Showing 15001 words to 18000 words out of 93195 words
Chapter 6 - Tsaka Mai Wuya Complete Hausa Novel By Janafty .txt
sosai ban zauna nayi kuka ba, ko hakurin Adda Fati da Ramatu suka rika ba ni, ko a fuskata ba su ga alamun na damu ba.
Duk da mgana ta zaga gari har gida ake zuwa da sunan yi ma Amma jaje, saboda kawai a ganni a fita ana nuna ni, a dangin Babanmu Baaba ce kad'ai ta lagos ta kira Adda fati suka yi mgana. Tace Goggon Kona ta fad'a mata aurena ya sake mutuwa, Kuma ta saka bayan Adda Fatin ta zo gida ta mata Flashing ta kira suka yi mgana da Amma.
Nima an bani tayi ta ba ni baki, Sai Baba Saminu da ya zo da safe Ana sati da abun ya share kafa yana ce ma Amma abun nan fa ya yi yawa,ya kamata a nema min mganin Farar kafa har da na maita ma.
Amma kamar ta yi kuka cikin Dauriya tace"Hasiya ba ta da Farar kafa, sannan ba ta da maita. Ba ta gaje ta ba, ni ba mayya ba ce sannan uban ta ma da Maye ne da kun sani"
Kalaman Amma yasa ya fara kame kamen mganganu kafin ya yi mata sallama ya shura takalmansa ya fice. Ranar Amma ta sha kuka, ni kaina mganar tasa ta dakeni Maita fa? Zargin maita ai abu ne mai wahalan sha'ani.
Saboda damuwar da na ga Amma ta shiga yasa na ce mata mu koma ga sana'armu tunda dai komai ya wuce, Da ya ke jarin duk ya lalace saboda sha'anin bikin nan, sai muka fara da Danwake ,shinkafa da waken sai zuwa gaba in jarin ya tarfu sauran siyayyan rogo da dawan ma Habiba taje kasuwa ta siyo komai ni ba ni da Damar Fita, Tunda in dai na fita sai na zama abun Nuniya.
Ni na ke jefa Danwaken Amma na taikamin da zubawa, kuma ana ciniki sosai, Saboda matan gidanmu suna siyan ma ya'yan su har da mazajen su.
Da kuma makota tunda a irin gidajen da muke zaune ba kasafai akan Dora abinci ba yawanci an fi siyan irin su Danwake da Shinkafa da wake na Saidawa sai su awara a samu a ci a sha ruwa.
Duk da ina nuna komai ba komai ba ne ni kada'i nasan Halin da na ke kwana ina tashi, Kirjina suya ya ke yi ji na nake yi kamar ba ni da Sauran amfani,ammh in na Tuna Amma sai naga ina da amfani a wajen Amma bayan ni bata da kowa.
Salisu na raina, ba ni da in da zan samu labarinsa shiyasa na ke masa addu'an Allah ya bashi lafiya ya dawo da kafafunsa cikin koshin lafiya.
Habiba sai asabar da Lahadi take zama a gidan ranakun Sati kuma tana zuwa makarantar Boko da Safe, da yammah kuma taje islamiya, da Daddare kuma ta je makarantar Dare.
Shiyasa yawancin ayyukan gidan suna kaina, Daman kula da Amma ni na Daukeshi a wuyana da kaina ina Kafa kafa da lafiyarta fiye da tawa lafiyar.
Adda Rukayya sai sati uku da Faruwar abun ta zo gida tana ta yamutse yamutsen Fuska tazo ta sameni ina Dafa shinkafar yammah, tunda mun fara satin da ya shige lokacin da ta shigo ina kofar Dakin Amma ina gyaran shinkafa.
Sama da kasa ta kalleni ba ta tankani ba sai ni ce na yi mata mirmishi ina fadin"Adda Rukayya ke ce tafe?Sannu da zuwa."
A saman lebe ta amsani ta rab'ani ta shige ciki ina jinta Suna gaisawa da Amma. Shuru na dan wani lokaci kafin naji ta ta na fad'in"Amma ya mganr da muka yi? Tunda Fati ta fad'amin Shima Salisun ya saki Hasiyar"
Kai Tsaye Amma tace"Wata mgana kenan?
Yaya Rukayya tace"Mganar tafiyar Hasiya wajen Adda Hari mana. Amma shawarar nan ita ce Mafita haka ma Baban su Amna ya ce da na Fad'a masa."
https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V
+201123302418
Ban ji me Amma ta ce mata ba sai dai naji Muryan Adda Rukayya a harzuke tana fad'in"To shikenan Amma ni mafita daman na kawo ai shikenan"
Ban tsaya jin sauran mganganun ba na tashi daga wajen zuwa wajen ma zubar ruwa na wanke shinkafa, acikin raina ina ta kokarin karfafa kaina, sanda ta fito ina zuba shinkafan ne cikin Tukunya.
Tunda waken Dabam mu ke dafa shi,Haka ta wuce ni Fuu ko kallo ban isheta ba ni ce na bita da cewa "A sauka lafiya"
Ina mirmishin takaici, matan gidanmu suka bita da kallo tunda duk suna waje ana hada hadan d'ora na dare, Masu d'orawan kenan irin su Maman Boy sai zaman gulma da yi da mutane tana fita suka fara kuskus ana kallona ana mgana, komai za su Fad'a bazan damu ba tunda sai bango ya Tsage kadangare ke samun wajen shiga.
Sai da Ramatu ta leko ni Daga awo take tazo Dubani, a bakinta na ke jin Salisu an yi masa aikin an daure inda ya samu karayan Musbahu ya kirata ya ke Fad'amata kuma yadda ya ke Fad'a jikin Salisun da sauki tunda yana cin abinci sannan kuma yana mgana.
A raina na yi Hamdala a fili kuma nace"Allah ya kara masa lafiya"
Ramatu ta amsa da Ameen sai yammah ta tafi, Muna ta zencen haihuwanta tunda ta shiga wata na Tara, Har ina mata Fad'an ta daina Fita hakanan kada ta haihu a Hanya.
Muka yi wasa da Dariya na Saba Rakata har bakin Titi ta samu adaidaita ko mashin, ammh yau ban fita ba saboda ina kauce ma idanuwan mutane a kaina.
Itama sanin haka yasa ba ta damu ba Habiba na saka ta rakata har bakin Titi, tunda Ranar ba islamiyan yammah jumma'a ce.
Ba mu da matsalan abinci Tunda muna ci cikin sana'ar mu, dagani sai Habiba Amma ce ta kan bukace koko ma wani lokacin amm ni in na ci Danwake na da Safe sai wani Daren kuma inna ci sauran Shinkafan da na kan rage mana ni da Habiba, Amma koko na kan Damata da Daddare ta sha, da Safe kuma wani Lokacin Add Fati na kawo mata kayan tea. Bata cika sha ba, in dai ba duka Zan had'a mana mu sha ba.
Ranar asabar da Safe ina Hada had'ar kwabin Danwake sai ga kiran Adda Fati ta wayar Maman boy, sai da gabana ya fad'i da Maman boy ta kawomin sai dai Hankalina ya tashi da naji ta na Fad'amin Ramatu ce ta kirata taje asibiti tun jiya maranta ke ciwo to sun Riketa sun ce Haihuwa ne, tana asibitin Abu na Tudun wada naje na sameta. Ina jin haka na ruga Daki na Fad'a ma Amma cikin Sauri tace"Maza ki hanzarta ki je ki sameta. Allah Sarki Ramatu Allah ya raba lafiya"
Cikin Saurin na Sauya kaya ko wanka ban tsaya yi ba, Habiba na bar ma kwabin Danwaken tunda ta iya cikin kudin Ciniki na Dauki 1k na mota na Zurma hijabina har kasa mai ruwan kasa,Fuskata Fuskata kozai kozai haka na fita Maman boy har ta gama yee kuwa da mganar sai fad'i suke yi Allah Sarki Ramatu Allah ya Raba lafiya.
Sai ga shi har na kai bakin Titi ina ta Faman rufe fuskata da Hijabina, adaidaita na samu zuwa Pizzet, Dagachan na samu na Tudun wada,na sha wahala kafin na gano Ramatu. Haihuwa ce ammh sai zuwa Dare sukace sun dai riketa ne tunda Maran na Damunta nayi mata sannu ta amsani cikin yanayin ciwo.
key din gidanta ta bani tace na je na kwaso kayan haihuwan da ta had'a acikin karamin akwatinta,vsai zannuwa da zan Dauko mata. Sai Fulas da Filo da kayan tea duk ta ce na Dauko. Sauri Sauri ko na sake hawa mashin naje na Dauko mata komai da komai na iske Fulas din cike da ruwan zafi Daukowa kawai nayi, kayan tea din kuma a kitchen dinta na gani na kwaso su duka.
Tunda Nura kam ba abunda ya Rage Ramatu da shi.
Sanda na dawo naguda gadan gadan,ina asibitin Inna talatu tazo bata jima ba tatafi, tunda kannen Nura da mahafiyarsa sun zo duk muna tare da su,bRamatu ta sha wahala sosai Nura baya nan sun tafi aiki Abuja Hankalinsa duk ya tashi yana ta kiran kannensa a waya domin jin ko ta haihu? ba ita ta samu bud'e ido ba sai Dare misalin goma.
Ni Daman ban ma yi tunanin komawa gida ba,hankalina bai kwanta ba sai da Nurse ta fito tace Ramatu ta sauka an samu y'a mace sannan ni da kannen Nura muka saki Hamdala.
Cikin lokaci kalilan Labarin Haihuwar Ramatu ta yi Tambari ni dai ba waya a hannuna ammah na san Inna talatu ta Kira Adda Fati, ita kuma zata sanar da Amma ko ta wayar Maman Boy ne.
Ni nace ma Kannen Nura su tafi gida ni na kwana da Ramatu ,sai Daukan bby na ke yi farinciki ya cikani Yarinyar mai kyau da ita, gaskiya jarirai na da ban sha'awa Ramatu sai Faman dariya ta ke yimin, duk ta rame Lokaci d'aya lalle Haihuwa yakin mata.
Ranar asibitin ya cika da Mutane Dangin Nura, shima adaran ranar ya Dawo, Bakinsa har kunne ni kuma ina masa tsiyar angon karni yana kwasar Dariya,komai da zamu bukata Nura ya siyama na. Sannan abinci daga gidansu Nura ake kawo mana Tunda suna Wajen Danmagaji ne.
Ramatu tayi ta yi naje gida na yi wanka nace mata bazani ba sai ta kyaleni, Washegari sai ga su Inna talatu har da Adda Fati da Amma, bakina ya ki rufuwa ganin Har da Amma akazo.
Zuwa chan kuma sai ga mutaan gidanmu Maman boy ce Jagoran su. Sun jima sai yammah suka tafi Amma ta zo min da kaya kala Biyu da Hijabi tunda tasan gidan Ramatu zan wuce,vkamar ko ta sani a daran aka sallame mu muka koma gidanta,Sai bayan suna zata koma wajen Inna talatu ta yi jegonta.
Ramatu ba kawa ba ce a wajena yar'uwa ce shiyasa komai na yi mata ban Fad'i ba, kan jikina na ke Hidima da ita ko ruwan wankan ta Safe da yammah na Dauke ma Kannen Nura ni nake yi girki ne suke taikamin wani Lokacin, ammh har wankan Bby na iya sai dai Kanwar maman Nura ke zuwa da Safe ta yi mata wanka Ramatu kuma Amma ce yakamata ta zo ta yi mata to bata da lafiya sai aka Dauketa mata,wata abokiyar wasan Ramatu ke zuwa ta yi mata Safe da yammah.
Ni kuma na ji da yan wanke wanken kayan Ramatu da baby, Nura kam ya shirya ma Ramatu sunanta daidai karfinsa, Shinkafa aka Dafa da wake Jalop,har da zobo Ramatu ashe ta yi mana Dankin wata Atamfa Cinghamvi, iri d'aya sai dai na yi hawaye,ita na saka na ci suna ba ni da Dan kunne da Sarka nata ta bani na akwatinta da ya rage guda d'aya bata yi amfani da shi ba. Na fito tsab da ni nima ina walwalina ni ce kuma kan komai na abincin, Adda Fati tun Safe tazo nan ta kwana ita da kanwar Inna Talatu Rahane daga Soba tazo.
An yanka Raguna Guda Biyu Yarinya taci sunan mahaifiyar Nura, Khadija Ramatu tace zamu rika kiranta Noor haske.
Washegari su Adda fati suka yi soye aka raba naman gida uku kashi Daya na dangin Nura D'aya kuma na Nura da Ramatu,D'ayan kuma na danginta, duka Ramatu tace kashi d'ayan a kai ma Inma talatu ta ba wa wad'anda suka kamata cikin na su ta Dibarmin nawa, sai da ta kwana Goma ta koma sabon gari gaban Inna talatu sai na rakata har chan sannan na wuce gida da sha tara na arziki daga Ramatu da mijinta.
Atamfa ta bani tare da su manshafawa, kayan kwalliya takalmi Sabulan wanka da na wanki, Hijabai kala biyu sabbi,ta kuma had'amin da kayan abinci tace na kaima Amma tunda gida zata koma kuma daidai gwargwardo sun fi mu rufin asiri. Nura kuma Dubi biyar ya bani nayi ta godiya har ina kwallah da na koma na nuna Amma itama tace an kawo mata nama mai yawa da yajin jego har da Fallen zani da Omon wanki.
Amma ta kalleni bayan ta gama Daga kayan da na zo da su Habiba ta Dauki Hoda da Jan baki tana fadin"Adda Hasiya ni dai ina son kayan kwalliyar kin ji don Allah"
Ina mirmishi nace"Ke daman nace zan ba ma wa dauka Habi"
Ta fara tsallen Murna muna yi mata Dariya ni da Amma. Dubi biyar d'in da Nura ya ba ni na mikama Amma ina fadin"Amma sai mu kara a jarin shinkafa ko?
Amma ta ki karb'a Lokaci daya tana Fadin"A'a kudin ki ne, ki rike a hannun ki Hasiya"
Ban samu zarafin mgana ba mukaji Ana maraba a tsakar gida, kamar Muryan Adda hari na rika ji sai da Habiba ta fita sai ga ta ta shigo da Buhu a hannunta bakinta har kunne tana Fadin"Adda ce da Badd'o'
Amma ta washe baki tace"Harin ce da yamman ne? Maraba da Hari ta Jari"
Hakan ta kan Fad'a daman Saboda chan Gada kowa da haka ya san su,in aka ga Amma ace mata Jarin Hari, in kuma aka ga Inna sai ace mata Harin jari.
Adda Hari bakinta har kunne Saboda Murna ni kaina murna duk ta cikani Yarta autarta Badd'o kuwa haka ta nade jikin Amma ta na mata oyoyo da Gurbattacen Hausanta,Tunda su sun fi jin Fullanci hausan na su sai a hankali ko Amma da zama ne ya yi zama bakinta yaji Hausa, ammh duk da haka akwai fullanci a harshenta mu kam mukan ji iya sunayen abubuwa da baza'a rasa ba.
Amma ta kasa zaune ta kasa tsaye,Sai da suka yi sallah suka natsa Ruwan zafi na dafa musu suka sha Tea da Buredi sannan aka zauna saman Hira bayan Inna Hari ta kwance Buhun tsarabanta,su Daddawa ne sai Fura da Nono da manshanu,sai garin kuni da yawa,Amma nata godiya ina tayata Habiba da Baddo na gefe suna ta shan Hira.
Adda Hari bata sako mgamar aurena ba ko kad'an ba Duk da Amma ta kirata ta wayar Adda Fati ta fad'amata mutuwar aurena da Salisu. Daman tace tana tafe in ta samu dama sai da Safe ta yi ma Amma zencen Lokacin ina waje ina Hidimar danwake, Habiba da Baddo suna taimakamin da Zubawa suka yi mganganun su adaki da yar'uwanta sai da muka gama na koma Daki sannan Adda Hari ta kirani nazo gabanta na zauna Kaina ta Dafa kafin tace"Ki kwantar da Hankalin ki Hasiya. Babu wani farar kafar da kike da shi, sannan ke baki gaji Maita ba. Watarana sai labari haka Allah ya Tsara" na kalleta ina gyad'a mata kai Duk da tana cikin Rugga Adda tana da iliminta daidai gwargwardo.
Sun cigaba da mgana da Amma duk a kaina ni ko ina chan gefe ina gyara kayana, ina ji Amma na fad'ama Adda Hari mganganun Adda Rukayya.
Adda tayi Dariya kafin tace"Kyaleta Jari. duniya ce zata gayama Rukayya gaskiya. Mganar Hasiya kuma ni kin ki min ne Jari da Tuni ta na hannuna."
Amma tace"sai dai ki dauke mu gabad'aya"
Inna Hari na Dariya tace"Duk zan iya da ku kin sani. Tun yaushe na ke hakilon ki dawo wajena?
Amma ta kad'a kai kafin tace"Saboda yaran nan ne Hari"
Inna Hari tace"Yara suna ina? Fati na gidan mijinta Rukayya ma haka. Hasiya da Habiba ne kuma na ce dukkan ku zan iya rike ku jari zaman ki anan bai da wani amfani ga shi ba ki da ishashiyar Lafiya.
Hasiya ce kuma kinga ga irin jarabawarta in zaki amince duka sai mu tattara mu koma da ikon Allah Hasiya zata yi auranta achan ta kuma zauna lafiya"
Amma ta yi shuru ba ta yi mgana ba ni kuma saboda ba da ni ta ke mgana ba yasa ban saka musu baki ba. Ammh ni kaina zan so mu koma chan da Rayuwarmu kila Hankalin mu zai fi kwanciya.
Adda Hari sati tayi mana sannan ta koma, kafin ta koma na rakata gidan Inna talatu ta yi ma Ramatu barka da yar Dubunta tace a siyama Noor kwalli, Sannan har gidan Adda Fati mun je itama tazo ita da mijinta sun gaisheta Adda Rukayya ce bata zo ba kuma bata kira waya ba, sannan ba wanda ya damu da ita. Cikin Dubi biyar din da Nura ya ba ni na cira 1k na bama Baddo, Adda Fati ko 8k ta kawo ma Amma tace a bama Adda Hari tayi na Mota sannan ta siyama Baddo kayan kwalliya da Hijabi.
Adda Hari ta koma akan Amma tace in ta shirya zata kirata tace ita ba ta da matsala.
Sauran Dubu hudu kuwa saka na ba ma Kultumen gidanmu tunda sana'arta ne, ta sakama Noor Huluna guda hud'u masu kyau, da ta gama naje da kaina na kaimata duk da sai da ta yi min Fad'an me yasa na kashe kud'ina? Na harareta ina fadin"Bansani ba"
Dariya ta yi har kuma a ranta taji Dadi, shi alheri komai kankantar shi yana da dadi sosai.
Kwanci tashi babu wuya a wajen Ubangiji, Har Ramatu ta gama jegon arba'in ta koma gidan ni naje na yi mata kwana biyu na tayata gyaran gidan,sai da Nura ya dawo sannan na koma gida Amma jiki ya yi kyau tunda in ba na nan ita ke Danwake,da yammah kuma ta yi shinkafa da wake, Mganar komawar mu wajen Adda Hari kuma ta sha ruwa tunda har Haya naji Amma ta yi ma Adda Fati mganar sake biyan na shekara. Wannan D'akin dubu Talatin muke biya duk shekara.
Tunda naji haka sai na cire ma raina Sauyin muhalli na kuma san dalilin Amma na kada ace da gaske zargin da ke kaina Shiyasa muka bar gari, tana danne komai ne saboda ni.
Adda Rukayya sai bayan Tafiyar Adda Hari tazo ita da ya'yanta kuma ma aranar sai da ta kara yi ma Amma mganar nan dai Amma ta kalleta ido cikin ido kafin tace"Ke Rukayya ki fita idona. Na ce ki fita idona na rufe ina ruwan ki da Hasiya ko akan ki take? Kina ci da ita ne ko kuwa akwai abunda kika Dauke mata ne da kika Kwazzabi kan ki sai ta bar miki garin nan ne?
Sai Adda Rukayya ta Fara kame kame Ran Amma ya baci ta nuna mata kofar fita tana fadin"Daga yau sai yau in dai kin san mganar Hasiya zata kawo ki to na gode ki zauna gidan ki ba sai kin zo ba, da ke ko baki zamu cigaba da Rayuwa Rukayya shi ruwa