Showing 9001 words to 12000 words out of 93195 words

Chapter 4 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt

Janafty   

10 Jul 2024

11456

kofar gida. Daman tunda naji ance Musabahu na kira na na saka faruwar abubuwa Biyu zuwa gareni.
Ina fita kuwa dayan da na saka ne ya faru Takarda ya mikomin cikin sanyin jiki na saka hannu na karb'a tunkafin na Bude na san me ke ciki ba wannan ne karo na farko, da na taba amsar irin ta ba.
Karfin halina Musbahu ya gani yasa ya ce"Kiyi hakuri Hasiya..Kiyi hakuri iya shi kawai zan iya ce miki.
Ammh ki sani Salisu ba shi da laifi har ga Allah fin karfinsa akayi"
Mirmishi nayi mai ciwo kafin nace"Bakomai Musabahu. Ka gaishe shi Allah ya bashi lafiya"
Ya amsa da Ameen kafin yace"Yanzu zamu dauki hanyar kano."
Na jinjina kai ina musu fatan Sauka lafiya.
Har na shiga Dakin Amma bata Fahimci yanayina ba, ko bud'e takardan ban yi ba. Na turata cikin jakata ta ajiyan karikitai. Na fita tsakar gida na samu Habiba na Hura gawayi zata Damama Amma koko.
Sai na Leka dakin Maman Boy nace ta aramin wayarta.
Ta dauka ta bani chan wajen bayi naje na saka lambar Adda Fati da na riga na Haddace na kirata ta na Dauka nace"Adda fati Hasiya ce!
Ban jira cewarta ba na cigaba da fadin"ki kira Inna talatu kuje ku yi mganar kwaso kayana gidan Salisu.
Saboda ya sake ni d'aazu"
Ina jin ta fara salati na yanke kiran. Lambar Ramatu na saka na kirata sai kudin suka kare ashe ya shiga sai ga shi ta biyo bayan kiran.
Ina Dauka ko cewarta ban jira ba nace"Ramatu shima Salisu ya sake ni"
Cikin Firgici Ramatu tace"Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Kina ina ne?
Ina danne kukan da naji ya tasomin nace"Ina gida. Wayar maman boy ce"
Kashe wayar nayi saboda Duhu naji yana mamaye ganina.
Ina juyowa muka had'a ido da Kaltume itama matar gidanmu ce tana kallona da alamu ta gama labemin taji duka mganata.
Cikin son gulma tace"Ba dai shima Salisun sakin ki ya yi ba?
Da kai na amsa mata. Ba na son kwakwazonta yasa na wuce ko kafin na kai Dakin ta fasa kururuwa tana Fadin"Shikenan shima Salisun ya saki Hasiya"
Salisu ya saki Hasiya"
Wancan ta karba wanchan ta karb'a har kunnen Amma.
Ina shiga Dakin tace"Zo nan Hasiya"
Ina kauce ma kallonta na zo na zauna agabanta. Cikin kallona tace"Salisu ya sake ki?
Kai na gyad'a mata ban yi mgana kawai sai ta ce"Saki nawa ne?
Ba musu na mike naje na Dauko Takardan na mikamata Ammi,tayi karatun boko da na addini. Kai tsaye ta warware takardan ta karanta kafin ta ninketa yadda take. Ni ta kallah cikin nazarina kafin tace"Allah yasa haka shi yafi zama alheri gareki damu gabad'aya Hasiya"
Ciki ciki na amsa mata da Ameen kafin nace"Na kira Adda Fati,da Ramatu na fad'a musu"
Kai Amma ta jinjina min kawai ni kuma sai ma mike na fice.
Duk suna Tsakar gida kamar jimamin gaske suke yi na mikama Maman Boy wayarta na juya na koma Daki.
Sai na tsiri gyara jakar kayana ina jin abunda ke sukan raina ya na tab'a har kashin bayana.
Da gaske kenan abunda mutane ke fad'a a kaina ya tabbata?
Tabbas ina da Farar kafa.
Sannan zamana ko rab'ar mutane ba alheri ba ne.
Salisu da Abubakar sun shud'e daga Duniyata gab'adaya, sun zama Tarihi kamar ma ba'a yi su ba.
Sun shud'e saboda ba su ne daman Mahadin kaddaran ki ba HASIYA.!


*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*










*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA..!*


*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabooks:JamilaUmarjanafty*


https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk


Ku zo ku yi sayayyarku tare da Yar Gidan Imam, inda za ku sami komai cikin sauki, tun daga kan kayan kicin, kayan yara,atamfofi da lesissika uwa uba da kayan gyaran jiki irin na manyan matan da suka San kan su,har counselling mu na yi yadda duk damuwar da ki ke ciki a game da aurenki da gyaran jikinki zaki samu solution. Ku dai ku shigo cikin wannan gidan na karamci kai tsaye domin more tagomashin da ke ciki.




*03*


Sunana Hasiya Mamman kona, sunan mahaifiyata kuma Aisha-Jari. Bafullatar Garin gadan mallam mamman da ke hanyar Abuja.
Mahaifina Alhaji Mamman Haifaffan garin zariya ne dake jahar kaduna, a cikin kuma tsangayar zariya wato anguwan limancin kona.
Sunan mahaifin shi wato kakanmu kenan wanda shine asalin Tushen mu, Alhaji Mammadi Mamman kona. Shima tun asalin tale talen iyaye iyayen su haifaffun garin zariyan ne ma'ana gaba da baya jinin zazzagawa ne su d'in.
Alhaji Mammadi Mamman kona Manomi ne kuma sannan masaki ne yana dinkin Sakan aikin hannu na manyan mutane har da sarakuna. Sannan yana saka hula shima na hannu kala kala, Dalilin da yasa ya yi suna shine Aikin hannu da kuma Hulan da ya kan saka ma manyan mutane da Sarakun gidan Sarautar zazzau.
shiyasa duk wanda ke garin zariya ya san tarihin tsohon gida na Alhaji Mammadi mamman kona. Tunda a zamaninsa da kudin Sakan sa yaje makka sannan ya mallaki gida kuma ya auri mataye har guda biyu a rana d'aya. Salamatu da Lauratu sune matan na shi suma kuma duka haifaffun garin zariya ne.
Kafin rasuwarsa ya tara ya'ya goma cif,Lauratu ke da Hud'u. Salamatu ita tayi shida, ciki har da mahaifin mu wanda aka maida masa sunan Muhammad, sai a ke kiransa Mamman kamar yadda sunan ya ke. Alhaji Tanko ne Babba sai Mamman, sai Hasiya, akwai muhammad Sani, Hajara sai Halima ita ce karamar su wacce yanzu haka take aure a garin ikko tana zaune tare da iyalanta da mijinta.
D'akin Lauratu kuma akwai Jibril shine Babba yanzu haka kuma yana nan da Ranshi yana aiki da babbar ma'aikata a kaduna sai Saratu, Goggon Kona kenan itama tana da ranta a garin zariya sai Saminu da Muhammad Auwal shi yana saurayi ma ya rasu ko aure bai kai ga yi ba.
Labarin mahaifina na ke baku, ammh zan tabo bangaran dangin babanmu ne saboda kusan ta ko'ina cikin gata na taso kafin tsaka mai wuyar da nake ciki ta jefani ni da iyayena da yan'uwana cikin halin k'ak'ani k'ani.
Babanmu Alhaji Mamman kona, ya yi karatun boko zuwa na arabi tunda Mahaifinsu mutum ne mai yalwata ma iyalansa kafin mutuwarsa. Ya yi kokarin had'e kan iyalansa kafin mutuwarsa kuma Alhamdulillah a lokacin kawunansu a had'e suke kafin mutuwarsa ta yi sanadiyar tarwatsa komai.
Tun bayan rasuwarsa aka raba iya abunda ya bari kowacce taja barayinta ita da ya'yanta daga lokacin sai zumunci ya samu Rauni, kowacce ita tayi fad'i tashin ta ita da ya'yan da aka mutu aka bar mata. Ita lauratu da ya'yanta su suka ci wannan gida na limancin kona,ita kuma salaamatu ta samu na anguwan Madaka itama tare da ya'yanta. Shiyasa sai kowacce ta koma inda ya'yanta da ita kanta suka gada suka zauna. Daga lokacin sai abun ya koma in na samu ya'ya na. In na samu dan'uwa da muka fito ciki D'aya sai had'uwa ta yi wahala abubuwa suka yi ta faruwa batare da Sanin junansu ba.
Alhaji Tanko shi ya gaji Alhaji Mammandi wajen saka huluna da Aikin hannu na riguna Darajar Mammandi kona yasa shima sana'ar ta karbesa sosai. Babanmu kuwa d'an boko ne tunda tun alokacin sai dai ya yi NCE. Sannan ya fara kasuwancin saida taki, tare da Dillanci sai da Filaye da kuma kama Hanyar gona in za'ayi Noma. Da wannan sa'anar ya yi karfi kuma da ita ya yi aure da mahaifiyar mu. A rugar da ke Gadan mallam Mamman ya ganta Farar Doguwar bafullatana da bata jin eh na ko da ilimin boko da arabiya, yana ganinta ya ji kuma ya gani ya na so. Sun je du ba wata gona ne ta wajejen ya ganta tana tallar Nono shikenan ya ga mata.
Amma a gidan auranta ta samu ilimin addini da mu'amala da mutane, Marainiya ce daga ita sai ya yarta Hannatu_Hari Adda. Sai baffan su da ya rike su ya rasu shekarun baya.
Mu dai mun taso mun bud'e ido mun ga rayuwarmu cikin gata da jin dad'i. A anguwan alkali na bude ido na ganmu muna rayuwa cikin gidan mahaifin mu tare da mahaifiyarmu da muke kira Amma da Sauran yan'uwana. Mu hud'u Amma ta Haifa Adda Rukayya ce Babba sai Adda Fati, sai ni Hasiya da Amma ta ce sunan kanwar baba ce da ta fad'a rijiya ta rasu aka maidamin. Sai Habiba da ita ce karamar mu.
Tun tasowar mu bamu san wani wahalan rayuwa ba har mota babbanmu ya mallaka sannan daidai gwargwado za'a sakamu cikin masu rufin asiri.
Na taso naga kowa a dangi na son mu da kaunarmu. Na kuma san babban mu ya rasa wasu daga cikin yan'uwansa ammh na san Alhaji Tanko Baban mu ne,Sai Goggo Halima dake aure a garin Lagos, muna kiranta Baaba. Na kuma san gidan Baba saminu da ke Limancin kona gidan da bayan Rasuwar mahaifiyarsu Lauratu suka gyara shi Baba Saminu ke zaune aciki da iyalansa.
Baba Jibril kuma yana garin kaduna yana aiki chan ya ke zaune tare da iyalansa. Tunda muna zuwa in aka yi haihuwa ko auren. Amma ta fi zuwa anguwa da ni, ni ma kuma tun ina yarinya ina da son yawo duk inda za'a je sai na saka Rigiman sai an je dani. Ko da muka taso kakarmu Salme ta rasu.
Amma tace auran su ba jimawa Allah ya yi mata rasuwa. Lokacin da na taso ba ni da wayau bansan me ake kira da rayuwa ba shiyasa ban taba kawo ma kaina a dangin Babbanmu kowa kansa ya sani ba Daga kafa sai kauri. D'ana nawa ne D'anka kuma na ka ne.
Doguwa ce ni sambal ba ni da kiba kamar a hureni na fad'i ne.
Ammaa na biyo har ta farar fatarta domin jajir take to ni har na fita Fari ma.
Kaf a dakin mu na fi su fari su kuma sun biyo Duhun Fatar babbanmu sai suka Sirka ammh ni Farina har yana Daukan ido, mutane in suka ganni sun sha tambaya ko iyayena Zabiya ne? Suna tunanin kalan Fari na kad'an ne ya rage ban zama zabiya ba.
Ga ni ba kiba sai farin kawai da Doguwar Fuska sannan ina da ga shi, wanda sai daga baya na same shi Amma tace ina yarinya kaina kwaikwai ne duk su Fati sun fi ni sumar gashin kaina ammh daga baya da na Fara girma sai duk nazo na Kire su sumar kai da cika.
Wani abun mamaki kuma komai na jikina karami ne kafafuwana sanda ne sirara, haka hannayena da kaina kamar kwai in ji su Adda Fati.
Na san mun samu ilimin zamani da na addini daidai gwargwado. Ban san wahala ba kuma ko labarinta ban taba ji ba, sai shekarar da na kamallah karamar sakandiri gobara ta tashi a gidanmu da komai sai da ya kone dagamu sai kayan jikin mu muka fita da shi. Daman Amma ta taba bamu labarin Ranar da ta haifeni gobara ta kama Dakin da Babbanmu ke ijiyan Takinsa ba'a fitar da komai ba. Dalilin wannan gobaran ma ya tafka asara mai yawa. Ban taba kawo kaina gobaran da ke faruwa da mu na da alaqa da ni ba, sai da bayan Baba ya kama mana Hanyar wani gida yana ta fad'in tashin neman yadda zai yi tunda asarori ya tafka ba kad'an ba. Wata gobarar ta kara tashi a inda muka koma,shi dai Allah ya takaita Daki d'aya ta ci wato dakin Babbanmu itama ta lashe kudad'e da wasu takardun filaye. To fa daga Lokacin aka fara mganganun a nemi taimako ana tunanin ko Aljananu ne.
Babbanmu duk ya toshe kunnewansa daga mganar mutane ciki har da yan'uwansa. Sai ya kasance Gobara ta zame mana jnin jiki. Ba'a daukan wata uku gobara bata Lashe wani abu na Kudi ko kaddara ba kuma arasa ta ina Gobaran ke tashi. Tun ana Fad'i daga nesa har ya zo kusa ballatana da karayan arziki ta samu babbanmu komai da ya mallaka sai da ya kare ya dawo gida ma yana jinya ciwon kafa haka kurum ta rika Duran ruwa ta kumbura fita ma ya gagaresa.
Ni bansan daga ina mganar ta fara fita ba ammh na san rana tsaka na zama abun gudun mutane da sunan cewa ina da Farar kafa haihuwata ita ce silar Komai sannan duk in da nake gobara bazata daina tashi ba. Sannan baza'a daina saran dukiya ba. Daga karshe ma har da rai sakamakon rasuwar babbanmu sai mganar ta fito fili kowa ya jita. Da rasuwar babanmu da Ciwon Amma duka acikin shekara d'aya komai ya faru. Da kuma tsarwatsewar rayuwarmu daga sama zuwa kasa. Tsangwama da Hantsara ba bu wanda ba mu sha ba a wajen Dangi da Mutanen gari ba duk saboda ni, Naman jikina ma sun ce ba mai kyau ba ne jini na ba jinin alheri ba ne.
Dalilin da yasa zama a ganuwar zariya ya gagaremu muka koma Samaru da zama a gidan haya.
Ba'a dogon gida muka fara zama ba sai da muka zauna a wani gida dake Anguwa y'an Randa, shima watanmu biyu akayi gobara maigidan ya tadamu, sai muka koma layin tsamiya Dogon Gida.
Fad'in irin fad'i tashin da Amma ta yi bazai fad'u ba, tana halin ciwo yau ciwo gobe sauki ta rika sana'o'in hannu domin inganta rayuwarmu. Ta yi saida abinci alale, Alkubus, Danwake da kayyyakin gidajen na mata duka Amma ta yi shi tunda Dangin Babbammu sun gujemu saboda ni kowa ya ce bazai Dauki bala'i ya kai gidan shi ba.
Kafin mu samu gida a samaru gidan Baba Saminu muka zauna Satin mu daya ya koremu saboda Gobara ta tashi a kitchen ranar ya ce Sanadina ne.
Tundaga lokacin Amma ta tsame kanta da mu daga rab'ar zuru'armu. Da taimakon Amma da kuma Jajircewan Adda yayar Amma muka cigaba da rayuwa, bayan Amma ta gama Saida komai na gadonta Adda bata barta haka ba taimako daidai misali tana kawo mana. Komai a ke fad'a a kaina Amma bata yarda ta kan ce"Hasiya ki kwantar da Hankali Canfi karya ne kambun baka Annabi ya sanar da mu. ba bu farar kafa ba bu maita"
Tun kalamanta na tasiri har suka Daina min tasiri na Fahimci da gaske dai ni Hasiya ina da Farar Kafa. Abubuwa sun yi san yi da Had'uwar Amma da Inna talatu a Dogon gida ni kuma muka kulle da Diyarta Ramatu sannan tun dawowarmu sai gobara bata kara bin mu ba, Na samu na cigaba da makarantar gwammati Adda Fati ce gwammati ta biya ma Neco. Adda Rukayya daman ta gama ita. Amma bata kwanta ba tana sana'ar sai da Danwake da wake da shinkafa da wake da mai da yaji kuma tana samu tunda ga Adda fati na tayata,nima kuma ba ni da kiyuwa ina da son aiki.
Da farko rayuwar ta juya mana baya ammh daga baya sai ta waiwayo mu. Adda rukayya ta samu miji mai hali ma'aikacin gwammati. Sai da mganar aurenta ne Amma ta nemi dangin su Babanmu suka shiga mganar, muna tunanin In Adda Rukkya tayi aure zata ji kanmu ashe ba haka ba ne.
Shanun Adda aka saida akayi mata yan kayan Daki tare kuma da sana'ar Amma na ba dare ba rana.
Adda Rukayya ta na da wani Hali bata da son yan'uwa kuma bata da Kulafacin uwa ballatana damuwa da Halin da muke ciki,bkomai daga bangaranta ba ma samu tun Amma na Damuwa har ta daina ni daman ban wani shaku da ita ba, tunda ta sha Hantarata da mai Farar kafa har tab'a ce min tayi"Wannan Farin fatar naki ba na banza ba ne. Yanzu haka na tsiya ne da Talauci."
Sai da Adda Fati ta yi aure ne sannan muka san taimakon daga bangaran gidan surukai, Habibu mijinta Bakanike ne, kuma yana da Rufin asiri yana sonta,shiyasa mu ma ya ke rikemu da Daraja alherai kala kala yana yi mana sai godiya.
Adda Rukayya kuwa ba ta ma Dauke mu da Daraja ba ballatana shima mijinta da Danginsa su darajamu. Mijinta ma kwata kwata zuwansa gaida Amma bai kai sau biyar ba. Kamar ma kyama muke ba shi. Ni ko daman Adda Rukayya ta sha fad'in ni ce na saka Baba ya rasa komai na shi muka talauce kuma kafin mutanen gari su fad'a masa ita ta gayamasa. Shiyasa bai taba amsa gaisuwata ba acewarsa irin mu ko mgana da Fatar baki ce sai ya bi mutum ya Lalace.
Bazan ce ban da mu da karatun boko ba,ga yanayin da mu ke ciki yasa ban zurafafa ma kaina sai na yi karatun boko ba, Na san na iya karatun Hausa da Rubutu sannan na iya karanta Turanci iya inda zan iya, Karatun addini kuma ban zurfafa ba,na yi islamiya a anguwan Alkali bayan dawowarmu Samaru na shiga makarantar Dare ta mallam Habu tare da Ramatu na san addinina daidai gwargwardo.
Sallah da yadda zan gyara ibada ta gabadaya da sanin hukunce hukunce tsarki da sallah,sanin abu mara kyau da mai kyau, sannan ina iya karanta bakin karatu a duk in da na ganshi.
Tun tasowata bazan ce ina da Farinjini ba, ballatana ga yanayina ba kowa ne in ya ganni yake jin ina Burgesa ba ko kawa ban taba yi ba sai akan Ramatu shiyasa har gaban Abada na ke jinta a raina. Sannan na ke sakata cikin farkon Farkon jerin masoyana. Ko a cikin dangin mu ana Hantara na ballatana ga jama'ar gari shiyasa kasancewa ta, mai farin jini bai dameni ba. Ban san me ake kira Saurayi ba sai dai in ga ana zuwa wajen Ramatu ni kuwa bai dameni ba na fi damuwa da lafiyar Amma tare da sana'o'in da muke yi domin rike kanmu.
Amma ciwon ta ba shi da suna ko sanadi, ta fara shi daga zazzabi mai zafi sai kuma karkawa da ciwon kai mai tsanani da abun ya yi girma sai ya ke had'a mata har da Ciwon duka gabbanta,kafa, Hannaye, baya da sauran su in ta farashi kamar bazata ta shi ba, sai an kai ta asibiti an mata allurai da ruwa sannan ta ke dawowa hayyacinta. An yi gwaje gwaje har an gaji an rasa gane sanadi ko ciwon, mgana D'aya ce Typoid da Maleria ne, ammh kowa ya ga yadda Amma ke jin jiki sai ya ce ciwonta ya fi karfin maleria. Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login