aya daga cikin su ta fad'i a kasa tana ta faman birgima da ihu.
Suna ganin haka wata mata ta kwalla kara ta na fad'in"Ku riketa ta tabatta mayyace ta kama Ladidi"
Ta fad'a cikin karaji ni dai na juya ina son sanin meke faruwa ba zato ba tsammani naji an cakume an yo baya dani ana fad'in bazan tafi ba sai na Tsallaka matar dake kwance tana Fizga kamar mai aljanu.
Ramatu na ja na ta na fad'in"Hasiya ba mayya ba ce don Allah ku bari mana.".
Ta na yi su Adda na yi Inna Talatu fad'i take"Shed'an ya shigo gidan nan don Allah ku bari mana."
Ba wanda ya Saurare su rikeni yan'uwan Baban Amna suka yi suna Rantsuwan sai na Tsallaka matar da ke kwance sannan zasu kyaleni.
Na rude na Dimauce domin ban tab'a ganin wannan tashin Hankalin ba. Ganin su Adda Fati suma sun taso sun Tare ni yasa Zainab tace ma mazan da suka kawo kaya su Rufe kofa su zo su kama mu su ni.
Innalillahi wa'inna alaihirraju'un Ban taba zaton haka Rayuwa ta ke cikin Tsaka mai wuya ba sai ranar. An ce sarki yawa ya fi sarkin karfi. Sun fi mu yawa su Adda baza su iya da su ba sannan ga Maza.
Haka wani Namiji ya rikeni daman ni ba auki ba, Matan kuma suma kaimun duka ta ko'ina Hijabin jikina haka aka yagashi a ka yar, A na jamin Rigan jikina Dankwalina ko Tuni ya yi ta kan shi Gashina ya bazu haka suke jamin ga shi suna Tunkud'a ni su Ramatu na Faman tareni ammh sun fi karfin su.
Bana so na tsallakata Saboda ni ba Mayya bace, gida ya cika da iface iface da Hayaniya wasu suka fita waje suka rika Ihun an kama mayya kafin kace me gida ya cika da Mata da maza.
Sai da suka min duka suka yayyagamin kayana dagani sai siket sai Bra a gaban Mutane mata da Maza Ramatu ta rufanin Hijabinta suka Cire suka watsar Adda Rukayya na ta Ihu sai kiran Wayar Baban su Amna take yi baya Dauka.
Su kuma sun yi Rantsuwan Wlh tallahi sai na Tsallakata ko su halakani,Tozarcin da ban taba ganin irin shi ba. Tsirara suka kusa yi min dagani sai siket. Haka na ke wani irin kuka zuciyata na zafi kamar zan Mutu Adda Fati kuka Adda Rukayya ma. Habiba ma kuka Ramatu kuka, duk wani mai imani da idon shi bai Rufe ba sai da ya Tausayamin.
Na tsugunna na Rufe kirjina ina kuka ina Fad'in"Wlh ni ba mayya ba ce.".
Wani Saurayi yace"Ki ta shi ki Tsallakata sai mu tabbatar da ke ba Mayya bace"
Ban yi shawara da kowa ba na mike ina Duke jikina na tsallaka matar nan dake numfarfashi. Ba ta tashi ba suka ce sai na kara na kara shima bata tashi ba. Suka ce sai na kara cikin ikon Allah ina kara yin na uku sai gata ta mike ta na faman zare ido ganin Mutane a kanta yasa ta ke fad'in"lafiya me ya faru.?
Kawai wajen ya Rud'e da Hayaniyar "Laa! Wlh da gaske Mayya ce." Ko kafin na yi wani yinkuru sun Rufeni da Duka Inna Talatu ta fita da Gudu waje tana neman agajin jama'a.
Adda Rukayya ta shiga cikin su tana Ihu ta na Fad'in"Kai kai ku bari mana."
Ramatu ko wayarta ta Dauko ta Kira mijinta ita kanta garin kareni dukanta ake yi Noor sai sai Faman Tsala kuka take yi.
Inna talatu na Kofar gida ta ga zuwan Mijin Adda Rukkayya a mota. Daman yana Hanya zuwa ne bai ga ko kiran Adda Rukayyan ba inna Talatu ta nufe shi cikin tashin Hankali tana fadin"Za su yi kisa wlh zasu kasheta."
Hankalin sa ya tashi jin hayaniya ya Fad'a gidan a guje.
Shi kanshi ya shiga Tashin hankali ganin gida cike da mata da Maza daman tare ya ke da abokinshi.
Adda Rukayya na ganinshi ta Nufeshi ta na kuka fad'i ta ke yi"Wlh wani abu ya samu Hasiya ba ni ba kai har Abada Adamu."
Bai tsaya jin ba'asi ba suka fara watse taron da Kai kai ku bari mana Jumai da Zainab sun fi kowa zakewa wajen dukana. Baban Amna da Abokinsa suka kwaceni lokacin sun gama Min lilis bakina da jini hancina na jini kaina daga goshi na sun fasamin har da masu tsigemin gashin kaina.
Sun samu nasaran balle zaren bra dina ta baya Dalilin da yasa na kwanta a kasa na Rufe kirjina da Hannayena ina wani irin kuka mai Cin rai kamar ba ni ba.
Baban Amna yace"Subhanallah.."
Ramatu ta kwance Noor ta zo ta lullunbamin zanin goyon nata Adda Fati kuma ta cire hijabinta ta Dagoni ta sakamin ta na kuka.
Baban Amna yace"Meke faruwa ne?miye haka..?
Nan zainab ta shiga warware masa komai ta karishe da fad'in"Ladidi fa ta kama sai da muka sakata ta tsallaketa sau uku sai ga shi ta tashi."
Ladidi cikin mamaki tace"Ni fa Inaga Lalurata ce ta tashi. Ina da Aljanu kuma suna yawan bugeni na Fad'i."
Sai wajen ya yi shuru.
Baban Amna yace"fisabillahi me ye haka.? Sai ku ce ta tafi gida menene amfanin wannan tozarcin?
Ni dai kuka kawai na ke yi, Ramatu ta kalli Inna Talatu ta na Fad'in"Inna Nura yazo zan tafi da Hasiya na wuce da ita gidana.?
Inna Talatu tace"Eh kada ta koma ta tadama Amma hankali kuje chan gidan ki kawai."
Ta amsa da Toh Adda Fati da Habiba suka taikamin na tashi zanin goyon noor na yi Daure gaba da shi, na saka Hijabin Adda Fati dakyar na ke tafiya Fuskata ta Suntuma saboda duka.
Adda Rukkaya kuwa fad'i ta ke yi"Wlh ni kuka Tozarta. Ba dai ni zaku yi ma wannan Tozarcin ba.!
Ta ke fad'a cikin Tsawa da karaji. Ba wanda ya kulata sai mijinta da ke ta ce ma Inna talatu ayi hakuri.
Ko tankashi ba wanda ya yi tunda yana mganar da an koreni ne ba sai an Dakeni ba kenan shima ya amince da komai da ake fad'a kaina.
Nura da mai adaidata yazo Tunda Ramatu tace yazo da abun hawa.
Nura sai sallalami ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login