Showing 21001 words to 24000 words out of 93195 words
Chapter 8 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt
ta ke iya tafiya, Kanta gabad'aya ba baki sai Furfura. Fuska duk ta tamuke sai dai Fatar taushi da hutu tare da jin Dadi ammh mganar gaskiya Inanni zata bama Chasa'una baya.
Umma ta tsorata da taga Inanni na kuka yarkace yarkace. Da Sauri ta riko hannunta tana fad'in"Ga ni nan Inanni lafiya? Ko yunwa kike ji ne?
Domin a tunanin Umma, Hajiya mama bata kai ma Innnani abun karyawanta ba. Tunda yau lahadi megidan na nan kuma ba da wuri suke karyawa ba. Tasan Innani da abinci kamar mai tsotsan ciki.
Shashenta baya rabo da abinci har cikin Dare sai ta tashi in ba abinci ta fashe da kuka.
Innani jin Muryan Umma sai taji sanyi ammh jin Abunda tace ne yasa ta kwace hannunta tana fadin"Matsa ba ni waje. Hala bani da aiki ne sai cin abinci kamar wata tsutsa!? Ana ta rai mai Daraja wa ke ta abinci?
Umma ta sauke muryanta kasa tana Fadin"Yi hakuri Innani mu je ciki sai ki fad'amin me ke faruwa?
Ta fad'a tana kokarin kamo Sandan hannun Inanni, ganin haka yasa Innani ta turje tana fad'in"Ina naga ta shiga ciki Salamatu? Ina nan tsaye har sai Sulaimanu ya fito"
Umma ta kalleta cikin mamaki kafin tace"Wani abu ne ya faru Innani?
Sai kawai Innani ta kalli Umma ta faahe da kuka da karfi tana Fad'in"Ina zan iya fada miki. Ai sai hankalin ki ya tashi bari dai shi Sulaimanun yazo shi Tunda namiji ne ya na da Dakiya zai iya saurarana"
Kafin Umma tace wani abu Mallam Tajuddeen maigadi ya zo in da suke da Sauri yana fad'in"Subhanallah Hajiya lafiya kuwa?
Ya fad'a yana kallon Inanni cikin damuwa ganin tana kuka, duk da kukan Innani in dai kana gidan Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi to ya zame maka jiki. Innani ko kallonta ka yi in bai yi mata ta ga daman ta fashe da kuka.
Innani na jin muryan Mallam Tajudden ta watsake ta daina kuka Umma ko ce masa tayi"Bakomai Mallam. Koma bakin aikin ka kawai"
Har ya juya Inanni tace"Ya koma ina Salamatu? Ai gwara ya tsaya in Sulaimanu ya fito aji in dole sai an had'a da ayoyin Allah. Mallam Saju tsaya tsaya Sulaimanu ya fito"
Umma ta rike haba cikin mamaki kafin tace"Innani Abban Su siyama fa bai fito ba! Ko kin kirashi ne?
Innani tace"Na aika yarinyar taki Sulsana ta taso min shi. Ina ya ga ta barci Magajin gida gabad'aya ba'asan inda ya ke ba"
Umma ta bude baki, kafin ta rufe Mallam Tajudden ya kalleta ta kalleshi kafin ta juya tana kallon Inanni da ke fad'in"Wai ina Sulaimanun ne? Kaji min watsewa ni Dije ni uwarsa ma na taso kan kafafuna shi uwar me ya ke yi da bai fito ba har yanzu? Kada fa na zama uwar banza ne yasa ban je har shashen na shi na taddo shi ba, na tsaya a bangaran salamatu"
Sai da Umma ta Murmusa kafin tace"Innani wata Sultanan? Sultanan da ke cikin daki tun dazu?
Da wani kallon Innani ta bita da shi kafin ta yi kwafa tace"Lalle ja'irar yarinyar nan da ni take mgana. Tunda taki zuwa ke uwarta je ki taso min Sulaiman."
Umma ta yi kokarin riko Innani tana Fadin"Mu shiga ciki Innani. Magajin gida kuma lafiyansa kalau. Kin manta yana Zariya yaje makaranta?
Innani ta yi shuru alamun Nazari kafin tace"Tsakaninki ga Allah Salamatu kwananki nawa baki yi mgana da Magajin Gida ba?
Umma tace"Na yi mgana da shi jiya ma Innani"
Innani ta kalleta kafin tace"Sai kin Rantse zan yarda da ke Salamatu."
Umma ta yi mirmishi Tana kallon Mallam Tajuddeen. Wanda ya juya shima yana mirmishin Diraman Innani da mutum ba ya gajiya da Dariya.
Umma sai da ta rantse sannan Innani ta amince da ita ta shiga Shashenta.
Ta zauna kan kujera ta na share hawaye da Haban dankwalin kanta.
Umma ta zauna gefenta ta ja Haban zaninta mai kyau da Tsada tana Share ma Innani hawaye cikin Sigan lallashi ta ke fad'in"Ki yi hakuri Innani. Magajin gida yana nan lafiya zai zo ya ganki kwananan in sha Allahu"
Innani ta yi mirmishi kafin tace"Shikenan tunda kin tabbatar da yana lafiya. Ni daman rashin samun sa ta wayar zamanin nan ne ya Dagamin Hankali. Ammh tunda ke uwarsa kin tabbatar da yana lafiya ba ni da tacewa"
Umma ta yi mirmishi kafin tace"Yana lafiya Innani in sha Allahu. Zan kuma sa ya kiraki in sha Allahu.
Innani ta gyada kai batace komai ba. Umma ta mike tana fad'in"Innani me zaki ci in kawo miki?
Innani ta yamutsa fuska kafin tace"Na riga na ci goro salamatu zauna abun ki. Nagode sosai Allah ya shirya miki zuru'a, yadda kike kula da lamarina kema Allah ya shiga lamarin ki"
Umma ta mike ta na ta amsawa da Ameem Ameen.
Duk da yadda Inanni ta ke da Tsine Tsine akwai saka albarka da kyawawan addu'o'' a bakinta. Umma kitchen taje ta hado abun karyawan su,Ta leka da kanta ta kira Sultana wacce har ta yi wanka ta saka Doguwar riga baka. Kai tsaye tace"Kina Fiki fiki da ido. Sai ki fito mu karya"
Dakyar ta fito tana Tafiya sannu Sannu taki dagowa su had'a ido da Inanni, ita ko sai faman Hararanta ta ke yi tana kyafci. Umma na kallon su tana Dariya. Bata yi mgana ba sai da Innani ta tabe baki tace"Bar wani rabe rabe. Kiyuwa ko? Kin koyi bakar Dabi'a wajen yaran chan na Suwaiba kamar ni na aike ki ki k'i zuwa ko?
Sultana ta zauna ta rab'e bayan Umma tana fadin"ki yi hakuri Innani"
Innani ta washe baki kafin tace"Me kika yi min yar nan? Ke dai bari Uwar ki tace magajin gida na lafiya. Ni daman lafiyarsa ya dameni in ta ni ce ai Sulaimanu ya kwana ya na barcin asara Mutumin banza kawai zai ce duk koken koken da nayi bai ji ba ne Salamatu?
Umma na Had'a tea tace"Bai ji Ba Innani. In da yaji kinsan zai fito shi da baya son ganin ki cikin damuwa."
Innani ta tabe baki bata kara mgana ba, sai dai Umma na janta da mgana Jefi jefi.
Suna gama karyawan Sultana ta kwashe komai zuwa kitchen. Daganan tana fitowa ta koma Daki ta dauki aikin makarantarsu tana Dubawa. Umma da Innani na Falo sun tsinke da Hira.
daga dakin tana jin muryan Innani a sama tana mgana da Anty Surayya sai faman bude murya ta ke yi.
Sultana ta Dafe kanta a fili ta Furta"Innani Hayaniya da kanta"
*****
Alhaji Sulaaiman Abubakar Shinkafi Bakin Dattijo Dogo baki. Ya yi sallama Shashen Hajiya Umma, Bayansa kuma Hajiya Mama ce Farar mace alkyabban mata.
Ta ci kwalliya sai faman tashin kamshi take yi. Suna tafe, wasu yara guda biyu mace da Namiji suna bin su a baya.
Da sallama suka shigo falon. Shashen Innani suka fara isa bata nan. Su san ba inda zasu sameta sai Shashen Hajiya Umma. Shiyasa suka garzayo da sauri.
Umma ce ta mike tana musu sannu da zuwa cikin natsuwa tace"Abban su siyama barka da Safiya.! Ina kwana Maman yara?
Afiya Gud mrning"
Umma ta fad'a ta na rike yar mace ajikinta. Namijin ya karisa gabanta tana fad'in"Umma"
Kansa ta shafa tana fad'in"Abadallah bawan Allah"
Wacce aka kira da Maman yara ta saki fuska sosai ganin Umma cikin Dariya tace"Hajiya Umma mun tashi lafiya? Ya kwanan Sultana?
Umma tace"Sai hamdala ya kwanan su Abdallah?
Mama tace"Ga su nan rigiman mu. Su Salima sun fara tsuwwaa sun gaji da su a maida su gidan su"
Umma na dariya tace" Nan ma ai gidan su ne. Ban da abun su salima."
Matan kadai ke hiran su Alhaji Sulaiman ya gurfana gaban Inanni yana gaisheta.
Sai da ta dafa kanshi Sannan ta amsa lokaci d'aya tana fadin"Allah ya yi maka albarka Sulaimanu. Allah ya albarkaci samun ka,da arzikin ka. Ya raya maka zuru'a ya shirya maka su. Allah ya tsole idon makiya a kan ka yarona."
Cikin jin dad'i ya ke ta amsawa'"Ameen Ameem Innani."
Sannan ya koma gefenta ya zauna yana gyara zaman shaddan jikinsa. Inanni kasa kasa take kallon Mama ganin haka yasa itama ta bi bayan mijinta ta zube tana gaisheta ta amsa a Kirne kafin tace"Yaran ki hala basu gidan nan ne Suwaiba?
Mama ta dago tana fad'in"Suna nan Mana Innani. Da Safe ma ai Siyama ce ta kawo miki abun karyawan ki"
Innani ta tabe baki kafin tace"Au ita ce? Ai ba ta jira na ganta ba afalo ta Damkwafar min da shi ta kara gaba."
Mama kanta na kasa tace"ki yi hakuri Innani zan yi musu mgana za su gyara."
Innani ta kauda kai ta maida wajen Danta da ke wasa da jikokinsa,Takaici ya isheta shi kuma ganin haka yasa da Sauri ya tura su gabanta yana fadin"Ku je ku gaishe da Inanni"
Gabanta suka tsaya suna kallonta. Ta dafa kan Afiya tana fadin"Yaran nan yaushe zasu koma gidan Uban su ne?
Falon shuru ya yi daga Umma har Mama an rasa mai mgana sai Abba ne ya yi gyaran murya kafin yace"Sa'imar ba su dawo ba ne. Da sun dawo zata zo ta Dauke su ko Sauwaiba?
Mama tace"Eh Innani da zarar sun dawo zata zo ta Dauke su'
Innani ta kallesu tsab har ta na wani gyara zaman gilashinta kafin ta tabe baki tace"ai shikenan.
Sulaimanu nace baka ji kuka na ba ne yau?
Da Sauri yace"Subhanallah me ya faru Innani?
Innani tace"To magajin gida ne ban ji sa ba kwana biyu. sai hankalina ya tashi na zata ko ya fad'a hannun banza ne, Sai da salamatu ta lallashe ni da cewa sun yi mgana sannan na yarda itama sai da ta rantse na yarda kasan karya ba ta da wuya a wajen Babba."
Abba ya nmurmusa kafin yace"Ya na nan lafiya Inanni. Jiya da Daddare ma mun yi mgana"
Innani tace"Shikenan tunda yana lafiya. Sati mai zuwa na fasa zuwa sha'anin nan na yar gidan Sammani Wajen jika na zani na gansa ko Hankalina ya kwanta"
Abba ya kalli Matansa suka kallesa sigina ya yi ma Umma shiyasa ta gyara zama tana fad'in"A'a Inanni ai basai kin je ba. Da kanshi zai zo ya ganki"
Innani ta yi shuru ta na kallonta ta cikin gilashinta kafin tace"In ma bai zo ba ke kika sani Salamatu. Alhakin rashin zuwa Duba magajin gida na kanki"
Umma na mirmishi tace"shikenan innani.
Sai kuma ta juya tana mgana da Abba kan bikin diyar kaninsa Sammani da za'ayi a Shinkafi Sati na sama Innani tace ita zata wakilceshi ba sai yaje ba.
Abba na fad'in"Innani tare zamu. Ina so na samu Daurin aure"
Kai tsaye tace"To da an gama Daurin auran ka dawo gida kaji ma na Fad'a maka"
Mirmishi ya yi kafin yace"Naji Innani."
Umma na jin su duk da Hankalinta na wajen su Afiya, sannan suna taba Hira da Mama. Sai dai ita tasan Dalilin Innani saboda kada yan'uwa su gansu su kawo bukatotunsu ba ta son D'anta na fitar da kudi. Abunda Inanni bata sani ba ko mako da son kudi Alhaji Sulaiman Shinkafi ya fita.
Mutum d'aya ne shi kadai jalli Tal ke iya saka shi fitar da kudi ko da bai yi niyya ba. Kuma shi ke iya yanke Hukuncin da Ko Innani bata isa ta ce A'a ba ballatana shi.
Innani mikewa ta yi tace zata koma Shashenta ta kwanta Harkarkarinta na ciwo. Abba Da Umma har Mama suka mike suna rawan jikin kamata. Abba ya rike mata Hannu Umma ta kama Sandarta. Ita kuma Mama tabi bayansu bayan tace ma su Afiya su zauna su dawo. Ko da batayi niyya ba dole ta raka su in ba Haka ba yanzu Innani zata hau ta kanta ta zauna.
Suna fita Haraban gidan Haushin kare Huhuhuu!!!
Innani ta razani ta kamkame Abba tana Fad'in"Innalillahi ni Dije? Yanzu daman Sulaimanu baka fita da wad'anan bakaken Halitun da ke Firgitani mutane da makota ba? Har ni uwarka suna hanani barci. Nan fa na gayama mala'ikun Allah basa ta kan mu tunda ka ke ijiye karnuka a cikin gidan ka"
Cikin ladabi yace"Inanni ai sabo gadi ne, kinsan irin Sana'ata"
Kai tsaye tace"Ka ci uwaka kai da sana'ar taka. Allah dai ya tsine ma wad'anan karnukan gabadaya"
Umma na Danne Dariyanta tace"Innani Kin manta Magajin gida yace miki a bar su yana so"
Nan da nan Innani tace"An yi haka kin ga ko na sha'afa salamatu. Sulaiman to kaji Magajin gida yace yana so. Kuma tunda magajin gida yace yana so an gama mgana maza ka barsu, sannan a rika basu abinci kada ya dawo kuma yaga an yi masa ba Daidai ba."
Kai tsaye yace"In sha Allahu Innani."
Yana mirmishi. Mama na baya sai bata rai take yi, har shashenta suka rakata nan din ma sai da suka gurfana gabanta har sai da tace su je su barta zata kwanta huta.
Dalilin da yasa suka yi mata sallama kenan suka fita.
Yau lahadi ce daman a ka'idan Alhaji Sulaiman akan had'u a falon Shashen sa shi da matansa su yi su tattaunawa yaji matsalolinsu.
Yau ma shashen nasa suka wuce bayan Mama ta koma Falon Hajiya Umma ta damkama Sultana su Afiya ta fice ta barta tana Tura baki.
Sam bata son Hayaniya gashi kuma Mama ta had'ata da wad'anan yaran.
Alhalin su Salima na chan kwance suna hutawarsu.
Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086
*Janafty*
*Sep 09/2023*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
+201123302418
Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086
*06*
*Zaria*
Samaru_Tsamiya.
8:11am.
A cikin anguwan samaru Layin Tsamiya, Ire iren gidajen su na b'arayin wajen zaku ga akwai d'akuna a waje saboda anguwa ce ta yan makaranta, Makaranta kuma Babba a Africa wato ABU ZARIA.
Ko bayan makaranta akwai y'an kasuwa da masu huldar arziki da neman na kansu, iren iren gidajen wajen duk akwai dakunan a waje domin ba da Haya na maza matasan yan makaranta.
A irin hakane na hango wani gida mai Damdamali a kofar gidan har da Rumfa sai Dakunan waje jere a layi Guda biyar, Daga gefe har da makewayin su na lalura.
Gidan na marasa karfi ne ammh kuma bai lalace sosai ba, yanzu haka kila ma megidan ya rasu dakunan magada ne.
Dakunan duka suna Rufe ne,Sai guda d'aya na farko ne a bud'e har da Labule, Kai tsaye sai ga wani Dogon Saurayi ya fito Sanye da kayan yan Bautar kasa completed, a jikinsa Farar Riga da Green din wando,sai Falmaran din su Green sai Facin cap itama kalan green mai haske.
Kafarsa sanye da Booth din takalminsu mai ruwan goro. Bayansa goye da wata Bakar Jaka karama ta baya.
Dukawa ya yi yana kara tamke igiyan takalminsa duk da yana Duke ne ammh Dole za'a kirasa ingarman Namiji Tunda ya had'a tsawo da Fad'i na Budewar cikakkun maza.
Ya nan nan a duke Wani farin Saurayi ya sake Fitowa daga Dakin shima da irin shigar sak, Daga gani ni masu yi ma kasa Hidima ne ma'ana Corpers.
Kofar Dakin ya Rufe ya saka makullin yana kullewa lokaci d'aya yana fadi'n"Hala yau tafiyar kasa zaka yi?
Ya fad'a daidai Lokacin da ya gama kulle Dakin, Shima yana da jakar baya kalan kayansa wato green. Sai ya kara gyara zamanta a saman kafad'ansa na Hannun Dama Key din kuma sai ya zura a aljihun wandonsa.
Wanda ke duke kuma bai tankasa ba,Illah cigaba da tamke igiyoyin takalminsa da ya yi, na tsayen ya kara kallonsa lokaci d'aya ya duba Bakin agogon Fatan da ke hannunsa cikin Kosawa yace"Mallam mun fa makara. Ka tsaya sai faman tamke igiyoyin takalmi ka ke yi."
Sai a lokacin ya mike yana kara Dage wandonsa sama har ana ganin sawowin kafarsa mai cike da gargasa ga su nan duk sun kwanta. kai tsaye ya kai duban shi kan agogon Silban da ke hannunsa 8:20am na safe kuma ya kamata By now ya isa inda zashi.
Yana shirin mgana wayarsa da ke aljihun wandonsa ta Dauki Vibration alamun ana kiran shi,Hannu ya saka ya ciro wayar yana duba mai kiran duk da yasan Daga gida ne, Tunda itace wayarsa da kowa ya san layin. Babbar waya ta makaranta ce da aiki ba kowa ya san shi da ita ba.
Sunan UMMA da ya gani ne yasa ya yi kasake shi bai dauki wayar ba, shi kuma bai maidata aljihu ba.
Saurayin da ke bayansa ya yi Dage tunda ya fishi tsawo ya leka yana Fad'in"Waye ke kira?
Ko SULTANA ce?
Da sauri ya kauce bayan ya jimke a wayar a hannunsa yana sauke numfashi, Dariya na gefensa ya saka kafin yace"Yarinyar nan na bala'in ji da kai, tana kulawa dakai kai kuma ga shi ban ga kana kula da ita ba"
"Tahir..."
Muryansa cikin Kaushi da asset din Zamfaranci acikinta ta katse Tahir da ke masa Tsiya. Rai ya bata kafin yace'Tahir me? Ba gaskiya na Fad'a ba. Ina fa lura da kai tun satin nan ta ke kiran ka da wayar Umma ba ka Dauka"
Mirmishi ya saki kafin ya juyo suna kallon juna. Fuskarsa Ma'abociyar Haiba da zati ta bayyana, Baki ne mai ruwan kalan haske doguwar Fuska garesa Dauke da Dogon Hanci da idanuwansa matsaikata. Yana da Zagayyen Saje da gemunsa baki Suluf Cikin Yanayin Mganarsa ta cikakkun maza yace"Au ashe? wa ya saka ka