Showing 18001 words to 21000 words out of 93195 words

Chapter 7 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11452

cikin cokali ya isa mai Hankali wanka"


Sum sum ta yi ta kai ta fara ba ma Amma Hakuri ganin ranta ya baci yasa har ta jima agidan, ganin har da yaranta suka zo yasa na yi jallop din shinkafa da rana mai allayahu yaranta ta koya musu bakin Halinta ko cin abinci ba su yi sun raina.
Amma ko har ta tafi bata kara kallonta ba, Kunya taji ta zaro dubi biyu ajaka ta sauke Gaban Amma tana Fadin"Amma ku kara wlh Baban su Amna ne ba su yi albashi ba."
A ciki Amma ta amsa da cewa"Allah ya ba da lada"
Har ja ya'yanta suka fice Amma bata kalleta ba ni ce ma ma aiki Habiba ta siyoma yaran Biskit, a rene Adda Rukayya ta amsa ba ko Nagode ni kuma bai dameni ba saboda nasan Har Abada Adda Rukayya ba ta isa ta sauya jinin da ke Tsakanina da ita ba
Ashe taji Haushin mganar Amma ta taka har Gidan Adda Fati ta na Fad'amata tazo Amma ta rufeta da Fad'a sabo da ni. Sannan har su Anma ba ta ja ajiki ba ta na jin haushinta domin ta kawo mafita.
Har ta na fad'in"Fati nima fa ina son Hasiya ai kanwatace kamar yadda ta ke kanwarki. Bana jin dadin zarge zargen da ke kanta ne, ni wlh ina mata Fatan Rayuwa mai kyau in ta koma gaban Adda Hari"
Adda Fati dai ta bata baki, ammh ta rike Amma ta ki kula ya'yanta Saboda ni,ita kuma tana so na ne ta nemar min mafita da Adda tazo tana gayama Amma,vkyafci ta yi kafin tace"Fati bar ni da Rukkyya Mutuniyar wofi ce. Ta zabi miji da danginsa da mutanen Duniya akan uwarta da danginta. Ba inda zamu koma tunda ba mu gagara lallaba rayuwarmu anan ba Fati. Adda ba shi gareta ba karfin Hali ne bazan kwashi jiki na koma na D'orata mata nauyi ita da ya'yanta ba. Sannan bazan bar Hasiya ta koma ba tunda nan aka Haifeta akwai nakasu in har na ce ta koma chan da zama"
Da haka Amma ta kashe mganar komawata wajen Adda, da Addan ta kira ce mata kawai ta yi"Adda zan zo dai na miki kwana biyu gabadayanmu in Habi ta yi Hutun makaranta in sha Allahu" Adda bata damu ba tace tana jiran mu duk sanda muka zo.
Tundaga Lokacin Adda Rukayya ba ta kara ma Amma mganar ba ko ta zo gidan sai ta koya ma kanta kame bakinta.
Ni ko na kama mutumcin kaina Daga gaisuwa ba na shige mata Hankalina na kan sana'ar da muke ci da kanmu da Rufin asirin mu, tare da Kula da Amma cikin wattani uku duk abubuwanan suka faru sai abunda ya Faru na aurena da Salisu ya lafa tunda har ina Fita Diban ruwa ko zuwa kasuwa ko chemist siyo mgani. Ba fargaba tunda daman abun na Lokaci d'aya ne yana wucewa shikenan kamar komai bai Faru ba.
A bakin Mutanen gidanmu naji Salisu ya dawo gida an saka masa karafa a kafafunsa na Dori da Karafan asibiti guda biyu ya ke tafiya.
Ammh duk bayan wata daya suna komawa sannan ana masa Dressing a gida.
Ni dai nawa yi masa fatan alheri da Fatan samun waraka komai tsakanina da shi ya jima da karewa kamar bai faru ba.
Na kuma tabbata daga kan Salisu kila na gama aure tunda yanzu dai ko daga nesa wani ya zo da sunan aure na, zuwa daya zai yi bazai kara Dawowa ba tunda za'a karanta masa komai a kaina har da karin gishiri da maggi.
Nasan kaddara ce ko in ce Jarabawata ce haka.
Ammh ban taba Tunanin Wata Kaddaran zata sake bibiyata nan kusa ba.
Bani kuma da masaniyar zanen kaddara ta na kusa da ni ban sani ba.




Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da Ciwan sanyi duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086




*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*








*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*


https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk


Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.


*05*


*GUSAU_ZAMFARA.*
_Area:Tudun wada_
*Lahadi, 10:40am*


"Wai wani shegen ne ke min burutun a shashe na da Safiyar Allah nan?
Ta fad'a cikin kufula da takaicin yadda aka maida ita banza tana ta mgana ita kad'ai.
Kokarin mikewa take daga zaunen da take lokaci d'aya tana Laluban sandar ta, tana cigaba da fad'in"Ko wani d'an jakar uba ne ya bari na fito mu ga juna yau sai na Deb'e masa albarka"
Ta samu mikewa kan kafafunta, ta kuma samu nasaran ganin Sandarta ta karfe a gefenta sai dai kamar akwai sauran rina akaba, tunda sai faman lalube take yi kamar ganinta na da rauni.
Garin lalubenta ne hannunta ya kai kan wani bakin gilashi ta dauko shi tana fad'in'"kaji rashin tabbas na Abun nasara yanzu gilashi na fuskata na nemesa na rasa. Mtswww aikin banza da wofi"
Bum! Taji kamar an fad'o dakin nata a rashin sukuni a zafafe ta saka gilashin nata cikin Masifarta da tun tana matashiyarta ya zame jiki har tsufanta tace"Nace wai waye zai zo ya Dameni da burumtu ne? To ko waye in bai yi mgana ba Allah ya tsinee..."

"Innani ni ce".


A kafad'a da wata sanyayyiyar murya mai cike da yarinta da kuruciya. Wacce aka kira da Innani ta d'ago kanta a masifan ce tana yamutsa Tace"Ke ce wa? Baki da suna ne? Ina na ke iya gane muryoyin yaran gidan Sulaimanu, ku rika wani make murya kamar wasu ya'yan gyare"
Ta fad'a lokaci d'aya ta na kara gyara zaman gilashin da ke fuskarta sosai ya cika mata fuska kir kuma ta sauke ganinta kan yar yarinyar dake gabanta sanye da Hijabi mai ruwan kasa. Kanta na kasa tana wasa da yatsun hannunta.


"Sultana ce. Sultana ce Innani"


Baki Innani ta washe kafin tace"Au ki ce Sulsana ce ta wajen Salamatu ko nace Matar MAGAJIN GIDA. uwargida Sarautar mata a gidan Abubakar Saddiqu alkawarin Allah sai ya cika da yardan Allah, ya ki nan yar nan taho ki zauna kusa da ni"
Ta fad'a tana ya fito ta da Hannu. Jikinta kamar ba karfi ko na ce wacce ta tashi matsananciyar jinya ta karisa gefen Innani ta zauna. Innani ta gyara zama tana fad'in"Ke kam ki rika kama jikin ki mana Sulsana. Ayi mace kamar wahainiya saboda rashin kuzari"
Ita dai kanzil bata kara ce mata ba, kanta na kasa tana wasa da yatsun hannayentaa. Innani ta kara kallonta cikin nazarinta kafin tace"Daman kece kika zo kina min bare bare a sasana? Tsiyana da ke wauta ko rashin wayau ne ma zan ce ni Dije? Ayi yarinya sai shegen tsoron mutane. Allah dai ya yaye miki kin ji ko"
Wannan karon ne ta murmusa ammah ba tayi mgana ba, ganin haka yasa Innani ta washe wawulan bakinta da babu Hakora ko d'aya duka sun gama barewa, Daman na Roba take makalawa in zata ci abinci abubuwa masu tauri kuwa sai dai ta saka wuka ta yi gutsi gutsi da shi, Kwad'ayi ne da Innani komai na Duniya ba bu abunda bata ci. Tace da wuya ta kasheta gwara dad'i ya kasheta.


https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V


Cikin Dariyanta tace"ina lafiyar ita uwar taki? In ji dai lafiyanta lau? Ina shi Baban naku? Tun asuba da ya leko muka gaisa ban kara ganinsa ba."
Muryanta a sanyaye tace"Umma tana lafiya. ABBA kuma yana bangaransa shi da Mama"
Nan da nan Annurin fuskar Inanni ya Dauke ta wani Dauke kai kafin tace"Uhm ko da naji."
Daganan tayi Dif tana faman girgiza sadan dake gefenta. Sultana sai satan kallonta ta ke yi tana danne mirmishinta. Sai jin mangari ta yi a kai lokaci d'aya Innani tace"Munahika yi dariyar taki mana a sarari yarinya sai bakar gulma kamar haihuwar Ssuwaiba.
Da sauri ta kalleta cikin mamaki Lokaci daya tana dafe kanta in da Inanni ta mangareta. Innani ta yayyako mata cikin masifa tace"Miye kuma kike kallona? Ko na fad'a a bakin yan baka ne ko ke ma kin koyi halin ya'yan Suwaiba ne ban sani ba?Allah to ya sauwake kin cuci Salamatu da Sulaimanu domin ba haka suka tarbiyantar dake ba"
Ko gajiya da mgana Innani ba tayi, haka Sultana ke fad'i a cikin ranta.
Mirmishi ta yi kafin tace"Innani.."
Innani ta kalleta batare da tayi mgana ba, ganin Sultana taki mgana sai kuma wasa da gefen hijabinta take yi yasa Innani ta yi tsaki kafin tace"Nace miye ne kika tasani kina faman kiran sunana?
Shuru Sultana taki mgana kanta na kasa sai wasa da gefen hijabinta ta ke yi, Innani tayi sakate kafin ta juya cikin jin haushi goronta da ke cikin wani karamin kwano ta jaho,ta fara yayyankashi a saman tafin hannunta. Chan kasa kasa taji Sultana ta kara kiran sunanta"Innani.."


"Kina kara kiran sunana zan kwad'a miki mari, bar ganin ina raga miki,sai naci mutumcin ki. Yarinya kin zo kin tasani kina faman kiran sunana, kuma ki yi mgana kin ki yi to uban waye shashasha irin ki? Mtswwww.."


Bayan taja tsaki ta cigaba da bambare gorinta tana watsawa cikin bakinta.
Sultana sai kallonta ta ke yi ta kasa mgana sai daga baya ta kara kiran sunanta ta juyo a zafafe da niyyar kara sauke masifarta.
Sultana ta lamgwabe kai lokaci d'aya tana mika mata siririn hannunta cikin Shagwaba tace'"Innani san min goron"
Innani tayi kwafa kafin ta dauko goro karami cikin kwanon gabanta ta dangwara ma Sultana a hannu Lokaci daya tana fadin"Na shige su da kwazzaban ki Sulsana. Wannan yarinya Magajin gida zai yi fama"
Fad'ar sunan yasa dukkansu suka kalli juna Sultana ta kauda kanta. Innani kuma kamar an tunasar da ita ta gyara zama tana fad'in"Ke sulsana kun yi mgana da Magajin gida ko kwanaki nan? Ni wajen kwana uku kenan bana samun sa a waya kuma bai kirani ba, Allah yasa lafiya ina ta zuci zuccin in yi ma Sulaimanun tad'insa sai sha'anin duniya ya mantar da ni."
Da kai sultana ta yi mata mgana da girgiza mata kai alamun itama ba su yi mgana ba. Nan da nan Innani ta kara Harzuka cikin daga murya tace"Ke uwarki. Baki zaki bude ki yi min mgana ba ne
Sultana tace" A'a Innani"
Nan da nan Hankalin Innani ya tashi ta fara salati tana Direwa kafin tace"Wayyo jikana. Yana chan wata uwa duniya ba uwa ba uba. Ba kuma dangi ko wani hali yake ciki? Ke sulsana dubamin wayata cikin daki ki zo ki kara kiramin shi Allah yasa jikana yana lafiya. Magajin Sulaimanu bayan shi ba shi da wani magaji anan duniya"
Ta ke fad'a tana kokarin fashewa da kuka. A sanyaye Sultana ta mike tana wannan tafiyar nata Innani ta kalleta cike da takaici tana fad'in"Zaki yi sauri ko sai na turaki da wannan Sandar ta hannuna? Ta fad'a tana kokarin dauko sandan nata da gudu Sultana ta shige cikin Uwar Dakin Innani, ta fara neman wayar na ta.
Ta duba ko'ina bata gani ba, ga shi daga Falo Innani sai faman kiran ta take yi sai da ta gaji ta fito ammh Daga gefe ta tsaya tana fad'in"Ni fa ban ga wayar taki ba Innani"
Yadda Innani ta kalleta da tana kusa sai ta sha duka da sanda, shiyasa ta tsaya daga baya baya. Tsaki tsaki tsut.!
Kafin tace"Ko ke ma idon naki na da Rauni ne na saka Sulaimanu ya kai ki in da ya kai ni aka ba ni wannan gilashin? Ammh ace waya na barta saman katifar da na kwanta ki zo kina ce min wai baki gani ba?
Ta fad'a tana nuna ta da Sanda,kamar zata daketa. Sultana ta tura baki tana kallon gefen kwanon Innani ga wayar nan kirar kamfanin Tecno karama, ammh tana ta kumfar bakin a saman katifa ta barta. An ci sa'a ne da tana cikin Lalinta ne zata rika bala'i tana tsine tsinen an sace mata waya. Yanzu ma ido ta mutsike tana fad'in"Baki gani ba fa da gaske Sulsana?
Allah dai ya tsine ma barawo da uwar barawo wlh"
Sultana ta zaro ido kafin ta karisa gaban Innani ta duka ta Dauki wayar ta mika mata tana fad'in"Ga fa wayar taki nan a gaban ki Innani"
Innani ta bi hannun Sultana da kallo kafin ta karbi wayar ta jujjuya tana Fadin"Ikon Allah! Ni fa saman katifata na barota. Ni fa daman na dad'e da sanin abun nasara ba shi da tabbas, sai ka ijiye abu ka nemeshi ka rasa sai chan ka ganshi a wani waje mtseww"
Ta karishe da tsaki daman Tsina da Tsaki a bakin Innani Allah ya fissheta kada ta zo mutuwa su kama bakinta.
Sultana ta kara damgwara ma wayar tana Fad'in"Maza kiramin magajin gida. Allah yasa yana hannu nagari."
Sultana ta dukufa kiran Magajin Gida kamar yadda Innani ta saka akayi mata Saving a lambarsa. Itama cikin mazari ta latsa lambar nasa sai dai kuma kuzarinta ya ragu da wayar ta ke kara duui! Sai kuma ta yanke, tayi haka har sau uku duk tafiyar d'aya ce tana ji Innani na fad'in"Kin samu magajin gidan ko?
Ta kasa bata amsa Dagowa ta yi ta kafe Inanni da ido. So ta ke yi ta ce mata ya yi blooking dinta ne,ammh tasan Innani ko za'a shekara bazata gane komai ba. Shiyasa ta mikama Innani wayarta ta ki mgana, da kallon mamaki ta bita baki bude kafin tace"Ke na ce kin samu magajin gidan a waya?
Sultana ganin Innani ta ki karban wayanta sai ta dungure mata a saman cinyarta ta mike tana fad'in"Innani wayarsa ba ta shiga."
Inna ta rafka salati tana fadin"Na shiga uku na lalace ni Dije. Ke kinga Sulsana maza jeki ki gayama Babanku yazo ina nemansa"
Sultana tace"Innani Abba kuma? Barci fa ya ke kinsan yau weekend ne"
Innani ta rarumi sandarta tana fadin"Ko barcin mutuwa ya ke nace ki taso min shi kaji min ja'irar yarinya tabbattaciya. Ba gwara ya tashi da wannan barcin da tashin hankalin da ke Tunkaromu ba, Magajin gidan ne gabadaya ba'a san inda ya ke ba yanzu kai co na Dije, daman wlh ban so tafiyar yaron nan ba, ya lallameni da Kalamansa na bayan ya had'a da su jawomin manyan ayoyin Allah Sai na amince ammh har cikin raina Hankalina bai kwanta ba"
Ta karishe fad'a tana face majina,Sultana ta yi tsaye tana kallonta ganin yadda Lokaci daya ta rikice, To daman ai shi kad'ai ne ke rikitar da Innani sannan kuma cikin Mintina ya ke dawo da ita saiti, wanda ko Abba da ta haifa sai ya Dauki awa Biyar Innani ba ta ji mganarsa ba.
Bata sani ba Inanni ta daga Sandarta sama tana fad'in"Zaki wuce ki taso min shi ko sai na Rafke ki?
Sakarya mara wayau in kina da Tunani da Hankali ai kema abun kukan ne ya same ki, in da kara zama zaki yi mu taru mu tashi gidan da koke koken mu"
Sultana dai da gudu ta fice daga Shashen Inanni tana haki kamar ta yi wani gudun tsere.
Babban gida ne mai shashena biyar,bi da bi, biyun na jikin juna suna da girma,Karamin ne ke chan gefe shashen Innani kenan, wanda ya fi girma gabadaya shine na jikin wani karamin Shashe shima.
Sai da ta tsaya a wajen ta kallah kamar zata ganshi ya fito. Sanin ba Fitowar zai yi ba yasa ta juya ta tunkari shashe guda biyun da suka fi girma.
Na farkon ta bude kofa ta shiga, Sad'af Sad'af kamar barauniya. Ta kawo Tsakiyar Falon taji an ce"Sultana."
Cak ta tsaya ko ba ta juyo ba. Ta san Muryan wacece Umma ce!
Cikin sanyin jikinta na Hallita ta juyo kanta na kasa tana had'e kafafunta alamun ba ta da gaskiya.
Doguwar mace ce,mai dan kaurin jiki baka zaune kan kujera remot a hannunta. Sanye ta ke da Atamfa super aura mai kalan Duhuwa ta ci Daurinta kamar wata matashiya. Alhalin zata ba ma Shekarun Hamsin baya.
Sama da kasa ta kalleta kafin tace"Daga ina kike da sassafe daga tashin ki a barci na duba ki ban ganki ba?
A sanyaye tace'"Shashen Innani na je"
Hajiya Umma ta gyad'a kai kafin tace"Ta na lafiya ko? Da kai ta amsa mata bata damu ba sanin Halinta. Mirmishi ta yi mata kafin tace"Sai ki wuce ki je ki yi wanka ki zo ki mu karya"
Kamar tana jira ta amsa da Toh ta wuce da Sauri Umma ta bita da kallon mamaki a ranta tana Tunanin Saurin me Sultana ke yi haka?
Tunaninta ya tsinke ni Lokacin da taji mganar Innani da karfi tana kwalamata Kira.


"Salamatu.. salamatu.."


Kina ina ne salamatu,?


Zumbur ta mike lokaci d'aya tana watsar da Remot din hannunta. Zata iya banzarta da kiran kowa ammh ba zata iya kyale kiran Innani ba. Uwar mijin da ta yi mata rikon uwar da ta rasa tun a zamanin baya.
Uwar da ta Fifita son da take yi mata sama da d'anta data haifa. Ita ko mai zata saka ma Innani? Ba bu ban da ta rika yi mata Biyayya da yi mata duk abunda take so har ma da wanda ba ta ce tana so ba. Da sauri ta fita daga Falon a kofar shigowa suka ci karo da Inanni ta fito tana dogara sandarta.
Kai wannan tsohuwa da Jaraba ta ke, ta tsufa har ta duke sai ma da taimakon sanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login